RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 53

78K to 81K   out of 157.3K words

ba ya saki bakinsa ta fara juya shi yadda take so.

Tun yana turjewa yana basarwa har dai ya bada kai bori ya hau, domin babu ?arya shi kanshi ba ?aramin kewarta yayi ba a cikin kwanaki biyun.
'Kawai dai ya janye jikinsa daga nata ne don ya nuna mata kuskurenta.

Ya sani asalin laifin nashi ne, amma a tsammaninsa akwai fahimtar juna da soyayyar da ko da wasa baza ta taSa yun?urin aikata mishi irin abubuwan da ta aikata ba. Wu?a ta Wauka za ta caka mishi fa? Wai shi ne Bintu take rantsewa da girman Allah idan ya kuskura ya ?arasa kusa da ita za ta caka mishi wu?a, sannan ta jefe shi da iyayensa da ba?a?e kuma munanan kalaman da ko tana cikin hauka tuburan ne bai taSa tsammanin za ta iya kallon cikin idanunsa ta furta mishi su ba...'

"Kayi ha?uri My dear... Don girman Allah SWT da Darajar Fiyayyen halitta SAW ka yafe min."
Ta faWa cikin kuka bayan ta raba bakinta da nashi, kamar ta san tunanin da yake yi.

Da saurin gaske ta zame zuwa ?asa ta ri?e ?afafunshi tana cigaba da rusa kuka wurjanjan, kamar wacce aka aikowa da sa?on mutuwar iyayenta duk biyu a lokaci Waya. Cikin kukan ta cigaba da magana
"Na sani ko kusa banyi amfani da hankali da tunani ba gurin aikata irin abubuwan da nayi... Na sani banyi maka uzuri ba, kamar yadda na sha al?arwarta maka a baya cewa duk juyin juya hali na rayuwa bazan taSa fahimtarka a bai-bai ba... Na sani ban saurareka ba balle har in baka dama kayi min bayanin gaskiyar abinda yake faruwa... Amma ya kamata ka fahimce ni My dear, ko Wan yaya ne kayi min uzuri, duk da ni na kasa yi maka uzuri sa'adda idanuna suka rufe ruf da tsananin kishi da matsanancin soyayyarka.

Wallahi ban taSa sanin haka kishi yake da azababben zafi da raWaWi ba sai a wannan ranar... Komai na duniyar ba?i-?irin yayi min Sweetheart! A wancan lokacin, Wallahi Tallahi ban ?i duniyar ta kife ayi mutuwar kasko ba duk a wuce gurin."
Taja shesshe?ar numfashi cikin kuka, kafin ta cigaba da cewa
"Babu ma amfanin maimaita abinda ya wuce. Kuskure ne nasan na riga na aikata, bazan gaji da baka ha?uri ba har sai ka furta ka yafe min da bakinka. Wannan shiru-shirun naka neman hallakani yake yi, gara ka Wauki duk matakin da za ka Wauka a kaina a wuce gurin. Idan yi min duka zai sa ka huce, ka daina fushi da ni..."
Da sauri ta mi?e ta isa gurin cajojinsu ta Wauko cajar kwamfuta da ta kasance mai kauri, ta dawo tasa gwuiyawunta a ?asa sannan ta mi?a masa.

"Ka zane ni My dear... Don Allah kayi min mugun duka har zuwa sadda za ka ji a ranka ka huce kuma ka yafe min."
Duk da bai karSi bulalar ba sunkuyar da kanta ?asa tayi, hannayenta Wage a sama tana mi?a mishi cajar, a lokaci guda kuma ta cigaba da rera mishi kuka sannu a hankali.

Jikinsa a sanyaye, yasa hannu ya karSi cajar. Duk da haka bata Waga idanu ta kalle shi ba, sai runtse idanu tayi tana jira ta ji saukar duka ta ko ina a jikinta.

A hankali, da wani irin salo na slow motion ya zame gwuiyawunsa zuwa ?asa bayan yayi hurgi da cajar gefe Waya. Rungumeta yayi tsam-tsam a ?irjinsa. A tare ita da shi suka saki nannauyar ajiyar zuciya.

A kunnenta ya raWa mata da wata irin tattausar murya
"Na yafe miki Bintuna. Allah ya yafe mana gaba Waya. Ni ma ina ro?onki ki yafe min, tun farko..."

Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe mishi baki. A shagwaSe ta ce
"Abinda ya wuce mu barshi a wanda ya wuce Abban Aadil. Mu fuskanci gaba kawai da sabuwar rayuwa mai cike da soyayya da ?auna."

A lokaci Waya suka sake ru?un?ume juna suna ?yal?yala dariya, nan da nan kuma dariyar ta sauya salo, daman kwana biyu sunyi kewar juna. Don haka duk ?o?ari suke kowa ya nuna ma Wan'uwansa lallai fa ya fi Wayan wahaltuwa a wannan yajin da suka ma juna na kwana biyu.

Tun daga wannan rana, suka dawo da gudanar da kyakkyawar rayuwarsu har ma fiye da da. Suka cigaba da rainon Wansu Aadil da yake ta kakkaSa girma tubarakallah cikin ?auna da soyayya. Basu ?ara tayar da zancen wata Zulaikha ba, balle kuma igiyoyin auren da aka ?a?aba ma Hafizu waWanda yake Waukarsu a matsayin wasan yara.

Kuma yana waya da Iyaye da ?an'uwansa. Duk bayan sati biyu yana zuwa ?auye kamar yadda ya saba, amma ko da wasa bai taSa ba da wata kafa da zai sa ayi zargin lallai shi da Zulaikha ba sa rayuwa a muhalli Waya ba.

Domin kamar yadda yake waya da iyayensu da ?an'uwansu, itama tana waya da su, duk da bai je da ita ?auyen ba, ko da wasa bata taSa alamta musu lallai fa akwai gagarumar matsala tsakaninta da Yayan nata ba.

"Hafizu ya Zulai take? Don Allah don Annabi kar ka Soye min komai. Ka ga dai ni ?ar'uwarka ce, sha?i?iyarka wacce za ku kashe ku rufe tare ba tare da wani ya ji abinda muke ciki ba. Na rasa dalilin da yasa duk irin amsar da kake bamu na tana nan lafiya ?alau, da irin amsar da itama take bamu na kuna zaune lafiya ?alau ni dai hankalina ya gaza kwanciya. Kuma nayi-nayi da Baffa ya barni ko ni Waya in je Habuja in gano halin da kuke ciki ya ?i, a ta?aice ma doka ya kafa mana gaba Wayanmu kar wacce ta kuskura ta ce za ta kai ma Zulai ziyara sai ta haihu, idan kuma Allah bai kawo haihuwar da wuri ba sai ta shekara cif kafin muje mu gano halin da take ciki."
A lokacin da Aunty Balira take mishi wannan maganar ruwa yake sha, amma tsabar yadda maganganun suka doke shi musamman maganar haihuwar Zulai bai san sa'adda ya sha?e da ruwan da yake sha ba. Nan take ya fara tari ba ?a??autawa.

"Sannu! Sannu Allah ya sauwake. Ka sha a hankali, ya bi ta ?aramin ma?ogwaro. Sannu Hafizu."
Aunty Balira ta faWa da damuwa a fuskarta, tana zaune kusa da shi tana mishi fifita.

"Haihuwa kuma Aunty Balira? Saboda Allah wani irin haihuwa kuma ana zaune ?alau? Daga yin aure kuma a shekara Waya sai haihuwa?"
Ya jera mata tambayoyin da dariyar ya?e a fuskarsa bayan ya samu tarin ya lafa mishi da?yar.

"Ji wani sakarci daga gurin Hafizu. Yo idan rabo na kusa me zai hana Zulai samun ciki ta haihu a cikin watanni tara zuwa goma ?"
Sai kuma ta ?an?ance idanu ta ?ara ?ure shi da kallo, ta sake jefa mishi tambayar
"Ko dai akwai wata matsala da kake Soye mana tsakaninku ne...?"

"Wani irin matsala kuma? Ke dai Wallahi duk kin damu kanki. Babu komai, ina sake maimaita miki babu komai. Lafiya ?alau muke zaune. Idan ma akwai matsala ko ni ban faWa ba a yadda Zulai take komai na ta a barbaje ai kin san za ta faWa muku. Ki kwantar da hankalinki pls! Ki cigaba da taya mu addu'a. Ko yanzu abinda yasa ban zo da ita kun ganta ido da ido ba don kar Baffa yayi faWa ne, amma lafiya ?alau muke zaune."

"Madallah! To Allah ya ?ara zaunar da ku lafiya ya kawo rabo mai albarka."
Tayi addu'ar bayan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Da waWannan maganganun da ya shirya mata ya samu ya kashe bakinta. Suka rabu lafiya tana saka mishi albarka.

Baiwar Allah Innaye kuwa hankalinta a kwance yake luf kamar tsumma a randa. Daman dai babbar damuwa da tashin hankalinta akan auren Zulai ce, to tunda wacce za tayi ya?in dominta ta bada kai bori ya hau ita mene nata da za ta ja ta ?ume kan cewa sai an raba auren? Sai kawai itama ta kwantar da hankalinta ta cigaba da bin su da fatan alkhairi.

Duk Waure fuskar da take ma Hafizu yanzu ta daina. Abu Waya da ba ta gajiya da shi shi ne a waya suke magana ko kuma ziyara ya kai musu ba ta gajiya da jaddada mishi lallai ya ji tsoron Allah ya ri?e Zulai amana, idan ya kuskura ya ci amanarta tabbas amana za ta ci shi.

"To Innaye! Zan kiyaye in Allah ya yarda. A cigaba da taya mu addu'a."
Amsar da yake ba ta kenan ako wane lokaci ba don maganganun na ta na shiga kunnensa su zauna a ?wa?walwarsa ba.
[2/1, 11:21 PM] Fareeda Abdallah: Duk zuwa ?auye idan yayi, Innaye ba ta gajiya da harhaWa mishi tsaraba irinna mutanen ?auye, musamman waWanda ta tabbatar Zulaikha tana masifar so. Kuka, kuSewa, daddawa, garin citta da sauran kayan ?amshi, garin ?uli, busasshiyar rama??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????, shuwaka, zogale, magarya, aduwa, goruba, kurna, haka za ta harhaWa mishi leda-leda gaba Waya ta ce ya kai ma Zulai.

Sannan ta kawo wasu kayayyakin masu yawa ta ce ya kai ma Matan Abba Lurwanu.

Don fita hakki duk sadda ta bashi waWannan sa?onnin sai tace mishi
"Ko za ka kira Fatima ka tambayi idan akwai abinda take so anan sai in baka ka tafi mata da shi? Na san su mutanen birni ba kasafai suka cika cimakar ?an ?auye ba. Ita kuwa Zulai rainon ?auye ce, ta saba da waWannan ciye-ciyen."

"Ai ba ma sai na kira ta ba Innaye. Idan ma akwai abinda take so sai Zulai ta Wiba mata. WaWannan kayayyakin da kika haWa ma sun isa, Allah ya saka da alkhairi ya ?ara lafiya."

Haka zai Wauki kayan a boot Win mota girma-girma har Abuja, amma tun kafin su isa gidanshi zai yi ma Mal Musa umarnin su fara wucewa gidan Mummy Saudah. Can yake dam?a ma Mummy tsarabar da cewa ga tsarabar ?auye nan, haka Mummy da Hajja za suyi ta godiya suna saka albarka.

Tun kafin ya bar gidan, Mummy za ta kira Zulaikha tayi mata umarnin shiga da kayayyakin kicin.
"Tsarabar gida ne Yayanku ya kawo mana, ki rarraba komai ki adana inda baza su samu matsala ba kin ji ?an matana?"

"To Mummy."
Da?yar take iya buWe baki ta gaisar da Hafiz sannan ta kwashi ledojin zuwa kicin, da yake an ce ba'a raba hanta da jini. Da ganin irin kayayyakin da ke cikin ledojin Zulaikha take gane takanas-ta kano wannan sa?on nata ne daga hannun Innaye. DaWi ne yake cika mata zuciya, sai tayi murmushi kawai ta cigaba da rarraba kayan zuwa inda suka fi dacewa.

Abubuwan ciye-ciye kuma tun kafin ta fice daga kicin Win za ta Wiba ta wanke na wankewa ta kai ma Mummy da Hajja falo.

A kwanakinta na farko-farko a gidan, idan Hafiz yaje har ya gama zamansa ya tafi bayan gaisuwa ba ta ?ara yarda wata magana ta shiga tsakaninsu. Sai wata rana da Hajja tayi mata tatas ta umarci taje ta raka Wan'uwanta gurin mota, haka ta fice ta bi bayanshi tana zumSura baki.

"Hmmm! Komai akai da jaki ai sai ya ci kara. Sai yanzu na ?ara yarda da aka ce ba?auye sai ya shekara arba'in a birni kafin Wabi'a da al'adun mutanen ?auye ya bar jikinshi..."

"Jaka mai faWa irinna ?an daba tana can yanzu za'a tadda ta a gida, da tsinin bakinta irinna jaSa. ?auyanci kuwa naga duk za ni ce ta tadda muje mu, wanda yake gorin shi ma har yanzu Wabi'a da al'adun ?auyawan bai sake shi ba tunda ko shekara ashirin baiyi a cikin birnin ba."
Tana gama faWin haka ta wuce fuuuu, ta koma cikin gida ta barshi tsaye a gurin, baki da hanci buWe don tsabar mamakin irin ?warin gwuiwar da Zulai ta samu har ta iya mayar mishi da mummunan ba?ar magana irin wannan.

Bai ma san ta shige ba, sai da ya dawo hayyacinsa yaga ba ta a gurin. A fusace ya Waga ?afa zai bi ta ya ci ubanta sai kuma ya tuna a gidan Mummy take fa, idan yayi wani mummunan action lallai zai zunguro sama da kara, ?arshenta Zulaikha ta tona mishi asiri, mutuncinsa na shekara da shekaru ya zube ?asa war-was a idanun Mummy.

Mota ya shige a fusace, ya Wauki wayarsa ya lalubo tsohon lambar Aunty Balira da a yanzu ya zama mallakin Zulaikha ya danna mata kira, yana fara ringing kuwa cikin sa'a ta Waga da siririyar sallama a bakinta.

"Ke don ubanki ni kike faWa ma ba?ar magana? Ni sa'an ki ne...?"

"Wrong number"
Ta katse shi da faWin haka tun kafin ya aje numfashin maganarsa, kafin ya sake cewa komai ?it! ta katse wayar. Ko da ya sake kira fiye da sau bakwai na'ura na faWa masa wayar a kashe take.

A fusace ya buWe motar ya fita ya ?walawa direbansa kira, wanda yake zaune acan gurin Maigadin gidan suna hirar rayuwa. A wannan ranar, haka ya isa gida ranshi na ?una da raWaWi, duk yadda Bintu tayi ?o?arin shawo kanshi ta kasa, kuma ya ?i faWa mata takamaimai abinda ya Sata masa rai.

A ?arshe sai kawai yayi mata ?aryar kanshi ke ciwo, da rawar jiki ta Wauko mishi paracetamol yasha, sannan ta lallaSashi ya kwanta, ta daidaita mishi yanayin sanyin A.C ta bashi guri da cewar yayi barci.
"Idan ka huta, in sha Allah ciwon kan zai tafi. Allah ya baka lafiya Sweetheart."

"Ameen."
Ya amsa da?yar yana cije laSSa, kamar da gaske ciwon kan yake yi. Nan kuwa tsabar Sacin ran kalaman Zulaikha ne da suke ta amsa kuwwa a ?wa?walwarshi kamar bitar karatu. Wannan shi ake cewa baki idan ya san abinda zai faWa, bai san amsar da za'a mayar mishi ba.

Tun daga wannan ranar, bai ?ara gangancin ta?alarta da mummunar magana ba. Sai dai ya ?ara kamewa daga gare ta, idan ya je gidan, ta gaishe shi a gaban mutane yana iyakar ?o?arinsa wajen amsawa da sakin fuska. Amma idan zai tafi ta bi bayanshi da niyyar yi mishi rakiya ko kallonta ba ya yi, balle har ta saka ran zai amsa Allah ya tsare hanyar da take mishi.


***** *****


Da gaske ne da ake cewa babu wani al'amari da ya gagari bawa ya koya, sai dai idan tun asali shi wannan bawan bai saka a ranshi yana so ya koya ba. Zulaikha da ta saka ma ranta kuma ta ?wallafa zuciyarta tana so lallai ta koyi turanci, sai ga shi a cikin watanni biyu an shiga na uku sosai bakinta ya faWa da turanci.

Bayan ?o?arin koyarwa kuma a sau?a?e da makarantar online Win da Karima tayi mata register suke da shi. Mummy, Karima, Imam sun taimaka mata ?warai gurin faWawar bakinta a iya magana da turanci, domin gaba Waya suka daina yi mata magana da Hausa, sai turanci.

Tun tana fahimta kaWan-kaWan, suna fassara mata manyan kalmomin da suke amfani da su a jimlolin maganganunsu. Wata kalmar kuma idan ta gani ko a kafar sadarwa a google take searching ta ga ma'anarta da Hausa. Daga nan fa ta kafa ma kalmar ?ahon zu?a kenan har sai ta haddace a ?wa?walwarta.

Yanzu dai a gidan idan aka ji tana hira da hausa tana ?yal?yala dariya da Hajja ne kaWai. Sauran mazauna gidan idan tana so suyi dogon hira dole sai da turanci, tun tana kwaSo jagwalgwalo suna dariya, a haka har bakinta ya goge da iya turancin.

Da gaske ne fa da aka ce da babu makoyi gwani ma da ya ji kunya. Zulaikha dai ta dage da koya, kuma Alhamdulillahi ta Wauko hanyar zama gwana.

Ta inda rayuwarta yake burge mazauna gidan shi ne, ba ma turanci kaWai ba, abubuwa da yawa waWanda bata iya ba a baya, yanzu ka'in da na'in ta dage da koyonsu. Rayuwarta ya Wauko hanyar canjawa gaba Waya, ta fara zama wata ?ar gayu kuma ?asaitacciyar mace ta musamman. Komai na ta ya canja, hatta yanayin yadda take magana yanzu a ?asaice kuma cike da yanga da nutsuwa take yi. Saboda kuskure ?alilan za tayi Karima ko Mummy su gyara mata, ita kuma da hanzari take karSar gyaran tayi godiya.

Yawan zuwan Hibbah gidan akai-akai. Da kuma yadda take Waukarta a mafiyawancin lokuta tana raka ta guraren sana'arta, ko babu Karima a gidan Mummy bata cika hana fitar ba, saboda ta yarda da nutsuwar Hibba da kamun kanta. Wannan yawan fitar, tana haWuwa da wayayyun ?anmata iri-daban-daban, shi ma ya ?ara taimakawa ?warai da gaske gurin gogewarta.

Abun daWin shi ne har yanzu bata yarda ta zubar da kyawawan halayenta na koyi da addininmu ba. Duk wani abu da za tayi addini shi ne gaba, kafin aikata komai.


***** ******


"Daddy pls kar ka yanke wayar, ga Aunty Zulai ta shigo ku gaisa."
Imam bai jira amincewar uban ba ya ruga a guje ya kamo hannun Zulaikha da shigowarta cikin falon kenan da waya ma?ale a kunnenta, tana magana tana sakin wani lallausan murmushi.

Ita da Mashkura ce a wayar, wacce da farko kamar zumuncin nasu zai yanke bayan barin Zulaikha gidan, saboda tsoron abinda zai je ya zo kasancewarta ?anwar Bintu.

Shi yasa Zulaikha ta so yanke duk wata ala?a ta kusa ko ta nesa da ita. Amma saboda naci irinna Mashku, duk yadda Zulaikha take ?in Waga wayarta ita kuma ba ta taSa gajiya da kira ko nuna Sacin ranta ba har dai ta gaji ta sakar mata. Suna gaisawa da zumunci ta waya sosai da sosai, tunda har yanzu da take cikin wata na uku a Abuja ta ?i yarda Mashkura ta san gidan da take zaune.

"Oyoyo Aunty Zulai."
Imam ya faWa cikin karaWin murna sannan ya rungumeta kamar sun daWe basu haWu ba.

Ri?e shi tayi ita ma tana dariya fuskarta na nuna jin daWin ganinshi ?arara. Da harshen turanci take tambayarsa yaushe ya dawo gidan? Ina tsarabar makaranta da ya kawo mata?

"Tsarabarki na nan ta musamman Aunty Zulai. Ga Daddyna can ya kira Vidio call a wayar Granny, zo muje ku gaisa. Pls yau ma kar ki ce a'a! Pls... pls... pls Aunty Zulai... ba don shi ba don

27 / 53