Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   49 / 53

144K to 147K   out of 157.3K words

ninka nata uku sau uku! In sha Allah!"

Sai ta samu kanta da sakin ?ar dariya, a hankali ta ce
"Sau tara fa kenan?"

"Eh! Ai tara ma kamar ya yi kaWan. Ko ita ma taran a ninka ta sau tara?"

Sosai ta sake dariya ba tare da ta shirya ba.
Ganin yadda ta sake tana dariya sai hakan ya sanyaya mishi rai.

Ya mike tsaye tare da mika mata hannu, babu musu ta sanya zara-zaran yatsunta a cikin nashi, yatsunta sun sha zanen lalle baki da ja, sun yi kyau sosai. Ya Wan Sata da?i?u yana kallon yatsun sannan ya janyo ta ta tashi tsaye.
Kai tsaye ya ja ta zuwa dakinshi.

Ya umarceta da ta shiga bayi ta dauro alwala. Da?yar, ta shiga bayin tayi alwala cikin dar-dar. Ganin yadda duk ta bi ta tsorata da shi a fili yasa yayi kokarin kin kai hannu ya tabata duk da yadda zuciyarshi take azalzalarshi da yayi hakan. Ya jira ta tayi alwalar ta fito, kafin shima ya shiga bayin don Wauro alwala.
Bayan fitowarsa daga bayin, kai tsaye inda take rakuSe a gefen gado ya fara kallah. Bai san sa'adda murmushi ya suSuce masa ba, ganin yadda ta wani takure, kamar ace kyat! Ta zura a guje.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya ?arasa kusa da ita, ya Wauki babbar rigarsa da ya ajiye a gefen gadon sadda zai shiga banWakin.
"Pls Wan bani mintuna biyu ?urratul-ayn, ina zuwa."

Kai kawai ta iya Waga masa alamar to. Shi ma bai takura sai ya ji maganarta ba ya fice daga Wakin. Mintuna uku tsakani ya sake komawa cikin Wakin, jikinsa sanye da jallabiya mai laushi sosai, kalar ruwan madara.

Hannunsa ri?e da darduma. Kai tsaye, wadataccen Sangaren da aka ware don yin a cikin Wakin ya nufa ya shimfiWa sallayar hannunsa.
"Amarya zo muyi sallah, mu gode ma rabbil-izzati da ya mallaka mana junanmu cikin ?an?anin lokaci. Sannan muyi addu'ar dacewa da dawwamammen zaman lafiya, kwanciyar hankali, zuri'a masu albarka."

Da yake idanunsa a cikin nata yake maganar, ya ga saukar lallausan murmushi a fuskarta. Sai kuma ta mi?e tsaye ta warware babban mayafin jikinta, ta rufa shi da kyau. Kamar kazar da ?wai ya fashe ma a ciki haka ta tafi la?a?ai-la?a?ai har zuwa bayansa, inda ya shimfiWa mata ?aramar sallayar da ya gani an ninke an ajiye da Al?ur'ani mai girma kan wani ?aramin stool da yake gurin.

Ya ja su suka yi sallar nafila raka'a biyu masu tsayin surori. Bayan sun idar, ya jima a zaune yana kwararo musu addu'ar samun daidaito da fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma zuriya Wayyiba, a hankali ita kuma take amsawa da Amin, har zuwa sadda suka shafa Fatiha.

Duk da tabbacin da yake da shi kan ilimin addininta, hakan bai hana shi yi mata tambayoyi kan addininmu ba. Kuma ya samu gamsassun amsoshi kamar yadda yayi hasashe.

Abinda ya gabatar na ?arshe shi ne matsawa kusa da ita, ya dafa goshinta yayi addu'ar da fiyayyen halitta SAW ya koyar don dacewa da alkhairinta, da kuma neman tsari daga dukkan sharrin da yake tattare da ita.

Bayan sun gama komai, a hankali ya kama hannunta ya mi?ar da ita tsaye, sannan ya saka idanunta cikin nasa ya fara kashe ta da lallausan murmushi, lokaci guda kuma yasa hannunsa yana aikin warware naWin gyalen da yake jikinta.

?ugunta ya ri?e da hannayensa biyu yana tafe da baya da baya suna tafe a slow motion cikin rausaya har zuwa tsakiyar Wakin, inda aka shimfiWa lallausan kafet, da wani irin salo na soyayya da kulawa ya zaunar da ita kan kafet Win. A kunne ya raWa mata
"?an ba ni minti Waya Sarauniyata, yanzu zan dawo."

Bai jira amsawarta ba ya fice daga Wakin da sauri. Falo ya koma, ya Wauko ledar da suka shigo da ita shi da Ibrahim.

Kai tsaye kicin Win Kareema ya wuce, ya samu babban faranti ya Wauraye, sannan ya warware ledar jikinshi na rawa, zuciyarsa cike fal da tunanin Kareema, da irin shape Win jikinta na coca-cola da ya gani yanzu da ya cire mayafin jikinta.

Yana gama warware ledar, daddaWan ?amshi ya cika hancinsa. Gashin naman talo-talo ne aka yi da albasa da tumatiri da yaji haWi da kayan ?amshi. Gaba Waya ya sake a cikin farantin, sannan ya Wauki wani farantin ya rufe ya kai Wakin Kareema da sauri.

Yana ajiyewa a gabanta bai Sata lokaci ba ya koma cikin kicin Win. Fridge ya buWe, ya Wauko kwalin lemun five alive, ya haWa da kofuna guda biyu, ya sake Waukar faranti guda Waya, cokula masu yatsu guda biyu, da ?ar ?aramar wu?a da cokula na cin abinci guda biyu ya koma cikin Wakin.

"Yau zan ?ara tabbatar miki ke Sarauniya ce a zuciyata ?urratul-ayni. Da kaina zan ciyar da ke har sai kin ce kin ?oshi."
Yayi maganar a tausashe, da ?ar ?aramar dariya a muryarsa.

Dirshan ya zauna a gabanta bayan ya tattare jallabiyarsa. Farantin naman ya janyo, ya fara yankawa sannu a hankali cikin ?warewa yana zubawa a empty plate da yake ajiye a gurin.

Lokaci Waya kuma a tausashe, bakinsa na raira mata wa?ar Ke ce Aljannata, na Auta waziri.

Duk da tana jin yunwa sosai, saboda rabonta da ?wa??waran abinci tun karin da tayi a Fa?o, sai Wazu da Zulaikha ta takurata ta sha ruwan tea mai kauri. A yanzu, ta kasa sakin jikinta sosai ta ci naman yadda ya kamata saboda kunya da fargaba, idan ta tuno irin sha?iyancin da Zulai tayi mata kan wannan dare, sai ta ji tsoro ya sake cika cikinta.

Ya dube ta kasa-kasa yana Wan murmushi
"Bari in ajiye miki sauran da safe sai ki Wumama ki ci kayanki. Kin san dai dole ne sai amarya ta ci naman amarci ko? Amma tunda naga kunya ta hana ki ci, ba zan takura ki ba. Sai dai assignment Wina na farko yanzu shi ne inyi ?o?arin cire miki wannan kunyar da take neman hana mu walawa yadda ya kamata. Don tsakani da Allah ni ba zan bari in cutu ba."

Bata amsa ba, sai Wan murmushi da tayi kanta a sunkuye. Sannu a hankali ya cigaba da yagar naman yana korawa da lemu.

Shi ma kaWan ya ci, don daman a ?oshe yake. Ma?asudin siyo naman ita ce, kuma ta kasa ci sosai. Yana gamawa ya Wauke komai ya kai kicin.
Yana dawowa ya fice zuwa Waya Wakin bayan ya faWa mata tayi shirin barci, yana dawowa.

Tunanin ya daren zai kasance a gare ta ne ya lulluSe zuciyarta, bata ankara ba kawai sai sallamarsa ta ji a bakin ?ofa, ko kafin ta amsa har ya shigo ciki, ya maida kofar ya rufe, tare da kashe wutar dakin.

Ganin duhu ya mamaye Wakin lokaci Waya yasa ta yi zumbur ta tashi tsaye tana laluben hanyar banWaki. Bata san sadda ya tako zuwa gare ta ba, sai ji tayi caraf ya ri?ota, lokaci Waya ya rungumota zuwa jikinsa.

"Haba Sanyin idaniyata, ni ne fa hasken Zuciyarki. Ko kin daina so na ne?"

Kanta yana jikinsa ta girgiza mishi kai a hankali.

"To tunda haka ne ki daina ?o?arin guduna. Ni fa ba dodo bane. Ba kuma zan taSa cutar da ke ina sane ba. Na san profession Win ki da ilimin da kike da shi sun sanar dake duk wani abu na rayuwar aure. To menene kuma na wani shure-shure bayan ba ya hana mutuwa? Sannan kuma idan baki sani ba ina so yanzu ki sani, babban burina shi ne nan da wata tara ki bani takwarar Innaye ko abokin zuwa Masallaci."

Cusa kanta ta ?ara yi a ?irjinsa a kunyace tana yar dariya.

"Au! Dariya na baki? Ko ya yi kusa ne?"
Kafin ta bashi amsa sai ta ji ya fara zuge zip Win rigarta. Sai kuma ya du?ar da kansa saitin wuyanta ya fara manna mata sumba, irin sassanyar sumbar nan da ke saka tashin tsigar jiki lokaci Waya.

Can kuma sai ya Wago fuskarta ya haWe leSenta da na shi, ya cigaba da sumbatarta a hankali yana Wan kallonta ta cikin hasken da ke shiga ta windojin Wakin, idanunsu ya hade waje Waya, zallar soyayya da kauna haWe da shau?i da suke yiwa juna manne akan fuskokinsu Saro-Saro.

Ya ?ara rirriketa a jikinshi yana jin kamar ya tsaga kirjinshi ya sanyata a ciki ko ya samu ya huta da abinda yake ji a game da ita.
"I love you baby girl, so much. Bakina da kalmomina har sun fara gazawa wajen bayyana miki hakan. Kin shigo cikin rayuwata kin haskata a lokacin da na gama cire rai da samun wani haske. Ina ?aunarki sosai, fiye da tunaninki."

Gaba-daya sai tsoron da take ji ya bar jikinta, ta daga ido ta kalleshi, zuciyarta na gaya mata wannan shi ne mutumin da ta amincewa ta mallakawa zuciya da ruhinta, wanda take yiwa so irin wanda bata taba yiwa kowa irinshi ba.

Bata san wa yayi motsi na gaba ba, ita ce ko shi? Kawai dai tasan cewa ta sake tsintar bakinta ne dumu-dumu cikin nashi, yana kwance duk wasu notikan kanta da suke kara maidata putty a hannunshi, ta kasa yin kataSus.

Haka ya cigaba da lulluSeta da soyayyarshi mai sanyaya rai, har bata san lokacin da ya kai ta kan gado ba, ya zare mata duk wata sutura ta jikinta. Ya hilaceta ta biye mishi suka keta hazon kauna, sai can da azaba tayi azaba ta fara shirin kwatar kwanta. Lokacin shi ai tuni ya gama yin nisa a duniyar da ta kaishi, baya jin kira balle ayi maganar dakatawa. Sai gashi tana bashi hakuri da kukan ya mata rai, shi ma yana bata hakurin.

Wannan dare dai bai saurara mata ba sai da ya maidata mace cikakkiya, sannan ya sarara mata, ya rungumeta cikin kirjinshi yana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa a lokaci guda. Kalamai yake amayar mata na godiya da zallar kauna, wadanda ita a karan kanta tasan cewa ba a cikin hayyacinshi yake fadarsu ba. Da yana sane kam da ya rage wani abun.

Dare ya tsala sosai lokacin da ya samu ya rabata da jikinshi da kyar, tana ta kuka da shessheka na azaba da zallan shagwaba. Shi da kanshi ya hada mata ruwan wanka bayan ya tsarkake jikinshi. Ya taimaka mata itama tayi wankan, yana bayin haka tayi a gabanshi duk da yadda taso ya fita.

Da ta gama kuma ya naWe ta da showel dauketa cak kamar jaririya, bai dire ta ba sai da ya je kan kujerar gaban mirror, ya jona hand dryer ya mika mata don ta busar da kanta, shi kuma ya tafi dauko mata kayan barci da zata sanya.

Bayan gama WaWWaga kalolin rigunan barcin a ?arshe ya zaSa mata wata doguwar riga tsayinta iya gwuiwa, kalar ruwan hoda. Rigar ta yi kyau sosai a idanunsa. Ganin duk motsin da zata yi sai tace 'wash!' yasa shi sake Waukarta cak zuwa kan gadon da ya gyara da kansa..

Gabadaya ta bi ta gama rikitashi da salon kissarta, sai nan-nan yake yi da ita. A ?arshe dai a ?irjinsa yayi mata makwanci bayan ya kunna musu ?wan lantarki mai duhu na barci, ko da ya duba fuskar wayarsa a lokacin, ?arfe uku da kwata na tsakiyar dare.

Lumshe idanunsa yayi da zummar barci, zuciyarsa cike da matsanancin farin ciki da ?aunar Kareema. Hannunsa na hagu dafe da tsakiyar bayanta, na dama kuma yana kanta yana aukin shafa lallausan gashin kanta da yake ta ?amshi.

A hankali yake jin saukar numfashinta a saitin wuyarsa, alamun ta fara barci.


********



Da saurin gaske ya ri?o wayar da take ?o?arin suSucewa daga hannunsa saboda tsananin mamakin da ya ji na maganganun da ke fita daga bakin Innaye.

Domin share ma kansa tantama, don tunanin ko kunnensa ne bai ji daidai ba ya saka shi cewa
"Innaye wai kika ce me?"

"Na ce ?aniyarka Hafizu"
Ta faWa daga can Sangaren, muryarta na Wan bayyana Sacin rai, saboda karo na uku kenan yana sake tambayarta tana maimaita mishi magana Waya.

?an dariya ya yi, idanunsa cikin na Ibrahim da yake tu?a motar za su je gaisuwar surukai gidan Mummy.
"Allah ya baki ha?uri Innaye. ?azu ina cikin mota ne, kuma kin san iskar hanya na saka network yin rawa ba'a ji sosai. Don Allah kika ce Bintu mene?"

"Na ce maka ?arfe goma sha Waya da rabi na safiyar yau a ?auyen nan ya yi ma Bintu. Da fari, duk mun zaci wani cin mutuncin ta zo yi mana, shi yasa bata samu wani tarba daga gare mu ba. Amma a yanzu tunaninmu ya canja Hafizu... Ina fatan dai ba tilastawa ko barazana kayi ma Bintu kan lallai dole ta zo ta bamu ha?uri cikin ?an?an da kai ba?"

"A'a! Wallahi ba ruwana Innaye. Ni ban san ma za ta zo ba."
Ya amsa da mamaki sosai a fuska da muryarsa.

"Madallah! To Bintu dai ta zo, ta bamu ha?uri sosai, har da kukanta Hafizu. Ta bi duk Wakunan su Laraba da na Baffanku ta zauna dirshan a ?asa ta nemi gafararsu. Wani abu da bata taSa yi ba shi ne shan ruwan Wakina, yau, ruwan randata Bintu ta sha Hafizu, na san ba ta shan komai ko cin wani abu na ?auyen nan, shi yasa ko tayi banyi mata ba. Amma da ta ji ?ishi da kanta ta ?arasa gurin randar ta buWe ta Webo ruwa da kofina ba tare da wani ?yan?yami ba ta kafa kai ta shanye Hafizu. Kuma ka san wani abun ban al'ajabi?"
Innaye ta jefa mishi tambayar da muryar da ke bayyana jin daWinta ?arara kan irin yadda Bintu ta girmamata a yau.

"A'a ban sani ba. Sai kin faWa Innaye!"
Ya amsa yana mamakin irin sau?in halin Innaye da sam ba ta da ri?o, ka shekara dubu kana Sata mata rana Waya idan ka tuba a gurinta an wuce gurin har abada. Lallai a gaida Innaye, a Sangarenshi kam ko kaWan bai Wauki al'amarin a wani abu da Bintu take yi har zuciyarta ba. Ya daWe da sanin ita ?wararriya ce a pretending, don haka duk wani salo-salo na makircinta baza ta taSa layance mishi ba.

Tunaninshi ya katse lokacin da Innaye ta cigaba da cewa

"Uhmmm! Da yake ban san za ta ci abincina ba, cikin Waki na barta na fita waje nayi aikin haWa dambun zogale da Baffanku ya ce yana sha'awa. Wallahi ina gama haWawa tun kafin inyi mata tayi ta ce
"Innaye a sammin dambun zan ci. Da mamaki na zuba mata, haka ta cire hijabin jikinta tana cin dambun nan tana shan ruwan randa, bata daina ci ba sai da ta cinye tas!

Ka ga abinda nake faWa maka ko Hafizu? Shi Wan Adam, ba'a taSa yanke masa tsammani da shiryuwa zuwa hanya madaidaiciya... Na san a yanzu haka tunani kake kila wani ?aryar ne yasa Bintu zuwa da wannan salon ko?"

Da mamakin yadda ta san tunanin da yake yi ya ce
"?warai kuwa Innaye. Kamar kin shiga zuciyata."

Ta yi dariya, sannan ta cigaba da cewa
"Hafizu kenan. To bari ka ji, da ace ana yanke ma bawa tsammani daga rahamar Ubangiji da ba'a ba bayi damar yin istigfari ba. Me yasa aka ce duk laifin da bawa ya aikata matu?ar ya tuba Allah zai yafe masa? Mu ma fa ?a?an Adam ne, muna kura-kurai da dama, kuma Allah yana yafe mana. Idan kuwa haka ne to me yasa mu????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? a junanmu idan muka yi laifi baza mu yawaita yafiya ga kawunanmu ba? DaWin gushi akan haka Kar dai ace ka manta da Hadithi na huWu da ke cikin arba'una? Ko wane bawa kafin mutuwarsa sai littafi ya tabbata a kansa sha?iyyun au sa'idun. Ina yi ma Bintu kyakkyawan zaton ta samu tuba ne tun kafin ajali ya riske ta."
Ta ?arasa maganar tana jinjinawa. Kafin ya ce komai ta cigaba da jaddada masa maganar da take yi
"Tabbas! Na hango tuba da shiriya na gaske a idanu da halayen Fatima a yau Winnan. Sai dai dalilin tuba da shiryuwar cikin ?an?anin lokaci ne dai Allah kaWai ya bar ma kansa sani.

Ni yanzu babban dalilin da yasa na kira ka shi ne, ko da ta zo bata tarar da su Rakiya ba. Rashida ta haihu a can ?auyen Wusar, sun tafi tun sassafe, ayi suna yau, gobe idan sun soya hakika su dawo gida. Na yi na yi Bintu ta komo Habuja yau ta ce baza ta bar ?auyen nan ba ko da kwana za tayi sai su Rakiya sun dawo ta ro?e su gafarar irin abubuwan da ta aikata musu tun daga farkon aurenku har zuwa yanzu..."

"Innaye ita Bintun ce da kanta ta ce za ta kwana a Fa?o?"
Ya sake tambaya da maWaukakin mamaki.

"?warai kuwa. Baffanku ma ya ce ta tafi, idan sun dawo shi da kanshi zai isar musu da ro?on gafararta ta ce ya yi ha?uri. Duk abinda ta Sata ita da kanta take so ta gyara, ashe wai ko zuwa ta bamu ha?urinnan iyayenta da Yayarta sun so su biyo ta tace su bari ta taho ita kaWai. Hafizu ko dai za ka kira ta a waya ka ce ta tafi kawai ba sai ta kwana ba...?"

"A'a Innaye!"
Ya katse ta da sauri.
"Ku ?yale ta kawai.. Tunda dai ita da kanta ta ce za ta kwana ba wani ne ya takura mata ba ai shi kenan. Kar a matsa mata da cewa ta tafi kuma taga kamar baku yafe mata irin munanan laifukan da ta daWe tana aikata muku bane..."

"Kuma fa haka ne."
Ta amsa da alamun gamsuwa da maganarsa.

"Yauwa to kin gani. Ku ?yaleta kawai, ita tace ta ji ta gani ai. Duk yadda ta yiwu dai zan kira ki anjima. Yanzu muna hanya ne za mu je gaishe da iyayen Kareema."

"To Hafizu, Allah ya kaimu jimawar. Ina fata dai Kareematun tana nan lafiya?"

"Lafiyarta ?alau Innaye."
Ya amsa fuskarsa cike fal da murmushin jin daWi don an tambayi lafiyar abar ?aunarsa.

"Madallah! Ka gaishe ta, yarinyar arziki. Tun da aka yi bikin nan yau kwanaki

49 / 53