Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 53

51K to 54K   out of 157.3K words

cikin shiru, babu abinda take ja a zuciyarta sai
'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahumma ajirnee fi musibati, wa aklifnee khairan minha.'

Baffa dai yana ta aikin kallonta, bai ?ara matsa mata da maganganu ba. Har sai da ita kanta ta samu nutsuwa hankalinta ya dawo jikinta, sannan ta tambaye shi
"Me tayi Malam?"
Kafin ya amsa ta cigaba da cewa
"Duk da ban san laifin me tayi maka ba don Allah kayi hakuri. Na san a baya ka ce ranar aurenta da aka sanya da Mudan bazai canja daga yadda ka saka shi ba, amma har yanzu ai da sauran kwanaki goma sha biyu. Me tayi? Ko kuma me ya canja wancan ?udirin naka?" Allah ya sani, ba na so a aurar min da Auta haka kwatsam ba tare da wata ?wa??waran sanarwa ba."
Ta jero maganganun da bayyanannen tashin hankali a fuskarta.
"Idan ka duba har yanzu Zulaikha ba ta cikin walwala. Fasa aurenta da Mudan ya ?ara jefa rayuwarta cikin zulumi ne da fargaba. Maganar da ta ji ana yi kuma na ranar auren bai canja ba za'a Waura da ko waye ya ?ara jefa ta cikin tunani da tsoron wane irin miji za'a aura mata. Ba ta walwala. Ba ta dariya. Magana idan ba ya zama dole ba sai mu kwana mu yini bata yi min ba. Dai-dai da abinci da ya zama dole sai na zauna kusa da ita na matsa mata sannan take Wan tsakura ta tashi. Kai baka ga yadda duk ta rame ta lalace ba? Allah ya sani ni da za ka ji ta tawa ma, ko nan da kwanaki sha biyun don Allah ka daga mata ?afa. Kai ne fa ke ?ara tunasar da ni aure lokaci ne Malam. Ina ji a jikina mijin Auta na musamman ne in Allah ya yarda. Ko ba jima ko ba daWe yana nan tafe, lokacin bayyanarsa a duniyarta ne kawai baiyi ba. In Allah ya yarda mijin da za ta aura zai kasance abin alfahari ne a gare ta da gare mu iyaye da ?an'uwanta da sauran jama'ar ?auyen nan baki Waya..."

"Kiyi ha?uri Rahina. Na riga na gama yanke shawara, tabbas in Allah ya yarda gobe iwar haka Zulai tana Wakin mijinta. Kiyi ha?uri, ki kuma yi fatan Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi, ya kuma sa shi wanda za ta aura abokin arzikinta ne."

Shiru tayi, tana kallonshi yana kallonta. Banda bugawa fafafat! Babu abinda ?irjinta yake yi, ta san halin Malam sarai. Tunda ya ce za'ayi tabbas za'ayi ne, babu abinda zai hana auren nan sai dai wani ikon Allah.

A raunane ta sake tambayarsa.
"Wa za ka aura mata?"

"Mijinta"
Ya amsa kai tsaye.

"Na sani mijinta za ta aura Malam. Sunan shi da ahalinsa za ka faWa min don Allah..."

"Wai duk wannan tambaye-tambayen na menene Rahina? Ke kin san dai idan ban fi ki son Zulai a cikin ?a?a ba sai dai muzo kan-kan-kan! Na ce miki ki kwantar da hankalinki. Banyi gaggawa a al'amarin Zulai ba, sati guda na kwashe ina Istikhara akan auren nan kuma babu abinda nake gani sai alkhairi. Ki nutsu, ki kwantar da hankalinki don Allah."

Ajiyar zuciya mai nauyi taja ta sauke, duk da yadda yake mata magana a tausashe don ta samu nutsuwa, Allah ya sani hankalinta ?ara tashi yake yi. Haka kawai ta ji Wakin yana mata wani irin zafi, numfashinta ya fara fita a wahalce. Tsam ta yun?ura ta mi?e tsaye, duk da ranar ita ce da girki, ita ya kamata ta kwana a turaka, ta rasa dalilin da yasa bakinta ya furta ma Malam Win
"Allah ya bamu alkhairi. Sai da safe."

Da idanu kawai ya raka ta har ta fice daga Wakin bai amsa mata ba.
"Uhmmm! Mata kenan"
Ya faWa a fili, sai kuma ya saki murmushi.

Kawar da tunanin komai daga zuciyarsa yayi ya koma inda ya zube dabino da goro da sweet, ya cigaba da cakuWawa yana zubawa a leda.


*****


Aka ce rana ba ta ?arya, sai dai uwar Wiya ta ji kunya. Washe gari, Kamar yadda Baffa ya faWa ma Innaye, mintuna goma sha biyar da idar da sallar azahar sai ga ?an samarin gidan da yara ?ananu sun shigo da sauri suna kwarmaton an Waura auren Zulai yanzunnan bayan an idar da sallar azahar.

?aura auren da tunda ?arfe goma na safe zuwa sha Waya tayi, Innaye ta fara tunanin ko dai Baffa da wasa yake mata? Duba da yadda cikin abokan zamanta biyu babu wacce tayi mata maganar auren, sannan cikin ?a?an Baffa mata takwas na ta da na kishiyoyinta da suke gidajen aure babu wacce ta je gidan da cewar ta je yinin biki.

Tsakanin Zulaikha da take cikin uwarWaki ta idar da sallah, da Innaye da take zaune akan dadduma tana lazumi, na rasa wacce ta riga wata isa bakin ?ofar fita.
Kawai ganinsu aka yi duk su biyun tsaye a bakin ?ofa sun ri?en labule.

"Labaran? Me kuka ce?"
Innaye ta tambayi babba daga cikin yaran bakinta na rawa-rawa.

"Wallahi da gaske Innaye. Yanzunnan aka Waura auren Zulai da Yaya Hafizu..."

Wani wawan ?a??arfan mahaukacin ihu da Zulaikha ta yanka a firgice, sannan ta tafi da baya tai wani mugun kifawa a ?asa shi ne abinda ya katse maganar da Labaran yake yi.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku na lalace... Auta...! Ke Auta... !! Me ya same ki? Zul..."
Luuuuu itama Innaye ta tafi za ta kifa a ?asa saboda tsananin firgici da tashin hankalin halin da Zulaikha ta shiga, da saurin gaske Labaran da ya isa gurin tun faWuwar Zulaikha ya ri?o Innaye ta kifa a jikinsa.

Cikin ?asa da mintuna biyu, har labari ya kai kunnensu Baffa da ke zaune a masallacin ?ofar gida ana ta rabon Sweet da addu'ar Allah ya bada zaman lafiya cewa ga Innaye can da Zulai sun suma.

Duk cincirindon mutanen da suke gurin fuskokinsu cike da alhini saboda jin abinda yake faruwa, Baffa ne ya fara shiga cikin gidan don kiyaye hakkin addini. Sai da ya shiga, can bayan wasu mintuna kuma sai ya aika yara aka shiga da sha?i?an ?an'uwansa da ?an'uwan Innaye maza.

A lokacin tuni Innaye ta farfaWo sanadiyyar ruwa da kishiyoyinta sukai ta she?a mata. Tana zaune a gefe sanye da zumbulelen hijabi tana sharSan kuka. Ita kuwa Zulaikha har lokacin bata farfaWo ba duk uban ruwan da aka watsa mata, sai dai an Wauke ta daga bakin ?ofa an shimfiWar da ita akan doguwar kujera.

Shigar ?an'uwan Baffa da na Innaye cikin gidan yasa abokan zaman Innaye da yaran gidan suka yi saurin ficewa daga cikin Wakin.

Ya zama saura Baffa ne zaune kusa da inda aka kwantar da Zulaikha yana tofa mata addu'o'i. Shigowarsu Baba Abubakar yasa Baffa ?ara gyara mata rufar hijabin da ke jikinta.

Har suka zaz-zauna, Innaye ta kasa Waga idanu ta kalli ko mutum Waya daga cikinsu, balle kuma har gaisuwa ya shiga tsakaninsu. Kukan da take yi ?asa-?asa kuma bata daina ba.

"Haba Rahina? Saboda Allah menene haka kike yi kamar ?aramar yarinya? Ni na zaci za ki fi kowa murna da wannan al'amarin saboda tuwon ki ne kuma man ki? Duk wannan kukan da kike yi har da su suma duk na menene?"
Yayan Innaye Mal Kabiru yayi maganar cikin faWa-faWa, saboda shi mutum ne mai zafin rai.

Innaye dai ba baka sai kunne, ta kasa ko Waga kai ta kalle shi balle yasa ran za ta amsa mishi.

"Assha! Assha! Yaya Rahina don girman Allah kiyi ha?uri. Wannan al'amarin fa duk ba wani abin damuwa bane kamar yadda kika Wauke shi, tunda dai ke da kanki kin san ba haramun muka aikata ba. To menene abin tashin hankalin?"
Baba Abubakar ya faWa a tausashe.

Shi ma dai bai samu amsa ba. Nan take kuma kowa a cikinsu ya fara tofa albarkacin bakinsa, suna sake tunatar da Innaye babu fa haramci a cikin auren Hafiz da Zulaikha tunda dai ba iyayensu Waya ba.

'Hafiz shi ne Wan da Innaye ta haifa a cikinta. Zulaikha ?a ce Waya tilo ga ?anwar Innaye da kuma ?anin Baffa mai suna Hamisu da suka kasance uwa Waya uba Waya.

Sun rasu ne sanadiyyar mummunar hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar komawa Fa?o daga Kaduna. Hatsarin da aka rasa rayuka da dama, Zulaikha tana cikin WaiWaikun rayukan da suka tsira a wancan lokacin shekaranta Waya da wata biyu a duniya.

Tun daga sannan, ri?on Zulaikha ya koma hannun Innaye da Baffa. Yarinyar da ?auna da sha?uwar da ke tsakanin iyayenta da su Innaye yasa suke mata wani irin so na musamman kamar ma fiye da ?a?an da suka haifa a cikinsu.

Duk da bata isa yaye ba a lokacin, yaye ta aka yi tunda tana tafiya. Kuma inda Allah ya sau?a?a lamarin shi ne tana cin abinci sosai. Sannan tun iyayenta na raye tana yawan yini a gurin Innaye, ta saba da su gaba Waya.

?a?an da Innaye ta haiha huWu ne a duniya, Balira ita ce Babba, kuma duk cikin ?a?an Baffa ma ita aka fara haifa. Sannan Rakiya, sai Ladidi, Abdul Hafiz wanda daga bisani aka yanke sunan ya koma Hafizu shi ne Auta, kuma shi ne Wa Namiji na farko da aka fara haifa a gidan Baffa.

A lokacin da ri?on Zulaikha ya koma hannun Innaye Hafiz yana da shekaru goma sha Waya a duniya. Amma kamar Wan shekara biyu zuwa uku, haka iyayen suke lelensa suna shagwaSa shi saboda tsananin ?aunar da suke masa.

Zuwan Zulaikha gidan shi ya hamSare gwamnatinshi daga gurin Innaye da Baffa. Kulawa, tattali, shagwaSa, lelen da ake masa duk suka koma kan Zulaikha. Hankalinsa bai ?ara tashi ba sai da wata rana Innaye ta rufe ido tayi mishi matsiyacin duka saboda kawai ya mari Zulaikha. Bayan dawowar Baffa kuma Innaye ta faWa masa abinda Hafiz Win yayi, cikin Sacin rai ya rama ma Zulaikha marin sannan ya rufe shi da faWa kamar zai dake shi.

Wannan shi ne mafarin ?ulluwar ?ar tsama tsakaninshi da Zulai. Wacce ita kuma tun da ta fara wayau ta lura ba ya ?aunarta ta masifar raina shi, a lokacin ita bata san ma ba Innaye bace ta haife ta.
[1/10, 10:29 PM] Fareeda Abdallah: Wata rana, a lokacin Zulaikha bata fi shekaru shida ba a duniya, cikin suSul da baka Hafiz ya goranta ma Zulaikha Baffa da Innaye ba iyayenta bane.
"Duk son da suke gwada miki da iskancin da kike yi suna goya miki baya na banza ne. Watan-wata rana za ki gane kuranki yarinya, tunda dai iyayenki ba sa raye."

Karaf! Maganganunnan a kunnen Baffa, ran Baffa ta yi mummunar Sacin da bai taSa yi ba. Bayan mugun dukan da ya lakaWa ma Hafizu kamar ba shi ya haifeshi ba, sai da ya tara iyalanshi kaf! Yara da manya ya kafa musu dokar cewa duk wanda ya sake goranta ma Zulai ba su ne iyayenta ba bai yafe mishi ba.

Wannan shi ne mafarin da yasa zancen ba Innaye da Baffa bane iyayen Zulaikha ya Sace Sat a gidan. Ta cigaba da zuba sangarta da shagwaSarta yadda take so, Innaye tana kiranta Auta. Kuma saboda ?a??arfan dangantaka da ke tsakanin su Innaye da Iyayen Zulaikha babu wanda zai ganta ya ce ba Innaye bace ta haife ta.

Hafizu kuma wannan laifin da yayi shi ne dalilin da yasa Baffa ya Wauke shi can-cak daga ?auyen Fa?o, ya kai shi wani ?auye mai suna Kasuwar magani gurin wani abokinshi, da niyyar yayi karatun Allo. Ashe rabon yayi zurfi a karatun boko ne.

Kasancewar ?auyen Kasuwar magani ta fi ?auyen Fa?o wayewa nesa ba kusa ba. Akwai makarantun boko har zuwa sakandire, saSanin Fa?o da makarantar boko iya firamare ne, a hakan ma ba ko wasu iyaye ke saka ?a?ansu ba. A kasuwar magani kuwa ga makarantun islamiya da makarantun hadda masu kyau babu laifi. Ko da Mal Bello ya tambayi Hafizu yana sha'awar karatun boko ya ce eh! Har ma ya ?ara da faWa mishi ya gama firamare acan Fa?o, Sai kawai ya saka shi a Sakandire da makarantar Islamiya da hadda, ba tare da sanin Mal Aminu ba. Wannan shi ne mafarin samun ingantaccen karatun Hafizu.

Kasancewarsa yaro mai tsananin ?o?ari ako wane fanni, ga nacin karatu, yana aji biyu na ?aramar sakandire malamai suka saka shi za na ?aramar jarabawa ta zuwa babbar sakandire. Yana aji biyar na babbar sakandire Principal ya saka sunanshi cikin Walibai masu zana jarabawar WAEC da NECO saboda ?o?arinsa.

A wancan lokacin, karatu a ?auyuka kusan kyauta ake yi, saboda iyaye basu gama yarda da bokon ba balle har su saki jiki suyi tururuwar kai ?a?ansu.

Bayan sakamako ya fita ne sunanshi ya fito cikin waWanda suke da maki mai yawa, anan ma dai principal Win shi yayi cuku-cuku ya jefa sunan Hafizu cikin Waliban da gwamnati ta Wauki nauyin karatunsu zuwa jami'ar Ahmadu Bello da ke zariya.

Acan ne kuma Allah ya haWa shi da Ibrahim Wan gidan Alh Lurwanu, taraiya ce irinta Wan gidan talaka futuk mai bala'in ?o?ari da Wan gidan mai kuWi mare ?o?ari amma akwai nacin karatu. Aka samu arashi kuma shi Ibrahim ba shi da girman kai ko kaWan, a ta?aice ma shi ne ya ma?ale ma Hafiz Win saboda ilimin da yake kwasa daga gare shi.

A can ?auyen Fa?o kuwa, tafiya ta tafi, an samu cigaba kaWan amma ba sosai ba. Sanin kowa ne ire-iren waWannan ?ananun ?auyuka da suke cikin lunguna sosai ba kasafai cigaban gwamnati ya cika samunsu ba, sai Wan abinda Allah ya tsaga da rabonsu kawai.

Sun samu cigaba ta fannin makaranta, an gina musu sakandire, amma fa irinta je ka na yi ka. Domin ko malaman da aka zuba musu ma ba kasafai suke zuwa aikinsu ba saboda nisan ?auyen.

An kai musu Network Win Glo a ?auyen. Sannan an gina musu ?aton asibiti amma fa babu wasu likitoci da ma'aikatan jinya sai Wai-Wai.

Zulaikha Aminu Fa?o, tana Waya daga cikin yaran da suka nace ma iyayensu bayan gama karatun firamare aka jefa musu a makarantar sakandire da ke ?auyen. Tafi-tafi za tayi karatun baza tayi ba har Allah yasa ta kai aji biyar na babbar sakandire sai kuma ta watsar da karatun. Saboda a lokacin duk ajinsu babu ?a mace mai shekarunta, ?an matan ?auyen da sun fara aji Waya, biyu, na ?aramar sakandire suke watsar da karatun ayi musu aure.

Ita kuwa da ta kai aji biyar na makarantar sakandire har wani kallo take yiwa kanta matsayin babbar yarinya. Duk da abinda ta tsira da shi a karatun bokon kawai hausa ne ta iya karantawa gar-gar, turanci kam ?ananun kalmomi kawai ta sani sai kuma ?an abinda baza'a rasa ba na ya?i da jahilci.

A bakin mutanen gari Zulaikha ta san ba su Innaye bane iyayenta, a lokacin ta kai shekaru goma sha biyar a duniya. A wannan ranar tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai fita, daga ?arshe zazzafan zazzaSi ya lulluSe ta. Kuma sam ta kasa faWa ma Innaye dalilin kuka da zazzaSin da take yi, a ganinta idan ta nuna musu ta san ba su ne iyayenta ba duk da irin wannan ?o?arin da suke yi a kanta bata yi musu halacci ba.

Da?yar ta iya yakice maganar a ranta ta kwantar da hankalinta, ta cigaba da yima iyayenta addu'a a Soye, ganin yadda Innaye da Baffa ke ta jelar kai ta asibiti ana yi mata allurai da bata magunguna kala daban-daban. ?an'uwanta da suke gidan aure na ta zirga-zirgar zuwa gaishe ta.

A lokacin ana gaf da yin bikin Hafizu. Ya gama karatu tuni, mahaifin abokinshi Ibrahim shi ya sama mishi babban aiki a Abuja saboda tsananin kyawun sakamakon karatunsa. Kuma cikin ?an?anin lokaci Allah ya tarfawa garinsa nono ya tara dukiya mai yawa, a hakanma don yana taimaka ma iyaye da ?an'uwansa da mutanen ?wauyensu. Hatta iyalin marigayi Mal Bello da ya zama sanadiyyar cigaba da karatunsa yana taimaka musu matu?a gaya.'

DaWaWWen buri ne a zuciyar Baffa tun da yaga yadda Hafizu ke samun manyan kuWaWe, da kuma yadda yaga hankalin Hafiz Win sam ba shi akan zama a ?auyen ko mis?ala zarratin, yaso Hafizun ya duba a cikin ?a?an ?an'uwa ko na mutanen gari ya zaSi mata a cikinsu.

Ta yadda duk cigaban da zai taka a duniya shi da matarsa dai tushensu Waya. Kuma matarsa baza ta taSa gudun ?an'uwansa ko kuma ta wula?antasu ba tunda dai garinsu Waya kuma ita ma ?an'uwanta ne. Amma kafin ya kai ga furta wannan ?uduri nashi ga Innaye ko Hafizu kawai sai ga zancen zuwa neman auren Bintu Hafiz ya zo musu da shi.
"Mahaifinta abokin Abba Lurwanu ne na kurkusa. Ya san komai a kan yarinyar da iyayenta, tare muka yi karatu da ita a Zaria. Amma saboda ita karatun Likita take yi shi yasa har muka gama ita bata gama ba. Amma yanzu ta gama har ta fara aiki, shi yasa iyayenta suka ce ta fitar da mijin aure. Za ka iya kiran Abba Lurwanu yayi maka cikakken ?arin bayani Baffa."

Sako sunan Abba Lurwanu matsayin abokin mahaifin Bintu ya katse ma Baffa duk wani hanzari. Domin Abba Lurwanu ya taka gaggarumin rawa a rayuwar Hafizu ta yadda bazai taSa iya watsa mishi ?asa a ido ba in dai shi Wan halak ne.

Haka nan ya watsar da burinshi. Kafin ma shi Baffa ya kira Abba Lurwanu shi Abban ne ya kira shi, cikin girmamawa da mutuntawa yayi masa bayanin duk halin da ake ciki game da yarinyar da Hafiz yake so.

A ?arshe ya ?ara da cewa
"To amma ya ka gani Baffa? Domin na faWa ma Hafiz duk matakin da ka yanke shi ne ?arshe, ni da shi duk umarninka ne abun bi a gare mu."

Wannan wu?a da nama da Abba ya mi?a ma Baffa yasa a kunyace ya nuna amincewa. Sannan ya ?ara da sallama ma Abba komai na hidimar bikin Hafizu, kama daga walittaka da komai da ake bu?atar uba mahaifi ya bar ma Abba. Godiya sosai Abba yayi da matu?ar farin ciki a muryarsa kafin suka yi sallama da Baffa.

Tun da aka yi bikin Bintu, ire-iren abubuwan da suke biyo baya na daga irin Wabi'un da

18 / 53