Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   37 / 53

108K to 111K   out of 157.3K words

fara kokarin yakiceshi da ?arfin tsiya jiki na rawa hawaye na kwarara a idanunta.

A rikice yake, gani yake kamar kokarin raba shi da ruhinshi take yi. Da dukkan ?arfinsa ya kara mannata da jikinshi har yana wasu ?an ?ananun shesshe?ar kuka.

Tsakanin su biyun ya rasa jikin wanne yafi na wani kaWawa. Murya cike da ?auna da matsananciyar soyayya yake rallashinta da daWaWan kalamai
"Ki taimake ni Zuly ta, taimakeni don Allah kiyi hakuri.... It has been so long...!"

Duk yadda ta daure kamar yadda ya ce ba ?aramar wahala ta sha ba, a jigace ta cigaba da sauraren labaran da yake bata daki-daki, cikin rawar jiki da fitar hayyaci.
Sai dai zuwa lokacin da ya samu nutsuwa, tuni ta gama yin wujiga-wujiga ta fita haiyacinta.

Ya haWeta da jikinshi yana jin kamar ya tsaga kirjinshi ya sanyata a ciki don tsananin so da ?aunar da yake mata. Sai kuma ya Wago fuskarta ya fara share mata hawaye da tarin zufan da tayi, duk da sanyin AC da ya wadaci Wakin.
******


Tunda suka yi sallar asubahi, ya haWa mata tea mai kauri ta sha, sannan ya bata paracetamol da ibuprofen ta sha saboda zazzabi da ta kwana da shi, suka koma barci.

Janta yayi cikin jikinshi ya rungumeta tsam! Duk da tabbacin cewa babu abinda zai mata da ya dinga faWa mata, bata natsu ba sai da taji yayi barci da gaske. Sannan itama ta saki jikinta sosai ta yi barci.

Wajen karfe tara na safe ta farka, ta ji dama sosai akan azaban raWaWin da take ji a jikinta da kuma zazzaSin da yake damunta. A hankali ta fara ?o?arin zare kafafunta daga na Kamal da ya haWe su da nashi ya makalkaleta.

Kafin ta gama zame jikin ta daga nashi ta ji ya sake janta ya rike ?am! Murya cike da barci yake tambayarta
"Ina zuwa da wannan farar safiyar?"

Agogon da ke jikin gadon ta sake kalla, da sha?a??iyar murya ta ce
"Karfe tara ta gota fa. Ya kamata mu tashi haka nan. Kuma ina son Wora mana abinda zamu yi karin kumallo da shi ne."

A hankali ya girgiza mata kai.
"Kar ki damu. Na san daga gidan Mommy za ta bada a kawo mana abinci. Don haka zo mu koma barci ni bai ishe ni ba."

Murmushi ta saki tana kallon fuskarsa da har lokacin bai buWe idanunsa ba. A tausashe ta ce
"Ai kuwa sai dai kai ka cigaba da barcin, amma ni dai na gama. Na gaji da kwanciya. Wanka nake son yi."

Ta gangara ta zame daga jikinshi ta dira daga kan gadon tana mishi dariyar yadda yaso ya sake damkota ta zulle.

Sai a lokacin ya buWe idanunsa gaba Waya yana kallonta da murmushi kaWan a fuskarsa.
"Ke ko? Za mu haWe ne yarinya"

Ta kuwa sake kyalkyalewa da dariya sannan ta faWa banWaki. Don ma kada ya biyo ta, sai ta murza makulli ta kulle ?ofar.

Aikuwa tana cikin haWa ruwan wanka ta ji ana kokarin turo kofar, tayi murmushi kawai tana mamakin rashin kunya irinta Abban Imam. Ko da asubahi duk yadda ta kai ga zullewa shi yayi mata wanka tsaf ya gargasa mata jiki, da?yar ya barta tayi wankan tsarki bayan ta bashi tabbacin za ta iya yi da kanta.

Daga can waje ya fara mata magiya yana ro?on ta buWe mishi kofar, tayi mirsisi kamar ba ta jin shi. Don ta san idan ya shiga ba lallai ya barta ta shirya akan lokaci ba.

Kuma yadda ta ji su Anty Balira suna fadin sammako za suyi gurin tafiya gida tasan lallai babu jimawa za su dira a gidan don yi mata sallama. Don haka ta kyale shi. Ya gaji da magiyarsa ya tafi dakinshi yana maimaita mata za ta sani ne idan suka haWu.

Ta sake shiga ruwan zafi sosai ta zauna a ciki kamar yadda Anty Balira tayi ta jaddada mata. Bayan ta gama wankan kuma ta samu man zaitun mai kyau ta shafe yammatancinta da shi.

Kwalliya sosai tayi cikin Winkin shadda surfani ?ar kasar Mali. Zama a group Win Aunty Hibbah yasa ta iya Waurin Wankwali iri-iri, ko da ta kalmasa, ta lan?wasa, ta cokara Waurin sai ta fito a amaryar sak! Da angon ya ganta kasa Wauke idanunshi daga kanta yayi.

Banda direba da ya kai musu abinci ya katse shi a lokacin, da lallai sai Ango Kamal ya saka ta sake sabuwar kwalliya, wata?ila ma har da sabon wanka.

HaWaWWen dahuwar naman kan rago da yaji kayan ?amshi kuma yayi romo sosai aka kai musu da wainar farar shinkafa. sai ruwan tea mai kayan ?amshi a cikin flask da biredi da sultan chips.
Zulaikha dai tunda ta zuba naman kai da uban romo shi taci tayi ?at! Sai da ya tilastata da rarrashi da ban baki sannan ta ci wainar kaWan.

Bayan sun gama duk yadda tai ta hana shi ?iyawa yayi, shi ya taya ta suka gyara wajen tsaf, ta jona burner ta zuba turaren wuta, nan da nan falon ya ?ara gamewa da ?amshin turare mai daWin ?amshi.

Bayan sun Wauraye farantai da kofunan da suka Sata jan ta yayi suka zauna akan Waya daga cikin kujerun falon suna hira mai daWi, ga kuma TV a kunne suna suke kallo jefi-jefi.

Cikin Wan kankanin lokacin Zulaikha ta fahimci Kamal mutum mai son haWa jiki da iyalinshi. Shi dai duk wani abu da zasu yi, to sai ya ji ta a cikin jikinshi. Idan cin abinci ne, hannunshi cikin nata, idan zama ne, sai ya jata cikin jikinshi, idan kwanciya ce, sai ya dangana jikinshi da nata. Tun tana dari-dari tana jin kunya, har ta sadakar ta hakura. Don kuwa bata ga alamun zai daina hakan ba.

Su Anty Balira basu je gidan ba sai bayan sallar azahar, nan din ma a tsaitsaye suka musu sallama suka tafi, saboda direbobin da za su mayar da su suna jiransu a waje.

Bayan abin arzikin da Mummy ta haWa su da shi, har da wanda za su kaima Innaye, Baffa, da kishiyoyin Innaye haka Kamal ya musu sha tara ta arziki.

Sun bar garin Abuja bakunansu har kunne, babu abinda suke faWa sai son barka da fatan alkairi. Sun gama tabbatar da cewa Zulaikha dai ta yi dacen abokin zama da surukai na gari.

Bayan tafiyarsu duk yadda yaso ya zauna a gidan hakan ya gagara, saboda ba?i da suka cigaba da zuwa ta Sangaren danginshi, da iyalan gidan Abba Lukman waWanda suka je ?wansu da ?war?watansu don ganin gidan Amarya.

A dole ya yi sallama da amarya ba don ranshi ya so ba ya tafi wajen abokanshi dake ta aikin kiranshi a waya tun safe.

Yanayin ba?in da suka dinga yi akai-akai yasa bata samu kanta ba sai can bayan La'asar sosai. Gidan ya rage daga ita sai Mashku da Karima, suna ta mata shakiyanci. Su din ma ana yin magriba da direba ya kai abinci, suka mata sallama suka tafi.

Sai lokacin ta samu ta zauna ta kira Innaye suka gaisa, taji cewa yan tafiya sun isa tuni. Bakin Innaye har kunne saboda murna da jin farincikin yadda kowa yake yabon halin da suka bar diyartata a ciki. Ita ma Zulaikha da murnarta take ?ara jaddada ma Innaye tana lafiya kuma tana cikin farin ciki.

Sun daWe suna hira, Innaye tana ta jaddada mata tayi ha?uri dai, don zaman aure sai da ha?uri kafin suka yi sallama.
Tana katse kiran ta shiga cikin messages ta fara maidawa angon nata amsar sakonnin da ya tura mata, bayan kiranta da ya dinga yi a waya akai-akai duk bayan awa guda sai ya tura mata sa?on yadda yake son ta da yadda yayi kewarta, tun tana tsayawa mayar mishi da martani har dai ta fahimci abin ba na ?are bane ta ajiye wayar ta cigaba da hidimar ba?inta.

Tana gama mayar masa da martanin za?a?an kalamai ta faWa wanka. Kafin tafiyar su Karima sai da suka gyara mata gidan ?al suka kunna turaren wuta, shi yasa bayan tafiyarsu wanka kawai tayi tai sallah ta tsantsara kwalliya ta zauna zaman jiran dawowar angonta. A gefe guda kuma tana cikin matsananciyar fargaba na yadda darensu na yau zai kasance, domin bata manta azabar da ta sha daren jiya ba.

Wajajen karfe takwas na dare ya shiga gidan tare da zugar abokanshi. Nan suka zauna suka sha shakiyancinsu, suka Wora da nasiha da addu'a da fatan zaman lafiya, kafin suka yi ma Amarya kyautar manyan kuWaWe da cewar na bakin da basu siya ba sannan suka musu sallama suka tafi.

Yana kallon yadda take tafiya tana wani dingishi da kanainayewa wai ita ala dole bata da lafiya. Har wani magana take yi kasa-kasa, motsi kadan sai ta taba gefen wuyanta ta ce
"Wash!"

Ba tare da gajiyawa ba yake ta jera mata sannu cike da tarairaya, ko abinci a baki ya ciyar da ita yana haWa mata da rarrashi, a zuciyarshi ko dariya yake mata, don shi kaWai yasan irin alwashin da ya ciwa dare na biyun nan.

?arfe goma na dare, ya samu kiran Oganshi yana tambayarshi wasu documents da shi Kamal Win ya haWa tun sati biyu da suka wuce. Umarni yai mishi cewar ya tura mishi documents Win a daren, zai yi wani aiki a kansu.

Da ?warin gwuiwarshi ya amsa da Ok Sir! Amma wani abin haushi da takaici a gare shi shi ne ko da suka gama wayar, ya duba cikin Wakinshi da nufin Waukar Kwamfutarshi sai bai gani ba. Nan ya gane ya barta a can Sangarenshi na gidan Mummy.

Agogo ya sake kallah a karo na biyu, goma da kusan rabi na dare. Wayarshi ya Wauka da nufin kiran Karima ya umarci ta Wauko Kwamfutar a Wakinshi ta ba direba ya kawo mishi amma sai yaji wayarta a kashe. Ko da ya kira Mummy kuma wayar tai ta ringing bata Waga ba, haka ma lambar Hajja.

Da damuwa a fuskarsa ya kalli Zulaikha yana faWa mata ?ila fa dole sai ya tafi can gida a daren nan.

"Ayya mana Abban Kamal... Ni kaWai za ka bari a darennan? Don Allah ka tafi da ni mana..."

"Keh! So kike Mummy tayi min faWa ta ce na fara yawo da ke tun yanzu..."

"Don Allah!"
Ta fara mishi magiya a shagwaSe.
"Ai baza ta san tare da ni kaje ba. Ni da kawai muna shiga zan wuce Sangarenmu na can gidan in Suya, idan ka gama abinda za kayi sai mu dawo."

Shi kanshi ba ya son barinta ita kaWai, don haka bai ?ara ja da nisa ba yace ta sako hijabinta su tafi.


*******
*******


"Laaa'ilaha illallahu muhammadurrasulillahi sallallahu alaihi wa-sallam! Na shiga uku ni Ta rasulu!! Waye anan??"
Hajja ta jero salati da maganganun cikin Waga murya da firgici, hannunta dafe da ?irji, idanunta a warwaje alamar tsorata ?arara.

Da yake barcin nata raba da rabi ne, baiyi nisa ba, ga kuma firgici da tsoron da zuciyarta ke ciki. Hajja na fara salatin ta buWe idanu a firgice tana kallonta.
"Hajja... Nnnnni ce fa... ni ce.. Zulaikha ce."
Tayi maganar cikin rawar murya.

Duk da muryarta da Hajja ta shaida, bata gasgata da gaske ita ce ba sai da ta kunna ?wan lantarki mai haske ta ganta ra'ayil aini. Domin ?ara share tantamar ita ce ko ba ita ba sai da Hajjan ta sake cewa
"Zulai? Da gaske ke ce nake gani anan ko gizo idona ke min?"
Tayi mata tambayar zuciyarta cike da mamakin abinda zai kawo Zulai da take Amarya Wanya shakaf cikin gidan kuma cikin falonta a irin wannan lokacin da dare ya fara tsalawa, Zulai dai da jiya ne aka kai ta gidan Kamal matsayin matarsa.

"Ni ce Hajja."
Zulaikha ta amsa a marairaice. Idanunta cicci????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ke da ?wallah.

"Ikon Allah!"
Hajja ta faWa hannunta Waya ri?e da haSa. Kafin Zulaikha ta ce wani abu ta sake jefa mata tambayar
"To me ya kawo ki gidannan? Kuma har kika shigo falo na a irin wannan lokacin na talatainin dare? Ca nake jiya ne yayyinki suka kai ki Wakin miji?"

Mar-mar tayi da ?wayoyin idanunta, wasu ?an ?ananun ?wallah suka gangaro, da rawar murya ta ce
"Hajja don Allah ki barni in kwana anan. Wallahi ni tsoron can nake ji. Mun zo ne fa tare da Abban Imam zai Wauki kwamfurarshi da ya manta, shi ne ni kuma na gudo gurinki."

Cikin ?asa da mintuna biyu Hajja ta gano abinda ke faruwa. A zuciyarta ?ara gamsuwa da irin tarbiyar da su Innaye suka ba Zulai tayi, lallai ita Win rainon ?auye ce, da aka hore ta da kunya da rashin rawar kai ba irin wasu ?an matan na yanzu ba.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta taka sannu a hankali ta ?arasa inda Zulaikha ke kwance bisa kujera mazaunin mutum uku ta zauna kusa da ita. A tausashe ta fara mata magana da sigar rarrashi.
"Haba Zulai, a ina kika taSa ji an Waura ma yarinya aure a darenta na biyu ta gudo ta bar angonta shi kaWai ? Kiyi ha?uri, ki kwantar da hankalinki. Ko wace mace da haka take sabawa kin ji ko?"

A raunane kuma a tsorace ta Waga kai, alamar ta ji.

"Kuma ma Abban Imam Win ki ne fa, ko kin manta halayensa ne na ha?uri da kawar da kai? Kin manta irin matsananciyar soyayyar da yake miki ne? Na tabbata a irin kyawawan halayen Kamalu da na sani bazai taSa yin wani abu don ya cutar da ke ba. Ko so kike tun a daren nan ki fara dasa mishi tunanin wata ?a mace a zuciyarsa?"

Da sauri ta girgiza kai, tana jin yadda ?irjinta ya buga daram saboda kishi daga jin saWarar maganar Hajja ta ?arshe.

"To in dai bakya so hakan ta kasance ya zame miki dole ki jure, ki daure, ki kwantar da hankalinki ki faranta ma mijinki rai a wannan dare da sauran dararen da za su biyo baya. Yanzu ina shi Kamalun?"

"Yana can"
Ta amsa da?yar! Kamar wacce aka sha?ewa ma?ogwaro.

"Tashi maza muje in raka ki gurin mijinki. Kuma kar ki kuskura ko da wasa ki ba Karimatu ko wata labarin abinda ya faru. Kin ji?"

A karo na uku kai ta sake Wagawa. Sannan ta mi?e tsaye jikinta a sanyaye ta bi bayan Hajja suka fice daga Wakin. Wani abin mamaki shi ne suna fita daga Sangaren Mummy suka hangi Kamal tsaye a ?ofar Sangarensu yana ta safa da marwa, bisa ga dukkan alamu ba shi cikin nutsuwarsa.

"Kin ga irin damuwar da kika jefa mijinki a ciki ko? Ki tabbatar kin bashi ha?uri bayan tafiyata. Kar ki sake aikata irin wannan shirmen ko ba yanzu ba, domin mazajenku na yanzu ba irin namu na da bane. Tun yana lallaSa ki yana bin ki a hankali kina botsarewa sannu a hankali zaiyi watsi da lamarinki ya fara nema ma kansa mafita..."

Maganganun Hajja sun Wauke ne bayan Abban Imam ya ?araso gurinsu da sauri. Sai da ya isa, sai kuma kunya ta kama shi, ja yayi ya tsaya yana Wan sosa ?eya cikin kunya.
"Hajja Afuwan! Ta taso ki ko?"

Duk yadda Hajjan taso cijewa sai da dariya ta ?wace mata ganin yadda yake ta sussunne kai, kamar ba Kamal Wan bokon nan da bai cika jin kunyarta ba.
"Kai dai Wauki matarka ku tafi. Na yi mai wuyar tunda na dawo maka da ita. Amma dai kar ka manta, matarka ba irin ?anmatannan bane masu buWaWWen idanu da suka san me ke cikin rayuwar aure tun kafin su shiga cikinta. Bayan haka kuma girman jikin ne kawai, amma yarinya ce ?arama. Ka bi ta sannu a hankali, kayi ha?uri da duk shirmen da za tayi maka. Allah ya bada zaman lafiya."
Bata jira amsawar Waya daga cikinsu ba ta juya za ta shige cikin falon Mummy.

"Amma dai ina fatan ba a cikin talatainin darennan za ku koma can gidanku ba?"
Ta tambayi Kamal tana daf da shigewa cikin falon.

"A'a Hajjah. Dare ya riga yayi. Gobe dai da asubah in sha Allah za mu tafi don kar Mummy tayi faWa."
Kamal ya amsa a nutse.

"Ba laifi. Allah ya tashe mu lafiya."

"Amin."
Kamal ya amsa da Wan ?arfi yadda za ta ji shi.

Bayan shigewar Hajja, tsayuwar da?i?u sittin suka ?ara a gurin, shi yana kallonta da karantar yanayinta, ita kuma tana kallon ?asa, gaba Waya jikinta a tsarmame, kamar kazar da aka tsoma a ruwan zafi aka tsamo.

"Kayi ha?uri Abban Imam"
Ta karya shirun da faWin haka, muryarta na Wan rawa, a kunyace.

Bai ce komai ba. A madadin yayi magana ma sai hannunsa ya mi?a a hankali ya kamo hannunta. A fili take jin yadda yake sauke ajiyar zuciya sauri-sauri, ya daWe a haka, kafin ya Waga hannunsa da ke ri?e da nata ya Wora a ?irjinsa daidai saitin zuciyarsa.
"Allah ya sani ina tsananin son ki Zulaikha. Ina son kasancewa tare da ke a wannan dare. Amma idan kin fi son kwana a gurin Hajja zan Waga miki ?afa... Har zuwa sadda ke da kanki za ki ji a ranki kina son kasancewa tare da ni. Kin amince? In mayar da ke gurin Hajja?"

"A'a!"
Ta amsa da sauri. Kafin yayi magana ta sake cewa.
"Kayi ha?uri."
Cikin sanyin murya.

A hankali kuma ta Waga kanta ta saci kallonsa, karaf! Idanunta suka faWa cikin nashi. Ya sakar mata lallausan murmushi.

"Kin amince da ni? Mu tafi Sangarenki mu kwana da asuba mu koma can gidanmu?"
Ya tambayeta a tausashe.

"Eh! Na amince."
Ta amsa a hankali, a zuciyarta take ta ?o?arin ?ara ?arfafa ma kanta gwuiwa tana ya?ar tsoron da ke dan?are da ranta.

?an shiru yayi, sai kuma ya sake cewa
"Baza ki sake guduwa gurin Hajja ki barni daga shiga cikin Waki ba ko?"

Kunya ne ya kamata. Hannunta Waya da bai ri?e ba ta Waga ta rufe fuskarta tana dariya ?asa-?asa, a zuciyarta take tuna abinda ya faru har ta gudu Wakin Hajja.

'Sai da suka gama shan madarar holandiya mai sanyi sosai da ya Wauko a cikin frig.

37 / 53