Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 53

21K to 24K   out of 157.3K words

take, suna sanye da kayan shan iska na turawa. Ga Wan ?aramin teburin glass nan a gabansu Wauke da yankakkun kayan marmari.

A mamakance suka Waga idanu suna kallon Zulaikha wacce ta bayyana a gabansu tsulum kamar an jefo ta. Ita kanta sai a lokacin ta lura da irin katoSarar da tayi, don haka da saurin gaske kuma a daburce ta juya baya tana soshe-soshe hankalinta a tashe.
"A'uzubillahi minasshaiWanirrajim."
Ta janyo a'uziyyar a ruWe, domin duk iya tsawon rayuwarta wannan shi ne karo na farko da taga mace da namiji a cikin makamancin irin wannan halin.

Tsananin Sacin rai da ba?in ciki cakuWe da dun?ulallen takaici yasa Bintu ta kasa magana. Sai kawai ta mayar da kanta kan ?irjin Hafiz ta kwantar, ta lumshe idanunta tana jan numfashi sama-sama saboda Sacin rai.

A Sangaren Hafiz kuwa duk da sanin da yayi Zulaikha ba ta da hankali, bai taSa tsammanin rashin hankalin nata ya kai haka ba. Ko da ya buWe baki da nufin zazzaga mata bala'i sai ya rasa ma abinda zai ce mata, domin da ace masifa da bala'i ko duka na saka Wan'adam ya kiyayi lamarin wani, lallai da tuntuni Zulai ta daWe da fita daga cikin harkokinsa gaba Waya.

A karo na barkatai ya sake kallon yadda take ta dawurwura guri Waya, ita bata fita daga falon ba kuma ita bata jiyo ta fuskance su ba balle har ta faWi abinda ya shigo da ita a daidai irin wannan lokacin.
"Me ya kawo ki?"
Yayi ?arfin halin tambayarta da sha?a??iyar murya.

"Dama... Dama... Innaye ce ... ta ce... Dama... in zo in karSi ruwan zafi..."
Ta faWi maganar a rarrabe tana zazzare idanu a tsorace kamar za ta kife a gurin.

Ta riga ta gama yanke ma ranta lallai mai hana Yaya Hafiz cin ?aniyarta a daidai wannan lokacin sai dai wani ikon Allah, don haka kawai sai ta fara matsar ?wallah, ta san ko ta gudu sai ya bi ta har gaban Innaye ya tattaka ta, shi yasa ma bata yi yun?urin gudu ba.

Sai dai ga mamakinta, tana jiran ta ji saukar duka ta ko ina a jikinta sai ji tayi ya sake cewa da sha?a??iyar murya.
"Je ki dafa a kicin."

A kiWime ta juyo tana kallonsu kamar bata ji abinda ya faWa da kyau ba. Sai kuma ta sake juya musu baya da sauri tana ?ya??yafta idanu. A hanzarce kuma sai ta kama hanyar zuwa kicin Win har tana haWawa da gudu-gudu.

"Ke! Ke!! Ke!!! Ina za ki?"
Bintu ta dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa haWe da jefa mata tambayar.

Cak! Taja ta tsaya a inda take ?afafunta na rawa, amma bata juyo ta kalle su ba, kuma bata amsa tambayar da Bintu tayi mata ba.

"Sweethert? Wai ko dai ka manta da wa kake magana ne? Ba fa Rabi ba ce mai aikinmu. Zulai ce da ta zo daga ?auye kake cewa ta shiga kicin Wina mai Wauke da kayan girki na zamani ta dafa ruwan zafi. Ta iya amfani da Gas ko electric cooker ne? Ko kuwa so kake ta haddasa mana gobara saboda jahilci da ?auyancinta?"
Maganganun Bintu masu kama da saukar tafasasshen dalma a zuciyarta suka sauka a kunnuwanta.

Jikinta a sanyaye ?warai ta juyo tana kallon Bintu da tun da ta faWi maganganun ta maida kanta ta kwantar a ?irjin Hafiz kamar ba ita ta faWa ba. A muzance, ta kalli Hafiz da shi ma ita yake kallo, idanunta ciccike da hawaye.

Shi kuwa na shi idanun Wauke da wani irin yanayi ne da baki bazai iya fassarawa ba. Kawar da fuskarshi yayi daga gare ta ya mayar kan matarshi, kafin ya amsa mata da cewa
"Kuma fa haka ne My dear. Wallahi shaf na manta."

Sai kuma ya sake mayar da idanunshi kan Zulaikha ba tare da wani yanayi na tausasawa ba ya ce
"Ke ajiye flask Win nan. Yanzu idan mun tashi Bintu za ta dafa ruwan mu taho mata da shi, daman akwai magunguna da alluranta duk za mu haWa mu taho da su. Ki gaishe ta da jiki, na dawo ofis Wazu a gajiye ne shi yasa ban shigo ba."

Baza ta ce ga sadda ta ajiye flask Win ba, balle kuma ta bada labarin yadda aka yi har ta fice daga falon. Kawai ta tsinci kanta ne a ?ofar Sangarensu tana tafe kamar ana jaye da ita saboda tsananin tashin hankali.

Har ta sa hannu za ta murWa hannun ?ofar Wakin sai kuma ta fasa, can kusa da famfo taje ta tsuguna, tasha kukanta ta gode ma Allah kafin ta Waura alwala ta shige cikin Waki. Har wannan lokacin, jin ta take a muzance. Duk da ba yau ne farau da Bintu take ci mata mutunci da tozarta ta ba, amma bata taSa gurza mata wanda ya tsaya mata arai kuma ya ?ona mata zuciya irin wannan ba.

A yadda take ji a ranta gidan da komai na cikinsa ya gama fice mata arai. Babu abinda take so irin ta buWe ido ta ganta a ?auyensu. Ko da ta shiga cikin Wakin, sai jan gefen hijabi take yi tana rufe fuskarta, sai kuma Allah ya taimaketa ta tarar Innaye na sallah, bata Sata lokaci ba itama ta kabbarta sallah.

Tana idarwa ta haye kan gado ta du?un?une jikinta da bargo kamar me jin sanyi. Tana jin shigowarsu Hafiz da Bintu ta sake Soye kanta, kamar bata san Allah yayi ruwansu a cikin Wakin ba.

"Zulai barci take yi ne?"
Bintu ta tambaya da karaWin murnar da Zulaikha ta rasa ko ta mece ce.

Ba Innaye da aka tambaya ba, hatta Hafiz sai da ya kalli Bintu da irin kallon nan na mamakin yau kuma ke ce kike tambayar Zulai?

Lura da irin katoSarar da tayi yasa tayi saurin gyara maganarta da cewa
"Gani kawai na yi ta kwanta ta rufa duk da zafin da ake yi. Ka san baya ba ta da kaWan, idan ba ta da lafiya ne ai gara ta faWa a bata magani. Anyway, Innaye ya ?arfin jiki?"

A hankali ta ajiye casbahan hannunta a gefe Waya ta ?ura ma Bintu idanu. A zuciyarta, addu'a take yi Allah ya kare ta da zuriarta daga sharrin Bintu. Dubi dai yanzu yadda take tambayarta ?arfin jiki da kulawa da damuwa a fuskarta da yake a gaban Hafiz ne, kamar ba ita ce ta wula?antata Wazu a asibiti ba.
"Auta lafiyarta ?alau. Ni kuma jiki na da sau?i Alhamdulillah."
Ta amsa da yanayi na ba yabo ba fallasa, bayan ta yi matu?ar ?o?ari gurin kawar da tunanin da ke dan?are a zuciyarta.

Irin kallon da Innaye ta ?ure ta da shi, shi ya Wan sanyayar mata da jiki. Nan take ta fara addu'a a zuciyarta kar Allah yasa Innaye ta tona mata asirin irin yadda ta banzatar da ita Wazu a asibiti. Ko da taji amsar da Innayen ta ba ta ta kasa sakin jiki ta cigaba da kwarkwasa kamar yadda ta shiga cikin Wakin da farko.

Ganin har lokacin idanun Innaye na kanta, sai ta fara jin ta a muzance. A dole ta saukar da ?wayoyin idanunta ?asa ?irjinta na bugawa kaWan-kaWan. Ta kasa ?ara cewa komai, sai Hafiz ne ya amsa maganar Innaye da cewa

"Ma sha Allah! Allah ya ?ara sau?i Innaye. Ga magunguna da alluranki nan Bintu ta taho da su.
Kuma kin ji wani ikon Allah ashe duk irin ciwukan da aka yi tsammanin samu a jikinki ma ba'a samu ba. ZazzaSin cizon sauro ne kawai sai typhoid da aka samu a jininki. Kin ga a wannan karon dai ya zama dole Innaye ki ha?ura da kwanciya babu gidan sauro. Kuma shan ruwan ?auyen nan ma ya zama dole ki ha?ura da shi, zan dinga aika miki da tsaftataccen ruwa duk ?arshen wata in sha Allah, domin likitoci sun tabbatar da hanya ta farko ta kamuwa da typhoid daga ?azantaccen ruwan sha ne..."

"Hafizu, wannan ruwan da kake kira da ?azantacce tun kafin a haife ka shi muke sha, muke komai da shi. Kuma kai Win ma kafin barowarka ?auyen ?azantaccen ruwan nan dai kake sha, kuma ya rayar da kai har zuwa girmanka."
Innaye ta katse shi da Wan murmushi a fuskarta na jin daWin yadda ?arara Wan nata ke nuna damuwa da lafiyarta.

?ara gyara zama yayi yana cigaba da yi mata ?arin bayani, a fuska da muryarsa babu abinda ke fita sai matsananciyar ?aunar mahaifiyarsa.
"Duk da haka dai Innaye. Kin san yanzu abubuwan sun canja ba kamar da ba. Yanzu cututtuka ba su wuyar shiga jikin Wan Adam. Ya zama dole mu dinga ?o?arin kiyaye duk abubuwan da aka tabbatar suna da rawar da suke takawa wajen Wabba?a samuwar cututtuka a jikinmu. Amma idan baki gamsu ba ga Bintu nan, tunda ita likita ce za ta miki cikakken bayanin da za ki fahimta na abubuwan da ya kamata ki kiyaye."

Ya maida idanu kan Bintu yana jiran tayi ma Innaye ?arin bayani kamar yadda ya nema. Abu Waya da bai sani ba shi ne Bintu dai ba baka sai kunne, sai a yanzu ne duk irin cin kashi da tozarcin da tayi ma Innaye tun bayan fitarsu yake dawo mata arai, a tsorace take sosai kar Innaye tayi suSul da bakan furta Waya daga cikin abinda ta aikata mata.
"Eh! Haka ne My Dear. Uhmmm! Innaye don Allah ki kiyaye. Duk abinda zan faWa My dear ya riga ya faWa, yanzu dai bari in haWa alluran inyi miki in baki magungunan. Ina fatan kin ci abinci?"
Ta ?arasa da tambayar har lokacin ta kasa Waga idanu ta kalli Innaye cikin ido.

"Eh na ci."
Innaye ta amsa idanunta na kallon irin ruWewar da Bintu take ciki. Duk da tayi hasashen me ya Waga hankalin Bintu cikin ?an?anin lokaci haka, amma sam bata yi niyyar tona abinda tayi mata ba. Idan tayi haka kamar bata gode Allah da ya dube ta ya haWa ta da Karimatu a lokacin da Bintu ta so tozarta ta bane.

Tana kallo Bintu ta haWa allurai har guda biyu tayi mata. Sannan ta Sallo magunguna kala huWu ko wanne Wai-Wai ta mi?a mata. Hafiz ya buWe Waya daga cikin gororin ruwan da ke cikin Wakin ya zuba a kofi ya mi?a mata.

Sai da tasha magungunan ta haWiye sannan Bintu ta fice daga cikin Wakin bayan ta basu uzurin za ta je ta amsa waya. Nan ta bar Hafiz suna cigaba da hira da Innaye ita dai ta cikawa bujenta iska tana sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Har lokacin bata daina addu'ar Allah ya kulle bakin Innaye kar ya bata ikon tona asirin tozarcin da tayi mata a asibiti.

Duk abinda ke faruwa har zuwa ficewar Bintu, da ficewar Hafiz bayan an kira sallar isha'i, Zulaikha tana jin su. Ko ?wa??waran motsi bata yi bane domin ba ta ?aunar tozali da Waya daga cikin fuskokin su biyun.

"Auta? Wai lafiya kike kuwa?"
Innaye ta jefa mata tambayar lokacin da ta yaye rufar da tayi ma kanta, ta mi?e ta zauna akan gadon tana mutsuttsuka idanunta kamar wacce ta farka daga barci.

"Lafiya ?alau. Kawai dai ba na jin daWi ne."
Ta amsa fuskarta ba walwala.
"Wallahi Innaye duk na ?osa mu koma gida."
Ta sake faWa fuskarta na bayyana gaskiyar maganar daga zuciyarta ne.

Da?i?u talatin Innaye ta Wauka tana karantar yanayinta. Irin shirun da Auta tayi tun bayan da ta idar da sallah, ta san ba haka kawai bane. Amma tunda bata faWa mata komai ba sai bata matsa mata da tambaya ba, don wani sashe na zuciyarta na tunanin ko don maganar auren da tayi mata Wazu ne ya canja yanayinta? Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta ce
"Ki kwantar da hankalinki. Kamar gobe ne za mu koma gida in sha Allahu."


*****


Duk da kasancewarta cikin mutane masu nauyin barci, irin numfarfashin da Innaye take ja sama-sama tana saukewa a wahalce ya fi ?arfin a ce ta gagara farkawa.

Bayan ?arfin nishin kuma kusa da kusa suke kwance. Tun tana jin nishin kamar a mafarki, har dai daga baya ta tabbatar ba mafarki take yi ba don haka ta farka a firgice.
"Innaye? Inna lillahi... Me yake damunki?"
Ta jera mata tambayoyin a ruWe. Kafin ta amsa da saurin gaske ta mi?a hannu ta taSa wuyan Innayen, matsanancin zafin da taji yasa tayi saurin Wauke hannunta a gaggauce.

"Subhanallahi... Jikinki zafi sosai Innaye... ZazzaSi kike yi ne? Bari in kira Yaya."
Ba tare da duba tsalawar da dare ya fara yi ba ta yun?ura za ta sauka akan gadon a galabaice Innaye ta ri?o hannunta.

"Dare... dare ya yi... ki ?yale.. shi zuwa safe."
Tayi maganar da?yar, da yanayin da ke bayyana tana cikin mawuyacin hali.

Tafin hannun Zulaikha da ke cikin nata ta sake ri?ewa sosai, ta ja hannun a hankali har zuwa kan goshinta, a jiga ce ta sake cewa
"Kaina ciwo sosai kamar zai faWi, ki kama min Auta."
Ta sake faWa a wahalce.

Kasancewarta mai saurin kuka tuni har hawaye ya wanke mata fuska. Ta matsa sosai kusa da Innaye ta Wauki kanta ta Wora akan cinyarta.

Kamun kai tayi mata kamar yadda ta bu?ata, bayan ta gama sai ta cigaba da tofa mata duk irin addu'ar da ya zo bakinta.

Ko da ta Waga idanu ta kalli agogon da ke ma?ale a bango cikin Wan madaidaicin hasken da suke bari a kunne idan za su kwanta. Sai taga ?arfe uku na dare saura minti takwas, sai a lokacin ita da kanta taga rashin dacewa kiran Yaya Hafiz a wannan tsakiyar dare.

Duk irin barcin da ke idanunta tuni ta neme shi ta rasa, a ta?aice ma idanunta bushewa suka yi, idanunta biyu tana hawaye tana tofe Innaye da addu'a har zuwa lokacin da ladanin unguwar ya kwaWa kiran sallar farko.
A wannan dare, ta shiga cikin gagarumin tashin hankali ne irin wanda bata taSa shiga ba a rayuwarta. Tun da tayi wayau bata taSa ganin Innaye cikin ciwon da ya jigatar da ita ya fitar da ita a hayyacinta cikin ?an?anin lokaci irin haka ba.

Ko wannan ciwon da take yi har ya zama sanadiyyar da yasa suka baro garinsu zuwa Abuja bai mata tsanani haka ba. Bata taSa tsammanin Innaye za ta kai asubahi a raye ba, ta gama fitar da rai da cewar Innaye za ta cigaba da rayuwa, saboda yadda numfashin ma a wahalce take ja tana saukewa da?yar. Amma da yake rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke sai ga shi cikin hukuncin Allah ana tayar da i?amar sallar asubah wani nannauyan barci yayi awon gaba da Innaye.

Minti Waya, biyu, sai ta kara kunnenta a hancin Innaye don ta ?ara tabbatar da barcin take yi ko dai ba barcin bane? Sai da ta tabbatar barcin ne kafin ta iya kwantar da kan Innaye a hankali bisa filo ta sauka daga kan gadon.

?afafunta duk sunyi tsami, idanuwanta sun kumbura sunyi tulu-tulu saboda kuka. Jikinta a sanyaye ta shige banWaki domin Wauro alwala.

Ko da ta idar da sallah, bata tsaya yin Azkhar kamar yadda take yi duk bayan sallar asubahi ba tayi addu'a a gaggauce ta sake hayewa kan gadon tana Wan tattaSa jikin Innaye. Cikin hukuncin Allah kuma sai taji zazzafan zazzaSin ya sauka gaba Waya, har ma wani zufa ne ya Wan tsattsafo akan goshinta.

Gefen hijabin da ke jikinta tasa ta goge ma Innaye gumin tana sauke nannauyan ajiyar zuciyar samun nutsuwa. A nan kan gadon, ta cigaba da Azkhar har zuwa sadda wani daddaWan barci ya kwasheta.

Sallamar da Hafiz yake ta dokawa a ?ofar Wakin shi ya farkar da ita a firgice daga wani mummunan mafarki da take yi a daidai lokacin. Karaf idanunta suka faWa kan agogo, ?arfe bakwai da minti arba'in da biyu na safe.

Izuwa lokacin, Hafiz ya gaji da sallamar da yake ta yi yana ?arawa ya shiga cikin Wakin don ganin lafiya suke kuwa?

Idanunsa cikin nata ya zabga mata harara.
"Don tsabar iskanci kina ji ina ta doka sallama kin ?i amsawa?"

"Yi ha?uri. Barci nake yi, sallamarka ce ta tashe ni. Ina kwana?"
Ta jera mishi maganganun cikin sanyin murya, kamar dai ba Zulai ba da yasan ta bala'in raina shi.

Irin yadda ta amsa mishi har sai da yasa shi ?ara kallonta sau Waya. Sai yaga ta sunkuyar da kanta ?asa tana wasa da yatsun hannayenta. TaSe baki yayi, ya ?arasa cikin Wakin har kusa da gadon idanunsa akan Innaye da har lokacin take barci.

"Wani irin barci Innaye take yi haka? Ina fatan dai lafiyarta ?alau?"
Ya tambayeta ba tare da ya amsa gaisuwarta ba. Babban dalilin da yasa shi yin tambayar kuwa shi ne barci bayan sallar asubahi ba Wabi'ar Innaye bace, ko lokacin azumi ita ba ta komawa irin barcin nan na bayan sallar asubah.

Zama take tai ta tasbihi da istigfari har gari yayi haske sosai tayi sallar walha. Ko za ta kwanta sai bayan ta idar da sallar walha, tara da rabi zuwa karfe goma na safe.

"Ba ta da lafiya. Kwana tayi da zazzaSi mai zafi a jikinta kamar baza ta wayi gari ba..."

"Bakinki ya sari Wanyen kashi. Sakarya kawai wacce bata iya magana ba. Kawai don ta kwana da zazzaSi a jikinta sai ki ce kaman baza ta wayi gari ba?"
Nan ya cigaba da zazzaga mata faWa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kawai don ta ce Innaye kamar baza ta wayi gari ba.

Ita dai Zulaikha shiru tayi mishi, a madadin ta ce wani abu ma sai ?ara sunkuyar da kanta ?asa tayi idanuwanta na tsiyayar da hawaye. A zuciyarta take ?ara tunanin irin rijiya da bayan da Innaye ta tsallake jiya, duk da tana yarinya kuma ba'a taSa yin mutuwa a gabanta ba ta san bata yi kuskuren cewa irin zazzaSin da Innaye tayi jiya kamar baza ta wayi gari ba.

Amma tunda ba a gabanshi aka yi ba dole tayi mishi uzuri, ta san babu ma amfanin yi mishi ?arin bayani don bazai fahimce ta ba. Tana jin shi har ya gama zazzaga masifar da yake yi ya fice daga Wakin a

8 / 53