Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   50 / 53

147K to 150K   out of 157.3K words

bakwai kullum da safe da yamma sai ta kira ni ta gaishe ni. Don Allah Hafizu ka ri?e matayenka da amana ka ji ko?"

"To Innaye. Na gode. In sha Allah zan ?ara kiyayewa."

"Madallah"
Ta amsa sannan ta aje wayar.

A Sangaren Hafizu inda suka gama magana da Innaye nan ya watsar da zancen Bintu, ko Ibrahim bai ba labarin abinda yake faruwa ba, shi ma Ibrahim Win bai tambaye shi abinda yake faruwa ba.


******


Mintuna biyar Innaye ta ?ara a Wakin Umma Laraba suna ?ara jajanta irin canjin da suka gani a gurin Bintu, sannan ta fice daga Wakin zuwa na ta.

Da siririyar sallama ta shiga cikin Wakin, tausayin Bintu ne ya kamata, ganin yadda take kishingiWe akan daddumar Innaye da tayi sallah tana barci, kuma da alamun barcinta ya fara nisa, domin numfashi take saukewa cikin kwanciyar hankali.

?ara tabbatar da gaskiyar canjin da ta gani a tattare da Bintu tayi. Wannan ya wuce a ce duk tana yi ne don kissa ko makirci. Kamar dai ba Bintun nan mace ?ar gayu mai cike da ?walisa da gwalli ba. Bintun nan da ko akan kujerar Wakinta ba ta iya zama sai ta shimfiWa sabon daddumar da ko wane lokaci ba sa rabo da shi a mota. Yau ita ce kwance akan daddumar Innaye, ?afafunta na taSa dandaryar tile, lallai da gaske ne ba'a yanke ma bawa ?auna daga rahamar Ubangiji.

Innaye ta sake ?ura ma Bintu idanu, sai a lokacin ta lura ba ?aramin rama tayi ba, fuskarta ya ?ara tsawo, sai karan hancinta ya fito sosai. Nannauyar ajiyar zuciya Innaye ta sauke, sannan ta shige uwar Wakinta da tafiyar sanWa don kar ta tashi Bintu. Zuciyar Innaye cike da sa?e-sa?en ko auren da Hafizu yayi ne yasa Bintu yin laushi? Allahu aa'lamu. (Da yake ko da Baffa ya koma gida ranar Waurin aure bai faWa ma Innaye Hafizu ya saki Bintu amma ya saka shi ya mayar da ita ba.)

Kusan ko wane ?auye suna da Wabi'ar shimfiWa tabarmi a tsakar gida daf da sallar magriba, idan aka idar da sallah a fita tsakar gida yara da manya a zazzauna akan tabarmi. Wacce take da girki ta zuzzuba abinci, ana cin abinci ana hira. Wannan al'adar har yanzu ana yinta a ?auyaku, musamman lokacin zafi.

Su Innaye suna zaune a tsakar gida, Umma laraba ce tayi tuwon dare, tuwon dawa miyar busasshiyar kuSewa. Da an doshi gurin abincin babu abinda ke tashi sai ?amshin daudawa.

Su Innaye suna zaune akan tabarma suna cin abinci a kwano Waya su uku, yara na zaune a gefe Waya. Ita kuma Bintu tana cikin Waki Innaye ta dafa mata ruwan zafi ta kai mata kayan tea, duk da ta ce a ?oshe take ba ta jin yunwa, domin da rana dambu ta ci da yawa, har lokacin cikinta dam yake.

Ga mamakinsu kwatsam sai ga Bintu ta fito tsakar gidan, da murmushi a fusjarta ta zauna a gefen tabarmar da ta gani Innaye ta shimfiWa a ?ofar Wakinta.
"Sannunku da hutawa Innaye. Tun ina cikin Waki ?amshin daudawa ke bugun hancina. Ko za a Wan saka min tuwon kaWan in ci..."

"Kin gani fa Hajiya Bintu."
Inna Ladiyo ta Waga kwanon tuwon da suke ci ta nuno ma Bintu da sauri, kafin Bintu ta amsa ta cigaba da cewa
"Tuwon dawa ne fa, kin gansa ba?i?irin babu ko kyawun gani a ido sai laushi a baka. Wannan tuwon na tabbata ko an zubo miki a mugun ?yan?yamin da muka sanki da shi baza ki iya ci ba, kila ma ya saka ki amai..."

"Zan iya ci."
Bintu ta katse ta da faWin haka. Fuskarta na ?o?arin Soye rashin jin daWin kalaman da Inna Ladiyo ta jingina mata, amma da ta tuno abinda aka faWa Win halayenta ne ada, sai kuma cikin sauri tayi watsi da Sacin ran da ya fara damunta.
"Ummanmu tana yi ma Daddy tuwon dawa lokaci bayan lokaci, a zubo min kaWan, in sha Allahu zan iya ci."
Ta ?ara da faWin haka tana ?o?arin maye gurbin damuwarta da murmushi.

Umma Laraba da kanta ta mi?e zuwa kicin, ta yanki tuwon kaWan ta saka ma Bintu. Wani ?arin kulawa da tayi ga Bintun shi ne Waukar dun?ulen maggi mai star da tayi ta Wan barbaWa a miyan Bintu, ta Webi yajinta na tafarnuwa da ya ji maggi da kayan ?amshi ta zuba kaWan a gefe, sannan ta kai mata tuwon.
"Na dai yi karambanin barbaWa miki yaji, ban san ko kina so ba..."

"Na gode Umma, Allah ya saka da alkhairi."
Bintu ta faWa a ladabce sannan ta karSi tuwon.

Mamakin da Bintu ta sake shayar da yara da manya na gidan shi ne cinye tuwon da tayi tas, ta Wauki kwanon ta kai gurin wanke-wanke. Kuma ta cigaba da zama a tsakar gidan tana jan yaransu da hira ta hanyar tambayar sunayensu da na sauran ?an Wakunansu har aka kira sallar isha'i. Sannan ta sake alwala ta shiga Wakin Innaye tayi sallah.

Tun misalin ?arfe biyar na yamma Innaye ta shiga Wakin da Hafizu ya gina matsayin masaukin iyalansa, ta ?ara gyarawa tas! Magriba na yi ta kunna maganin sauro ta kai Wakin sannan ta rufo ?ofar.

Sai dai ko da ?arfe tara na dare tayi, Innaye ta gabatar ma da Bintu Wakin a matsayin inda za ta kwana, shiru tayi cikin tunani na wasu da?i?u.
Can kuma sai ta Waga kanta tana kallon gefen Innaye, idanunta ?asa-?asa, da sanyin murya ta ce
"Innaye in dai bazan takura miki ba ni na fi so in kwana anan, ko kan dpguwar kujera ma ya ishe ni. Amma idan zan takura miki sai in je can Win in kwanta..."

"Babu komai, ki shiga ciki ki kwanta kawai. Allah ya tashe mu lafiya."
Innaye ta faWi haka tun kafin ta aje numfashin maganarta.

"Na gode. Allah ya tashe mu lafiya."
Ta faWa sannan ta shige cikin Wakin.
Tsohon fallen zanen Innaye da yake ma?ale jikin bango ta Wauka ta Waura, bayan ta cire sket Win leshin da yake jikinta. Da bismillah a bakinta ta haye gadon Innaye da yasha gyaran zanin gado sabo fil, an lafe shi tas!kamar gadon Wakin matashiyar mace.

Da yake bata yi tunanin kwana zai kamata ba, shi yasa bata zo da shirin komai na kwanciya barci ba. ?uriii tayi da idanu tana kallon saman POP Win Wakin Innaye, zuciyarta cike da tunanika mabanbanta.

'Lokacin da sa?on text message Win Hafiz ya riske ta, daman tana cikin tension, domin ko a lokacin kwananta biyu a kwance bata da lafiya. Kuma ta ?i yarda sam a kaita asibiti, sai likita ne yake zuwa gida yana kula da ita.

A lokacin da sa?on ya shiga cikin wayarta, suna zaune ne ita, Ummansu, da Aunty Sadiya da ta je gidan ?ara duba lafiyarta. Kamar baza ta Waga wayar ba, sai kuma ta Wauka ta buWe, duk da wani sashe na zuciyarta na faWa mata ?arar shigowar sa?on da ta ji bazai wuce na kamfanin MTN ba.

Tun kafin ta gama karanta mummunan sa?on da ta Wauke shi a mafi munin wula?antaccen sa?o da Hafiz ya taSa aika mata a iya tsawon rayuwarsu, jikinta ya Wauki kyarma kamar ana kaWa mata ganga. Tana gama karantawa ta saki wayar a ?asa, tayi diri-diri tana zazzare idanu kamar sabuwar kamun hauka, sai kuma ta ?walla wani gigitaccen ihu da yasa Ummansu da Aunty Sadiya toshe kunnayensu a tsorace.

Bayan gama ihun, ?a??arfan kuka ta fashe da shi a lokacin Umma da Sadiya suka taho kusa da ita a gigice suna tambayarta Lafiya? Me yake faruwa?

"Yayarsu Wauki wayar ki duba mu ji sa?on me aka aiko mata da har ya jefa ta cikin wannan halin?"
Umma ta faWi haka ga Sadiya bayan ta lura Bintu baza ta nutsu ta faWa musu abinda ke faruwa ba.

Da saurin gaske Sadiya ta rarumi wayar Bintu da ke yashe a ?asa, tana gama karanta sa?on, saboda tsananin ba?in ciki da takaicin da Bintu ta ba ta ri?o kafaWar Bintun ta yi da hannu Waya, Waya hannun kuma ta yi amfani da shi wajen gaurama Bintu wani ?a??arfan marin da yasa lokaci Waya ta Wauke wuta Wif! Kawai ?arar da take ji a kunnuwanta shi ne dummmm!!!

Ta dawo cikin nutsuwarta ne ta ji muryar Aunty Sadiya tana ta zazzaga faWa kamar za ta ari baki.
?aiWaikun kalmomin da suka shiga kunnenta su ne
"Idan kin raina ma su Ummanmu hankali ni baki isa ki raina min hankali ba, mintuna ashirin na baki, ki harhaWo kayanki mu wuce can gidana, idan dai ba dussa bane a cikin ?wa?walwar kanki kwanaki bakwai ya ishe ki koyon yadda ake mu'amala da mutane.

Kasancewar Aunty Sadiya babbar ?a a gidan, kuma ta mori hankali da nutsuwar da iyaye da sauran ?annenta gaba Waya suke alfahari da ita. Da wannan dalilin yasa a mafiyawancin hukunci idan ta yanke ba'a mata musu a gidan. Kafin Daddy ya dawo, har ta Wauki Bintu da take sharSen hawaye da kumburarren kumatu sun wuce gidanta, sai a waya ta kira mahaifinsu ta faWa mishi duk abinda ke faruwa.

"To babu damuwa. Amma duk yadda ake ciki dai kar ta daWe, tunda mijinta ya mayar da ita Wakinta gara ayi duk mai yiwuwa ta koma Wakinta cikin ?an?anin lokaci."

"To shi kenan Daddy. In sha Allah."

Zaman gidan Aunty Sadiya da tayi na kwanaki bakwai, wata sabuwar rayuwa ce ta samu Bintu da taimakon Allah da taimakon Aunty Sadiya.

Aka yi sa'a kuma a lokacin da taje gidan Yar mijin Aunty Sadiya tana gidan tana jinya bayan sun gama jerangiyar asibitoci babu sau?i sai na Allah. Da farko dai Mummunar hawan jini ne ya haifar ma da mare lafiyar mutuwar Sarin jiki, daga bisani kuma sai ciwon ya juye kamar asiri aka yi mata, tana kwance sharSan kamar matacciya, Kashi a kwance fitsari a kwance haka take yi.

Akwai yaran mare lafiyar guda biyu da suke gidan suna jinyarta, sannan ga mai aikin Aunty Sadiya, amma duk da haka ta ga yadda Yayarta ke cin uban aikin kashi kamar Ummansu ke kwance tana jinya. Ganin hakan shi ya fara sanyayar mata da jiki.

Wani abu da ta ?ara lura da shi shi ne wani extra ordinary kulawa ta musamman da mijin Aunty Sadiya mai suna Alh Buba yake mata.
Ba tare da jin kunyar idanun Bintu ko ?a?ansu ba a gaban kowa yake yawan faWin
"Allah ya miki albarka Sadiyata. Allah ya sani Ina alfahari da ke, amma kulawa da Yaya Asabe da kike yi yasa na ?ara alfahari da ke. In dai Aljannarki a ?ar?ashin ?afata take, na Waga miki ki shiga a sau?a?e Sadiyata."

Idan ya jero ma Yayar tata waWannan kalaman, daga irin murmushi da wani Wan mirgina kai da take yi, ta san daWi da matsanancin farin ciki ne ke kai mata karo.

Kafin ta amsa sai ta Wanyi fari da ido, sannan ta mayar mishi da martani a tausashe
"Na gode Alhajina. Nima ina alfahari da kai. Kuma in banda kai da abinka... Yaya Asabe ai ko ba ?ar'uwa bace ta cancanci kulawa da kyautatawa saboda jarabtar da Allah yayi mata. Fatanmu dai Allah ya bata lafiya. Ina kuma ?ara ro?on Allah ya barmu tare har a Aljannatul-Firdaus."

"Ameen."
Suke amsawa gaba Waya. Bayan haka kuma Kamar ba tsofaffi ba, sai suyi musayar tattausan murmushi a tsakaninsu.

Bayan zama na fuska da fuska da suka sha yi a mabanbantan lokuta ita da Yayar tata tana mata rihazal Win munanan halayenta, da irin matakan da za ta bi a sau?a?e gurin gyara rayuwarta sannan ta gyara rayuwar aurenta. Ta kuma ?aru da sake kusanta kanta sosai da Ubangiji, duk inda ?arfe uku da rabi na dare tayi, Yayarta za ta fito turakar mai gida ta tashe ta, ta saka ta yin ibada, ba ta sake kwanciya sai misalin ?arfe takwas da rabi idan ta yi sallar Duha.

Daman dai sakaci ne irin namu na ?a?an Adam, amma duk inda damuwa da ?unci haWe da ba?in ciki suka yi yawa, to babbar mafita da hanyar da za'a kama mai Sullewa shi ne a kusanta kai da Ubangiji, sannan ayi ta istigfari da hailala.

WaWannan abubuwa da Aunty Sadiya ta koyar da Bintu cikin kwanaki bakwai, yasa ta samun wani nutsuwa da kwanciyar hankali na musamman, wanda ita da kanta baza ta iya tuna lokacin da ta shiga cikin makamancin wannan nutsuwar ba.

Har yanzu Hafiz da Wanta Aadil suna cikin sahu na farko a rayuwarta, amma fa kaso saba'in cikin Wari na yadda al'amarinsu ya dame ta a baya, yanzu ba ya damunta.

Sun tattauna muhimman batutuwa da ?ar uwarta, ta kuma gane kura-kuran da ta daWe tana tafkawa. Wani abun burgewa kuma shi ne da gaske ta Wauki aniyar gyara kura-kuranta.

Da wannan dalilin yasa bata yi ?asa a gwuiwa ba wajen zuwa ?auyen Fa?o neman gafarar su Innaye. Ba kuma don barazanar da Hafiz yayi mata ba.'

Nannauyan ajiyar zuciya ta ja ta sauke sadda ta zo nan a tunaninta, ta Waga hannu biyu sama ta karanto addu'ar barci ta shafa a fuska da sassan jikinta. Sannan ta lumshe idanu tana sauke numfashi cikin nutsuwa, har zuwa sadda nannauyan barci yayi awon gaba da ita.

Kamar yadda ta fara sabawa da Wabi'ar da Auntynta Sadiya ta Wora ta akai na tashi cikin dare yin ibada, ?arfe huWu saura minti goma na asubahi ta farka da salati a bakinta.

?ankwalin kanta da ya zame saboda barci ta Wauka ta Waura a kanta, sannan ta sauka daga kan gadon ta fito da nufin zuwa waje don Wauro alwala.

Tana fitowa Falo, ta ga Innaye tana sallar nafilfili, kamar yadda itama ta saba gabatarwa ko wane dare. Ajiyar zuciya ta ja na ?ara samun nutsuwa, ta Wauki buta nan lungun kujerar da take kusa da ?ofar Wakin Innaye, ta buWe ?ofa ba tare da tsoron komai ba ta fita tsakar gida ta Wauro alwala.


********


?arfe biyu na rana tayi ma su Aunty Balira a gidan Baffa. Da yake duk basu da labarin zuwan Bintu, turus suka yi da Waurarriyar fuska suna aika mata da kallon banza lokacin da suka ganta zaune dirshan a tsakiyar Wakin Innaye tana cin Wanwake.

Da farko jikin Bintu ne ya Wanyi sanyi bayan ta tuna irin tozarcin da tayi musu a haWuwarsu ta ?arshe. Sai kuma ta yi ?o?arin yalwata fuskarta da murmushi, a zuciyarta take godiya ga Allah da yasa bata bi dokin zuciya da zugar shaiWan ta mi?a su gurin ?ansanda ba. Yau da ina za ta saka kanta da kunya?
"Oyoyo... Sannunku da dawowa Auntys Wina. Ku shigo mana?"
Tayi maganar da sanyin murya, har lokacin murmushin fuskarta bai Sace ba.

"Uhmmm! Bintu kenan! Wani salon munafurci da kisisinar ce kuma ta saka ki yi mana murmushi? Kar dai ki manta, mu Win ne dai warki daidai da ?ugun kowa, la'ada waje za mu ci..."

Idanunta ciccike da hawaye ta katse Rakiya da cewa
"Wallahi Tallahi alkhairi ne ya kawo ni gare ku ba sharri ba Aunty Rakiya. Na zo neman gafararku ne, don Allah ku yafe min."

Dariyar da Rakiya da Ladidi suka saka mata yasa ta ?ara jin duk ta tsani kanta.

"Uhmmm! Bintu kar dai ace a cikin kwanaki bakwai da auren Hafizu da ?ar mutunci da arziki Kareematu har kin nuna kinyi luguf Win da za ki gane Borno gabas take..."

"Miye haka Ladidi? Me kike faWa haka? Wani irin maganganun banza ne haka kuke min a cikin Waki?"
Innaye da ta idar da sallah ta faWi haka ranta a Sace.

Kafin ta sake cewa komai Baffa yayi sallama a ?ofar Wakin. Da saurin gaske duk su ukun suka amsa masa sannan suka nemi gurin zama suka zazzauna a ?asa.

Baffa yana shigowa ya nemi gurin zama kan kujera ya zauna. Bayan sun gaishe shi, barka da dawowa ya fara yi musu, sannan ya tambayesu yadda aka yi taron suna. Bayan sun amsa da lafiya ?alau ne ya buWe taron da addu'a. Nasiha mai shiga jiki yayi musu akan falalar da ke tattare da yafiya, sannan ya ?ar?are maganganunsa da faWin abinda ke tafe da Bintu.

Ba don sun yarda Wari bisa Wari Bintu ta shiryu ba, duk suka yafe mata don ganin idon Baffa da Innaye.

Da yanayin jin daWi a fuska da muryar Bintu tayi musu godiya. Baffa ya ?ara musu ta?aitaccen nasiha sannan ya fice daga Wakin, bayan ya jaddada ma Bintu lallai tayi gaggawar gama cin abinci, ga direban da zai tafi Kaduna can Wan ma?wafcinsu sai ya wuce da ita.
Duk yadda Bintu ta so ganin sakin fuskarsu Aunty Balira abun ya gagara, ko da tayi nakwa-nakwa da fuska za ta saka musu kuka ?asa-?asa Aunty Rakiya ta galla mata harara, ta haWa da jan siririn tsaki ta kawar da kai.

Ita kuwa Aunty Ladidi don haushi ma buta ta Wauka ta fice daga Wakin, a cewarta, bayi za ta je.

"Kin ga Bintu, tunda dai duk mun furta mun yafe miki don Allah kar ki nemi ki takura mana. In banda ma zuciyar musulunci mai cike da imani ta ya lokaci Waya bawa zai yafe tozarcin da aka yi mishi shi ba sau Waya ba ba sau biyu ba ba sau uku ba? Ki tafi kawai Bintu. Don yafewa mun yafe miki, amma Worewar kyakkyawar mu'amala a tsakaninmu da ke zai biyo bayan yadda kika cigaba da mu'amalantarmu ne. Allah ya mayar da ke gida lafiya.."
Aunty Balira ta faWi haka, da fuska mara walwala.

Innaye bata nemi matsanta musu ba, saboda ta san suna da gaskiya. Bayan haka ma zuciya kowa da irin tasa, wata zuciyar ko ta yafe sai a hankali za ta manta abinda ya faru. Nasiha ta Wora musu daga inda Baffa ya tsaya har zuwa lokacin da aka aiko yaro wai idan Hajiya Bintu ta gama ta fito su tafi.

Bintu da taje garin daga ita sai ?aramar jaka rataye a kafaWarta, sai ga shi ta tafi da buhu guda na tsarabar da iyalan Baffa suka haWa mata. Tana zaune a cikin mota, tayi shiru tana tunanin halayen Innaye, Baffa, da ahalinsu. Zuciyarta cike da da na sani a karo na barkatai.

Duk da bata taso a gidansu ta

50 / 53