Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 53

42K to 45K   out of 157.3K words

yafe min. Kai mahaifi ne a gare ni idan baka yafe min ba ina zan saka kaina? Na rantse da Allah ba da gan-gan na so hana ku Waukar jaririn ba. Likitan yara Dr. Kauthar da ta fita yanzu kafin shigowarku ita ce ta ce lallai a kiyaye yawan Waukarshi saboda gudun kwasar cutuka domin fatar shi babu ?wari. Don Allah kuyi ha?uri ku yafe min. Baba Abubakar ku ma don Allah kuyi ha?uri. Malam ku yafe min don Allah bazan sake ba. Don Allah kuyi ha?uri. My dear kai ma ka yafe min."
Irin yadda take rusa kukan tana magiyar su yafe mata ba ?aramin tausayi ta basu ba.

Gaba Wayansu basu wani ja da nisa ba suka ce sun yafe mata. Har suka sa baki Hafiz ya ce babu komai ya wuce. Bata daina kuka ba har sai da taga Baffa ya karSi jaririn a hannunsa yayi masa addu'o'i.

Sannan ya mi?a ma Malam Ahmad ya sake yi masa huWuba ya raWa masa suna. Kafin ya raWa sunan ko da ya tambayi Hafiz ko suna da wani zaSin suna da suke so a raWa ma yaron da sauri ta riga shi cewa, duk dai a ?o?arinta na ?ara share laifinta ta ce
"Malam ka raWa masa sunan Baffa ne don Allah. Daman tun kafin in haihu na ?uduri niyyar in dai namiji ne sunan Baffa za'a sa idan kuma mace ce sunan Innaye za'a saka."

Da wannan maganar da tayi yasa Malam ya raWa ma yaron suna Aminu (Al'ameen).

Rabi da take kicin tana laSe tana kallo kuma tana jin duk abinda yake faruwa babu abinda take yi sai dariya.
"Iya duniya ya fi iya mota."
Ta faWa a fili tana sakin dariya ?asa-?asa. Da saurin gaske ta koma gurin aikinta ganin Bintu ta taso daga gaban su Baffa ta nufo kicin Win da sauri.

Tun safe, ta saka Rabi tayi mata farfesun kaji a zambaWa kayan ?amshi da Wan daddawa su dahu ruguf, ko za ta iya ci sosai saboda tunda ta haihu bakinta babu daWi.

Tana shiga cikin kicin Win ko kallon Rabi bata yi ba ta Wauki Waya daga cikin kulolinta masu tsada ta juye farfesun gaba Waya.
"Ki Wauko farantai da cokula ki kawo min falo."
Ta ba Rabi umarni gaf da za ta fice daga cikin kicin Win.

Da kanta ta zuzzuba musu farfesun ta ajiye a gabansu tare da basu ha?urin su ci kafin a ?arasa abinci. Ta mi?e za ta haura sama a fakaice ta kalli babynta da har lokacin yana hannun Mal Ahmad suna hira da Hafiz suna ta dariya.

Kamar ta ce ya kawo shi su ci abinci, amma tsoron kar ta sake Sallo ma kanta ruwa yasa kawai ta wuce zuwa sama duk zuciyarta a ?untace.

Lallai da gaske idan ka ji ?i gudu sa gudu ne bai zo ba. A irin wannan tsaka mai wuya da ta shiga cikin ?an?anin lokaci, bata taSa tsammanin za ta iya samar ma da kanta mafita cikin sau?i haka ba. Sai ga shi tsabar tashin hankali da tsoron abinda zai biyo baya tsakaninta da Hafiz yasa ?wa?walwarta buWewa, ta aikata aikin basira, hikima, wayau da bata taSa tsammanin za ta iya aikatawa ba.

"Hmmmm!"
Ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta huro iska mai zafi daga bakinta, sannan ta buWe ?ofar Wakinta ta shiga da siririyar sallama a bakinta. Duk jikinta a sanyaye, ga idanunta sun canja launi sun kumbura, alamun ta sha kuka.

Kallo Waya Raudha da take kwance akan gadonta tana daddanna waya tayi mata ta mi?e zaune da sauri. Idanunta warwaje ta ce
"???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????awata lafiya? Me ya samu idanunki?"

"Uhmmm! Ke dai bari Raudha. Yau na tsallake rijiya da baya. Sai fatan Allah ya kiyaye na gaba."
Amsar da ta iya ba ta kenan ta shige banWaki.


*****


?wan zabi ?warya uku, kajin hausa manyan zakaru guda goma. Garin kukar miya mai kyau da garin busasshiyar kuSewa su ne tsarabar da Baffa ya ri?o ma Hafiz da gidan Alh Lurwanu.

Duk yadda suka so tafiya da wuri sai da suka kai ?arfe Waya da minti goma a gidan Hafiz. Sun ci abinci sunyi nak! Sannan Baffa ya Wiba musu tsarabar ?wan zabbi ?warya Waya, kaji guda huWu, kuka da kuSewa dai bai Wiba musu ba, domin bai ga alamun cin tuwo a gidan Hafizu ba.

Baya ga haka ita kanta Innaye da ta bada kuka da kuSewar da sunan iyalan Alh Lurwanu ta bayar.

"Ita kuma matar Hafizu fa?"
Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa.

Sai da tayi dariya kafin ta amsa da
"Matar Hafizu ?ar gayu ce ta bugawa a jarida. Har muka gama zamanmu a gidan ko da kuskure bamu ji ta ambaci tuwo ba."

Dariya suka yi duk su biyun kafin ya sake mata sallama, ita kuma tayi mishi addu'ar Allah ya tsare hanya sannan suka fice daga gida.

Hafiz da kanshi ya tu?a su a mota zuwa gidan Alh Lurwanu. Ya rabbi! Mal Bahaushe ya ce in da ba ?asa nan ake gardamar kokawa. Wata irin tarba ta girma kuma ta musamman da basu taSa tsammanin samun irinta ba suka samu a gidan Alh Lurwanu.

Duk da sun daWe da shaida shi Win mutumin kirki ne. Amma a wannan ranar ya ?ara tabbatar musu da halayen kirki da karamcinsa. Ya kuma ?ara tabbatar musu da fa babu wani banbanci tsakanin talaka da mai kuWi, ko kuma banbanci tsakanin mutumin ?auye da na birni.

Irin yadda ya sake a cikinsu suna hira da SaSSaka dariya irinta manya suna caccafkewa a tsakaninsu wanda bai sani ba sai yayi tsammanin aminai ne na ?ud da ?ud. Tun ana gobe za su zo Hafiz ya sanar da shi zuwan su Baffa, don haka ya soke duk wasu shirye-shiryenshi na ranar da za su zo.

Kamar wasu manyan ba?i da suka taho daga wata ?asa, ?ayatattun girke-girke na musamman yasa aka yi musu. Bayan sun ci sun sha ya cika su da abubuwan arziki masu yawan gaske. A dole aka yi asaran tikitin jirgin ?arfe biyu da Hafiz ya yanka musu aka sake booking Win jirgin ?arfe huWu.

Wani ?arin karamci na musamman da yayi musu shi ne tun kafin su isa Kaduna akwai direba na musamman da Alhajin ya tura yake jiran isarsu. Suna isa, ba tare da Sata lokaci ba ya kwashe su da kayayyakinsu suka kama hanyar Fa?o a wata luntsumemiyar mota da idanu kaWai zai bayyanawa mai kallonta mai masifar tsada ce.

?arfe bakwai da rabi na yamma suna ?ofar gidajensu. Wannan tafiya dukkansu ba ?aramin daWinta suka ji ba, babu abinda ke fita daga bakunansu sai addu'ar fatan alkhairi ga Alh Lurwanu da duk zuri'arsa.

Ana sauke kayayyakinsu ba tare da Sata lokaci ba direba ya juya zuwa Kaduna, duk yadda suka so ya tsaya ko abinci ya ci ya ce musu a ?oshe yake. Ya tafi suna ta bin shi da addu'ar Allah ya tsare hanya ya maida shi gida lafiya.


******


Da mamaki a fuskarta take kallonsa. Da yake har ta fara barci ya tashe ta, sai tayi tsammanin ko kunnuwanta ne basu ji da kyau ba.
"Me ka ce Baban Yasin?"
Ta tambaye shi don ?ara tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiye mata.

"Na ce miki Hafizu ya kira ni Wazu da rana, ina cikin Kaduna ya ce in sami mai POS a tura mishi da Akawun namba. To a ta?aice dai bayan an tura mishi ba a daWe ba ya saka dubu Wari. Bayan ya tura kuWin ya sake kira na ya ce in samu motocin Bus guda biyu duk da tawa uku kenan musha mai, gobe idan Allah ya kaimu mu kwashe ku da sauran masu shirin zuwa suna mu kai ku Abuja..."

"Shi Hafizun ne ya faWa maka akwai masu shirin zuwa suna gidansa har mota uku?"
Ta tambayeshi tana Wan harhaWe giran sama da ?asa. Kafin ya amsa mata ta ?ara da
"Ai kuwa za ku mayar masa da kuWinsa. Domin ko ni da su Ladidi ba ma wani shirin zuwa suna balle sauran ?an uwa su ce za su je. Suyi sunansu lafiya, mu dai babu inda za mu je..."

"Wani irin zancen banza ne kike yi haka Balira? Matar Wan'uwan na ku sha?i?i namiji Waya tilo ta haihu kuma haihuwar farko ku ce baza ku je suna ba?"

"To miye a ciki? Mun yi murna, kuma munyi addu'a Allah ya raya. Zuwa suna Habuja ne dai baza mu je ba."
Ta faWa da dukkan gaskiyarta.

Kallonta yayi mamakinsa na ?ara girmama, sai kuma ya tuna tun bayan dawowarsu Abuja da daWewa bai ?ara ji tayi mishi zancen zuwa gidan Hafizun ba. Lallai akwai wani abu da ya faru a wancan lokacin amma bata faWa mishi ba.
Guri ya nema ya zauna a kusa da ita, a tausashe ya ce
"Me yake faruwa Balira? Ko akwai matsala tsakaninku da matar Hafizu ne?"

"Babu matsalar komai."
Ta faWa da sauri. Domin a ganinta matsalar da ta shafi Wan'uwanta daban! Haka zalika matsalar da mijinta zai sani daban. A ganinta babban kuskure ne ta kwaye ma Wan'uwanta baya a gaban mijinta. Kowa da muhimmancinsa daban!

"In dai kuwa babu matsala suna dole sai kun je. Domin kuWin da ya turo har mun ciccika tankin motocinmu da mai. Gobe sai tafiya da misalin ?arfe sha Waya na safe in Allah ya yarda. Bari ma in kira Baffa in faWa masa halin da ake ciki..."

"Ko ka faWa masa shi ma bazai goyi bayan zuwanmu suna ba. Kuma zan kira Hafizun yanzu in mishi kaca-kaca tunda ba ya jin magana, tun rannan na faWa mishi baza mu je suna ba amma don neman zance shi ne ya tura muku kuWin mai. To kuwa sai dai yayi asara, ni kam ba ni zuwa ko ina"
Baban Yasi dai bai saurareta ba ya fice daga Wakin ya barta tana bambamin faWa kamar za ta ari baki.

A fusace ta Waga filon da kanta yake kai ta Wauko wayarta, ?an?ance idanu tayi ta lalubo lambar Hafiz ta danna mishi kira. Second Waya biyu sai ta ja tsaki ranta a Sace. A can Sangaren Hafiz da yake ya san yadda suka rabu da ita tun sa'adda ya tambayeta masu zuwa suna yana ganin kiranta ya ki daga wayar, a karshe ma sai ya kashe wayar gaba daya don kar ta cigaba da damunsa.
[1/4, 7:40 PM] Fareeda Abdallah: Zancen d'aukar shatar motoci da Hafiz yayi ga masu niyyar zuwa suna gidansa yana isa kunnen Baffa ya karbi maganar da hannu bibiyu. Irin yadda ya dinga nuna farin ciki da zumudi, ba karamin mamaki ya ba Innaye ba. Domin tun a daren ya fara kiran mazajen 'ya'yansa mata da suke gidan aure yana nema musu izinin tafiya suna gidan d'an'uwansu a Habuja.

Ya kira 'yan'uwansa ya sanar da su lallai su fada ma matansu da yayansu da suke gidan aure, duk wacce take son zuwa suna gidan Hafizu mota kyauta ne zuwa da dawowa.

Ya aika gidansu Innaye ya fada ma yan'uwanta. Tun Innaye tana shiru taga iya gudun ruwansa, sadda ta ga ya fara aikawa gidan abokan arzikinta yasa ta kasa hakuri har sai da ta ce mishi
"Anya Malam gayyar mutanen nan da kake yi zuwa gidan Hafizu zai haifar mana da d'a mai idanu kuwa? Matar Hafizu ba irin matan birnin nan bane da suke son mutanen kauye fa..."

"Ba don ita za su je ba. Don shi ne, tunda dai shi namu bai guje mu me ya dame mu da halinta na gudun mutanen kauye? Na tabbata Hafizu bazai taba bari matarsa ta wulakanta masa yan'uwa ba."
Ya katse Innaye tun kafin ta aje numfashin maganarta.

"To shi kenan! Allah ya kaimu goben Lafiya."
Ta yi addu'ar jikinta a sanyaye.

"Ameen."


*****


Motoci ukun da Hafiz ya dauki shata sai da suka cika tam da yan'uwa da abokan arziki saboda kara irinta mutanen kauye. Duk yadda Yaya Balira taso zille ma zuwa sunan sai da Baffa ya tilasta ta tafiya, haka nan ta shirya yan kayayyakinta kala biyu a cikin jaka suka kama hanya, duk zuciyarta a kuntace. Domin Allah ya gani sam bata so tafiyar ba. Ita da yan'uwanta da suke daki daya fuskokinsu ba yabo ba fallasa.

Su kuwa sauran yan'uwa da basu san dawan garin ba bakunansu har kunne. Sai murna suke suna dararraku, ko wacce tana baje labarin irin nisan tafiyar da ta taba yi a rayuwarta. Dukkansu dai kololuwar tafiyarsu Kaduna ne, hatta yan'uwan Hafiz da suke uba daya basu taba zuwa gidanshi ba tunda yayi aure sai yanzu da za su tafi.

Karfe biyar na yamma suka isa gidan Hafiz. Da yake ya shirya ma zuwansu sosai, wadataccen abinci yasa aka dafa musu da ya ji nama zuk'u-zuk'u. Katan-katan na lemu masu sanyi aka tare su da shi da ruwan gora, komai dai sun same shi a wadace sai da suka ci suka sha suka bar saura.

Dakunan BQ da suke manyan dakuna kuma a wadace tun kafin su isa yasa an gyara ko ina fes! Daman akwai funitures a ciki, duk abinda babu kuma kafin su isa an tanade shi.

Gidan Hafizu bai fara d'aukar harama da nuna alamun gidan da za'ayi suna bane sai da suka isa. Duk da tazarar da ke tsakanin inda suke da ainahin inda matar gidan da daidaikun yan'uwa da kawayenta ke zaune har nan ake jin hayaniyarsu.

Bintu ta cika tayi fam kamar za ta fashe. Ita kadai sai huci take yi kamar kububuwa, amma ta kasa furta ko uhmm! saboda Hafiz yana gidan. Kamar wata sakarya, da ya shiga dakinta ko kuma ya kira ta zuwa dakinsa sai tai ta washe mishi baki tana dariya duk don dai kar ya ji a zuciyarsa kamar ba ta maraba da zuwan 'yan'uwansa.

Tun abinda ya faru ranar da su Baffah suka je a tsorace take. Don ma Allah ya taimaketa Hafiz din ba mutum bane mai rik'o. A sadda abu ya faru, idan ya nuna bacin ransa cikin kankanin lokaci zai warware ya koma da walwalarsa. Shi yasa take iya yinta wajen kiyaye abinda zai sake janyo mata wani bacin rai da ba ta tunanin za ta iya warwareshi cikin sauki.

Abu daya da ya aikata ta ji nutsuwa kadan a ranta shi ne bai bar yan'uwansa sun shiga bangarenta ba. Umarnin shiryawa yayi mata sannan ya dauki Baby Al'ameen wanda ake yiwa inkiya da Aadil suka je bangaren da aka sauki bakin suka gaisa.

Tana ji tana gani sukai ta damukar jaririn ranta yana k'una, amma ko a fuska ta gagara nunawa har suka gama gaisawa da tambayar lafiyar su Innaye sannan ta fice ta barsu da d'an'uwansa. Har d'an tsayawa tayi ko za'a ce ga Aadil ta wuce da shi amma ta ji shiru, haka nan ta fice ta barsu da Hafiz tana ta jan kananun tsaki a zuciyarta.

Gudummuwar naira dubu talatin 'yanuwansa suka hada mishi a matsayin gudummuwa. Sadda Aunty Balira ta kebe shi gefe ta bashi kudin ji yayi kamar zai saka kuka. Zuciyarsa ta kara cika da kaunar 'yan'uwansa.

"Mun so mu siya ma Babanmu kayayyakin jarirai sai kuma muka ji tsoron siyan abinda bai dace da ku yan birni ba. Shi yasa kawai muka yanke shawarar taho maka da kudin, kayi hakuri. Ka san yanayin garin..."

"Haba! Ba komai Wallahi Aunty Balira, na gode. Allah ya bar zumunci. Na ji dad'i sosai Wallahi. Amma yanzu dai ki ajiye min kudin a gurinki, zuwa safe in sha Allah zan karba."

Da haka suka rabu, ya karbi jaririn da ke ta barci hankalinshi kwance ya mayar da shi gurin Mamansa. A lokacin ana ta kiraye kirayen sallar Magriba a masallaci.

Washe gari da asubah tafiyar aiki mai matukar muhimmanci ta kama Hafiz da wasu daga cikin abokan aikinsa. Lagos za su tafi, bai so tafiyar ba ko kaWan, amma da yake kira ne da suka daWe suna jira daga branch Win su da ke Lagos yasa tafiyar ta zama dolen-dole. A gaggauce ya fara shiryawa yana rarrashin Bintu da take ta matsar ?walla, ta ci burin taron sunan nan ayi da shi, sai ga shi tafiyar ta bazata ta rusa musu bodjet.

Taron suna ne suka shirya shi irinna ?an birni kuma yan gayu, domin ba ma a gidan za'a yi taro ba. Event center suka kama mai matu?ar kyau da tsada, acan suka shirya za'ayi taron sunan. Duk Winke-Winken da tayi sunyi ne tare da Hafiz, taron suna ne da suka shirya gudanar da shi kamar gagarumin taron bikin aure. Sai ga shi tana ji tana gani tafiyarshi ya rusa kaso arba'in cikin dari na tsarin da suka yi ma bikin sunan.

Ranta a bace ta raka shi har gurin mota yana kara rarrashinta da tausasan kalamai, bata koma cikin gida ba sai da taga direba ya fice da motar sun nufi Ofis inda za su haWu da sauran abokan tafiyar tasa.

Sai da suka yi nisa da gidan sannan ya tuna da su Aunty Balira, goshinsa ya dafe kadan alamun bai ji dadin mantuwar ba, ya dauki wayarsa ya kira ta suka yi sallama bayan ya jaddada mata in sha Allah a ranar zai dawo.
Tun da Hafiz ya bar gidan, sai ya zama kamar an shafe su Aunty Balira da manawarsu a zuciyar Bintu. Ta manta gaba daya da babinsu balle ma har ta tuna da suna cikin gidan, ko kuma tayi kokarin sauke wani hakki na su da yake kanta a matsayinsu na dangin mijinta.

Harkokinta kawai take yi cikin yan'uwa da kawayenta. Da kuma matasan yara mata 'ya'yan Alh Lurwanu da suka je gidan tun da wuri, ta kuma karSe su hannu bibiyu kamar yadda ta saba, domin su ta ri?a a matsayin dangin mijinta na gaske, ba waWancan gayyar ?auyawan da ta raina ma ajawali ba.

Hatta abin karyawa sai da aka doshi ?arfe goma da rabi na safe sannan Aunty Balira ta shiga can cikin gidan tayi ma Bintu maganar abin karinsu.
"Kin san mutanenmu basu saba Waukar lokaci mai tsawo basu karya kumallo ba. Kuma wasu a cikinmu sun zo da ?ananun yara, idan manya sun jure yunwa kin ga yara baza su jure ba."

Ba kunya ba tsoro ta kalli Aunty Balira cikin

15 / 53