RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 53

3K to 6K   out of 157.3K words

watanni bakwai kenan babu wacce ta sake tako ?afarta zuwa cikin gidan.

Gare ta hakan ta fi nono fari, ba ta da niyyar raba su da Wan'uwansu, amma tana so lallai su tsaya iya limit Win su. Su gane tsakanin shi da Allah ya tsamo shi daga rayuwar ?auyen ?ayau zuwa cikin birni, yayi zuzzurfan karatun boko, Allah yayi mishi gyaWar dogo ta hanyar samun babban aikin gwamnati da gaggawa, ya tara ma?udan kuWaWe cikin ?an?anin lokaci, ya tamfatsa babban gida sannan ya auro ta ?ar manyan mutane bayan shekaru biyar da suka kwashe suna buga zazzafar soyayya akwai tazara mai ?ololuwar yawa a tsakaninsu. Baya ga duk waWancan ni'imomin da suke ciki ita Win babbar likita ce da take aiki a babban asibitin Abuja. Taya a matsayinta na wayayyiyar mace ?ar boko ma'aikaciyar lafiya da ta san illar yawan cuWeWiya tsakanin Wan birni da na ?auye za ta yarda waWannan gidadawan mutanen da suke a matsayin dangi da iyayen mijinta su dinga mata jela a gida?

Shi dai da yake nasu kuma suka zama dolenshi tana Waga mishi ?afa lokaci bayan lokaci yaje gurinsu, amma fa ko kwana idan ya wuce Waya ba ta taSa yarda yayi. Kuma yana dawowa tun kafin ya taSa komai na amfanin gidan take haWa mishi ruwan wanka da sinadarai masu kashe ?wayoyin cuta ta sille shi da kanta. Ba ta samun nutsuwar zuciyarta har ta iya rungumarshi sai bayan ta shafe shi da turarukan jiki na maza masu mabanbantan ?amshi...'

"Heyyyyy! Tunanin me kike yi haka?"
Hafiz ya katse mata zuzzurfan tunanin da ta afka ciki ta hanyar girgiza kafaWunta da Wan ?arfi.

Firgigit! Ta dawo daga duniyar tunanin da take yi.
"Na'am! Iye? My Dear magana kake yi?"
Ta jefa mishi tambayar a daburce.

Bakinshi ya matsar kusa da kunnenta sannu a hankali ya raWa mata maganganu masu daWi da taushi da za tayi amfani da su gurin ba Innaye ha?uri. Sai da ta gyaWa mishi kai alamun ta ji, kuma ta fahimta sannan ya kama hannun ?ofar Wakin ya murWa, suka shiga ciki a tare bakunansu Wauke da sallama.

Kallo Waya Zulaikha tayi musu tayi saurin wawurar hijabinta da ke ajiye gefe Waya ta zura a jikinta. Tsabar sauri ma a baibai ta saka, bata damu da hakan ba ta juya musu baya tana kallon bango, ciki-ciki ta fara ?un?uni ?asa-?asa bakinta a gaba yadda babu mai jin abinda take cewa sai ita kaWai.

Daga Bintu har Hafiz babu wanda ya kalli Zulaikha ballantana su damu da abinda take yi. Kai tsaye gaban Innaye da take zaune a gefen gado suka ?arasa, ba tare da wani ?yama ko tsantseni ba Hafiz ya zube a gabanta gwuyawunshi a ?asa. Ita kuwa Bintu ?asa-?asa ta ?arewa kan tile Win kallo, duk da a share yake tas kuma a goge har yana Waukar idanu ta kasa zama ko kuma tasa gwuiwa a ?asa kamar yadda mijinta yayi.

Sai da ta runtse idanu, ta cije leSe, kafin ta iya tsaro maganganun kamar yadda ya faWa mata.
"Maganar komawarki gida ma don Allah kiyi ha?uri, ki ?ara mana lokaci kaWan kafin ki koma. Kin ga har yanzu ban gama tattara sakamakon gwaje-gwajen da aka yi miki a asibiti ba. Kuma ko gobe ma idan zan tafi tare za mu fita, akwai wani gwaji da za'a sake miki na ciwon suger, kafin a karya ake yin shi. Shi yasa za mu fita da wuri, don Allah ki bar maganar komawa mu tattali lafiyarki tukunna. Kin ga babu daWi ace kin taho da ciwo kuma ki koma da ciwon ba tare da an samu sau?i ba. Ki yi ha?uri don Allah, in Allah ya yarda baza'a sake samun matsala makamanciyar wacce aka samu yau ba."

Shiru Innaye tayi kamar baza ta amsa ro?on ba. Hafiz har ya buWe baki zai cigaba da magiya daga inda Bintu ta tsaya sai ya ji Innaye ta ce
"Zuwa yaushe za'a gama duk gwaje-gwajen a bani magunguna?"

A tare duk su biyun suka yi magana. Hafiz cewa yayi
"Bazai wuce nan da wata biyu ba in Allah ya yarda."

Ita kuma Bintu cewa tayi
"Nan da kwanaki goma ma an gama komai Innaye."

Ba Innaye da mamaki ke neman sumar da ita a zaune ba, hatta Zulaikha sai da ta juyo da wani irin mamaki sosai a fuskarta tana ?are musu kallo. Su kansu kallon junansu suke yi, irin kallon nan mai bayyana rashin jin daWin yadda aka samu banbanci a maganganunsu, kuma a daidai gaSar da ya kamata su haWa baki gurin furta abu Waya.

Kallon baki kyauta min ba Hafiz ya jefa mata, sai kuma ya du?ar da kai a kunyace yana jin babu daWi sosai a zuciyarsa.
Ko yana so ko baya so ya san Innaye da maganar Bintu za tayi amfani, tunda dai ita ce Likita. Amma Allah ya sani yana matu?ar son zama da mahaifiyarsa na Wan lokaci, shi yasa ya faWi maganar watanni biyu, domin a daidai wannan gaSar da zaman gidansa ya sanewa Innaye a zuci ya san zancen lafiyarta ne kawai zai sa ta danni zuciyarta ta ?ara daWewa yadda yake so.

Ita kuwa Bintu ko a jikinta, tana sane ta ce nan da kwanaki goma duk da kafin shigowarsu Hafiz ya nuna mata bu?atarshi na son mahaifiyarsa ta daWe a gidan.

Amma tun a yanzu cikin sati Waya an fara samun irin wannan gagarumin matsalar ta ya za tayi saken da zamansu zai ?ara tsawo a gidan? Gaskiyar magana shi ne duk abinda za'a yi ma tsohuwar a asibiti bazai wuce kwanaki goman ba za'a gama komai. Don ma tun zuwansu bata yi himma akan komai na binciken lafiyar tata ba ai da yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba. Da a gaggauce za ta haWa mata duk magungunan da take bu?ata su ?ara gaba, Umma ta gaida Assha. Ba'ayi wata halitta a duniya da za ta zo lokaci Waya ta dagula zaman lafiyar da ta Wauki lokaci tana shimfiWawa a gidan aurenta ba.

Aka ce abinda babba ya hango, yaro ko ya hau dutsen dala bazai taSa hangowa ba. Duk su biyun Innaye ta fahimci inda suka sa gaba, hakan ne ma ya saka ta sakin wani Wan ta?aitaccen murmushi.
"To shi kenan. Allah ya kaimu nan da kwanaki goman. Bayan nan ?arin kwanaki huWu za muyi in Allah ya yarda za mu koma inda muka fi wayau."

"Nan da sati biyu kacal Innaye?"
Hafiz ya tambayeta da sanyin murya.

"Eh! Nan da sati biyu idan Allah ya kaimu Hafizu. Zuwa lokacin ka ga satinmu uku kenan. To ina laifi? Ni da ka Wauko ni da wayan bai fi in kwana huWu ba ka mayar da ni gida ga shi yanzu zanyi har sati uku? Ai babu laifi ko?"

"?warai kuwa Innaye. Mun gode Allah ya ?ara lafiya."
Bintu ta faWa a gaggauce.

Har ta mi?e za ta fice daga Wakin ba tare da jiran komai ba karaf! Idanunta suka faWa kan sababbin kulolin abincin Mijinta da ke ajiye gefe guda. Da mamaki sosai ta ?ara ware idanu tana kallon kulolin, eh tabbas su ne. Kulolin da duka-duka basu wuce sati uku da tayi Odarsu suka iso akan naira na gugan naira har dubu Wari da ashirin ba.

Shi kan shi Hafiz da ya kasance miji mafi soyuwa a zuciyarta, wannan shi ne karo na biyu da ta zuba mishi abinci a cikin kulolin. Amma saboda tsabar rashin adalci da rashin sanin darajar abu mai tsananin tsada ya rasa inda zai kawo mata haWaWWun kulolinta sai gurin tsohuwar ba?auyiyar Mamarsa da jahila fitsararriyar mara kunyar ?anwarsa? Lokaci Waya idanunta suka cicciko da hawaye. A jere ta haWiyi wasu kauraran miyau har daki biyu masu barazanar yaga mata ma?ogwaro don tsabar ba?in ciki da takaici.

A haukace ta nufi gurin kulolin za ta Wauka ta wuce da su sai jin muryar Zulaikha tayi a ladabce kamar ba ita ce ke yi mata magana a tsaitsaye ba tana cewa
"Aunty Bintu bamu ci abincin ba fa. Daman Yaya ne ya kawo ma Innaye to kuma zan zuba mata kenan kuka shigo. Kije kawai, idan mun gama zan kai miki kulolin kicin."

Duk yadda ta so daure Sacin ran da ya cunkushe zuciyarta kasawa tayi. A fusace ta waiga ta aika ma da Zulaikha wani kakkausan kallo tana zazzaro idanu kamar za ta haWiWiyeta. Karaf! Akan idanun Innaye da Hafiz da tun da Zulaikha ta fara magana hankalinsu ya koma kan abinda yake faruwa. Ta buWe baki za tayi magana a bazata wani ?a??arfan kuka ya taho mata, ba shiri ta fice daga Wakin da sassarfa hannayenta biyu dafe da bakinta don kar ta fashe da kuka a gaban waWanda take ma kallon ma?iya.

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu bayan ficewarta. Duk sun fahimci dalilin fusatarta tunda dai su ba yara bane. Amma tsakaninsu an rasa wanda zai fara cewa uffan! sai can bayan mintuna uku Innaye tayi ?arfin halin cewa.
"Da ganin kulolinnan sababbi ne, kuma za suyi tsada sosai. Ko kusa basu yi kama da irin kular da aka saba zubo mana abinci a ciki ba. Me yasa ka Wauko mata sababbin kuloli ka kawo mana abinci a ciki Hafizu?"

"Innaye... waWannan kulolin fa da sunan nawa ta saye su. Saboda Allah menene aibu don na Wauko kular abincina na kawo ma mahaifiyata?"
Ya ?arasa da tambayar ?arara fuskarsa na bayyana rashin jin daWin canjin fuskar da matarsa ta nuna kan abinda bai taka kara ya karya ba.
"Uhmmmm!"
Ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Muryarta na fita sannu a hankali ta cigaba da cewa
"Hafizu kenan. Baza ka gane abinda nake ?o?arin nusar da kai ba. Amma don Allah ina ro?onka daga yau, kar ka sake irin wannan. Tunda dai ana zubo mana abincin, duk ranar da ba'a kawo akan lokaci ba in sha Allah zan tura Auta ta Wauko, tunda dai ta san kicin Win. Ta shi kaje can Sangarenka ka huta. Kayi ?o?arin daidaitawa da matarka, kar ka kuskura wannan abin da ya faru ya janyo saSani a tsakaninku."

"In sha Allah zan kiyaye Innaye."
Ya amsa shi ma tasa muryar na fita a sanyaye.

Har ya kama hanyar ficewa daga Wakin ya waiga yana kallon Zulaikha, akayi arashi karaf suka haWa idanu. A fakaice ya watsa mata harara.
"Kina ji na? Daga yau ki tabbatar kin kiyaye duk abinda zai kai ki can Sangaren, idan kika sake shige ma Matata na rantse da Allah ba abinda zai hana ni goya mata baya ta zane ki ciki da bai."
Ko kusa bai yi kuskuren saka idanunsa a cikin na Innaye ba don ya san bazai sha da sau?i ba. Fuuu ya fice daga Wakin kamar zai tashi sama.

KwaSa-kwaSa tayi da fuska tana kallon Innaye ta ce
"Innaye kina jin shi ko...?"

"?yale shi Auta. Duk ranar da matarsa ta sake dukanki ba tare da kin mata komai ba ko ban gama karSan maganin ba a wannan ranar za mu bar gidannan. Rabu da su, in Allah ya yarda munyi zuwan farko kuma na ?arshe."
Ta ?arasa maganar a raunane. Irin raunin nan da ke fita tun daga ?ar?ashin zuciya.

'Ba tun yau ba ?an'uwan Hafiz suka sha zuwa mata da ?ananun maganganu kan yadda ?arara Bintu take nunawa a fili tana ?yamarsu. Su da suka zo gidan ba sau Waya ba ba sau biyu ba, zuwan farko ne kawai suka koma da daWin rai. Na biyu da na uku duk labaran da suka koma mata da shi ba mai daWi bane.

Kuma babban abin haushi da takaici shi ne duk irin abubuwan da take nunawa da wanda take yi a aikace Hafiz bai taSa nuna Sacin rai ko damuwarsa akan hakan ba.

Ita kuma da yake Dattijuwa ce ta gaske da aka shaide ta da tsananin ha?uri bata taSa mayar da hankalinta ko ta saka ma ranta damuwa kan irin maganganun da suke yi ba. Zulaikha ita ce mai biye musu, tai ta ?ara ingiza su tana tuna musu irin abubuwan da Bintu ke nunawa wanda ?arara duk mai hankali zai fahimci ?yamarsu take yi.
"Ni fa shi yasa tun ranar farko da Yaya ya kawo ta sam! bata kwanta min arai ba..."
Da Zulaikha ta fara irin waWannan maganganun a tsawace Innaye ke korarta daga Wakin.

Su kuma Yayyin nan take za ta kwaSe su ta nuna musu Sacin ranta. Kamar dai abubuwan basu taSa damunta ba. Duk abinda ke faruwa idan Bintu taje can kawar da kai take yi tayi kamar bata gani ba kuma bata damu ba, sai dai ma tayi ta bin Bintun da murmushi a matsayinta na matar shalelenta Hafizu.

Kamar misalin rashin shan ruwan Wakinta da Bintu ke yi. Kuma duk tsaftar dadduma ko sabuntar tabarma idan tasa aka shimfiWa mata da umarnin ta zauna ba ta taSa zama sai ta Wauko wani sabon dadduma daga mota ta shimfiWa sannan za ta zauna tana yamutsa baki a fakaice, domin sam ba ta hawa kan kujerunta da suka fara kwana biyu.

Duk da ginin gidansu da Wakunan gidan yana daga cikin gini mafiya kyawawan gini na bulo da bulo a ?auyen, saboda Hafiz ya sa an gyara gidan sosai. Kuma ya gyara mata Wakunanta ya zuba mata sabbin kayan Waki irin dai na tsofaffi masu gata. Bintu ta dinga kalle-kalle kenan tana Sata fuska, alamun dai komai bai mata yadda take so ba.

Ruwan sha, abinci, kayan ciye-ciye dangin ?walam da ma?ulashe da Bintu za ta bu?ata na ?an awannin da za tayi a ?auyensu duk da abinta take tafiya a cikin mota.

Wani tozarci da wula?anci da tayi musu da yasa ta ?ara ficewa a zuciyarsu wanda har yau sun kasa mantawa shi ne haihuwar Aunty Balira tayi. Da rawar jiki Hafiz ya Wauki Bintu suka je har gidan Yayar tasa barka. Aunty Balirar ita ce babbar ?a a Wakin Innaye. Shekarunta ashirin da aure Allah bai ba ta haihuwa ba sai a wannan lokacin. Shi yasa duk wani makusancinsu yake Wokin haihuwar, saboda abu ne da aka daWe ana nema har an fidda rai sai ga rabon ya samu.

Ko da suka isa, sai suka tarar yaron yayi kashi, an cire mishi nafkin ana wanke mishi kashin a cikin baho nan tsakar Wakin. Da saurin gaske Bintu ta sake gyara zaman face mask Win da ke hancinta. Ta sake tamke fuska tamau, ta kawar da kai tana shan ?amshi. Daga irin zaman da tayi Wofane a bakin kujera kamar wacce ke kan ?aya za'a gane a takure take ?warai. Shi kanshi zaman, kafin tayi sai da Hafiz ya bata umarnin ta zauna mana, fuskarsa babu walwala ko mis?ala zarrah. Shi yasa ta zauna tana jin babu daWi a ranta, a zuciyarta take ta addu'ar Allah yasa kar ta kwashi kuWin cizo ko ?an matan kaduna a jikin kujerar.

Da rawar jiki Ladidi wacce Hafiz yake bi ta gama wanke ma jariri kashi, aka naWe Wuwawunshi da sabon fallen zani aka mi?a ma Bintu. Da farko kamar ba za ta karSe shi ba, ko tunanin me tayi? Oho!
Sai ta buWe jakarta ta zaro safar hannu ta saka sannan ta karSi jaririn a wula?ance. Irin wasa-reren ri?onnan da ko jikinta bata yarda jinjirin ya taSa ba.

Kamar za ta yar da shi, daga ?arshe dai cikin sauri Hafiz ya karSi Wan yana mata tsiyar a matsayinta na babbar likita bata iya Waukar jariri ba, zai ga wanda zai dinga Waukar mata nata idan ta haifa.

"Dear! Ka san jaririn da zan haifa zai kasance dabanne da duk wasu jarirai da ka taSa gani a rayuwarka. Ko shugaban ?asar Sa'udiyya ne ba zaiyi ?yamar taSa Wana ba saboda tsananin kyawu da tsaftar jikinsa da na muhallin da muke ciki."
Amsar da ta bashi kenan a gaban kowa ba tare da damuwar maganar za ta ma ?an'uwansa daWi ko akasin haka ba.

Kamar bai ji abinda ta ce ba, haka Hafiz ya nuna, sai ma ya ?ara mayar da hankali kan addu'o'in da yake karantawa ?asa-?asa yana tofa ma jaririn.

Aunty Rakiya da ta kasance mara ha?uri daga cikin ?an'uwansa, har ta buWe baki za ta ba Bintu amsa da sauri Aunty Balira ta mintsine ta. A dole tayi shiru ba don ranta yana so ba sai don bin umarnin na gaba.

Ko da suka tashi tafiya, dubu ashirin Win da ta ajiye da cewa a siya ma jariri pampers babu wanda ya ce uffan! Balle tasa ran samun godiya kamar yadda suka saba yi mata sadda take amarya jikinsu na Sare-Sare idan tayi musu alkhairi, kamar ba yayyen mijinta ba.

Ko da suka ba Innaye labarin, bata nuna Sacin ranta ba sai ha?uri da ta basu da kalamai na kwantar da hankali. A ?arshe ta Suge da nunar musu da illar mi?a ma Bintu jaririn ba tare da sun sake yi mishi nafkin ba.
"Ku kalli irin suturun da take sakawa a jikinta mana? So kuke yaron yayi mata fitsari a jiki? Idan yayi mata fitsari duk cikin kayan sakawarku kuna da kwatan-kwacin wanda za ku bata ta saka a jikinta?
Haka dai ta kore maganar ba tare da ta nuna musu ta ji babu daWi kan abinda ya faru ba.

Ko da suka ce mata sun yanke zuwa gidan Wan'uwan nasu id??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an ba da wani ?wa??waran dalili na dolen-dole ba bata takura su da cewar su cigaba da zuwa ba.
"Daman in banda da abinku, jelar tafiya daga nan Fa?o, zuwa Kaduna, a sake hawa mota zuwa Abuja ai ba nan kusa bane. Ku Waga ?afan ya fi, tunda dai Allah ya sa shi Hafizun yana ?o?arin zuwa akai-akai ai babu laifi. Idan kuma wata bu?ata ce ta gaggawa kuke da ita sai ku tuntuSe shi a wayar zamaninnan da ta samar ma talaka sau?i. Da katin naira Wari za ku isar da sa?on da idan zuwa za kuyi sai kun kashe kuWin mota fiye da dubu biyar."
Da waWannan zantukan ta sake ?arfafa musu gwuiwar janye ma zuwa gidan Hafizu akai-akai.

Da gaskiyar Bahaushe da yace gani ya kori ji. Kwanaki uku na farkon zuwanta gidan a cikinsu kawai za ta ?aras da marari da Wokin ganinta a wajen matar gidan. A bayan

2 / 53