Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 53

9K to 12K   out of 157.3K words

zuwa ?arfe goma an gama komai za ta saka a dawo da ke gida."

Bata ce komai ba sai idanunta da ta Wauke daga kan fuskarsa. Ta Wan kalli Bintu da tun fara maganar Hafiz take haske shi da murmushi, ta Wan girgiza kai ta yun?ura da nufin kai hannunta ta buWe ?ofar baya na motar don ta shiga ta zauna.

Da saurin gaske Hafiz ya riga ta kai hannu ya buWe mata ?ofar. Sai da ya tabbatar ta gama daidaita zamanta sannan ya sake yi mata a dawo lafiya ya maida ?ofar ya rufe.

Gurin matarshi da take zaune a mazaunin direba ya ?arasa da murmushi a fuskarsa yake sake bata ha?urin ?ara Sata mata lokacin da aka yi.

Har wannan lokacin murmushin da take yi bai bar kan fuskarta ba. A tausashe ta amsa mishi da cewa
"Kar ka damu My Dear. Komai zan iya yi don kai kaWai. Bayan haka ma Innaye ta wuce komai a gurinmu, zan iya jure fiye da haka saboda ita."

?aunarta da ganin girmanta ne ya ?ara cika mishi zuciya, bai iya mayar mata da za?a?an kalamai ba saboda Innaye da ya san tana saurarensu illah cewa da yayi a ta?aice
"Na gode"
Sai ya ja da baya ya Waga hannu yana mata bye-bye ita kuma ta tayar da motar yana tsaye yana kallonsu har ta fice daga gidan bayan mai gadi ya wangale mata get.

Daga nan tsakar gidan, kai tsaye Sangaren da aka sauki Innaye ya wuce. Babban burinsa ya Wan sassaSa ma Zulaikha kamanni kafin Innaye ta dawo gidan.

Wani rashin sa'a da yayi shi ne yana murWa hannun ?ofar sai ya ji an rufe ta ciki.
"Ke! Ke!! Ke Zulai?"
Ya kira ta da sunan da shi yake faWa mata cikin tsawa. Kafin ta amsa ya cigaba da magana cikin hargagi
"Me kike yi a cikin Wakin har da rufe ?ofa? Zo ki buWe min ?ofar nan yanzun nan tun kafin in shigo ciki in same ki."

?irjinta ne ya buga daram! Tana jin shi, amma ta sake yin luf akan gadon ko ?wa??waran motsi ta kasa yi.
'Tun jiya ta san a masifar ?ufule yake da ita, sanin halinsa na mugunta musamman a kanta yasa sam bata so tafiyar Innaye asibiti ita a barta a gida ba.

Daga yadda ya daka mata gigitaccen tsawan da yasa ta baro Innaye a gurin mota ba tare da ta jira ta ga tafiyarsu ba. Ta ?ara yarda ma kanta lallai akwai wani mugunta da Yayan yake kitsawa a zuciyarsa game da ita, shi yasa ko da ta koma Waki ta shige ciki har ta zauna tana matsar ?walla sai kuma ta tashi da sauri taje ta rufe ?ofar ta murza Wan makulli.

Shi da kanshi ya nuna musu yadda ake kulle ?ofar ranar da suka je gidan, ya kuma ?ara musu da bayanin idan suka kulle ?ofar suka bar mabuWin a jiki to ko daga waje wani ya je da irin makullin zai buWe ?ofar bazai taSa buWuwa ba.

A sadda yake musu wannan bayanin, bata Wauki abin da wani muhimmanci ba, kawai dai ta saurare shi ne ba don ta wani ba bayanan nashi muhimmanci ba. A ganinta, cikin wannan ?aton gidan, kuma a unguwar masu kuWi da tun a ?ofar shigowa layin sojpji ne masu gadi wani abin cutarwa ne zaiyi gigin kawo musu farmaki? Ai kura ma ta san gidan mai babbar sanda. Ko ?ananun Sarayi ?an kuci ku bamu irin waWanda ta sani a ?auyensu da waWanda take ji a labarai sun san irin gidajen da suke shiga suyi sata ba irin na Yayanta ba.
8)




Shi yasa daga ita har Innaye basu taSa kulle ?ofar da makulli ba, ko wani dare da sun tura ?ofar a haka suke barin t...'

Da saurin gaske ta dawo cikin hayyacinta lokacin da ta sake jin muryarsa yana mata magana cikin faWa da Waga murya.

"Zulai? Baza ki zo ki buWe min ?ofar ba ko? Na san kina ji na. Na rantse da girman Allah idan kika bari na Wauko safayar makulli na buWe ?ofar Wallahi na lahira sai ya fi ki jin daWi. Gara ma tun wuri ki buWe in kora miki kashaidi da jan kunnen da zanyi miki a wuce gurin tun kafin in buWe ?ofar da kaina."

A karo na biyu ?irjinta ya sake bugawa daram! Ta zazzaro idanu a tsorace hannayenta biyu dafe da ?irjinta. Tsoron ta Allah tsoronta ya buWe ?ofar da kansa yayi mata mugun bugun da tunda uwarta ta haife ta ba'a taSa yi mata shi ba. A raunane ta yun?ura da nufin tashi taje ta buWe mishi ?ofar sai kuma ta sake tunawa da yadda yai ta jaddada musu idan suka kulle ?ofar suka bar makulli a jiki babu wanda zai iya buWewa daga waje.

Ajiyar zuciya mai sanyi ta sauke. Ta sake komawa tayi la?was akan gadon tana jin kwanciyar hankali kaWan akan fargabar da ya lulluSe ta.

Daga can waje shi kuwa bai fasa buga ?ofar yana zazzaga mata masifa da shan alwashin irin dukan da zai mata idan ta bari shi da kanshi ya buWe ?ofar.

"Ai kuma sai kayi."
Ta faWa ?asa-?asa yadda ta tabbatar bazai taSa ji ba.
"Ta Allah ba taka ba, idan ka buWe kar ka barni da rai."
Ta sake faWa a hankali tana murguWa baki kamar yana kallonta.

Ita kam ta rasa dalilin wannan ?iyayya da Yayanta yake mata. Kamar ba ciki Waya suka fito ba? Ta ja tsaki ?asa-?asa.
"Duk abinka dai baka isa ka canja ni a matsayin ?anwarka ba."

Ta sake faWa idanunta na kawo ruwa tana ?o?arin mayar da su ba. Da taji bugun ?ofar ya ?i tsagaitawa yatsunta manuniya guda biyu tasa ta toshe kunnuwanta da ?arfi, har ya gama hargaginsa ya wuce a gurin bata sake jin Wuriyarsa ba.


******


"Innaye minti biyu don Allah, zan shiga gidan Raudha in karSi wasu sakamakon gwaje-gwajen marasa lafiya a hannunta. Yanzu zan fito, ki jira ni a cikin mota."

Ko kafin Innaye ta amsa har ta buWe ?ofar motar ta fice, da makullin hannunta tayi amfani wajen kulle motar ta waje sannan ta shige cikin gidan da ta kira na Raihana.

Fiye da mintuna arba'in ta Sata a cikin gidan bata fito ba. Tun Innaye tana zaman daWi har ta koma yin na wahala, kasancewar gilashin Sangaren da take zaune kaWai a buWe, kuma shi ma Wan kaWan ne a buWe, shi yasa shige da ficen iska yayi ?aranci a cikin motar.

Innaye ta haWa zufa tayi kashirSin. Kayan cikinta sai hautsinawa suke yi kamar za tayi amai duk da babu abinda ta karya da shi. Ta muskuta ya fi sau ashirin, tun tana iya fifita da gefen hijabin jikinta har tayi la?was ta zuba ma sarautar Allah idanu tana jira taga ta inda Bintu za ta Sillo.

Can bayan wasu mintuna goma sha biyar sai ga Bintu ta fito daga cikin gidan ita da wata matashiya da baza ta wuce sa'arta ba suna magana suna dariya. A ?ofar falon gidan suka sake tsayawa, akan idanun Innaye suke maganar da ba ta jin me suke cewa saboda tazarar da ke tsakaninsu suna nuna motar da take ciki da yatsa manuniya suna cigaba da ?yal?yala dariya.

Don tsananin ba?in ciki da takaici, Innaye bata san sa'adda ta sunkuyar da kai wani zazzafan hawaye ya silalo daga cikin idanunta ba. Da saurin gaske tasa babbar yatsa ta Wauke hawayen tun kafin Bintu da take ?arasowa gurin motar fuskarta a Waure tana daddana waya ta ga kukanta.

Kamar ba ita ne ta gama ?yal?yala dariya da Aminiyarta ba. Ta buWe baki a cushe ta ce
"Innaye yi ha?uri fa. Na Wan daWe ko?"

Innaye kasa cewa komai tayi, don a yadda take jin Sacin rai a zuciyarta, lallai tana buWe baki da nufin yin magana tabbas mummunar magana za ta faWa. Shi yasa tayi shiru don koyi da faWin Fiyayyen halitta SAW.

Bintu ma bata ?ara cewa komai ba ta tayar da motar ta Waga ma ?awarta da ke tsaye can nesa hannu ta figi motar a guje suka fice daga gidan.
Kasancewar gudu take da motar ba kaWan ba cikin ?an?anin lokaci ta isa asibitin da take aiki.

Izuwa wannan lokacin, Innaye da take zaune a bayan mota ta kai matu?a wajen galabaita, abu goma da ashirin ne ya haWe mata, ga yunwa, kasancewarta mutumiyar ?auye wacce tayi sabo da karin kumallo da sassafe matu?ar ba azumi take yi ba, ga gajiyar zaman da tayi a cikin mota ga zafi da ya fara taka muhimmiyar rawa gurin fara galabaitar da ita. Ga irin gudun da Bintu tai ta zugawa da motar kamar wacce za ta kai wasi?a.

Gaba Waya kayan cikinta sun takura sun dun?ule guri Waya, miyau bakinta sai tsinkewa yake yi, alamun ko wane lokaci amai yana iya kawo mata ziyarar ba-zata duk da babu komai a cikinta. Ita kaWai take sakin nishi sama-sama.

Bintu tana jin ta sarai, kuma tana kallonta ta madubin da ke gaban motar. Amma ta tafasa sauke bata ce mata don tsananin haushin tsohuwar da jikanyarta da take ji tun bayan abinda ya faru jiya. In banda hanya mai haWin zumuntar dole ta ina za ta haWu da wannan ba?auyiyar balle har wani dangata ya ?ullu a tsakaninsu?

Shi yasa a mafiyawancin lokuta take ?ara godiya ga Allah da ya kasance Hafiz Win ta bai Wauko kamannin tsohuwar ba. Da marigayi mahaifinsa yake kama, mahaifin nasa kuwa ya kasance kyakkyawan bafulatani ne amma mazaunin ?auye.

Ta Wauki tsawon mintuna biyu tana ?ara gyara kwalliyar fuskarta da kayan kwalliyar da ta ciro a cikin jakarta, bayan ta gama ta ciro wani farin gilashi ta ?wama a idanunta sannan ta buWe ?ofar ta fita.

Har Sangaren da Innaye ke zaune ta zagaya ta buWe mata ?ofa sannan ta ce
"Fito muje Innaye."

Sau uku tana yun?urin fitowa sai kuma ta koma ta zauna la?was! A galabaice, Bintu na kallonta amma sai ta kawar da fuska kamar ba ta ga abinda ke faruwa ba. Sai a karo na huWu Innaye tayi ?arfin halin fitowa da?yar ta tsaya bisa ?afafunta da taimakon motar da ta jingina da ita.

"Innaye daurewa fa za kiyi, saboda Allah kina gani dai asibiti muka shigo, kuma bamu taho da Zulai ba balle ta dinga Wawainiyar ri?e ki zuwa Wakin gwaje-gwaje. Ni kam muna shiga ciki Ofis Wina zan wuce don marasa lafiya na can na zaman jira na, ?o?ari Waya da zan iya miki dai shi ne zan haWa ki da ma'aikaciyar jinya Waya ta raka ki Wakin gwaji. Ina fatan dai baki ci komai ba tun bayan tashin ki da asubah?"

"Eh"
Ta amsa da?yar! tana jin yadda Sacin ranta ke ?ara hauhawa. Gefe ta kawar da fuskarta ta tofar da miyau mai yawa kwaSal, sannan ta sake mayar da fuskarta tana kallon Bintu da take aiko mata da kallon ?yama a fili.

"Haba Innaye! Wani irin ?azanta ne kike mana haka saboda Allah? Ki kiyaye pls! Nan fa asibitin birni ne ba irin na can ?auye da kika saba gani a wula?ance ba."
Bintu tayi maganar da muryar faWa-faWa kamar tana yi da ?anwarta. Sai kuma ta ja tsaki ?asa-?asa ta cigaba da cewa
"Ki jira ni anan, zan turo a shiga da ke ciki."

9)


Daman tunda za ta fito daga cikin motar ta gama tattaro duk ?an kayayyakinta, Don haka kulle motar tayi da makulli ta nufi cikin asibitin ko waige ba ta yi, zuciyarta a Wugunzume da ganin wannan ?azantar da Innaye ta tofar a gabanta, ji take kamar za tayi amai. Har ta ?arasa cikin asibitin tsaki take ja akai-akai fuskarta a Waure.

A karo na biyu, wasu zafafan hawaye suka gangaro daga idanun Innaye, da sauri tasa hannu ta share tana Wan waige-waige. Ganin babu mai kallonta yasa ta sunkuyar da kanta ?asa tana ?ara sakin nauyinta a jikin motar.

Zuciyarta cike da mamakin yadda halayen mutane ke saurin sauyawa a mabanbantan lokuta.
'Duk da shedar da suka yi ma Bintu na sanin kirkinta ragagge ne. A karon farko na zuwa da ita asibiti washe garin ranar da suka zo garin, ko kaWan bata fuskanci irin wannan tozarci da wula?ancin daga Bintu ba. Ko don a wancan ranar tare suke da Hafiz shi yasa Bintu tayi musu tarbar arziki tayi ta ina aka saka ina aka aje da su?

Da ta san a wannan karon lamarin zai sauya, tabbas da ta tilastawa Hafiz su taho tare kamar wancan lokacin, ko kuma ta matsa mishi lallai Auta tayo mata rakiya. Ga shi garin sauri da gudun Satawa Bintu lokaci yasa ta manta da wayarta a gefen gado.

Da a gaban Hafiz ne ta tabbata Bintu baza tayi mata haka ba. Ko a gaban Auta ne ta tabbata wula?ancin da Bintun za tayi bazai kai haka ba, don sam! bakin Auta ba ya mutuwa duk kuwa da yadda take yawan tsawatar mata. Ba ta taSa yin shiru musamman kan abinda ya shafi mahaifiyarta ko ?an'uwanta.

Da ace kuma ta taho da wayarta, wata ?ila da ko Waya daga cikin ?a?anta mata da suke can ?auye ta kira za su Webe mata kewa da wannan dun?ulallen Sacin ran da ya tsaya mata a wuya shi bai sauka ciki ba kuma bata amayar da shi ba...'

"Assalamu alaikum! Wai ke ce Innaye?"

A bazata ta ji saukar wata zazza?ar murya a kunnuwanta. Kafin ta amsa sallamar, sai da ta Wago idanunta ta kalli matashiyar yarinyar da take tsaye a gabanta sanye da kayan ma'aikatan jinya, lokaci guda kuma tana aika mata da wani sassau?an kallo mai tafe da rangwame.

Sallamar ta fara amsawa, kafin ta ?ara da cewa
"Eh ni ce."

"Yauwa! Ina kwana? Daman Dr. Bintu ce ta aiko ni in shiga da ke ciki."

"To! Na gode."
Ta amsa a raunane. Har ta yun?ura za ta Waga ?afarta da niyyar fara tafiya sai tayi taga-taga kamar za ta faWi ?asa.

"Subhanallahi! Sannu Innaye. Kiyi a hankali fa kar ki faWi."
Yarinyar ta jera maganganun cikin sauri a lokaci guda kuma tasa hannayenta duk biyu ba tare da wani ?yama ba ta tare Innaye daga faWuwa ?asa.
"Sannu!"
Ta sake faWa a karo na biyu.

"Idan baza ki iya tafiya ba sai in Wauko kujerar asibiti ki zauna in tura ki zuwa ciki."
Ta sake faWa a tausashe. ?arara fuskarta ke nuna yanayin tausayi da jin ?ai da ake bu?atar gani a fuskar duk wani ko wata ma'aikaciyar lafiya.

"Zan iya! Na gode Yarinya."
Innaye tayi maganar a hankali. Har za tayi shiru sai kuma ta ga kar ta cuci kanta, da alamun wannan yarinyar da bata sani ba tana da kirkin da yayi ma Bintu ?aranci. Sai ta ?ara da cewa
"Kawai dai na Wan galabaita ne da zaman mota ga kuma tsayuwar da daWe ina yi anan. Idan baza ki damu ba, don Allah ko hannuna ne ki Wan ri?a mu ?arasa ciki in samu gurin zama..."

"Laaa... don wannan babu komai Wallahi. Mu je."
Matashiyar ta katse Innaye da ta?aitaccen fara'a a fuskarta.

HaWuwar jini ne na farat Waya ya faru tsakanin Innaye da matashiyar ma'aikaciyar jinyar nan. Tallafin da Innaye ta samu a lokacin da bata taSa tsammani ba yasa tayi wani irin sakin jiki da Matashiyar kamar dama can sun daWe da sanin junansu.

Ita kuwa yarinyar kasancewarta mai surutu da saurin sabo, ga kuma ?auna ta farat Waya da taji tana yi ma Innaye yasa ta saki jiki sosai da ita, suna hanya ta faWa ma Innaye cikakken sunanta Karima Idris Madobi.

Kamar wacce ta samu Kakarta ko Yayar mahaifiyarta, haka ta tallabe Innaye suna tafe sannu a hankali da fara'a sosai a fuskarta ta ke ba ta labarin Kakarsu da ta kasance fitinanniyar tsohuwar da ta gallabi kowa a gidansu.

"Ba ma taSa samun hutu da surutunta idan ba barci tayi ba, ko kuma mu muka fita zuwa wajen aiki ko wani al'amari na daban. Ba wai ni da Yayana da muka kasance jikokinta ba fa, hatta Mummy da ta kasance Wiyarta duk mun san ha?uri take yi da al'amarin tsohuwar."

Da murmushi sosai a fuskar Innaye ta jefa mata tambayar
"In banda ke da abinki Karimatu ta yaya ?a za ta gaji da hidimar mahaifiyarta?"

"Ba'a gajiya ko Innaye?"
Ta maida mata tambayar da wata tambaya alamun ?uruciya ?arara bayyane a furucinta.

"Eh mana. Ai duk Wa ko ?a ta kirki ba ta taSa gajiya da hidimar mahaifi ko mahaifiyarsa. Yanzu ne fa lokacin nan da Allah ya ce kar ku taSa ce musu uhhmmm don wata Wawainiya ko wahala tasu da kuke yi. Sun wahalta muku kuna ?anana, ku kuma sai ku saka musu suna tsofaffi masu rauni kan rauni. Idan kuma kina tantamar abinda na faWa miki, wata rana ki gwada aibata ita Kakar taki a gaban Mamanki..."

"TaS! Ki ce in janyo ma kaina gaggarumin tashin hankali tsakanina da Mummy. Duk fa wannan wahalar da muke ganin tana yi da Hajja yanzun nan muna fara ?orafi za ta zazzage mana kwandon masifa tana faWin ina ruwanmu? Ita ta fi son Hajja fiye da komai da kowa na duniyar nan. Don haka mu ?yale ta ta hidimta ma tsohuwarta wata rana sai labari."

FaffaWan murmushi ne yalwace a fuskar Innaye tana jin matsananciyar ?aunar uwar Karima da ita kanta Karimar a zuciyarta. Suna wannan hirar ?asa-?asa, har suka ?arasa Wakin gwajin da Bintu ta umarci Karima ta kai Innaye.

Kuma da yake ita Win ?ar arziki ce bata bar gurin ba sai da aka gama duk abinda ya kamata ta sake ri?ota suka fito daga cikin Ofishin. Killataccen gurin zama da Nurses suke zama ta zaunar da Innaye, sannan ta bata uzurin tana zuwa.

A gaggauce ta wuce Ofishin Bintu ta sanar da ita an gama komai da ta umarta.
"In sh???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?igo da ita nan ne?"

"A'a!"
Bintu ta katse ta da sauri, hankalinta na kan rubutun da take yi a cikin folder na mara lafiyar da ta gama dubawa ko sararin Waga kai ta kalli Karima bata samu yi ba. Ita har ga Allah ta ma manta da wata Innaye balle

4 / 53