Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   48 / 53

141K to 144K   out of 157.3K words

ya koma ba Baffa kunya, a ganinsa ai ba wani abun azo a gani bane yayi idan aka haWa da irin gwaggwaSan karamci da girmamawar da suke mishi da iyali da duk wani da ya shafe shi.


*******


Bayan gama waya da Baffa, jikin Hafiz sanyi ?alau ya zube a gefen gadon Wakin hotel Win da suke ciki da abokansa.

Allah yana gani bai so mayar da Bintu ba, shi yasa yake ta Soye maganar sakin don kar su Baffa su ji. Ko Zulai baiyi gigin faWa mata ya saki Bintu ba, ya sani idan ta ji, kamar Innaye ne ta ji.

Yana cikin wannan halin na damuwar abokinsa Ibrahim Wan gidan Abba Lurwanu da suke zaune a falo da sauran abokansu suna shirye-shiryen zuwa dinner ya shiga cikin Wakin ya tarar da Hafiz a wannan halin.

"Ya aka yi ne Ango? Me yake faruwa..?"

Da Sacin rai sosai ya amsa mishi
"Uhmmm! Wallahi yanzu Baffa ya umarceni in mayar da Bintu Wakinta."

"Shi ne kake ta wani ciccin magani kamar ka kurSi maWaci? Common guy, kar ka kuskura ka bari wannan zancen ya Sata mood Win ka na farin ciki. Yau kake sabon ango fa, ka aje duk wani Sacin rai gefe Waya ka rungumi farin cikin da ke tattare da kai.

Kawai shawarar da zan baka Waya ne, kar ka kuskura ka bari kayi saken da za'a sake samun matsalolin da aka samu a baya tsakaninka da Bintu. Kuma tun yanzu idan kana da wasu tsare-tsare da dokoki ka kira ka faWa mata tun yanzu, idan ta shirya sake zama da kai a karo na biyu za ta amince, idan bata shirya ba da kanta za ta sake neman ka sauwa?e mata. Ka ga shi kenan, ka yada ?wallon mangwaro ka huta da ?uda."
Yana gama wannan maganar bai jira cewar Hafiz ba ya fice zuwa falo gurin sauran abokansu.

Maganganun da Ibrahim yayi mishi, su suka dawo ma da Hafiz farin ciki da walwalar da yake neman rasawa sanadiyyar mayar da Bintu Wakinta. Wayarsa ya Wauka da yake ajiye gefensa, ya lalubo lambar Bintu ya buWe gurin tura sa?o ya tura mata sa?on cewa
_*"Kamar yadda albarkacin kaza ?adangare ke shan ruwa a kasko. Haka Albarkacin Baffa na amince ma sake zama da ke ayau. Na mayar da ke Wakinki Bintu, amma bisa sharuWWa guda biyu. Na Waya shi ne, nan da kwanaki uku masu zuwa ki shirya ki tafi har gida ki ba Innaye da sauran ?an'uwana da sauran matan Baffa ha?uri kan irin cin mutuncin da kika yi musu. SharaWi na biyu kuma shi ne ki shirya komawa zaman Fa?o, a gidan Baffa zan sama miki Wakin zama, sannan za ki dinga cin abinci da abinsha ?ar?ashin kulawar Innaye ne har zuwa lokacin da ni da kaina zan gamsu za ki iya zama da ni ba?auye da ?an'uwana ?auyawa. Idan kin amince da waWannan sharuWWan, ina miki maraba da sake zama matar Hafiz a karo na biyu. Idan kuwa baki amince ba ki faWa min don Allah, ni kuwa yanzun nan zan faranta miki ta hanyar datse sauran igiyoyin da suka rage tsakanina da ke. Hafiz Aminu Fa?o."*_

Yana aika mata da sa?on, ya mi?e tsaye ya fice zuwa falo gurin sauran abokansa suka cigaba da harkokinsu cikin walwala da farin ciki.

Zuciyarsa cike da tabbacin ?arshen zamansa da Binto ya zo a sau?a?e, domin ko rantsuwa yayi babu kaffara, ya sani a girman kai irinna Bintu, ba ta yadda za ayi ta amince da waWannan sharuWWan da ya gindaya mata. Shi kuwa bazai Sata lokaci ba gurin cike mata sauran saki biyun da ya rage a tsakaninsu, yana da tabbacin Kareema ita kaWai, ta ishe shi rayuwar duniya da lahira.



*********


Ana idar da sallar magriba, manyan motoci masu numfashi suka cika ?ofar gidan Mummy don Wiban Amarya da manawarta zuwa wajen dinner. Daman tun da yamma Zulaikha ta faWa ma Hafiz kar ya wahalar da kansa wajen zuwa Waukar amarya.
"Ni zan wakilce ka Yaya, sabuwar motar da Abban Imam yayi min oder ta iso last week. Tunda aka kawo ta ban hau ba, na tsaya jiran wannan ranar mu fara hawa tare da Aunty Kareema..."

"Zzzzzulai...?"
Ya katse ta da kiran sunanta cikin rawar murya.
"Kin yi hauka ne?"
Ya sake faWa hankalinsa a tashe.
"Yaushe kika koyi tu?in mota da har zanyi gangancin bari ki Waukar min amarya zuwa wajen dinner? Don Allah ki bari, kar ki fara yi min wannan gangancin, in za ki tu?a kanki bismillah tunda mijinki da yake can wata ?asa ya amince. Amma ni dai ban yarda ba, tunda dai ba karen hauka ne ya cijeni ba..."

Da sauri ta katse wayar tana tuntsira dariyar ?eta, a zuciyarta ta ayyana za kuwa ta bashi mamaki. Wato ita rayuwarta a banza ko? Ai kuwa zai gani, da Wanshi da Amaryarshi ita za ta kai su wajen dinner, duk abinda zai faru ya daWe bai faru ba.

?arfe shidda da rabi dai-dai ta shiga Wakin da Amarya da ?awayenta suke ta ce Hibba da Amarya su fito su tafi.

"A'a! Na zaci Ango da kansa shi zai zo Waukar amarya?"
Wata daga cikin ?awayen Amarya mai kafiWirin tsiya ta faWi haka tana wani fari da idanu.

Yatsa manuniya Zulaikha tasa tayi ?asa-?asa da gilashin da ya mamayi kusan rabin fuskarta ta aika ma da yarinyar kallon uku saura kwata, ta yatsuna fuska kamar ta ga kashi sannan ta amsa da
"Idan na Wauki Amarya kamar Angonta ne ya Wauke ta, dmin ni Win ?anwar Ango ce. Ko akwai wani banbanci tsakanin ?anwar Ango da Ango?"

"A'a! Mayar da wu?ar ?anwar Ango. Ni ban Wauka da zafi ba."
Ta faWa cikin waskiya tana dariya.

Ko kafin motocin da za su kwashi jama'a su iso, tuni Zulaikha ta kwashi Kareema, Hibba, Aadil, Imam sunyi gaba, babu abinda take yi sai dariya cikin ranta.

"Yaya, kar kayi wahalar zuwa gidan Mummy Waukar Amarya, mu munyi gaba. Amma kana iya tarar da mu a ?ofar event center Win don ku shiga tare, Amma fa idan tu?in rashin ?warewa ta bai sa na kashe maka amarya ba."
Sa?on da ta tura ma Hafiz kenan bayan sun isa gurin
*******


Kamar yadda aka tsara, a daren ranar aka wuce da Amarya gidan Abba Lurwanu. Sun sami tarbar girma, tun a daren aka ringa ina aka saka ina aka aje da su har zuwa washe gari.

Bayan sun karya kumallo misalin ?arfe tara na safiya suka kama hanyar tafiya Fa?o. A cikin tsadaddun motoci guda huWu da Abba Lurwanu ya bada ayi tafiyar da su.

Sun yi tafiyar ne a wadace, babu takura ko kaWan. Mota Waya aka saka Amarya, Zulaikha, Hibba, sai Waya daga cikin ?awayen Amarya mai suna Maryam. Mota Waya aka Matan Abba Lurwanu biyu, matar Ibrahim, babbar ?ar Abba Lurwanu mai suna Aunty Zainab.

Mota Waya kuma ?annen Momy guda biyu, sai ?annen mahaifin Kareema biyu. Mota Waya kuma aka Wauki ?an biko da suka zo daga Fa?o. Sai babbar motar Hillux da aka cike bayanta aka sha?e da kayan garar surukai wanda za a kaiwa su Innaye.

Da yake direbobin an faWa musu tafiya ce mai nisa a gabansu, shiyasa basu yi tu?i na wasa ba. Wajen karfe Waya na rana suka isa Fa?o. Kun dai san mutanen ?auye da karamci, balle ma su Innaye da suka samu shaidar kirki da sanin ya kamata. Sun samu tarba ta girma sosai a wajen su Anty Balira da Innaye, abokan zamanta.

Dama tunda bikin ya matso, kasancewar gidan Baffa akwai fili sosai daga can Sangaren Wakin Innaye, nan Hafiz yasa aka yanka mishi fili, duk a ?o?arinsa na gyara kuren da yayi a zamansa da Bintu, ya Wauko ?wararrun magina daga Kaduna, cikin sati biyu aka gama gina uwar Waka da falo da bayi, a cikin sati uku kuwa, hatta funitures an zuba a cikin Wakunan. A ganinsa har da rashin kwana biyu da basa yi a cikin ?auyen shi yasa sam Bintu bata saba da ?an'uwansa ba, ya gyara nan Win ne a matsayin gurin saukarsa da iyalinsa. Kwana Waya, biyu, uku, idan ta kama har sati Waya ko biyu za su dinga yi a ?auyen.

Sannan yasa aka ?ara gyara duk inda ke bu?atar gyara a gidan, aka yi fenti mai masifar kyau, sannan ya canja ma su Innaye da abokan zamanta da Baffa kayan Wakunansu gaba Waya.

Ginin da Hafiz yayi nan aka sauki Amarya da manawarta, kafin ?iftawa da Bismillah aka dabaibayesu da kayan abinci cima iri-iri da katan-katan na lemuka. Wani abun burgewar kuma shi ne a kayayyakin abincin da su Innaye suka tarbi Amarya da manawarta da shi har da kalolin cima ta marmari, irin wanda ba'a cika samu a birni ba sai a ?auyuka. Sun ci, sun sha, sun yi hani'an! A nutse su ka yi sallah, fuskokinsu gaba Waya cike da farin ciki. Bayan sun huta, suka dauki Kareema zuwa gurin su Innaye domin yin buWar kai.

Dangin Hafizu ?wansu da ?war?wata kowa ya fito. Cikin gidan Innaye cike yake da bil'adama dan-?am babu masaka tsinke. Kuma abinda ya ?ara ?ayata bikin shi ne masu kiWan ?warya da aka tafi har garin Kaduna aka Wauko hayarsu, Sune suka je tun da misalin sha biyun rana, aka ware musu gurin zama ta cikin gidan Baffa suna ta wa?e-wa?ensu na gargajiya matan ?auye suna juya mazaunai.

Fitowar Amarya da danginta da niyyar zuwa Wakin Innaye yasa masu kiWa canja salon kiWansu da yanayi mafi daWaWawa, nan take filin rawa ya ?ara tumbatsa da mata, masu girgiza na yi, masu guWa nayi, masu kirari na yi, abin dai gwanin ban sha'awa.

Wani harkar girma da Matan Abba Lurwanu da Auntys Win Kareema suka yi shi ne, kafin su wuce zuwa Wakin Innaye, sai da suka Wan tsaya da Amarya a filin rawar, suka yi ma masu kiWi da mai wa?a da masu rawa yayyafin kuWi masu yawa, sannan suka ja hannun Amarya zuwa Wakin Innaye aka bar Hibba da Maryam a fili da Zulaikha, wacce jin guWar da ke alamta an fito da Amarya yasa ta fitowa daga uwarWakin Innaye.

Innaye tana zaune cikin ?an'uwa da abokan arzikinta, ta yi kwalliyarta gwargwado ta mutanen da, saboda kyawun jikinta babu wanda zai ce ita ta haifi su Aunty Balira. Ta sha atamfarta super Holland, Waya daga cikin Winke-Winke masu tsada har kala goma sha biyu da Zulaikha ta aika mata da su, shida Hafiz ne ya siya, shida Zulai ta siya, sannan ta haWa duka sha biyun ta ba tela da na su Aunty Balira hurhuWu ya Winka musu.

Matan Baffa kuma kala uku-uku, sauran yaran gidan kuma mazansu da mata yara da manya kowa kala bibiyu.

Baffa kalolin shadda da yaduka har bakwai ta Winka mishi. Su Baba Abubakar da matansu duk sun shiga cikin kasafi, har Liman da Ladan da suka kasance abokan Baffa sun karSi rabonsu. Ma?udan kuWaWe Abban Imamu ya sakar mata, sannan ya ?ara da jaddada mata lallai ta tabbatar ta yi ma kowa tsaraba, idan kuWaWen basu isa ba ma ta faWa mishi ya ?ara mata.

Wani aikin hankali da Zulaikha tayi shi ne mota guda ta aike musu da shi na kayayyakin ana saura kwanaki uku bikin Hafiz. Shi yasa tun da Zulai ta isa gidan, kamar tauraruwa haka ta zama, kusan kowa so yake ya gaisa da ita yayi mata godiya. Da?yar ta yakice kanta ta gudu uwarWakin Innaye bayan ta basu uzurin kanta na ciwo, duk da haka sai da yayyinta uku suka bi ta, bata fito ba sai yanzu da ta ji an fito da Amarya.

Innaye babu abinda take aikin yi sai sakin murmushi a kunyace, lokacin da aka dam?a mata amanar Amarya ita da abokan zamanta. A ta?aice tayi addu'a, bayan haka ta kasa ?ara cewa komai, har zuwa sadda aka fara shigo da manyan randuna na kayan gara da buhuna na kayan abinci, tun matan ?auye suna ?irga buhu da kwalaye har bakunansu ya mutu-murus.

Tsakiyar falon Innaye da ?ofar Wakinta sai da aka sha?e taf da kayayyaki. Abin dai ba'a cewa komai sai hamdala. Bayan waWannan kayan abincin kuma, Zannuwa da shaddodi guda goma sha biyar Mummy Saudah ta bayar na su Innaye, abokan zamanta da yayyen ango.

Tuwon girma aka ce miyarsa nama. Nan take iyaye da ?an'uwan Hafizu suka fara kwance haSar zani suna fito da kuWin da za su haWa ma Amarya na tarba. Zulaikha ta shigo da fara'a ta haWa zufa tai sharkaf saboda rawar da tayi, ta Wan tsallaka ta shige cikin Waki, bandir Win dubu Wari ta Wauko a jakarta ta mi?a ma Aunty Balira cewa a haWa a cikin kuWin sallamar Amarya.

Abu dai anyi shi cikin mutunci da arziki. An mayar da Amarya Sangaren da aka sauketa da kuWi naira dubu Wari biyu da hamsin da biyu. Domin matan Abba Lurwanu da Aunty Zainab su ma dubu Wari suka bada, Innaye da abokan zamanta da ?a?ansu suka haWa dubu hamsin da biyu.

Washe gari da safe haka aka yi hidima da Amarya da danginta, hidima ba ?ar kaWan ba, da yake duk abinda za'a nema Baffa da Hafiz sunyi matu?ar ?o?ari gurin tanadarsa. ?arfe goma da rabi Amarya da danginta da Zulai suka bar garin Fa?o.

Al?awari Zulaikha ta Wauka ma Kareema sai ta kaita har Wakinta na gidan Hafiz, shi yasa ba tare da ta gama gaisawa da Iyaye da ?an'uwanta ba ta sake bin Amarya suka koma Abuja, bayan ta faWa ma Innaye kwanaki goma masu zuwa za ta koma Fa?on, a lokacin za tayi sati Waya. Kuma lokacin ne za ta tafi da Aadil su Innaye su ganshi.


********


Duk tarin abokansu da suka rufa mishi baya gurin hidimar bikin sun koma gurin ayyukansu, saboda jinkirin da aka samu wajen kai Amarya Fa?o. Yau da ya kasance Amarya ta isa gidanta bayan sallar Isha'i, Ibrahim ne kaWai yayi mishi rakiya.

Lokacin da suka shiga gidan babu kowa sai Zulaikha. Iyaye da sukai rakiyar Amarya duk sun koma gidajensu. ?awayen amarya da suna jin labarin Kareema ta koma gidan Mummy suka dawo, duk ta kore su bayan ta basu kuWin sallamar da suke yiwa ?wa-?wa. A cewarta, ba za su bata wa yayanta lokaci da zancen kuWin sayen baki ba, balle har su shiga lokacinshi da na amarya.

Ita da aka bari cire mayafinta tayi ta ?ara gyara wajen Sangaren Amarya da yayi kyau sosai, saboda an narka dukiya wajen tsara gurin ba kaWan ba. Ta dauko burner da humidifier duk ta jonasu da zuba abin kamshi a ciki. Gidan ya kaure da kamshi kashi-kashi. Idan ka shiga har ka rasa wanne za ka shaka.

Wajen karfe tara da rabi suka ratsa ta cikin main parlour suka shiga Sangaren Kareema, Hafiz da Ibrahim sun sha Angon babbar shadda wagambari, fara, ta sha surfani iri Waya. Fuskar Hafiz sai she?i take yi da annuri irin na angwaye.

Lokacin da suka shiga, Zulai da Kareema na zaune a falonta da ya sha saitin wasu hadaddun leather seats ruwan madara. Hafiz ya kalli Zulai ya watsa mata harara
"Kin shiga uku da masifar sa'ido Zulai. Ke kuma zaman uban me kike yi anan bayan tun Wazu an ce kin sallami ?awayen Amarya?"

Ta kyalkyale da dariya, sai kuma ta Wan kumbura fuska ta ce
"Yaya ai ni tudu uku nake ci. ?anwar Ango, Yayar Amarya, kuma ?awar Amarya. Don haka kuWin sallamar da baka biya ba ni za ka ba, idan ba haka ba daga nan har gobe Amarya baza ta buWe maka baki da fuska ba."

Duk da ya san tsokanarsa take yi, da saurin gaske ya Wan narke fuska, a marairaice ya fara ro?onta
"Haba-haba An Zulai ta Innaye da Baffa. Ai na san baza kiyi ma Yayanki haka ba? Ko kin manta ni da ke mun shirya tsakaninmu yanzu ba ta Saci?"

"Ban manta ba Yaya."
Ta amsa da dariya.

"To tunda haka ne zo ki wuce gidanki. Na gode da ?o?arinki ?anwata, Allah ya bar zumunci. Za muyi waya da safe, kina iya tu?i da daddare ko in haWa ki da direba...?"

"Direban Mummy na waje yana jira na Yaya, sai da safe..."
Tana gama faWin haka ta rataya jaka, ta gyara zaman mayafi a kafaWarta. Sai da ta kai bakin ?ofar fita daga falon sannan ta waiga ta ce
"Yaya?"

"Na'am Zulai."
Ya amsa da sauri, bayan ya mayar da hankalinshi kanta.

"Ka ji tsoron Allah don Allah Yaya, ka bi min ?awa a hankali..."
Ta ?arasa maganar haWe da ficewa a guje tana dariya.

"Uhmmm! Zulai ?uruciya dangin hauka. Allah ya shirya. Kamar ba ?ar lukuta ba sam ba ta jin nauyin jikinta."

Ba tare da kunyar idanun Ibrahim ba ya maye gurbin da Zulai ta tashi kusa da Kareema, kan kujera mazaunin mutum biyu.

Ibrahim na tsokanarshi
"Ko kunyar idona ba ka ji Hafizu?"

Ya jefa mishi harara ba tare da ya amsa ba.

A gefe guda Ibrahim ya zauna, ya fara da sallama sannan ya buWe taron da addu'a. Nasiha sosai ya yi musu game da zaman aure da zamantakewa, kafin daga baya yayi musu addu'a sosai da fatan Allah Ya Waurar da auransu har a gidan Aljanna. Daga ?arshe ya yi musu sai da safe ya fice daga falon

Da?yar Hafiz ya iya tashi ya raka shi bakin ?ofar babban falo, daga nan ya coge ya ce mishi
"Na gode Aboki, a gaida Madam da yara"

A Nan ma sai da Ibrahim ya ?ara mishi shakiyanci kafin ya mishi sai da safe ya tafi. Shi kuma ya tsaya ya rufe kofa da tagogin falon.

Ya samu Amarya a yadda ya barta, da alamun ko ?wa??waran motsi bata yi ba. A hankali ya ?arasa ya tsuguna a gabanta yana leka fuskarta ta cikin lullubin jikinta.

A sanyaye ta zuba mishi idanunta da suka yi ciki sosai, alamun kukan da ta daWe tana sharSa.

Cikin marairaice fuska, ya ce
"?urratul-ainiy? Kuka kika yi? Sai kace dai wadda aka kawo ki gidan makiyinki ba masoyi ba? Idan ma kina zaton wai ba zan iya kulawa da ke kamar yadda Mommy take yi to ki canza shawara. Domin yadda zan kula da ke ma sai ya

48 / 53