Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 53

66K to 69K   out of 157.3K words

ya sake yin awon gaba da ita nan kan daddumar da tayi sallah.


***** *****


?irjinta ne ya buga daram!! Ganin kiran Innaye na shigowa cikin wayarta, abinda bai taSa faruwa ba tun bayan musayar lambar waya tsakaninta da Innaye matsayinta na Uwar mijinta.

Matsanancin tsoro ne ya lulluSeta, ?irjinta ya cigaba da bugawa akai-akai. Kamar baza ta Waga kiran ba, domin duk a tsammaninta Zulaikha ce ta kira Innaye ta kai mata ?ararta.

Har kiran farko ya tsinke na biyu ya sake shigowa tana canki-cankar ta Waga ko kar ta Waga kiran? Tunanin idan bata Wauka ba Innaye za ta iya kiran Hafizu ta kora mishi kashaidi zuwa gare ta yasa tayi shahadar ?uda ta Waga kiran, a zuciyarta take tunanin yaushe rabonta da magana da Innaye ko da ta waya ne balle har suyi ido biyu?
"Barka da safiya Innaye, ina kwana? Da fatan duk kun tashi lafiya?"
Tayi saurin mi?a gaisuwa bayan ta yi sallama da ?ar karkarwa a muryarta kamar tana gaban Innaye.

"Lafiya ?alau Fatima. Ya wanka?"
Innaye ta tambayeta a nutse.

Bayan ta amsa da lafiya lau daga can Sangaren Innaye sake gyara zama tayi akan daddumar da ta idar da sallar walha. Cikin nutsuwa ta sake jefa ma Bintu tambayar da shi ne ?wa??waran dalilin da yasa ita da kanta ta Waga waya ta kira Bintu ba sa?o ba.
"Am nace ba? Ina fatan dai Hafizu ya faWa miki matsayin da Zulai take da shi yanzu a gurinsa?"

"Eh ya faWa min. Ya ce za ta taya ni ?an aikace-aikace har zuwa sadda zan gama wanka."
Bintu ta amsa kai tsaye, ba tare da tunanin komai a tambayar da Innaye tayi mata ba.

"Uhmmm!"
Innaye ta faWa daga can Sangarenta, fuskarta bayyane da Wan mamaki kaWan, domin daman ta yi tunanin hakan zai iya faruwa. Ta daWe da fahimtar idan al'amari ya biyo ta Sangaren Bintu kamar dai Hafiz tsoronta yake ji. Shi yasa ta kira da kanta don ta faWa ma Bintu yanzu Zulai matsayin matar Hafiz take, kuma tayi mata ?wa??aran jan kunne kan kar ta kuskura ta ce za tayi gigin ci mata amanar Zulai, idan hakan ya faru da ita da Hafizu za su gamu da mummunar Sacin ran da basu taSa tsammani ba.
"Shi Hafizun ne yace miki an kai Zulai ne don ta taya ki aiki?"

Kafin ta amsa da zafi-zafi a muryar Innaye ta cigaba da cewa
"?arya yake yi, bai faWa miki gaskiya ba. Yanzu Zulai matsayin matarsa take ta sunnah kamar yadda kike matarsa. Shekaran jiya Baffansu ya Waura musu aure... Domin ita Zulaikha ba ni na haife ta ba, Wiyar ?anwata ce..."

?if! Wayar ta Wauke daga can Sangaren Bintu bayan wani ?a??arfan ihu da ta yanka da yayi barazanar kashe ma Innaye dodon kunne.

"Subhanallahi! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Fatima lafiya kuwa? Me yake faruwa?"
Innaye ta tambaya hankalinta a tashe bayan ta kawar da wayar daga kunnenta saboda amsa kuwwar da ihun yayi mata a kunne, daga bisani kuma ta mayar da wayar bayan taratsin ihun ya ragu a kunnuwanta. Shi ne har take jera ma Bintu waWannan tambayoyin, duk a tsammaninta, wani abun ne can na daban ya Waga hankalin Bintu ba maganar da taji daga bakinta ba.

Jin shirun yayi yawa babu amsa daga can Sangaren yasa ta ciro wayar ta duba, sai a lokacin ta fahimci kiran ya tsinke. Hankalinta a tashe ta sake danna kiran lambar Bintu, nan take na'ura ta sanar da ita wayar a kashe take. Amma da yake ba jin abinda ake cewa take yi ba sai da ta kira kamar sau biyar ana maimaita mata amsa Waya sannan ta ha?ura da kiran lambar.

Da damuwa a fuskarta ta ajiye wayar ta cigaba da lazumin da take yi.
'Idan kuma ya kasance matsanancin kishi ne yasa Bintu ?wallah ihun da kika ji ta waya fa?'
Kwatsam! Wani sashe na zuciyar Innaye ta jefa mata wannan tambayar.

"Autata."
Ta faWa a fili hankalinta a tashe.
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un! Auta tana cikin gidan kuma tun Wazu da Hafizu ya kira ni mu gaisa ko da na nemi ya bani Auta ya faWa min tun safe yana Ofishin shi."
Ta sake faWa a fili, tashin hankalinta na ?ara hauhawa.

Sai a lokacin ta tuna ai Balira ta faWa mata ta ba Auta wayarta ?ar sha-fa ta tafi da shi Habuja. Kenan idan ta kira lambar Baliran za ta ji a wane hali Autarta take ciki... Ba tare da wani Sata lokaci ba ta rarumo wayarta ta fara bin lambobi tana neman lambar wayar Balira, wanda aka yi mata saving da alamar ?wallo a jikin lambar.

Saboda tsananin ruWewa da?yar ta iya gano lambar, jikinta na Wan karkarwa ta danna ma lambar kira. Sai dai kuma cikin hukuncin Allah kira tayi har sau bakwai bai shiga ba.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel. Ya Allah ka tsare min Zulai aduk inda yake."
Tayi addu'ar a fili hankalinta a tashe. Zuciyarta cike da fargaba da tsoron irin kishin matan birni da take jin labari a radio. Matan birni da idan kishinsu ya motsa don su yanke ma namiji mazakuta ba komai bane a gurinsu, tsoronta Allah tsoronta kishi yasa Bintu ?ona mata Auta da tafasasshen ruwan zafi. Domin a irin labaran kishin matan birni da take ji a shirin In da Ranka... wannan ba komai bane.

Da saurin gaske ta lalubo lambar Hafizu mai alamar mota ta danna mishi kira. Yana Wauka, bata tsaya jan wani dogon zance ba ta fara kora mishi ?wa??waran kashaidi
"Hafizu, kabar duk abinda kake yi yanzunnan ka tafi gidanka ka duba min halin da Auta take ciki. Domin na kira Bintu na faWa mata Zulai matarka ce, na ji ta ?wallah ihu, to ina rantse maka da Allah idan mahaukacin kishi yasa Bintu illata min Auta bazan taSa yafe muku ba har duniya ta naWe..."
?if! Cajin wayarta ta Wauke ba tare da ta gama kora ma Hafizu kashaidi ba.

Duk yadda take ta kunna wayar a ?o?arinta na sake kiransa, wayar da ta kawo sai ta Wauke. A zuciye tayi cilli da wayar akan gado ta mi?e tsaye tana safa da marwa, bakinta Wauke da duk wata addu'a da ta zo zuciyarta.

A Sangaren Hafiz ma ko da ya gwada kiran lambar Innaye ya ji swich off! Ya kira lambar Bintu ita ma a kashe, ya kira lambar Aunty Balira da yake hannun Zulai ita ma ya ji a kashe. Hankalinsa a tashe ya tsallake tarin ayyukan da ke gabansa ya fito daga cikin Ofishinsa ya nufi gida.


***** *****
Ba ita ta farka ba sai ?arfe tara da minti biyu na safiya, ganin yadda garin ya waye sosai yasa ta yin mamakin irin barcin da tayi akan dadduma. Da sauri ta faWa banW??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aki ta yi wanka ko jikinta ya ?ara warwarewa daga gajiyan da yake tare da ita.

Bayan ta fito ne ta lura da wata ba?uwar fallen takarda da aka nannaWe ajiye a gaban madubi. A hankali ta ?arasa ta Wauka.

"Mashkura"
Shi ne sunan da ta gani rubuce da manyan ba?i a farkon sa?on. ?an murmushi ne ya suSuce mata kafin ta fara karanta ta?aitaccen rubutacciyar sa?on da ya kasance da hausa ne.
_"?awata, Na shigo mu gaisa sai na ga kina barci. Sanin jiya baki wani samu isasshen barci ba shi yasa na kasa samun ?warin gwuiwar tashinki. Ki huta lafiya ?awata, ni na wuce makaranta. Idan na dawo in sha Allah yau za mu fara Waukar darussanmu kamar yadda muka tsara. Bye._"

A hankali ta nannaWe takardar har lokacin murmushin da take yi bai bar kan fuskarta ba.
"Allah sarki Mashku. Ubangiji Allah ya dawo min da ke lafiya. Na gode ?warai da karamcinki a gare ni."
Tayi maganganun a fili. Gefen gado ta ?arasa ta Wauki wayarta, sai a lokacin taga wayar a kashe. Ko da ta kunna sai taga ashe cajin wayar ce ta ?are, kuma Aunty Balira bata ba ta cajar wayar ba.

?an Sata fuska tayi alamun bata ji daWin haka, wayar da wasi?ar da Mashkura tayi mata ta cusa a aljihun jakar kayanta sannan ta ciro manshafawarta ta zauna a gaban madubi ta fara shafawa. Zuciyarta cike da tunanin Innaye.

Ta so ?warai ta kira Innaye yau da safennan su daWe suna hira. Abinda yasa ta kasa kiran Innaye jiya shi ne ba ta so ta ?ara Waga mata hankali, shi yasa duk yadda take son jin muryarta ta danni zuciyarta har zuwa safiyar yau. Sai kuma ga shi wayar nasara ta yi mata tsiya.

Ta gama shiryawa kenan a fisge ta ji kamar an yanka ihu daga can waje. Tsam! Ta tsaida hankalinta guri Waya ta ?ara saurarawa, sai kuma bata sake jin ihun ba. Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke, ta Wauki hijabinta ta zura ta kama hanyar ficewa daga Wakin a niyyarta na zuwa kicin don sama ma kanta abinda za ta karya da shi.

Hankalinta yayi nisa sosai a tunanin da take yi, kuma baza ta ce ga takamaimai abinda take tunani ba. Sam bata lura da tahowar Bintu a haukace ba sai ji tayi anyi mata wani wawan angiza da yasa lokaci Waya tayi taga-taga ta zube a ?asa.

A tsorace ta Waga idanu tana kallon Bintu da tayi amfani da wannan damar na faWin da Zulaikha tayi ta haye ruwan cikinta tayi mata wani mugun sha?a, ko da ta kalli cikin idanun Bintu, matsanancin tsoro da firgici ne suka ?ara lulluSeta ganin yadda idanunta suka kaWa suka yi jajur.
"Munafuka, algunguma, matsiyaciya, tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkhairi ba. Da gaske ne an Waura miki aure da Mijina Hafiz ko kuwa wancan tsohuwar banzan ?arya take min?"
Ta ?arasa da tambayar tana zazzaro ma Zulaikha idanu kamar wacce ta hau aljanu.
[1/28, 7:23 PM] Fareeda Abdallah: Sai a lokacin Zulaikha ta fahimci dalilin haukar Bintu, idanu ta Wan runtse jin yadda Bintu take ta ?ara tattare hijabinta da wuyanta tana ?ara sha?o ta da hannayenta duk biyu. Lokaci Waya kuma tana ?ara maimaita mata tambayar cikin tsawa da Waga murya
"Za ki amsa min tambayar da nake miki ko sai na illata ki? Da gaske ne ?iyayyar da matsiyata kuma ?auyawan iyayenku suke min ya kai matsayin da yasa suka aura ma mijina ke ko ?arya tsohuwar banzan nan take min?"

Da Sacin ran yadda Bintu take ta furta kalaman tozarci ga iyayensu saboda mahaukacin kishi da ya rufe mata idanu yasa ta amsa mata tambayar ita ma cikin tsawa da Waga murya.
"Eh! Da gaske ne. Shekaran jiya an Waura aure na da Yaya Hafiz. Idan kina da abinda za kiyi ko kuma kin isa kiyi wani abu sai kiyi."
Tana gama faWin haka da ?arfi tasa hannuwanta biyu ta SamSare hannayen Bintu daga wuyanta, tayi kukan kura ta wancakalar da Bintu daga ruwan cikinta ta mi?e tsaye a zafafe.

"Ke jaka kuma dabbar ina ce da za ki dinga zagin tsofaffin da suka zama silar zuwan mijin da kike ta?ama da shi duniya? Ko kina tunanin tsoronki suke ji da za su zuba ido kiyi ta wula?anta su a gidan Wan da suka haifa da cikinsu? Wannan auren ba kowa ne ya janyo shi ba face ke da kanki, ba?in halinki da mugun halinki na dabbobi yasa suka nema ma kansu mafita ta hanyar Waura ma Wansu aure da ni. Domin sun san duk tsiya ni bazan taSa wula?anta su ba, ranar naka sai naka... ko sun fi haka ?auyanci da jahilcin da kike kira bazan taSa tozarta su ko in banbanta su da nawa iyayen ba..."

A haukace, Bintu ta sake ?wallah wani gigitaccen ihu a karo na biyu. Kalaman Zulaikha kamar zuban tafasasshiyar dalma haka suke sauka a kunnuwanta zuwa ?wa?walwarta.
"Ni za ku ciwa amana??? Ni kike faWa ma irin waWannan banzayen maganganun? To na rantse da Allah yau ko ni ko ke a gidannan. Zan kashe ki har lahira, in ga uban da ya isa ya tsaya miki duk faWin tsinannen ?auyen naku da jahilan iyayen naku da kike ta?ama da su."

Bintu tana gama faWin haka, da mugun gudu ta nufi cikin babban kicin Win ta da yake falon. ?aya daga cikin sababbin wu?a?enta manya masu masifaffen kaifi waWanda bata taSa amfani da su ba ta Wauka, ta sake ficewa da gudun gaske.

Zulaikha da take tsaye hannuwa ri?e da ?u?umi tana huci duk ga tsammaninta Bintu taSarya za ta Wauko, shi yasa ta tsaya domin ta gwada mata idan hauka da Wanyen kai take ji ta dame ta ta shanye.

Hango wu?ar da ke ?yalli a hannun Bintu yasa ta zare ido, bata tsaya raba Wayan biyu ba ta juya da gudu zuwa Wakin da aka yi mata masauki, tana shiga ta danno ?ofar Bintu ta isa gurin. Da?yar ta samu nasarar murza makullin ?ofar daga can ciki ta kulle tana numfarfarshi.

Bintu a haukace ta kai ma ?ofar wani wawan suka da wu?ar hannunta, amma da yake dakakkiyar ?ofa ce mai tsada Wan karcewa kaWan jikin ?ofar tayi.
"Ashe ke ?aramar mara kunya ce? Jaka, kucakar ?auye dabba, na rantse da Allah yau sai na ga bayanki a gidannan. Zan nuna miki mijina nawa ne ni kaWai, ko da macen birni ?ar gayu bata isa inyi sharing Win shi da ita balle ke da nake miki kallon ?azantacciya a cikin dabbobi. Na rantse da Allah yau sai na bar ma waWancan munafukan tsofaffin mummunar tabon da bazai taSa gogewa a zukatansu ba. Zan kashe ki, in kashe banza a banza, duk faWin ?auyenku sai in ga idan da shegen da ya isa yayi shari'a da ni..."
A haukace ta sake kaima ?ofar wani wawan tokari da ?afafunta, ihu ta ?wallah saboda azaban zafi da raWaWin da ya ratsa ?afar nata lokaci Waya, sai kuma ta zube ?asa ta fashe da wani ?a??arfan kuka gwanin ban tausayi, hannayenta duk biyu Wore a kanta. Ga kuma wu?ar da take ri?e da shi tsirara har lokacin bata yar da wu?ar ba.

A haka Hafiz ya shiga cikin falon a sukwane Raudha na biye a bayanshi. Ya matsa zai ?arasa kusa da ita da saurin gaske ta nuno shi tsinin wu?ar hannunta.
"Munafuki! algungumi!! maci Amana!! Wanda bai san darajar Al?awari ba!!!"
Ta jefa mishi munanan kalaman cikin matsanancin kuka na tashin hankali.
"Na rantse da Allah idan ka ?araso kusa da ni sai na caka maka wu?ar nan sannan in cakawa kaina. Gara duk muyi mutuwar kasko in san babu wata tsinanniya da za ta sake rayuwa da kai a matsayin mijin aurenta."
Ta cigaba da magana cikin kuka.

Hankalinsa a tashe, ya fara mata magana da taushin murya don ya kwantar mata da hankali.
"Bintu, Bintu, kin ga, don girman Allah kiyi ha?uri ki ajiye wu?ar, ki saurare ni..."

"Me zan saurara?"
Ta katse shi cikin tsawa tana wani zaro mishi idanu kamar ba ita ba.
"?arya? Ko kuwa kalamanka na yaudara da daWin baki da ka saba cika kunnuwana da su? Ayau na tabbatar babu soyayya tsakanina da kai Hafiz, kuma na rantse da Allah sai dai idan Munafukar Allah ta'alan nan baza ta fito daga Wakinnan ba, sai na kashe ta har lahira, sai dai duk abinda zai faru ya faru."

Bai san muhimmancin tahowa da Raudha da yay ya kai ?ololuwa ba sai da yaga cikin hikima ta ?arasa kusa da Bintu ta rungumota jikinta, sannan a dabarance ta zare wu?ar da ke ri?e a hannunta tayi hurgi da shi gefe Waya.

Cikin kuka da magagin kishi take yi ma Raudha bayanin abinda Hafiz yayi mata.
"Ki ?yale ni Raudha... Hafiz ya ci amanata... ku kuke faWa min namiji ba Wan goyo bane ni kuma ina muku tutiyar nawa Wan goyo ne har da majanyi... Ashe duk mazan mamugunta ne halayensu Waya? Ashe da gaske ne da Hajiya Binta take yawan faWin Namiji ?anin ajali? Wai Raudha kamar ni Hafiz zai yaudara? Ni zai ciwa amana ya karya min al?awari? ?auyensu ya tafi aka Waura masa aure da tsinanniyar ?anwarsa amma saboda ya raina ni shi ne yake faWa min ya taho da ita ne don ta taya ni aikin gida? To na rantse da Allah sai na kash..."

Da saurin gaske Raudha tasa hannu ta rufe mata baki. A tausashe ta fara ma Bintu magana, fuskarta na bayyana yanayin Sacin rai da jimami, alamun itama tana jin ciwon abinda Hafiz Win yayi ma Aminiyarta.
"Tabbas! Hafiz bai kyauta ba Bintu. Amma kar ki manta, idan hankali ya Sata hankali ke nemo shi. Yanzu abinda nake so da ke kiyi ha?uri, ki kwantar da hankalinki. Ki sama ma kanki nutsuwa ko Wan kaWan ne don mu samu mafita cikin ?an?anin lokaci. Tashi mu tafi zuwa Wakin ki, Hafiz Win me? Ina ?udan yake balle romonsa? Ai shi ma ya san yayi kaWan, ba irinmu ake yiwa wannan cin amanar a zauna lafiya ba."
Da ire-iren waWannan kalaman tayi amfani har ta samu nasarar mi?ar da Bintu tsaye, tana ri?e da ita a jikinta suka taka a hankali tana sake faWa kalaman kwantar da hankali har suka haura sama zuwa Wakinta.

Suna Sace ma ganinsa, hankalinsa a Wugunzume ya ?arasa zuwa ?ofar Wakin. Ya daWe da sanin Bintu tana da masifaffen kishi, amma bai taSa tsammanin kishi zai iya rufe mata idanu har tayi yun?urin kisan kai ba. Yau in da ace kafin dawowarsa gidan ta samu nasarar caka ma Zulai wu?ar nan fa?
"A'uzu billahi minasshaiWanirrajim"
Yayi ta'awizi da sauri yana ?o?arin kawar da mummunan tunanin daga zuciyarsa.

Wu?ar da Raudha ta cillar zuwa gefe Waya ya fara Wauka ya kai kicin ya Soye, ba ma ita wannan wu?ar ba, duk wasu wu?a?e manya da ?ananu da suke kicin Win kwashe su yayi gaba Waya zuwa cikin wata durowa ya kulle, ya zare makullin ya jefa a aljihu.

?ofar Wakin da Bintu take ciki ya koma ya fara ?wan?wasawa. Bintu da take ciki hankalinta a tashe, izuwa wannan lokacin ta shiga bayi sau biyar don tsananin firgita da tashin hankali. Cikin ?an?anin lokaci

23 / 53