Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   36 / 53

105K to 108K   out of 157.3K words

baki suke yi cikin tsananin ?auyanci da mamaki suna ?arewa gidan kallo. Tun daga farkon unguwar za'a gane ba ta ?ananun masu kuWi bane.

Tsarin gidan na musamman ne. Madaidaici ne zaman mace Waya da iyalanta da tarkacen da ba za a rasa ba.

Ya so ?warai ya sake zama acan Sangarenshi da ke gidan Mummy, kamar yadda suka zauna da marigayiya matarsa. Amma shi kanshi ya rasa dalilin da yasa Mummy ta ce su zauna a sabon gidan nashi da ba'a daWe da kammala komai ba. Sai dai can Win ma yana nan a matsayin nashi, an ?ara gyarawa an zuba sabbin kayayyaki, da yake shi Win mai yawan tafiye-tafiye ne sai Mummy ta ce idan zaiyi tafiya Zulai za ta dinga komawa can gidan tana zama kafin ya dawo ?asar.

Tsarin gidan Amarya Zulai idan aka shiga falo babba za a fara tararwa, wanda aka tsara shi da tsadaddun funitures, daga can jikin bango kuma wata ?atuwar TV stand ce wadda ita ginata ma aka yi kuma aka kafe wata ?atuwar TV plasma dake barazanar cinye bangon saboda girma. A gefe da gefe kuma ga wasu tsadaddun show glass waWanda aka ?awata cikinsu da kayan ado da hasken wuta mai she?i.

Acan wani Sangare na falon kicin yake, inda aka Sata basira wajen zuba duk wani abu da ?a mace za ta bu?ata a cikin madafin gidanta, na gargajiya da na zamani. Abin sha'awar kuma shi ne komai an killaceshi wajen da ya dace.

Store Win ta sha?e yake da kayan gara wanda
Hafiz ya siya kamar bai san zafin kuWi ba, nan ma dai babu ce kawai babu a cikin kayan abincin.

Daga can wani Sangare na falon kuma Wakunan ba?i ne guda biyu da bayi a cikin ko wane Waki. Can gefe guda kuma matakala ce da za'a haura sama inda ?aramin falo da Wakunan mazauna gidan suke.

Dakin Zulai daban, shi ma ya sha jerenshi, na Abban Imam yana kallon nata, duk da a rufe yake amma shima a gyare yake tsaf. Idan ka matsa gaba kaWan kuma zaka tarar da Wakunan yara na maza daban na mata daban.

Gida kam ya haWu iya haWuwa, sai dai fatan Allah Ya ba mazauna cikinshi zaman lafiya da zuriya masu albarka.

Bayan tawagar amarya sun gam kallon gida sun huta, suka yi watanda da soyayiyar shinkafa da ta ji soyayyen nama da ganyayyaki, ga soyayyar agada da coleslaw, suka kuma Wora da kalolin lemuka mabanbanta.

Sai da aka yi la'asar sannan Mummy ta kira Aunty Balira ta sanar da ita su yi ma Amarya sallama, za a mayar da su gidanta su kwana, washe gari kuma da sassafe za'a mayar da su Fa?o.

Da jin wannan maganar nan da nan sai idanun Zulaikha suka fara kawo ruwa, tsakaninta da Allah ita duk tunaninta anan ?an'uwanta za su kwana.

Ta kalli Karima cikin marairaicewar fuska ta ce
"Ayya mana Aunty Karima don Allah ki sa baki su zauna anan mana su kwana? Kin ga fa har yanzu bamu gama sallama da su Aunty Balira ba."

Karimah ta kama baki tana dariya ?asa-?asa tace
"Lallai ma yarinyar nan, daman wa ya faWa miki ana gama sallama da dangi? Ai auren kenan. Ko so kike Yaya ya ci ?aniyata da yammacinnan? To wallahi ba dani ba aikata wannan Wanyen aiki. Ke baki lura da yadda tun Wazu mijinki yake ta auno min kira yana tambayar ba?i sun tafi? Kina tunanin idan ya zo ya samu gidannan da mutane zai saurara min ne? Bayan haka kuma dai umarnin Mummy ne a dole za kiyi ha?uri."

Shigar Aunty Balira cikin Wakin yasa dole suka bar maganar, Karima ta fice daga cikin Wakin tana yima Zuly dariya ganin yadda ta kwaSe fuska ta cigaba da matsar ?wallah.

Kusa da ita Aunty Balira ta zauna, itama da fara'a sosai a fuskarta ta fara raira ma Amarya wa?ar ke kika ce kina so, da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba. Duk yadda Zulai ta kai ga Sata fuska bata san sa'adda ta fara ?yal?yala dariya ba.

Ganin ta saki fuskar yasa Aunty Balira amfani da wannan damar ta ?ara yi mata nasiha mai Nasiha mai shiga jiki.

Daga bisani ta Suge da bata sirruka da kissosin kama miji a tafin hannu irin nasu na mutanen ?auye, amma fa kamu wanda zai ?ara kwantar da mace a cikin zuciyar mijinta, babu boka balle Malam. Zulai har mamakinta ta dinga ji.

Anty Balira ta kalleta da dariya ta cigaba da cewa
"Haba yarinya! Don kina ganinmu a ?auye kuma sai aka ce miki kan duk dusa ne? Mun fa san yadda zamu bi da mazajenmu, dai-dai gwargwado ba na tunanin ko wata ?ar birnin za ta iya kamoni ta wannan fannin. Ke dai ki ri?e abinda na faWa miki za kiga aiki da cikawa."

Ana haka su Aunty Rakiya da Ladidi suka shigo, a gurguje suka yi nasu nasihar sannan sauran waWanda suka rakota duk suka shigo suka mata sallama. Har bakin ?ofa ta raka su sannan ta rungume Yayunta cike da kewa tana kuka su kuma suna aikin lallashi.
A haka dai har suka lallabata ta koma cikin gida ita da Karima su kuma suka shige motoci suka tafi.

Duk yadda su Aunty Balira suka gyara gidan saboda Sata shi da abinci da ?an'uwansu suka yi. Suna tafiya Mummy ta tura masu aiki suka sake ?al?ale gidan, aka kunna turaren wuta a lungu da sa?o na gidan.

Hibbah da isarta gidan kenan ta sa Zuly ta sake yin wanka, sannan ta suka taimaka mata ta shirya cikin tsadaddiyar lafaya mare nauyi, tayi mata sassau?ar kwalliya.

Daga cewa za su zagaya cikin gidan su ga yanayin kwalliyar fulawoyin tsakar gidan sai jin tashin motar Hibba tayi. Ko kafin Zulai ta sauka ?asa ta le?a har mai gadi ya buWe musu get sun fita.

Haka ta tsaya a tsakiyar falon ?asa jikinta a sanyaye. Ko da ta Waga wayarta ta kira Aunty Karima, wayar har ta ?araci ringing Win ta bata Waga ba daga can Sangaren.

Sai bayan kiran ya tsinke ta turo mata da gajeren sa?o cewa tayi ha?uri ta bi Hibbah sun wuce gida, amma gobe da safe tana nan tafe.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina kai bayan ta gama karanta sa?on. Duk da fargaba da tsoron da ke dan?are da zuciyarta bai hana ta ?are ma falon da yake matsayin mallakinta kallo ba. Duk da falon bai kamo na gidan Hafiz tarkace da kayan ?awa ba, amma fa daga kallon farko ta san ya kere na Hafiz aji da kashe naira kamar ba'a san zafinsu ba.

Ta lallaSa cikin sanyin jiki ta koma Wakinta, ta lalubi bakin gado ta zauna tana ta aikin sauke ajiyar zuciya jefi-jefi, zuciyarta cike fal da tunanin yadda ranar zai kasance tsakaninta da Angonta.

Babu jimawa kuma taji dirin mota a waje, kafin ta ji an shigo cikin falon gidan. Kafin ta ankare ta yi wani abu, an turo ?ofar Wakinta an shigo, bakinshi Wauke da siririyar sallama cikin nutsuwa da tausasa murya.

Kamar wacce aka kullewa baki, ta kasa amsa sallamarsa. Sai Waga kai da tayi a hankali tana kallonsa, bugun zuciyarta yana ?aruwa sannu a hankali kamar ana luguden daka. Farar shadda ce a jikinshi kar da ita, ta sha Winkin hannu irin na gidan sarauta da zare kalar brown mai cizawa, hular kanshi sai ya sanya brown wadda ta hau da takalmin kafarshi sau ciki.

Wani kwantaccen murmushi mai matukar daukar hankali ne akan fuskarshi, da ba don yadda cikinta yake cunkushewa da fargaba ba, a gefe guda ga wata irin matsananciyar kunya da ta rufe ta, da baki za ta buWe tayi ta yabon kyawun da yayi a idanunta. Don kuwa yayi kyau sosai da sosai, ya fito a Ango Wanye sharaf!

Ya ?arasa shiga cikin Wakin tare da maida ?ofar ya rufe. Rufewar da yayi daidai da ?ara saurin bugun zuciyarta. Tsoronta ya sake ninkuwa.

Shi kuwa ko a jikinshi, duk da ya kula da yadda take ta wani mutsu-mutsutu akan gadon kamar mai jin fitsari.

A hankali da wani irin taku na ?asaita ya ?arasa jikin gefen gadon, inda aka ajiye Wan ?aramin teburi, ledar dake hannunshi ya ajiye akai. Sai kuma ya hau kici-kicin cire babbar rigarshi yana kallonta murmushin fuskarshi yana ?ara faWaWa.

"Manya-manya maganin ?ananan ?wari. Hajiya Zulaikha amarya a gidan bawan Allah Kamaluddeen! Iye!! Irin wannan kyawu Ummu Imam anya ba zaki sa Wan Mommy ya ?arasa haukacewa a kanki ba?"

Kalamanshi suka bata kunya matu?a, har ta kai ga sanya hannu tana kare fuskarta, a Soye take sakin wani lallausar murmushi tsigar jikinta na tashi.

A gefenta ya ajiye rigar, ya zauna a kusa da ita har jikinshi yana gogar nata, kamshin turaren da jikkunansu ya cakuWe ya haWe waje Waya, ya bayar da wani irin daWi mai matu?ar sanyaya zuciya. Ba ma kamar daddaWan ?amshin da Zulai din take yi na haWaWWiyar humra ta amare da Anty Hibba tayi mata amfani da shi.

Cikin ?an?anin lokaci Kamal ya ji kamshin yana neman ya sanyashi fita a hayyacinshi. ?o?arin zamewa Zulaikha take yi saboda kusancin da suka yi da juna yayi yawa.
Fahimtar abinda take ?o?arin yi yasa shi yin caraf ya kamo ruwan cikinta, sannu a hankali da wani irin salo ya ja ta cikin jikinshi yana sauke numfashi sannu a hankali.

Lokaci Waya Zulaikha ta hau kifkifta idanu kamar wacce tayi ma sarki ?arya. Jin ba?on lamari a tattare da ita yasa ta faWawa cikin matukar kidime, tsoro da fargaba ya sake lulluSeta.

Lura da halin da ta shiga yasa shi kama hannuwanta ya rike ?am a cikin nashi, cikin taushin murya mai nuna kulawa da son amintar da ita yake mata magana, ?amshin Listerine yana fita daga bakinshi yana bugun fuskarta, lokaci Waya yana aikawa sassan jikinta wasu irin sa?onni da suka sanya taji jikinta ya fara rawa sannu a hankali.

"A'a fa! Kar muyi haka dake ba Babyna. Kina sane da al?awarin da muka yiwa juna ko? Ko in tuna miki? Da bakinki kika yi ta jaddada min za mu gudanar da rayuwar gidanmu babu kunya, babu tsoro, kuma shakka sai girmamawa da so da kaunar juna. Ya aka yi kuma tun a yanzu zaki sage min gwiwa Ammata?"

Tayi shiru ta kasa magana. Ya kai hannu ya daga fuskarta yadda zata kalleshi da kyau, amma ta kasa haWa idanu da shi sam. A maimakon ta kalleshi ma sai ta lumshe idanunta.

"Uhmmm! Ko dai don ban sayi bakin amaryar tawa bane take sha min ?amshi? Kiyi hakuri to! zakwaWi da zumuWin zuwa inyi tozali da kyakkyawar fuskarki ni kaWai ?wal ya sanyani hana masu sayen bakin zuwa, don nasan lokaci za su Sata min. Amma a min uzuri, in Sha Allah gobe za a sayi bakinnan da abu mafi daraja! Kin ji?"

?an murmushi tayi kawai, har lokacin idanunta na lumshe. Sai ta hau girgiza mishi kai alamun ba haka bane fa.

"To menene?"
Ya jefa mata tambayar bayan ya fahimci manufarta. Kafin ta amsa ya sake cewa
"Ko rowar daddaWan muryar ake min ni marayan Allah?"

Yadda yayi maganar yana lan?wasa kai gefe guda sai ya bata dariya. Ta sake yin murmushi tana kara girgiza mishi kai a nutse.

"Talk to me pls Baby! Tun dazu babu abinda nake ta son gani da ji kamar ke da kuma muryarki. Me yasa zaki hanani jin muryarki a yanzu?"
Ya ?arasa maganar a marairaice kamar zai saka ihu.

Ganin yadda ya matsa yasa dole ta buWe baki kamar mai tsoron magana, don taga alamun bashi da niyar barinta ta sarara matu?ar bata buWe baki ya ji muryarta ba.
"Yi ha?uri Abban Imamuna. Ina yini?"

Yayi murmushi sosai har hakoranshi suka bayyana
"Yauwa! Good girl. To ko ke fa amaryata? To ya amarcin? Ya hanya? Ya kuma kika baro su Innaye?"

A hankali da dabaru ya fara janta da hirarraki, tun tana amsawa a Warare har ta saki jiki da shi. Daga ?arshe ya mi?ar da ita, suka fara takawa sannu a hankali gwanin ban sha'awa har zuwa ?aton bayin dake manne a dakin.

Alwala suka Wauro, ya ja su suka yi sallar nafila raka'a biyu. Bayan yayi sallama ya dafa kanta yayi addu'a sosai da sosai, yayi mata tambayoyi kan addininta tana amsa mishi da gwargwadon sanin da take da shi. Ya sha mamaki ?warai jin irin sanin da take da shi a addinance duba da inda ta rayu. A fili ya dinga shi mata albarka yana godewa Allah da ya mallaka mishi ita matsayin matarsa.

Shi da kanshi ya zare mata hijabin jikinta sannan ya ce
"Kiyi shirin kwanciya Beb, ina zuwa."
Ledar da ya shiga da ita cikin Wakin ya Wauka ya fice da ita.

Zaman minti biyu ta ?ara a gurin bayan fitarsa, babu abinda ?irjinta ke yi face dakan lugude. Amma tunawa da karin maganar da take cewa duk wayon amarya sai an sha manta yasa ta mi?e a hankali ta nufi wardrobe din ta ta buWe.

Kafin tafiyar Karimah duk ta nuna mata yanayin yadda tsarin shirin kayayyakinta suke, shi yasa bata sha wahalar gano Sangaren kayan barci ba.

Dai-dai gwargwado tana da iliminta na addini, na fannin rayuwa ma da zamantakewa tana da su gwargwado. Ta san tana son mijinta kamar yadda shi ma yake sonta, don haka tayi Wamarar kula da shi da sauke duk wani nauyi na shi da ke kanta in dai ba tana son ta wayi gari taga wata mai zafin naman ta yi wuff da shi bane.

A hankali take WaWWaga tarin kayan barcin da aka zube mata tana dubawa har Allah Ya hadata da wata doguwar riga mai gajeren hannu ruwan madara. Ta dauka ta sanya, ta ?ara feshe jikinta da turare.
Da ta tsaya gaban mirror taga yadda rigar tayi mata kyau ta kuma kamata, sai taji ba zata iya tsayawa gabanshi a haka ba musamman a daren yau.

Don haka ta Wauki madaidaiciyar hijabi ta dora akai wadda ta tsaya mata a ruwan ciki.
Tana cikin saka hijabin sai gashi ya shiga dakin saye da pyjamas na barci masu budadden kirji. Hannunshi rike da babban tray.

Tayi duru-duru tana kokarin hana idanunta kallonshi, kafin kuma ta yunkura da nufin karbar farantin hannun nashi, yayi gaggawar dakatar da ita. Ya ajiye farantin a tsakiyar daki, ya zauna yana linke kafafunshi tare da kama hannunta ya kara zaunar da ita kusa dashi kugu da kugu.
"Yau ke amarya kike fil! Oya, zo in ciyar da ke in kuma shayar da ke madara."

Haka nan tana no?ewa da sussunne kai, ya dinga yankar wani lafiyayyen gashin nama yana bata a baki, gefe guda kuma ga tatacciyar madarar yoghurt mai masifar daWi yana bata. Sai da ya tabbatar ta koshi sannan shi ma ya ci yayi nak!

Ko da ya tashi da niyar dauke kayan wannan karon hana shi tayi, ta daukesu ta kai kicin. Sauran naman ta nade a foil paper ta sanya a cikin firjin, kayan da suka Sata kuma ta daurayesu ta jingine a jikin rag.

Ta tunkari hanyar dakinta zuciyarta na bugu, jiki na mazari. Da ta je jikin kofar ta jima tana kokonton budewa, har sai da ta jiyo muryarshi daga cikin dakin yana cewa
"Wai dodo ne a cikin dakin da ba zaki shigo ba Umman Imam? Ko dai so kike in bar miki Wakinki in koma nawa?"

Kamar kazar da ?wai ya fashe ma a ciki ta buWe Wakin ta shiga. Sai ta gan shi har ya kwanta yana danna waya.

Shigowarta cikin Wakin ne yasa shi ajiye wayar, ya juya yana kallonta yana mata wani murmushi kasa-kasa.
"Zo kiji wani labari mai daWin gaske."

Tayi duru-duru tana kallonshi duk a daburce. Bakinta na rawa ta ce
"Uhmmm... dama... bari in wanke bakina"

Ya gyaWa kai
"Ok! je ki wanke ki dawo. Ina nan ina jiranki"

Ta fada banWakin a sukwane ta rufe kamar wacce wani abin tsoro ya biy. Shi kuwa me zayyi in ba dariya ba.

Yana kallonta ta dinga shige da fice tsakanin bandakin da dakin, babu wani takamaimai abinda take yi kuma sai zirga-zirgar.

Da dai yaga abin nata ba na karewa ba ne, sai ya tashi da kanshi yayi caraf da ita tana fitowa daga bayin sai ganin mutum tayi a gabanta ya ri?o ?ugunta da sauri.
Ya cakumo wuyan hijabinta da hannu Waya lokaci guda ya ?arasa haWe ta da jikinshi.

Wata irin ajiyar zuciya mai nauyi ya saki sannan ya fara kokarin zame mata hijabin, suka hau kici-kici, yana ?o?arin cire mata ita kuma tana hana shi.

Murya can ?asa ta yadda take jin shi ?asa-?asa ya ce
"Don Allah don Annabi kada kiyi min iyaka da abinda Allah Ya halatta min. Nasan kin fini sanin hukuncin hakan, kiyi ha?uri. Nayi tunanin mun gama magana akan kunyar nan? Don gaskiya wahalar da ke kawai zata yi, ni dai babu ruwana. Ba zan taSa yarda kunyar nan ta dinga shiga hakkina ba!"

Yana maganganun a lokaci Waya kuma yana cusa hannunsa Waya a cikin rigarta. Bayan nasarar cire mata hijabin da yayi har ya fara Salle maSallan gaban rigarta.

Zulaikha dai kunya ta gama rufe ta, ji take ina ma kasa za ta tsage ta shige ciki don kunya. Kamal dai ko a jikinsa, a ?arshe ma cusa kanshi yayi tsakankanin kirjinta yana sakin wani irin numfashi mai nauyi. Duk yadda taso ta hana wata nannauyar ajiyar zuciya da ta taso mata kasawa tayi.

Ya saki murmushi a tausashe jin ajiyar zuciyar da ta saki. Lokaci Waya kuma ya cigaba da kokarin cakuda mata lissafi a matsayinta na sabon shiga a wannan harkar.

Tsananin kamshin da ko'ina na jikinta yake yi da taushin fatarta da wani irin yanayi da ya ziyarceshi irin wanda zai iya rantsewa bai taSa shiga cikin makamancinshi ba, ya taimaka kwarai wajen fitar da shi daga dan sauran hayyacin da ya rage mishi a jiki.

Ya manta yaushe ne karshe da ya jingina jikinshi da wata mace da sunan romanciyya. Labaran da ya fara bata sun fi karfin tunani da jikinta baki daya.

Musamman da yayi nasarar danganata da gado. Sai idanunta suka raina fata, ta

36 / 53