Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   42 / 53

123K to 126K   out of 157.3K words

da Raudha ta gama ziga Bintu iya ziga, sannan ta fara rarrashinta da cewar ta adana kukanta ya isa haka. Kawai ta jira dawowar Hafiz suyi duk wacce za suyi, amma tana ?ara jaddada mata ko sama da ?asa za su haWe kar ta kuskura ta bar Aadil ya kwana biyu a ?auyen Fa?o.
Wannan tashin hankali da Raudha ta tarar da Bintu a ciki, shi ya hana ta faWa mata maganar Karima da Hafiz. Tsoronta Waya kar Bintu ta sume mata idan ta ji labarin tashin hankalin da ya ninka maganar kai Aadil Fa?o.

Ko a yanzu ba ?aramin tsorata tayi ba da wani irin numfarfashi da Bintun take ja akai-akai kamar mai cutar athma. Shi yasa ta ?ara Sata lokaci tana rarrashinta da tausasan kalamai, ta gyara mata Wakunan sama kafin isowar Baba Rabi.

Bata bar gidan ba sai da ta tabbatar Bintu ta Wan samu nutsuwa kaWan, ta sha paracetamol ta kwanta barci. Sannan ta samu ?warin gwuiwar barin gidan jikinta a sanyaye, zuciyarta cike da tausayin ?awartata da sai a yanzu ne namiji ya fara buWa mata shafi-shafi na munanan halayensa.

Babban fatanta Waya shi ne, Allah ya ba Bintu ikon fige wannan kazar wahalar a sau?a?e. Domin ita shaida ne, duk abinda zai biyo ta kan soyayyar da Bintu take ma Hafiz ba ta Waukar shi da sau?i balle har tayi gangancin Waukarshi a wasa. Yarda take da shi mai girma akan irin son da Hafiz yake mata, da wanda ita take mishi, babu kunya babu tsoron Allah take bugun ?irji a cikin ?awayensu tana tutiyar mijinta ya fita daban da sauran gama-garin mazaje. Tsakani da Allah ta fara tausayin Bintu.

Har ta isa gidanta zuciyarta cike take fal da tunanin mabanbantan hanyoyin da za ta bi wajen taimaka ma Bintu da dukkan ?arfinta da dabararta. Domin Bintu ta yi mata halarci mai yawa a rayuwa, baza ta taSa mantawa da taimakon Bintu gare ta ba har zuwa wannan matsayi da take kai a yanzu, sakamakon kyautatawa kuwa kyautatawa ce.



*******


Saboda tafiyar da baiyi da wuri ba, kuma ko da ya isa can Fa?o ma bai fito da wuri ba. Ya isa gida ne da misalin ?arfe goma sha Waya da minti biyar na dare. Kallo Waya za'ayi mishi a fahimci tabbas a jigace yake. Ga wahalar hanya, ga wahalar tu?a mota kuma tafiya mai nisan gaske, abinda ya daWe baiyi baiyi ba.

Ko a yanzu don direbansa ba ya nan ne, ?arsa ta cikinsa Allah yayi ma rasuwa bagatatan a garin Suleja. Dole suka tafi da Hafiz yayi ma iyalanshi gaisuwa, yayi musu sha tara ta arziki sannan ya tu?a motar da kansa ya koma Abuja.

Duk da dare ne, tsakar gidan ko ina haske ne tar kamar rana, saboda wadatattun ?wayayen lantarki masu haske sosai da aka ma?ala guri-guri a tsakar gidan.

Duk da tsarabobin da su Innaye suka haWa mishi a cikin mota ya kasa Waukar komai. Wayarsa kaWai ya iya Wauka sai makullin motarsa da ya zare ya nufi babban falonsu. Sannu a hankali yake tafiya saboda gajiya, yana isa bai tsaya wani Sata lokaci ba ya murza hannun ?ofar ya cusa kanshi cikin falon.

KiciSus suka yi da Bintu, wacce duk wannan dare da ya fara tsalawa idanunta biyu. Tsayuwar motarsa a tsakar gidan yasa ta Wauki hijabi ta saka ta sauko ?asa zuwa falon a gaggauce, ba don komai ba sai don zakwaWin ganin shin Hafiz ya dawo mata da Aadil? Ko kuwa su Innaye sun shirya tarbar bala'i da masifarta ne yasa suka yi gangancin ri?e mata Wa?

Abu na farko da ta fara yi shi ne kallon hannayensa, ganin wayam! yasa ta jefa mishi tambaya da murya mai cike da tartsatsin tashin hankali ba tare da ko sannu da zuwa ta samu sararin furta mishi ba.
"Hafiz ina ka kai min yaro na?"

Da yake Hafiz Win namijin duniya ne, ko kallonta baiyi ba. Sai ma hannunsa da yasa a hankali ya matsar da ita gefe Waya, saboda bake-bake tayi a gabansa ta tare masa hanyar shiga cikin falon.

Da yake a cikin bala'i take, sam bata lura da yanayin da yake ciki ba. Don haka da saurin gaske ta sake shan gabansa ta ?ara bake-bake har da ri?e ?ugu. Bakinta har yana tartsatsin miyau saboda masifa ta cigaba da cewa
"Babu inda zan matsa, na rantse da Allah babu inda zan matsa sai ka faWa min in da ka kai min Wan jaririn yaro na..."

"Bintu...!!!"
Ya ?walla kiran sunanta da wani irin tsawa mai taratsi da barazanar fasa mata dodon kunne.

Duk turjewa da daurin zuciyarta bata san sa'adda ta Wan ja da baya ba saboda firgitan da tayi. A Wan tsorace ta Waga ido tana kallonsa, sai a lokacin ta lura da yadda ?wayoyin idanunsa suka kaWa suka yi jajur, kamar ba nashi ba.

Da wata irin gwarjejiyar murya mai cike da fitina ya ce
"A yau! Ke Bintu kin ci albarkacin rayuwar mutane uku mafiya muhimmanci a gare ni. Na rantse da Wallahi! Tallahi!! Billahi!!! Ba don waWannan mutane uku ba da yanzu tsakanina da ke wani mummunan zance ake yi ba wannan ba. Don haka, ki matsa ki bani hanya in shiga ciki salin-alin ba tare da wani tashin-tashina ba. Idan kuma kin shirya taron Aradu da ka, don Allah ki sake yun?urin tare min hanya Bintu."

Duk yadda ta shafe tsawon yinin tana shan alwashi kan irin balbalin bala'in da za ta sauke mishi idan ya dawo gidan ba tare da Aadil ba, ta rasa dalilin da yasa maganganunsa suka yi ma sassan jikinta wani irin dukan da yasa lokaci Waya tayi la?was! Ba ma kamar waWannan manyan rantsuwa uku da ya jero mata a lokaci Waya. Duk da bata gama fahimtar inda maganganunsa suka dosa ba lallai jikinta yayi mutuwar da yasa lokaci Waya ta nemi duk wani bala'i da masifa da ta yini tana ji da su ta rasa.

Ita da kanta ta ?ara janye jikinta daga kan hanya. Shi kuma ya shiga cikin falon da wani irin taku na cikakken namiji ya nufi hanyar da zai hau sama ba tare da yayi mata kallo na biyu ba. Saboda wani irin ba?in Bintu da yake gani.

Bayan shigarsa cikin Waki, wayar hannunsa da makulli kawai ya ajiye ya faWa banWaki. Cikakkun mintuna ashirin da biyar ya Sata yana gasa jikinsa da ruwan zafi kafin ya fito, jikinsa sanye da rigar wanka.

Wasu mintuna goma sha biyar ya sake Satawa gurin shafa mai, shirin barci, ya fesa daWaWan turarukansa masu sanyin ?amshi sannan ya Wauki wayarsa ya bi lafiyar gado.

Ba tare da duba tsalawar da dare ya fara yi ba ya lalubo lambar Zulai, ya tura mata Wan gajeren sa?o mai Wauke da kalaman godiya da addu'ar Allah ya ?ara dan?on zumunci a tsakaninsu.

Bayan sa?on ya tafi ajiye wayar yayi, ya janyo lallausan bargon ya lulluSa har zuwa saman ?irjinshi. Luf yayi akan filo ya lumshe idanu yana tunanin abinda ya faru bayan Innaye ta tabbatar mishi baza ta karSi Aadil ta yaye shi ba.

Har ya kama hanyar komowa gida, zuciyarsa cike da shan alwashin yadda Innaye bata karSi Aadil yaye ba itama Bintu bata isa ta kai shi gidan Ummanta ba. Sai dai ta yaye shi ita da kanta a gidansu, idan kuma ba haka ba to saidai ta cigaba da bashi nono har zuwa sadda shi da kanshi Aadil Win zai yaye kansa.

Har ya kusa isa gida sai ga kiran Zulai ya shigo cikin wayarsa, karo na farko tun bayan da tayi aure.
"Yaya... Yanzu muka waya da Innaye ta ke cemin za ka je Fa?o yau. Don Allah idan baka yi nisa ba ga sa?o ka tafi mata da shi. Nima da yau za mu je, sai kuma bagatatan tafiya ta kama Abban Imam. Allah yasa dai baka yi nisa ba."

"Ban yi nisa ba Zulai. Na juyo ne, yanzu haka ma gani na kusa isa gidana..."
Ya amsa mata da cusasshiyar murya mai bayyana damuwa ?arara.

"Toh fa!! Lafiya? Me yake faruwa?? Ko ka fasa tafiyar ne???"
Ta tambaye shi cikin sanyin murya, zuciyarsa cike da tunanin me ke damunsa haka? Duk lalacewar Wan'uwa Wan'uwa ne, lokaci Waya ita ma Zulaikha ta ji ta shiga cikin damuwa. Duk da bai faWa mata abinda ke damunsa ba.

"A'a! Ba fasa tafiyar nayi ba..."

"To ko baka da lafiya ne?"
Ta sake katse shi da tambayar tun kafin ya aje numfashin maganarsa.

Da yake zuciyarsa cunkushe take da damuwar da shi kanshi ya san tabbas yana bu?atar abokin tauna wannan damuwa. Kuma ?arin shawara daga wani Sangare na zuciyarsa da ta tunasar da shi mai shawara fa aikinsa ba ya Saci, sai dai ace yana da ?arancin sirri. WaWannan dalilan guda biyu suka ja mishi gora wajen zaiyane ma Zulai duk halin da yake ciki.

Da takaicin munanan halayen Bintu a muryar Zulaikha ta ce
"Lallai ma Innaye. Ita Bintun wacece da har za'a ji tsoron ri?e Wan da ake da tabbacin ba nata ne ita kaWai ba? Allah yasa dai baka yi gaggawar mayar mata da Aadil Win ba?"

"Ban mayar mata da shi ba. Amma ga ni a hanya zan mayar mata da shi. Ya zanyi Zulai? Dole in mayar mata da shi tunda dai ba ni da mai ri?e min shi... Ke dai kin san tunda Innaye ta ce baza ta ri?e shi ba cikin su Aunty Balira ma babu wacce za tayi gangancin ri?e shi. Balle ma yadda ba?in halin Bintu bai tsallake kowa ba..."

"Duk da haka dai Yaya... Ai hannun mutum bai taSa ruSewa ya yanke ya yar! Ni idan baza ka damu ba ka kawo min shi in yaye."

Saboda tsabar yadda maganarta ya dake shi bai san sa'adda ya taka burki da ?arfi ba. In da Allah ya taimake shi shi ne a lokacin ya shiga cikin layinsu, da a kan babban titi yake irin wannan burki da ya taka na ba zato babu abinda zai hana motar bayanshi ta buga mishi.

Da saurin gaske ya gangara gefen hanya sannan ya kashe motar, bakinshi na rawa ya jefa mata tambayar
"Me kika ce Zulai?"

Dariya tayi sannan ta sake maimaita mishi abinda ta ce.

"Amma don Allah da gaske kike yi Zulai?"
Ya sake tambayarta da wani irin yanayi Soyayye, shi ba farin ciki ba shi kuma ba ba?in ciki ko fargaba ba.

"Wallahi da gaske nake yi. Amma idan baka amince ba sai in ha?ura..."

"Na amince. Wallahi yanzu zan kawo miki shi Zulai. Na gode. Na gode. Allah ya saka miki da alkhairi yayi miki albarka. Ga ni nan zuwa."

Bai jira cewarta ba ya tayar da motar da sauri yayi revers ya mi?e hanya. Fuskarsa bayyane da matsanancin fara'a zuciyarsa tumbatse da nutsuwa.

Har ya yi nisa sosai a hanyarsa ta zuwa gidan Zulaikha, sai kuma ya tuna ai duk wannan budurin da suke yi shi da Zulai basu sako mijinta Kamal a ciki ba.

Kuma tsakani da Allah in dai shi matsayinsa na babba yana da lafiyayyen hankali ya kamata ya tuna yanzu fa ba kamar da bane. Hatta Innaye da take kamar mahaifiya ga Zulai Kamal ya fi ta iko da Zulai.

Jikinsa a sanyaye ya Wauki wayarsa ya buWo lambar Zulai ya danna mata kira. Yana shiga ta Wauka, abinda ta fara tambayarsa shi ne
"Yaya ka ?araso ne?"

"A'a!"
Ya amsa mata. Sai kuma ya Wanyi shiru kafin ya cigaba da cewa
"Zulai kar inyi aikin marasa hankali. Kina ga Kamal zai amince a haWa Amaryarsa da raino alhalin ba haihuwa tayi ba?"

Dariyar da Zulai ta ?yal?yale da shi yasa shi ma ya Wan saki dariyar, amma jikinsa a sanyaye.
"Allah da gaske nake yi. Kin san fa Aadil har yanzu jariri ne. Shekararsa Waya ne kacal saboda tsabar fitina irinta Bintu ta tsiro da zancen yaye shi."

Ajiyar zuciya Zulaikha ta sauke bayan ta tsagaita da dariyar da take yi.
"Kar ka damu Yaya! Ko ba ya tafiya za ta iya yaye shi a shekara Wayan balle kuma yana tafiyarsa ko ina. Batun Abban Imam kuma ka kwantar da hankalinka, sam ba shi da matsala. Ko rantsuwa nayi babu kaffara bazai taSa yun?urin hana ni duk wani abu da ya shafi ?an'uwana ba, saboda ya san muhimmancinsu a gare ni. Ta gwaSa mishi magana da gan-gar. Kuma yau Winnan yayi tafiya, zai Wauki tsawon sati shida acan. Anjima nima zan tattara ?an abubuwan bu?ata ne in koma gidan Mummy... ka san ta kuma ba ta da damuwa."

"Haka ne! To ga ni nan zuwa."
Ya amsa da sanyin jiki yana jinjina maganar da ta gwaSa mishi a zuciyarsa.

Yana isa gidan Zulaikha, Aadil ya farka da wani irin gigitaccen kuka kamar wanda aka sa mishi wu?a a wuya. Da wannan dalilin yasa Hafiz yana shiga da motarsa harabar gidan ko gama daidaita fakin baiyi ba ya sungumi Wan hankalinsa a tashe ya nufi babban falon gidan.

Sau biyu ya ?wan?wasa bai jira an buWe masa daga ciki ba ya fara murza hannun ?ofar yana ?walla kiran Zulai hankalinsa a tashe da irin kukan da yaron yake yi. Shi daman ba irin mutanen nan bane masu masifaffen son yara, duk yadda suke dariya da Aadil da zarar ya fara kuka zai mi?a ma Bintu shi.

Daga can cikin falon, a gigice Zulai ta ?arasa sako hijabinta tazo ta buWe mishi ?ofa. Bai saurari kalaman barka da zuwa da take furta mishi ba ya fara mi?a mata Aadil da har wannan lokacin yake tsula kuka.

"?an tsaya mana Yaya."
Tayi maganar a nutse.
A hankali tasa hannunta na dama ta Waga fuskar Aadil tasa idanunta a cikin na shi. Da?i?u goma bayan nan sai ta haske yaron da lallausan murmushi, sannan ta Waga hannuwanta biyu ta mi?a mishi alamar ya zo.

Tun Zulai tana ?arama, ba sau Waya ba sau biyu ba Hafiz ya sha ji Innaye tana yi ma Zulai kirari da mai baiwar iya sarrafa ?ananun yara. Duk irin ?wuiyar yaro da fitinarsa sai dai idan Zulai bata so ?ulla har?alla da shi ba. In dai zuciyarta na son Wa, to fa ko ke uwar Wan sai dai kiyi ha?uri, domin idan za ta jera wata guda tana zuwa Waukar Wa ko ?a zuwa gidansu ana hana ta baza ta taSa gajiyawa ba. Idan kuwa har yaro ya saba da ita to fa uwa da kanta za ki ji tana aika ma da Zulai yaron ko bata je Waukarsa ba.

A wancan lokacin, bai Wauka baiwar na ta ya kai yadda Innaye take kururutawa ba sai yanzu da yaga ikon Allah. Aadil da kanshi ya mi?a ma Zulaikha hannu ta Wauke shi. ?arin mamakin kuma yana zuwa jikinta ya kwantar da kanshi a kafaWarta, sannu a hankali yake rage ?arfin kukansa har zuwa sadda yayi Wif! Kamar anyi ruwa an Wauke.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na samun kwanciyar hankali. Godiya ya fara yi mata haWe da kyawawan addu'o'i.
"Na gode ?anwata. Ubangiji ya baki duk abinda kike nema duniya da lahira. Allah ya ji?an mahaifanki da gafara."

"Amin thumma Amin."
Ta amsa addu'ar da murmushi a fuskarta.
"Ya yi break fast ne a gida?"
Ta tambayeshi kafin ya ?ara cewa komai.

"A'a! Tun misalin ?arfe uku na dare dai Mamanshi ta bashi nono, daga nan barci yake ta yi sai yanzu ya farka."

"To ba damuwa. Yanzu dai shigo min da kayayyakinshi, ina zuwa."
Ko kafin ya gama shigo da kayayyakin, Zulai ta haWa tea mai kauri da zallar madarar peak ta 1,2,3 wanda take ma Imam amfani da shi idan ya je gidan ta zuba milo ba tare da ta sa suger ko Wigo ba ta fara ba Aadil da Wan ?aramin cokali, yana sha tana mishi ?an wa?e-wa?e da wasanni.

Cikin ?an?anin lokaci sai ga yaron yana ?yal?yala dariya. Sai da ya ?oshi taf sannan ta surka ruwa tayi mishi wanka fes! Kafin Hafiz ya bar gidan, har Aadil yayi barci goye a bayan Zulai, abinda sam bai samu ba a gurin Mamanshi wai don tsoron kar tsayayyun nonuwanta su faWi.

Ganin ?arfe goma sha Waya saura mintuna kaWan yasa Hafiz mi?ewa tsaye, sai da ya gama kai sa?onnin Zulaikha da zai tafi ma da Innaye cikin mota sannan ya koma a tsaitsaye ya bata abinda ke tsakaninshi da Kareema.

Tsananin murna da mamakin lamarin yasa bakin Zulaikha ya ?i rufuwa, ta kasa cewa komai, har ya gama yi mata ?arin bayanin cewa
"Wannan dalilin ne yasa komai rana in sha Allah zan tafi Fa?o ayau Winnan. Domin gobe da wuri nake so su Baba Abubakar su shigo su samu Abba Lurwanu aje wajen iyayenta maza. Tunda dai Mummy ta bani dama gaskiya ba na son a Wauki wani lokaci mai tsawo ba tare da anyi komai an wuce gurin ba."

"Uhmmm! Ai ni na ma kasa magana Yaya. Allah ya tabbatar da alkhairi. Lallai ma Aunty Kareema, wato shi ne ana ta kwasar love da Yayana ko a gista min..."

"A'a kar ki ga wani laifin ?urratul-Ayni.. Ni ne nan na umarceta tayi shiru da bakinta har sai lamarin ya fara nuna. Yanzu da ya kamata ki ji ba ga shi na faWa miki ba?"
Ya Wauki laifin komai ya jibga ma kansa don kawai ba ya so a ?ullaci rabin ransa.

Ita dai Zuly ta kasa daina dariya... Abubuwa da yawa ne suka haWe a zuciyarta.
"Amma kuwa Bintu ta sani Yaya?"
Ta tambaye shi tana hasashen irin tashin hankali da haukar da Bintu za tayi idan ta ji irin gagarumin tashin hankalin da ke tunkaro ta.

"Bata sani ba. Amma zan faWa mata idan na dawo."
Ya amsa a lokacin da ya kama hanyar fita daga falon.

Sallama suka sake yi, tayi mishi addu'ar Allah ya tsare ya kiyaye hanya sannan ya fice daga cikin falon. Tana tsaye jikin window tana hangenshi har maigadi ya buWe mishi ?ofa ya fice daga gidan.

Labulen windon ta saki, ta koma tsakiyar falon sannan ta saki wata ?a??arfar dariya da yasa Aadil da ke bayanta motsawa kamar zai tashi, da sauri ta toshe bakinta don rage ?arfin

42 / 53