Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   32 / 53

93K to 96K   out of 157.3K words

Akwai wani abu da ya faru acan gidan ne? Ko kuwa sun shirya komawarta can gida ne gaba Waya?"

Da farko shiru yayi, ya rasa amsar da zai bata, domin dai asalin wannan tafiya ba shi ya tsara ba, kuma shi kanshi bai san takamaimai abinda zai kai Zulai Fa?o ba. Amma saboda kar ya kware mata baya a gurin Mummy ita ma ta kware masa nasa bayan a gurin Innaye yasa shi cewa
"A'a Mummy, ba abinda ya faru. Kiyi ha?uri, za ta dawo in sha Allah. Innaye ce hankalinta ya ?i kwanciya ganin tunda Zulai ta taho bata taSa zuwa can ba sai dai su gaisa ta waya, shi yasa zan tafi da ita don hankalinta ya kwanta. Amma ba na jin za ta wuce sati Waya ko biyu, idan na je sati na sama zan dawo miki da ita. Kiyi ha?uri don Allah."

"Shi kenan. Allah ya tsare ya dawo da ku lafiya."

"Amin Mummy. A faWa mata ta fito da sauri don Allah."

Duk yadda yake sauri sai da Zulaikha ta sake Sata mintuna arba'in kafin ta fito cikin rakiyar mutanen gidan, Abban Imam da Imam ne kawai basu biyo ta ba.

Manyan sabbin jakunkuna biyu da yaga Karima na jaye da su har zuwa gurin boot Win motarsa ne yasa shi buWe baki da mamaki a fuskarsa.
"WaWannan kayayyakin fa?"
Ya tambaye ta.

"Na Zuly ne."
Ta amsa mishi a ta?aice.

A zuciyarsa ya ce
'Uhmm! Su Zuly manya.' Sai kuma a fakaice ya juya ya kalli Zulai da aka kira da Zuly, a bazata, ?irjinsa yayi wani wawan bugawa, ganin wasu canje-canje ?arara da yake gani tattare da Zulai.

Kamar dai ba ita ba. Ta zama wata babbar yarinya mai aji da kwarjini, doguwar rigar abaya da yake jikinta ya zauna mata cas! Kamar wata Hadiza gabon sadda take da ?iba kafin tayi sleeming. Ta yi kwalliyarta sama-sama, wanda ya ?ara bayyana cika, ?asaitarta, da wayewarta.

A Wan firgice, ya mayar da hankalinsa kan Hajja ta take masa tsiyar irin wannan sammako da ya bugo musu kamar wanda zai bar ?asar?

Har suka bar ?ofar gidan, da dariyar ya?e yayi ta bin su Mummy. Zuciyarsa cike da Wumbin mamakin gagarumin canjin da ya gani tare da Zulai, wanda bai taSa mayar da hankali ya lura ba sai a yau da suka kama hanyar zuwa Fa?o shi da ita bayan watanni shida da wasu ?an kwanaki da tayi rabonta da ?auyen.

Duk da yadda ba?a?en maganganu ke cike da bakinshi kafin su haWu, ya kuma yi niyyar yi mata wankin babban bargo tas! Domin ta san har gobe fa ruwa na maganin dauWa. A yanzu da suka haWu, kuma suna tare a cikin mota Waya sai ya zama kamar wanda aka Waure masa baki, ya kasa ce mata komai. Lokaci bayan lokaci dai yana Wago fuskarsa ya kalleta ta cikin madubi.

Ita kuwa bata ma san yana yi ba, kanta yana ?asa, tana danna sabuwa kuma tsadaddiyar wayarta, fuskarta cike fal da wani lallausan murmushi.

Mamaki da tsoro mai girma ne ya kama shi ganin wayar da ke ri?e a hannunta,
'Na shiga uku! Kar dai a ce Zulai ta fara bin maza?'
Wani sashe na zuciyarsa ya jefa masa tambayar, sai kuma yayi saurin kore maganar ta hanyar yin ta'awizi.

Kamar bazai tambayeta game da wayar ba, sai kuma ya tuna idan bai tambayeta ba tabbas ya ci amanarsu Baffa. Fuskarsa a Waure, ya daka mata tsawa ya ce
"Keh! Wannan wayar fa? Ta waye kike amfani da ita kamar ta ki?"

A ta?aice, ta Wan Wago kai ta kalle shi da gefen idanunta.
"Tawa ce, Mummy ta siya min jiya."
Ta amsa mishi a ta?aice, sannan ta sake mayar da hankali kan chatting Win da take yi da Abban Imam.

Har zai bar maganar a yadda ta faWa, amma sai zuciyarsa ta kasa nutsuwa guri Waya. Wayarsa ya Wauka ya kira Mummy, bai ji kunya ba yake tambayarta wai ita ta siya ma Zulai waya?

"Eh! Ni ce. Akwai wata matsala ce tattare da hakan?"
Ta tambaye shi.

A daburce ya amsa da
"A'a! Babu komai Mummy. Daman kawai na yi mamaki ne, Allah ya saka da alkhairi ya ?ara arziki."


******


?arfe goma sha Waya da rabi a ?ofar gidan Baffa tayi musu. Tun kafin direba ya gama daidaita fakin Win motar a ?ofar gidan, Zulaikha da ganinta a ?auyen nasu ya taso mata da matsananciyar kewar Innaye da ?an'uwanta ta buWe motar da sauri ta fice da sassarfa ta nufi cikin gidan.

Hafiz yana ?walla mata kira amma ko saurarenshi bata yi ba, kafin ?iftawa da bismillah har ta Sace ma ganinshi.

"Assalamu alaikum! Mutanen gidannan barkanku da safiya... Oyoyo Innaye na..."
Tayi maganganun da karaWinta da mutanen gidan suka daWe suna kewa.

Kai tsaye Wakin Innaye ta nufa a guje saboda rashin ganinta a tsakar gida, sauran mutanen gidan suka rufa mata baya bakunansu har kunne don murnar ganinta.
"Maraba lale marhaban da Amarya Zulai... Lale lale, barkanku da zuwa... Sannunku sannunku, kun sha hanya. Sannunku da zuwa.
Ire-iren kalaman da ke fita daga bakin mutanen gidan kenan yara da manya, cikin ?an?anin lokaci aka cika Wakin Innaye taf da jama'a.

Ita dai Zulaikha har lokacin tana ma?ale da Innaye tana bin masu iyaye da ?an'uwanta da dariya, ta hana Innaye tashi gaba Waya, don gani take kamar mafarki take yi, Innaye tana tashi daga kusa da ita za ta farka daga nannauyan barcin da take yi.

Mama Laminde da Mama Laraba su ne sukai ta Wawainiyar kawo ma Zulaikha da Hafizu da ya shigo daga baya ruwa da sauran kayayyakin motsa baki. Tunda a lokacin ba'a gama abincin rana ba.

Ko kafin su fice daga Wakin har labarin zuwa da Zulai da Hafizu yayi ya iske Baffa da ke can bakin kasuwa. Ai kuwa sai ga shi bagazan-bagazan yana saSa babbar riga, bakinshi har kunne. Da gaske yayi kewar ?ar marainiyar Wiyar tashi, matsayinsa na namiji ne kawai ba ya magana kamar yadda Innaye take yi.

Kuma sanin da yayi a yanzu Hafizu ya fi shi ?arfin iko da Zulai shi yasa bai taSa mishi ?orafin me yasa baya zuwa da Zulai ba? Yau da shi Hafiz Win da kanshi ya yanke shawarar tahowa da ita, ba ?aramin faranta mishi rai hakan yayi ba.
Ba ma kamar yadda yaga Zulai ta ?ara kyau da cika na musamman, alamun da ke nuna lallai fa ba ta cikin matsala ko kaWan. Idan ya kalle ta yayi murmushi, sai ya kalli Hafiz yayi murmushi. Alamun da ke nuna zuciyarsa cike take da matsanancin farin ciki.

Minti Waya biyu kuma sai ya kalli Hafiz ya ce
"Hafizu na gode. Lallai ka cika Wan halak! Allah yayi maka albarka."

"Amin Baffa."
Ya amsa addu'ar da farin ciki sosai a fuskarsa, domin ya manta rabon da yaga irin wannan farin cikin a fuskar mahaifinsa.

Ita kanta Innaye bakinta ya ?i rufuwa, kamar gonar auduga haka take ta ya?e ha?ora tana shafa kumatun Zulaikha da ta ji sun ?ara laushi sosai.
"Zulai? Auta ke ce kika koma haka? Tubarakallah ma sha Allah! Lallai Hafizu baka watsar da amanar da na baka ba. Me kuke ba Autar tawa ne tayi irin wannan cikar Wakin Hafizu?"

Ya rasa amsar da zai ba Innaye, sai kawai yayi murmushi yana Wan sosa ?eya.

Ita kuwa Zulaikha da ake ta caftar a kanta ganin irin matsanancin farin cikin da tsofaffin suke ciki yasa jikinta yin sanyi. ?uduri na daban ke a cikin zuciyarta, a yanzu kam ta shiga tsaka mai wuya, anya idan ta zama sanadiyyar yanke wannan farin cikin a cikin ta?aitaccen lokaci ta yi ma tsofaffin da suke matsayin mahaifa a gare ta adalci kenan? Ko kuwa ha?uri za tayi ta cigaba da zama a sagale, cikin wata iriyar rayuwa ita ba mai ?anci ba ita ba mare ?anci ba har zuwa lokacin da bata san iyakarsa ba?

Tana wannan sa?e-sa?en da canki-cankar, har aka kira sallar azahar. Baffa da Hafiz suka fita zuwa masallaci, ita da Innaye suka yi alwala suka yi sallah a cikin Waki. Ta daWe sosai tana addu'o'i kala-kala bayan ta idar da sallah, har Innaye ta tashi ta fice ta shigo ma da Zulaikha abinci bata tashi daga kan dadduma ba.
[2/10, 10:39 PM] Fareeda Abdallah: "Auta addu'o'in sun isa haka. Ki katse haka nan ki tashi ki ci abinci."
Innaye ta faWa da murmushi cike fal da fuskarta, domin kallon Zulaikha da yadda ta koma kaWai ba ?aramin farin ciki yake saka ta ba.

"Innaye sannu da aiki. Ni fa bana ma jin yunwa, ki zauna mu ci tare don Allah. Na yi kewar hakan Wallahi."
Ta ?arasa maganar a shagwaSe.

Suna zaune gaban farantin abincin, suna ci suna hira Hafizu da Baffa suka sake shiga cikin Wakin.
"Kin ji Hafizu wai wucewa zaiyi yanzu, nayi-nayi ya tsaya su ci abinci ya ce a'a!"

"Ba dai tare da Auta zai koma ba ko?"
Innaye ta tambaya da sauri, idanunta a warwaje.

Yanayin yadda tayi tambayar yasa Hafiz da Baffa murmusawa.

"A'a Innaye. Ita kam tana nan, idan na dawo nan da sati biyu zan tafi da ita."
Hafizu ya amsa, har lokacin murmushin bai bar kan fuskarsa ba.

Nannauyar ajiyar zuciya Innaye ta sauke, kafin ta fara jera mishi addu'ar Allah ya tsare ya mayar da su gida lafiya.

"Amin Innaye. Na gode. Sai munyi magana ta waya."

"Yaya? Minti biyu don Allah"
Zulaikha ta kira shi da sanyin murya, a lokacin har sun juya za su fita shi da Baffa.

A tare suka sake juyowa suna kallonta.
"Ya aka yi?"
Ya tambayeta da Wan murmushi a fuskarsa, ganin idanun iyayen na kanshi.
"Ko za ki bi ni mu koma ne?"
Ya sake tambayarta, tsabar iya duniya irin nashi har yana wani Wan kashe mata ido Waya.

Martanin murmushinsa ta mayar masa, ?irjinta na bugawa sauri-sauri, amma ko kusa bata bari tsoro ya bayyana akan fuskarta ba. NannaWaWWiyar takardar da tun Wazu take ta yu?wu-yu?wu da shi a cikin hijabi ta fito da shi ta nuna masa
"Ka tuna wannan takardar?"

Kallon takardar da ke hannunta yayi, ya kalleta, duk da bai gane ko takardar mecece take nuna masa ba ya rasa dalilin da yasa ?irjinsa bugawa daram!
"Ban tuna ba. Takardar mecece?"
Ya tambayeta, sannan ya taka da sassarfa da nufin ?arasawa kusa da ita don karSar takardar ya karanta abinda ke cikinta.

Yana mi?a hannunsa da nufin karSa, ita kuma ta janye nata ta mayar cikin hijabi.
"Takardar da ka bani ranar da ka kaini gidan Mummy ne, har ka gwaSa min maganar cewa in dai su Baffa ba asarar kuWin tara suka yi ba idan na nutsu in zauna in karanta abinda takardar ta ?unsa. A wancan lokacin, Wallahi tallahi ko cikakkun sati biyu ba'a yi ba na karanta muhimmin sa?on da ka rubuta min a cikin takardar."
Tana zuwa nan a maganganunta ta sauke nannauyan ajiyar zuciya, ga mamakin iyayen biyu sai ga hawaye sun silalo daga kwarmin idanuwanta.

Shi kuwa Hafiz ?amewa yayi a tsaye kamar mutum-mutumi, jijiyoyin sadar da sa?onni daga zuciya zuwa ?wa?walwarsa suka tsaya da kai sa?onni na wasu da?i?u.

Da rawar murya Zulaikha ta cigaba da magana
"Yaya... Zaman ?aryan nan da yaudarar iyaye baza ta Sulle da mu ba. Na gaji da tunanin inda ?arshen tafiyar za ta ajiye ni, domin ta ko ina aka Sullo ni ce zan kwana a ciki. Don Allah, don darajar fiyayyen Halitta SAW, ina ro?onka kaji tsoron Allah, ka warware ma iyayenmu halin da muke ciki..."

"Mmmmmme yake faruwa?"
Baffa ya katse ta da tambayar da sauri, bakinsa na rawa. Kafin ta amsa ya ?ara tambayarta
"Me kike ?o?arin cewa Zulai? Hafizu me kuke Soye mana?"
Ya ?arasa maganar yana rarraba idanu tsakanin Zulai da Hafizu.

Ita kuwa Innaye, tuni ta fara jan duk wata addu'a da ta zo cikin zuciyarta, domin ta gama ha?i?ancewa duk abinda za su ji a yanzu, ba mai daWi bane a gare su.

Kafin Hafizu ko Zulai ta buWe baki tayi magana, sai ga sallamar Aunty Balira a bakin ?ofar Wakin, tun kafin a amsa mata ta yaye labulen Wakin ta shigo fuskarta cike fal da fara'a take cewa
"Wai ina Amaryar Hafizun take ne? Duk na ?osa in ?arasa aikin alalen da na tsira da ranar nan in zo inga irin ?iba da kyawun da yara suka kururuta min cewa kin yi."

Ganin yanayin da su Baffa suke ciki kuma sai tayi suuu a tsaye, lokaci Waya fara'ar fuskarta ta Wauke Wif
"Baffa me yake faruw..."

"Ne mi guri ki zauna."
Baffa ya katse ta tun kafin ta ?arasa tambayar da take niyyar yi mishi.

Jikinta a sanyaye ta zauna a ?asa kusa da Zulai da take ta aikin tsiyayar hawaye kamar an buWe famfo.

Umarnin zama Baffa yayi ma Hafizu, sannan shi ma da sanyin jiki ya lalubi hannun kujera ya zauna, saboda wani jiri da ya ji yana barazanar kayar da shi, tun ma kafin yasan takamaimai abinda yake faruwa tsakanin Zulai da Hafizu.

Idanunsa ya mayar kan Zulai, domin a ganinsa ta fi Wan dama-dama cikin yanayin da za ta iya musu gamsasshen bayani na abinda yake faruwa.
"Zulaikha?"
Ya kira cikakken sunanta a tausashe.

"Na'am! Baffa"
Ta amsa bakinta na karkarwa.

"Na sani tun kina ?an?anuwar yarinya ?ir?irar ?arya ki faWa don cikar wani buri ko son zuciyarki ba ya daga cikin halayenki. Kuma ina da kyakkyawar zaton har na aurar da ke baki canja daga wannan halin da na sanki ba. A bar ki dai da rashin ha?uri ga wanda ya shiga gonarki, da kuma Wan taurin kai ga wanda kika raina ajawalinsa. Amma na tabbata ko wanda kike ?i ne baza ki ?ir?iri ?arya ki jingina mishi don kawai ki cimma wani muradi na zuciyarki ba. Ina ro?onki kiji tsoron Allah, ki faWa mana gaskiyar abinda yake faruwa tsakaninki da Wan'uwanki kuma miji a gare ki..."

"Baffa... Tun da muka bar ?auyen nan, kwana Waya kacal nayi a gidan Yaya Hafiz... Duk sauran watannin nan na yi su ne a gidan Hajiya Saudah wacce yake kira da Mummy, ita Win Shugabansa ce a can gurin aikinsa..."

"Ban... gane ba..."
Innaye ta katse ta bakinta na rawa, zuciyarta na bugawa sauri-sauri don jin wani sabon labari da ko kusa hankalinta ya gaza Wauka.

"Rahina, kiyi shiru don Allah. Mu saurara tayi mana cikakken bayani yadda za mu fahimci abinda ke faruwa."
Baffa ya faWa ma Innaye da sanyin murya.

Hafizu dai har lokacin yana tsaye ?i ?am! Kamar wanda aka sassa?a shi. Duk da Baffa ya yi mishi umarnin zama, sam ya kasa motsa ?afafunsa balle har ya ja su zuwa gurin kujera, ko kuma ya zauna a ?asa kamar yadda sauran suke zaune. Baffa ne kawai a sama kan hannun kujera.

Ya riga da ya sani ko ba jima ko ba daWe fallasuwar abinda ke tsakaninshi da Zulai dole ne, amma bai taSa tsammani ko hasashe ko tunanin faruwarsa a irin wannan tsukun lokacin ba. Wani abin mamaki shi ne duk maganganun da ake yi yana ji tsaf, amma kamar wanda aka saka mishi dabaibayi a baki, sam ya kasa buWe baki ya ce uffan! Balle har yayi yun?urin kare kansa, ko kuma yayi ?arin bayani yadda baza'a ga laifinsa ba. A ta?aice ma, kansa ya kulle tamau, ya rasa ta ina ya kamata ya kamo bakin zaren kurar da Zulai take neman ta kwanto mishi.

Yana ji, Zulaikha ta gama bayar da labarin rikicin da ya shiga tsakaninta da Bintu, da har yayi sanadiyyar Wauke ta daga gidan da yayi zuwa gidan Mummy. A hankali, kuma cikin nutsuwa ta cigaba da bayanin zamanta a gidan Mummy, da irin kyakkyawar kulawar da ta samu a hannun zuri'ar gidan. Wanda shi ya hana rayuwarta tagayyara ko kuma taji ta ?osa ta dawo gabansu iyayenta.

Abu Waya da ta Soye musu a labarin shi ne soyayyarta da Kamal (Abban Imam), tafi-tafi har zuwa jiya da ta bu?aci lallai Hafiz ya kawo ta Fa?o ayau, ko kuma ita da kanta ta taho a motar haya.

Tana zuwa nan a labarin da take ba su tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, irinna wacce ta jima tana kuka. Muryarta a sha?e ta cigaba da cewa
"Rashin zama na a gidan Yaya ba shi ne abinda ya fi damuna ba Baffa. Wannan takardar da kuka ji ina tambayarsa ya tuna ta?"
Ta fito da takardar da har ta fara ji?ewa da gumi saboda cukwuikwuiyeta da tayi a tafin hannunta tana nuna musu, da karkarwar murya ta cigaba da cewa
"Duk da ya rubuta bayanin cikin takardar da yaren nasara ne, ba sa?on komai takardar take Wauke da shi ba illah na yanke igiya Waya daga cikin igiyoyi uku da suka ?ulla aure tsakanina da shi... Sannan ya rubuta takardar ne tun ranar da ya rabo ni daga gidansa, saboda rashin iya karatun turanci yasa ban san me takardar ta ?unsa ba sai bayan sati biyu da ba ni takardar. A yanzu haka kuma fiye da watanni shidda kenan da faruwar wannan al'amari, kuma duk da yana zuwa gidan Mummy ga shi nan ku tambaye shi na rantse da Allah bai taSa furta cewa ya mayar da ni Wakina ba har na gama iddah... A ta?aice dai Baffa, Innaye, Aunty Balira don Allah kuyi ha?uri ku yafe mana irin wasa da hankalinku da muka yi ni da Yaya, amma zance na gaskiya shi ne babu wani aure ko zamantakewar aure tsakanina da shi."

Lallai wannan shi ne asalin karin maganar nan da Malam bahaushe ke cewa Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana.

Izuwa yanzu da Zulaikha ta gama koro musu wannan cukurkuWaWWen labarin da basu taSa tsammanin faruwarsa a nesa da ?auyensu bama balle har ya faru a cikin ahalinsu. Ba Hafizu ne kaWai bakinsa da tunaninsa ya tsaya na wucin gadi ba, Innaye da Aunty Balira ma sun bi sahunsa.

Shi kuwa Baffa tsananin mamaki, takaici, ba?in ciki, haushi ne suka taru suka zame mishi wani dun?ulallen abu a ma?oshi. Sau uku yana ?o?arin kalato miyau don ya haWiye ko zai samu

32 / 53