Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   20 / 53

57K to 60K   out of 157.3K words

da suke masa, abu Waya da suka fi jaddada masa duk su biyun shi ne lallai yayi ?o?arin ri?e amanar Zulaikha. Tunda dai sunyi -sunyi da Baffa ya bari ko mutane uku su raka ta Wakinta ya ?i.

"Ka ji tsoron Allah Hafizu. Ka ri?e ?ar'uwarka amana don girman Allah. Ka ga marainiya ce, Fiyayyen halitta SAW ya ce ni da mai taimakon maraya kafaWa da kafaWa za mu shiga aljannah. Ka ga kai riba biyu ma za ka ci, ga ta matarka ce, sannan kuma marainiya ce. Don Allah ka ji tsoron Allah, ka ri?e ta amana. Kar ka ga don ba idanun iyaye da ?an'uwa ka ce za ka zalunce ta."

"In sha Allah! Zan kiyaye"
Ya faWa da?yar! Kamar me ciwon baki.

Ko da ya isa ?ofar Wakin Baffa, ya daWe a tsaye cikin shiru, kamar kar ya shiga ciki yake ji. Amma ya sani ko bai shiga yanzu ba dole ya shiga Wan anjima kaWan, ya gaida Baffa sannan kuma yayi mishi sallama. Domin da safen yake so su juya zuwa Abuja.

Huci mai zafi ya fesar a bakinshi, idanunshi sun kaWa sunyi jaa, ga wani fitinannen ciwon kai da yake damunsa. Domin Jiya kwana yayi a takure cikin mota, ?wa?walwarsa a cushe, ya ma rasa wani irin tunani ya kamata yayi. Bai samu wani wadataccen barci ba.

Fargaba da tsoro ne cike taf da zuciyarsa, a yanzu da zai sake fuskantar Baffa, bai san kuma wasu zafafan maganganu zai zo mishi da su ba. Haka kawai, ya tsinci bakinsa da yin addu'o'i yana tsaye a ?ofar Wakin, sai da ya shafa addu'ar, kafin yayi ?arfin yin siririyar sallama, ya shiga Wakin bayan an amsa mishi daga ciki, a bayyane yake jikinsa a sanyaye.

Mamaki ne ya rufe shi ganin fuskar Baffa yalwace da murmushi, abinda bai sani ba shi ne, tun tsayuwarsa a bakin ?ofar da duk abinda yake yi Baffa yana kallonshi ta cikin labule.

"Zauna mana Hafizu"
Baffa ya bashi umarni.
Da saurin gaske kuma a tsorace yakai gwuiyawunsa zuwa ?asa ya zauna. Idanunshi har lokacin na kan Baffa, duk a tsammaninsa ko laifi yayi. Amma fara'ar da ke fuskar Baffa ita ke saka shi cikin wasi-wasi.

"Fushi kake da ni ko Hafizu?"

"A'a Baffa"
Ya amsa da sauri.
"Wallahi ko kaWan ba na fushi da kai. Wane ni inyi fushi da kai Baffa? Kawai dai al'amarin ne yazo min a bazatan da ban taSa tsammani ba. Ka yafe min irin yanayin da na nuna a jiya..."

"Babu komai Hafizu. Allah yayi muku albarka."

"Ameen Baffa"

"Ka yi ha?uri. Ka rungumi ?addarar da ta afka maka. Ni kaWai nasan dalilan da suka sa na yanke shawarar haWa aurenka da Zulai, ba tare da ita kanta Rahina ta san zan haWa auren ba. Idan ka ri?e Zulai da kyau, lallai nan gaba kaWan in Allah ya yarda za ta zame maka matar rufin asiri. Amanarta na dam?a maka ! Amanar Zulai na baka Hafizu!! Ina umartarka da ka ri?e Zulai da Amana Hafizu!!! Lallai idan ka ci amanarta za ka gamu da mummunar Sacin rai daga gare ni.

A yanzu Zulai matarka ce, kamar yadda Bintu take matsayin matarka. Idan ka fifita Bintu a kan Zulai ka zalunce ta, kuma ni ma ka zalunce ni, Allah bazai taSa barinka ba Hafizu.

Lallai ina mai tunasar da kai ka kiyaye ha??o?in iyalanka biyu da Allah ya Wora a wuyanka. Kar ka kuskura son zuciyarka ko tasirin ?iyayyar da kake yima Zulai tun tana ?an?anuwa, ko kuma zugar shaiWaniyar mace yasa idanunka su rufe ka kasa yi ma Zulai adalci. Ko kuma ka kasa sauke nauyin ha??inta da Allah ya Wora a kanka, idan hakan ta faru, tabbas za ka tashi a ranar lahira da shanyayyen Sarin jiki.
Yaushe ne tafiyar taku?"

"Da safen nan ne Baffa."
Ya amsa a hankali, gaba Waya hankalinsa a Wugunzume, saboda nasihar da Baffa yayi mishi sun ?arasa kashe mishi jiki gaba Waya.

"Tashi kaje ka gaida Rahina. Allah ya kai ku lafiya ya kiyaye hanya."

"Ameen Baffah"
Haka ya mi?e ?afafunsa a sake kamar wanda ya wuni yana zawayi ya fice daga Wakin.

Ko da yayi sallama a ?ofar Wakin Innaye ya shiga ciki, bayan amsa sallamar da gaisuwarsa da ta amsa a ta?aice babu wata magana da ta sake shiga tsakaninsu. Kamar surukan juna na gaske, haka suka kasance.

Shi kanshi yana ?asa yana Wan matsa yatsun hannayensa kaWan-kaWan yana jiran jin abinda za ta ce masa. Ita kuma fuskarta na kallon gefe, fuskarta babu walwala ko kaWan, casbahan hannunta take cigaba da ja sauri-sauri.

"Innaye?"
Ya katse shirun da ke tsakaninsu ta hanyar kiran sunanta a raunane.

A fakaice ta kalle shi, bata amsa ba ta sake kawar da kanta gefe Waya.

Ajiyar zuciya yaja ya sauke kafin ya cigaba da cewa
"Da safen nan za mu tafi. Kiyi ha?uri, a saka mana albarka..."

"Idan ka bari Bintu ta zalunci Auta ban yafe maka ba Hafizu."
Innaye ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa, da muryar faWa-faWa.
"Sannan kuma ban yafe maka ba idan ka Soye ma Bintu matsayin Auta a gare ka yanzu. Duk da dai wannan al'amarin ba wai ya kwanta min arai bane, har izuwa yanzu tunanin yiwuwarsa ko rashin yiwuwarsa nake yi, amma a iya Wan zaman da Auta za tayi da ku kafin mu samu hanya mai Sullewa, idan kai ko Bintu wani ya cuta mata don zalunci ban yafe masa ba. ?ace min da gani"
Har ya mi?e zai fita yana rangaji ta sake kiran sunanshi a tsawace.

A hankali ya juya yana kallonta, idanunsa sun ?ara kaWewa sunyi jajur!

Babu tausayinsa ko kaWan a fuskarta ta sake cewa
"Kuma ban yarda idan kuka isa can Habuja ka ajiye min Auta a wannan ?aton ginin na bayan gida inda kuka saba saba yasar da mu ?auyawa ba. Ita ma ka ajiye ta cikin aljannar duniyar da kuke kai da matarka, tunda dai a yanzu itama matarka ce. Allah ya bamu alkhairi."

Ko da ya buWe baki zai amsa addu'ar, inda kasan an saka zare da allura an Winke masa baki. Ga wani nauyi na musamman da bakin yayi mishi, a dole ya amsa addu'ar a zuciya ya kama hanyar ficewa daga Wakin.

"A'ah! Ango Ango! Na Bintu da Zulai ba da kanka a sare kaje gida ka cewa Innaye ya faWi."
Aunty Rakiya da ta sanyo kai cikin Wakin tayi maganganun da salon tsokana tana kallon cikin idanunshi.

Ita kuwa Aunty Balira cewa tayi
"Idanunka kenan Hafizu? Jiya ?ad da bus muka neme ka a cikin gidannan muka rasa. Ko duk murnar auren gatan da Baffa yayi maka ne?"

Ya rasa dalilin da yasa, yana kallon cikin idanun Aunty Balira wasu hawaye masu Wumi suka cicciko idanunshi. Kawai sai ya ?ara sauri ya fice daga Wakin don kar hawayen su zuba a gabansu.

Bai san Aunty Balira tana biye da shi ba, sai da ya shiga cikin soron gidan yaji muryarta Wan nesa da shi kaWan tana kiran sunanshi.

A yadda zuciyarsa ke wani irin zafi da tu?u?i, gani yake idan ya buWe baki da nufin yin magana tabbas babu abinda zai hana shi fashewa da ?a??arfan kuka. Don haka kawai ya zaSi yin shiru yana kallonta, har ta ?arasa kusa da shi ta ri?o hannunsa na dama a cikin nata.

A tausashe, da yanayin kalami mai nuna rarrashi da damuwa da halin da yake ciki ta ce
"Kayi ha?uri ?anina."

?an shiru ne ya ratsa tsakaninsu, kuma har lokacin ya kasa buWe baki yayi magana, sai ajiyar zuciya kawai yake saukewa akai-akai.

Ita ne ta cigaba da cewa a tausashe.
"Na sani ba'a kyauta maka ba Hafizu. Kayi ha?uri ka ji? A cikin biyayyar iyaye duk tsananinsa in dai ba saSon Allah bane in sha Allah alkhairi ne yake biyo baya. Saboda yardar Allah tana tare da yardar iyaye. Fushin Allah shi ma yana tare da fushin iyaye. Kar ka kuskura ka biye ma son zuciyarka ko kuma wata ?iyayya ka saSa ma iyayenka ka ji ko?"

"Na gode Aunty. Zan kiyaye in sha Allahu"

Ta?aitacciyar nasiha ta sake mishi har Aunty Ladidi ta shigo ta tarar da su a tsaye a zauren. Ita ma ta Wan tofa albarkacin bakinta cikin sigar rarrashi da tausasa kalami.

Godiyar ya sake musu, da al?awarin zai yi aiki da duk shawarwarin da suka bashi. Kafin ya fice zuwa waje, su kuma suka koma cikin gida.
[1/18, 10:59 PM] Fareeda Abdallah: Duk yadda Zulaikha ta so ta cigaba da nuna dauriya kasawa tayi, lokacin da taga gadan-gadan da gaske tafiya Abuja za a sake yi da ita. A Abuja ma ba ko ina za'a kaita ba sai gidan Bintu, Bintu da ta tabbatar duk cikin ?an'uwansu ta fi tsanarta. Kuma za ta je gidan ne yanzu ba'a matsayin ?anwar miji ba, a'a! Matsayin matar maigidan za ta je.

Ita ba jahila bace, daidai gwargwado tana da sani sosai a Sangaren Islamiya. Domin wani jajirtaccen malami suka samu daga ?ungiyar malamai masu shiga ?wauyuka yin da'awa. Tun da aka ajiye musu shi a ?auyen yana koyar da ?an mata da safe, da rana matan aure, da yamma samari, da daddare maza magidanta fiye da shekaru biyar bai taSa barin ?auyen da sunan tafiya gaba Waya ba. Sai dai ya je can birni gurin iyalinsa kwana Waya, biyu sai ya sake komawa ?auyen.

Da yawan ?anmatan da yake koyar da su karatun shashatau suke yiwa islamiyar, tana daga cikin WaiWaikun yaran da suka nace ma karatun, domin a yanzu haka tana da haddar izu ashirin cif a kanta. Kuma ta samu karatun littattafai da dama.

Domin lokuta da yawa ita ke ?ara ma su Innaye karatun Al?ur'ani mai girma a gida da sauran littattafai, hatta wasu hukunce-hukuncen addini ita suke fara tambaya, idan ta sani ta amsa musu, idan bata sani ba sai ta tambaya musu Ya Sayyadi a makaranta.

A yanzu, ta sani tunda aka Waura aurenta da Hafiz ha??o?inta sun hau kansa, kamar yadda nasa suka hau kanta. Kuskure kaWan za tayi mala'iku su fara tsine mata. Bata son auren ko baya son auren wannan bai isa uzuri ba a gurin Allah SWT. Idan tana son kanta da arziki ya zama dole tayi taka tsantsan wajen kiyaye ha??o?insa da suke kanta, har zuwa lokacin da Allah zai ?addara rabuwar auren. In dai ba kuma tana so ta jefa kanta a halaka bane.

Kafin ta birkice musu da kuka na tashin hankali, a Soye Aunty Rakiya ta ja ta zuwa Wakin Umma Laraba, tayi mata karatun dallah-dallah na yadda za ta zauna da Bintu, har ma da shi kanshi Hafiz Win ba tare da ta wahala ba.

Bakinta a gaba ta ce
"Aunty Rakiya auren nan fa Innaye ta tabbatar min bazai wuce sati Waya ba, don zaman sati Waya da zanyi acan ni me ma zai sa in shiga harkarsu har su wula?anta ni..."

"Amma ke kam anyi sakaryar yarinya Auta. Wai halin Bintun ne kika manta ko kuwa tsoronta kike ji? Kina sane da cewa in dai daga ?auyen nan mutum ya je gidan Hafizu ko na yini Waya ne muguwar yarinyar nan sai ta san yadda tayi ta ?untata masa.

Hatta su Baffa basu tsira da wula?ancinta ba. Balle kuma ke da tun a farkon-fari a bayyane take nuna ma kowa ba ta son ki ba ta ?aunarki. Kuma kin sani sarai ba wani shiri kuke yi da Hafizu ba, balle ganin idanunsa yasa ta jin shakkar yi miki wani muguntar.

Yarinya idan ma za ki zage damtse ki shiga gidan da shirinki gara ki zage, idan ba haka ba kuwa..."
Ta saki ?a??arfan ?wafa kafin ta cigaba da cewa
"Ba sati Waya ba, Ko zaman auren kwanaki biyu za kiyi a gidan irin gashin aya a tafin hannun da Bintu za tayi miki na rantse da Allah sai kin gane shayi ruwa ne. Don haka gara ma ki farka daga magagin da kike yi, ki shiga da shirinki da ta?amarki, ki nuna mata Zulan nan fa da ta sani a baya mare tsoro da Waukar iskanci har yanzu dai ke ce ba'a canja ki ba."

Haka Aunty Rakiya ta Sata lokaci sosai tana ?ara kitsa mata yadda za ta dinga ?watar kanta a hannun Bintu da Hafiz. Kuma inda Allah ya taimake su shi ne Mama Laraba ita ke aikin abin kari, har Aunty Rakiya ta gama yi ma Zulaikha bayanin da za ta mata babu wacce ta shiga cikin Wakin ballantana a kwaSa mata.

Basu fito ba, sai da Aunty Rakiya ta ji muryar Ladidi tana jajen ina suka shiga.

"Ki ji tsoron Allah Rakiya, me kike kitsa mata? Na fa san halinki ba ki da ha?uri kamar zawo."
Aunty Ladidi ta faWa tana Wan hararar Rakiya cikin wasa.

"Ba ruwana. Nasihar zaman aure kawai nayi mata irin wanda ake yiwa ko wacce amarya."
Ta amsa tana dariya.

"Ai kuma sai kiyi, dama ba'a san asalin balbela ba sai ta ce daga madina take. Kin ji Auta zo muje kiyi wanka, lokaci ya ?ure, tun Wazu Hafizu ke aiken idan kin gama shiryawa za ku wuce ga shi ko wanka baki yi ba."

Tun daga jin kalmar za su wuce Winnan jikinta ya ?ara wani irin sanyi ?alau. Nan take ta fara matsar ?wallah, har Aunty Balira tayi mata wankan Amare da ruwan turare da lalle kuka take yi ?asa-?asa.

Da yake fuskar Aunty Baliran a Waure yake tamau, shi yasa ko kaWan bata samu damar kawo mata wargi ba har aka gama wankan, da su haya?in tsuguno da na jiki, da wasu mabanbantan turaruka da tayi ta mutsuka mata a sassan jiki, a dole nata kallo da shatatar hawaye har aka gama shiryata cikin wata doguwar riga ?ar saudiyya mai kyau, kuma sabuwa fil, wacce bata san daga ina Aunty Baliran ta samo ta ba. Ta saka mata sabon hijabi mai girma da ya sauka mata har ?asa saboda ba wani tsawon azo a gani take da shi ba.

Sannan Aunty Balira da Ladidi da take ta yaba irin kyawun da tayi suka kama ta a lulluSe jikinta babu inda ba ya rawa suka kai ta gurin Innaye da tun Wazu take zaune a falonta ta zuba tagumi, idanunta sun kaWa sunyi jaa, kallo Waya za ayi mata a hangi gagarumin damuwa a tare da ita.

Sai da aka zaunar da ita gaban Innaye da cewar tayi mata nasiha sannan Zulaikha ta samu damar sakin ?a??arfan kukan da tuntuni take dannewa. Lokaci Waya ita ma Innaye ta saki na ta kukan a raunane, da alamun tun Wazu kukan ke son ?wace mata tana matsewa. Abin dariya abin tausayi, Zulaikha kuka Innaye kuka, haka ?a?an suka tasa su gaba suna kallo kamar suyi dariya ga kuma tausayin da ya lulluSe zukatansu, saboda a bayyane yake ga kowa irin matsananciyar sha?uwa da ?aunar da ke tsakanin Innaye da Autar ta. Basu taSa tsammanin aure zai nesanta su nisa mai nisa irin haka ba.

Ganin irin kukan da Innaye ke sharSa yasa lokaci Waya Zulaikha ta sake birkice musu da kuka kamar wacce aka ce mata idan ta tafi ta tafi kenan har abada.

Tun ?a?an suna rarrashi su kaWai, har sai da su Umma Laraba da Mama Laminde da sauran ?a?an gidan mata da suka je gidan suka shiga Wakin su ma suka fara aikin rarrashi.
Suna cikin wannan halin, Baffa ya shiga Wakin da sallama a tsawace, amma a wannan karon duk tsawa da hargaginsa bayyi tasiri kan Zulaikha ba, ?am! Ta ri?e ?afafun Innaye tana rusa ihun kuka da kurarin ita babu inda za ta je, a barta a gurin Innayenta in dai ba so ake ta mutu ba. Ita ta yarda a kwance aure da Hafiz a Waura mata da ko tsoho ne, ko gurgu ko kuturu ta yarda za ta zauna tayi biyayya in dai kusa da Innaye ne.

A fusace Baffa ya fice daga Wakin zuwa Wakinsa da nufin Wauko zabgegiyar bulalarsa da yake ladaftar da yaran gidan ?ananu, lura da abinda yake shirin yi yasa da saurin gaske Yayyinta suka SamSareta da?yar daga jikin Innaye suka fice da ita zuwa mota tana gunjin kuka.

?an kayayyakinta daman tun da sassafe an riga an zuba a cikin mota, fitowarta kaWai Hafiz da direba suke jira, ya riga ya gama sallama da kowa. Ranshi yayi mummunar Saci da yadda ?ar ?an?anuwar yarinya kamar Zulai take ta Sata mishi lokacin tafiya, sai dai ko kaWan bai nuna ba. Domin babban burinsa a wannan gaSar shi ne ya rabu lafiya da iyayensa.

Da farko yana zaune ne a ?ofar gida kan dakali, amma da yaga wasu daga cikin mutanen ?auyen sun ?i sarara mishi ya huta, kowa da irin neman taimakon da zai zo gurinshi, shi kuma ga irin ?uncin da zuciyarsa ke ciki, da yayi iya taimakon da zai iya kuma Zulaikha bata fito ba kawai sai ya shige Wakin ?annenshi maza da ke cikin zauren gidan.

Kukan da Zulaikha ke yi lokacin da za'a wuce da ita ta cikin zauren shi ne abinda ya dawo da shi hayyacinsa daga zuzzurfan tunanin da ya afka.

Mamaki mai tsanani ne ya kama shi jin irin kukan da take yi. Sai kuma ya mele baki gefe Waya ya mi?e tare da Waukar wayoyinsa ya fice daga cikin Wakin.

[1/20, 11:43 PM] Fareeda Abdallah: Akan idanunsa Aunty Balira ta buWe tafin hannun Zulaikha ta saka mata wayar Android Win da ya bata. Kamar Aunty Baliran ta san kallonta yake yi da mamaki a fuskarsa, sai ta juya tana kallonshi da ?ayataccen murmushi a fuskarta.
"Aro na ba ta ba kyauta ba. Na san a matsayinta na matar ?anina Hafizu nan da kwanaki kaWan za ka siya mata ?ar sha-far da ta ninka wannan a tsada, ka ga idan ta mallaki na ta sai ta dawo min da nawa."

"Uhmmm!"
Abinda ya iya ce mata kenan ya mayar da hankalinsa gurin dandazon ?an'uwansa da suke tsaye jikin motar suna ?ara rarrashin Zulaikha da har lokacin take kuka ?asa-?asa da tausasan kalamai.

Ranshi ne ya ?ara Saci, da ma ace yana da ikon yin abinda yake so ba tare da an samu mishkila

20 / 53