Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA Complt Complete Hausa Novel by Fareeda Abdallah

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   46 / 53

135K to 138K   out of 157.3K words

shawara.

Haka Sangaren haWa kayan akwati, ba tare da jin zafin kuWi ba haka ya dinga antaya mata manyan kuWaWe tana shiga kasuwa ita da Hibba da Karima suna haWo kayan akwati. Ba tare da ?yashi ba kuwa Zulai ta dinga zaSo komai mai bala'in tsada, cikin ?an?anin lokaci ta haWa mishi akwatuna guda goma sha biyu cif!

Sai daga baya ne ma da Mummy ta ga kayan tayi faWa kamar za ta ari baki. Ta rage kaya masu yawa har akwati biyu ta dam?a ma Zulaikha da cewar lallai ta aika ma Innaye da su Aunty Balira su samu na cin buki.

Ko da Hafiz yaje gidan, Zulaikha ta faWa mishi yadda aka yi kuma ta nuna mishi kayan ba ?aramin kimar Mummy ne ya ?aru a idanu da zuciyarsa ba. A ransa yake ji lallai yanzu ne fa zaiyi aure.

Idan ya kalli Aadil kuwa farin ciki da nishaWinsa ?ara ninkuwa yake yi. Duk yadda Bintu take ji tana gatanta yaron sai dai kawai ace ita ta haife shi, amma ko rantsuwa yayi babu kaffara an fi gatanta shi a gidan Mummy fiye da gurinta.

Kuma wani abun burgewa shi ne yaron sam yanzu ba ya ?wuiya, ga wani wayau da ?iba, kyau na musamman da yaron ya ?ara. Ba shi gurin Mummy, ba shi gurin Karima, ba shi gurin Hajja, balle kuma Zulaikha da take riritasu shi da Imam kamar su kaWai ne ?a?aye a duniya.


********

Tsawon sati biyu kenan da faruwar al'amarin amma Bintu ta kasa komawa dai-dai. Tun iyayenta suna hantarar ta, suna share al'amarinta, suna watsi da damuwarta, har sun zo sun fara tausaya mata. Amma a Soye, saboda dukkansu sun san irin matsanancin soyayyar da take ma Hafiz.

Duk wanda yasan Bintu a baya, idan ya ganta yanzu abu na farko da za'a fara tambaya shi ne
"Ta yi rashin lafiya ne?"

?ara auren Hafiz, da sakin da yayi mata na bagatatan, wasu abubuwa ne da ko ana ya?in duniya na uku a zamantakewar aurensu bata taSa tsammanin za su gitta a tsakaninsu ba.

Ta daWe da gama sakankancewa Hafiz na ta ne ita kaWai. Don ita kaWai aka halicce shi kamar yadda aka halittota don shi kaWai.
Duk da tun kafin faruwar wannan al'amarin zamantakewar na su ya Wan fara tangal-tangal sanadiyyar sakaci da kasa danne zuciyarta ita bata taSa tsammanin zai iya kallon wata ?a mace da idanun so balle har ya nemi sama mata sarari a filin zuciyarshi ba.

Saki kuwa... Idan ta tuno wannan kalmar wasu sababbin hawaye ne ke sake Salle mata kamar an buWe famfo.
'Ita Bintu Hafiz ya saka? Ita? Ita Bintu fa?'

Zuciyarta na cika da tantamar anya kuwa Hafiz ne da kanshi ya iya sakinta? Ko dai wani mai ba?in ciki da aurensu ne ya shiga rigar Hafiz ya tafka wannan ?atoton kuskuren? Sai ta yi kamar baza ta yarda da sakin ba kuma sai ta tuna ai ranar da abin ya faru ta ga ficewar Hafiz daga layinsu. Kuma wanda ya bata takardar sakin wani mai mutum ne mai muhimmanci a rayuwarta da bazai taSa yi mata ?arya don ya kassara ta ba.

A cikin waWannan kwanakin ?unci da raWaWin, ta yi Allah ya isa ga Innaye da ?a?anta mata ya fi baki dubu!! Domin ita a ganinta duk su ne ummul-aba'isin faruwar waWannan munanan al'amura a gareta.

A karo na barkatai, ta yi juyi akan gadon, zuciyarta cike da ?unci da matsanancin damuwa. Sannu a hankali ta fara jan shesshe?ar kuka kamar yadda ta saba, tana yi tana taushe bakinta don kar Mashku ta ji kukan da take yi.

A karo na farko, tun bayan faruwar al'amarin da tsawon dararen da ta kwashe tana raba biyu bisa uku da kuka Mashkura ?anwarta da suke kwana Waki Waya tayi mata magana a tausashe.
"Aunty Bintu a ganina kukan nan da kike kwashe tsawon lokaci kina yi ko wane dare, ke baki yi barci ba, ni baki barni na yi nutsattsen barci ba bazai taSa miki magani ba. Why not baza ki Sata lokacin kukan akan dadduma kina kaima mahaliccin sammai da ?assai kukanki ba...?"

"Mashku... Don Allah ki faWa min. Aduk cikin wannan al'amarin ina abin saki? Me nayi ma Hafiz da zai sake ni? Me nayi masa?"
Ta katse Mashkura da jerin tambayoyin muryarta na fita da matsanancin kuka.

Abu Waya da Mashkura ta fahimta a maganganun Bintu shi ne har yanzu ita bata yi da na sanin abinda tayi ba. Kamar ma laifin Wungurungum ta kwashe ta Wora kan Hafiz ne da danginsa, bayan kuma ita ke da laifi kaso casa'in da biyar bisa Wari.

Kafin ta amsa Waya daga cikin tambayoyin Bintu, lalubawa tayi a kusa da filonta ta Wauko wayarta ta duba lokaci, ?arfe uku da minti arba'in na dare. Barci ne sosai a idanunta, don haka ta katse dogon maganar da Bintu ke neman jan ta da shi ta hanyar cewa
"Uhmmm! Ba ni da amsar Waya daga cikin tambayoyinki Aunty Bintu. Ni dai shawara kawai na ba ki, da ki dinga Sata tsawon lokaci kina rusa kukan da bazai miki magani ba, gara ki dinga Waukan lokacin kacokan kina kai ma Allah kukanki. Ko babu komai za ki samu sanyin zuciya da nutsuwa. Allah ya tashe mu lafiya."
Daga haka bata sake ce mata komai ba ta juya mata baya.

Da yake Bintu ba ta daga cikin irin matannan da ibada ya dame su, duk da wannan shawarar da ?anwarta ta ba ta bata yi amfani da shi ba. SharSen Kukanta ta cigaba da yi, tana haWa da jan ajiyar zuciya tana saukewa, ta Wauki tsawon lokaci a haka har zuwa sadda gwanin iya sata da taimakon shaiWan yayi awon gaba da ita, lokacin ana ta kiraye-kirayen sallah a wasu masallatai.

Washe gari, kamar yadda Raudha ta saba zuwa gidan duba jikin Bintu duk bayan kwana biyu, misalin ?arfe huWu na yamma tayi ma gidan dirar mikiya.

A waWancan kwanakin, duk zuwan da take yi bata taSa samun damar yin nutsattsen hira da Bintu ba. Cikin kuka ta faWa mata Hafiz ya sake ta, sannan kuma zai ?ara aure. Daga haka har ta bar gidan ba ta ?ara samun kan Bintu balle har suyi wata doguwar magana, sai dai ta gama zamanta da maWaukakin damuwa a fuskarta daga bisani tayi ma Umma sallama ta tafi.

A yau, ko da ta isa gidan ta yi mamakin samun Bintu cikin ?ar nutsuwa kaWan. Ta yi wankanta tsaf, duk da dai babu ko Wigon kwalliya a fuskarta. Wayarta ne ma a hannunta tana dannawa, fuskar nan a Waure tamau.

"Raudha... Ashe don tsabar wula?anci tun ranar da muka je Fa?o misalin ?arfe biyar da rabi na yamma Hafiz ya turo min sa?on saki ta text message..."

"Da gaske kike yi?"
Raudha ta jefa mata tambayar da mamaki a murya da fuskarta.

Bata iya amsawa ba, sai wayar ta mi?a mata tana nuna mata sa?on.

"Uhmmm! Allah ya kyauta... Sai ha?uri kawai."
Raudha ta faWa jikinta a sanyaye, bayan ta gama karanta sa?on.

"Ni yanzu kin san menene damuwata?"

"A'a! Sai kin faWa!"
Raudha ta amsa mata.

"Wace ?ar iskar matsiyaciya tsinanniya annamimiyar yarinyar ce za tayi gangancin aura min miji uban ?a?ana? Duk tunanina ya ?u?e, na rasa gane wace Karimatu ce? Ko dai wata ba?auyiyar ce matsiyatan danginsa da basa ?aunar Allah da Ma'aiki SAW suka sake haWa shi da ita..."

"Uhmmm! Za kiyi mamaki idan na ce miki Nurse Karima ce, ?ar gidan Hajiya Saudah da kike kira Mummy sama Mummy ?asa..."

"Mmmmm.... me kika ce Raudha? Dddddddda gaske kikkkkkkkeeee yi?"
Bintu ta tambayeta da wata fitinanniyar in'ina a muryarta saboda tsananin tashin hankali.

"Wallahi da gaske nake yi. Lamarin maza ba sai dai a barsu ba Bintu? Abinda ya kawo ni gidanki kenan ranar sai na tarar da ke cikin tashin hankalin Wauke Aadil da Hafiz yayi."
Gyara zama Raudha tayi, ta kora ma Bintu labarin duk abinda ya faru wancan ranar a asibitinsu gaban idanunta.

"Karima dai Raudha? Karima? Yanzu sakayyar da Mummy za tayi min kenan? Ni ce fa na shiga na fita har na sama mata aiki a asibitinmu, ashe sakayyar da za suyi min kenan?"
Ta jera ma Raudha tambayoyin cikin rawar murya da tashin hankali.

Kafin Raudha ta amsa ta cigaba da cewa
"Saboda Allah me Karima take da shi wanda ni bani da shi da har za ta Wauki hankalin Hafiz..."

"Uhmmm! Bintu kenan! Sau nawa ina faWa miki Namiji Wan kunama ne ga za?i ga harbi kina saka auduga ki toshe kunnenki? Ko da yake yanzu da layi ya biyo ta kanki ai za ki ?aras a gaba."
Raudha ta katse mata sambatun da take yi hankalinta a tashe kamar wacce ?wa?walwarta ya fara taSuwa.

"Bar tuna min Raudha! Don girman Allah ki bar tuna min."
Bintu ta katse ta da sauri, da murya mai bayyana matsanancin takaicin da zuciyarta ke ciki. Babbar yatsarta ta sanya ta Wauke wasu zafafan hawaye da suka sake taruwa a kwarmin idanunta. Da asubahin ranar tasha alwashin in Allah ya yarda za ta danne zuciyarta baza ta sake yi ma wannan mummunan al'amarin kuka ba, amma duk yadda ta so tsayar da fitar hawayen ta kasa, shi yasa take saurin share hawayen tun kafin su gangaro zuwa kumatunta su saka ta azumin kaffara.

Nannauyar ajiyar zuciya ta ja ta sauke, a hankali ta cigaba da cewa
"Abinda ya wuce mu barshi a matsayin wanda ya wuce Raudha. Ilimi Waya da na ?aru da shi a cikin kwanakinnan shi ne, duk mazajen duniya halayensu Waya, kuma a kullum sauyawa suke yi kamar wahainiya. Lallai da gaske ne duk matar da ta Wauki namiji uba za ta mutu marainiya... Yanzu dai mafita nake nema da gaggawa... Ya zanyi Raudha? Ya zanyi? Wallahi zuciyata zafi da tafarfasa take min kamar za ta babbake... Don Allah ki taimaka min"

"Kul! Kul!! Kul Bintu!! Kar ki kuskura ki bari zuciyarki ta buga akan namijin da idan kika mutu yau, ya yi tsananin daWewa ne yayi wata shida zai manta da shafinki ya buWo na wata kamar yadda yake shirin faruwa da ke a yanzu."

Ta yi shiru tana mayar da numfashi, sannan ta cigaba da magana a hankali, tana yi tana waige-waige, alamun duk abinda za ta faWa ba ta so kowa ya ji
"Akwai mafita... Amma sai kin nutsu sosai kin saurare ni da kunnen basira..."

Jikinta a sanyaye ta tari numfashin Raudha da cewa
"Allah yasa dai mafitar ba na bin hanyar da Hajiya Rabi ta faWa min rannan bane."

Sai da Raudha tayi dariya sannan ta amsa da
"Wannan old version kenan ai. Ita ma don tsohuwar yayi ce shi yasa har yanzu take ganin idan ba ta hanyar malamai da bokaye da ?an tsibbu ba babu hanyar da za ta bi wajen ladabtar da ?A NAMIJI har yayi laushin da zai rusuna mata..."


Fitowar Mashkura daga banWaki, wacce shaf Bintu ta manta da shigarta daf da Raudha za ta shigo cikin Wakin, shi ya katse Raudha daga maganganun da take yi masu Wauke da zallar cika baki.

A tsorace suka kalli Mashkura, itama ta Waga idanu tayi musu wani kallo mai bayyana ?as?anci ?arara. Sannan ta Wauki hijabin sallarta ta zura a jikinta ta fice daga Wakin.

Da damuwa sosai a fuskar Raudha ta ce
"Na shiga uku ! Amma dai Bintu baki kyauta min ba. Me yasa tun Wazu baki faWa min Mashkura tana bayi ba kika barni ina ta zuba zance? Allah dai yasa bata ji maganganun da nake yi ba..."

"In Allah ya yarda ma bata ji ba. Wallahi sam na manta ta shiga wanka sadda kika shigo, kuma kin santa da bala'in daWewa gurin wanka kamar wacce za ta canja halitta. Yanzu dai ina ga ki tashi kawai ki tafi, ma ?arasa zancen da muka fara yi a waya..."

Numfashin maganarta ne ya Wauke Wif lokacin da Ummansu ta shiga cikin Wakin da wata iriyar murtukakkiyar fuska, kamar bata taSa dariya ba.

A Warare duk su biyun suka kallete da yanayin rashin gaskiya. Da saurin gaske Raudha ta yayimi jakarta da mayafi ta mi?e tsaye.
"Bintu bari in wuce, sai na sake le?owa..."

"Ki le?o ina Raudha?"
Ummansu ta tambayeta cikin tsawa.
"Munafuka algunguma, dama ke ce kike hure mata kunne har kika hana ta zama gidan mijinta bayan ke kina naki gidan?"

Cikin rawar murya da in-ina Raudha ta fara yun?urin kare kanta.
"Babbbbbbaaaa haka bane Wallahi Umma..."

"Idan ba haka bane to yaya ne? Saurareni ki ji da kyau!! Daga yau, na raba ki da Bintu tunda dai ke ba ?awar arziki bace. Idan kuma kika bari na sake samun labarin kin zo gurinta, ko kuma ita taje gurinki har a ganku tare, ko kuma ki kirata a waya ko ita ta kira ki na rantse da Allah da Aliyu zan haWa ki. Kuma kin san halinshi sarai, don ya bi ki har gidan mijinki ya hukunta ki ba abinda ya dame shi bane. ?ace min da gani munafuka kawai."

Sum-sum Raudha ta fice daga Wakin kanta a ?asa, hankalinta a Wugunzume, ko ?wa??waran kallo ta kasa Waga idanu tayi ma Bintu balle mahaifiyarta.

Har ta fita daga Wakin, Bintu ko ?wa??waran motsi ta kasa yi, tsumu tayi a zaune inda take kamar kazar da aka tsamo a cikin ruwan zafi. Hankalinta a tashe ainun, miyaun bakinta ya ?afe ?af! Ta rasa wasu irin kalamai ne ya kamata tayi amfani dasu gurin ba Ummansu ha?uri.

"Ke kuma na dawo gare ki! Sakarya! Wawuya!! Shashasha!!! Wacce duk irin shekarun da tayi a duniya bata san inda yake mata ciwo ba."
Mahaifiyarta ta katse mata tunani da faWin waWannan maganganun cikin matsanancin fushi da Sacin rai.

Kafin ta buWe baki tayi magana Umma ta cigaba da cewa
"Ba ni da lokacin Satawa wajen baki shawara Bintu, saboda kin daWe da goge min hadda, kin yi abinda ban taSa tsammanin ko rabi-rabinshi za ki aikata ba. Abinda ya faru yasa na daWe da yanke tsammani a kanki Bintu. Magana Waya zuwa biyu zan faWa miki a yanzu, idan kin so ki bi, idan baki so ba za ki iya aikata duk abinda ya kwanta miki a rai. Ni kuma za ki ga abinda zan aikata a matsayina ta wacce tayi na?udarki zuwa duniya.

A matsayina na mahaifiyarki, daga yanzu har zuwa nan gaba ko da wasa kika yi yun?urin aikata wani abu, ko sakawa a aikata wani abu da zai cutar da Amaryar Hafiz, ko shi kanshi Hafiz Win, ko auren da yake yun?urin yi ban yafe miki ba.!"

A haukace Bintu ta Wago kai, jikinta babu inda ba ya rawa, da?yar ta iya buWe baki ta ce
"Umma..."

Da saurin gaske Umma ta Waga mata hannu alamar dakatarwa.
"Magana ta biyu shi ne idan kika sake zuwa gurin Raudha, ko kiranta a waya, ko ita ta kira ki a waya kika Wauka har kika yi amfani da Waya daga cikin munanan shawarwarin da take baku ban yafe miki ba.
Na ga kamar dusa ne a ?wa?walwarki, dole sai ana yi ana taka miki burki ?arfi da yaji. Sakarya kawai."
Da gama faWin haka bata tsaya saurararta ba ta fice daga Wakin, bayan ta ja wani dogon tsaki kamar bakinta zai taSa ?asa.

Ta fita ta bar Bintu cikin wani mawuyacin hali na tashin hankali. Zuciya da ?wa?walwarta a tsaye cak! Ta ma rasa wani irin tunani ya kamata tayi?


*******



Labarin sakin da Hafiz yayi ma Bintu, abu ne da ya zama a sirrance ta Sangaren Hafiz Win. Ko da wasa baiyi gigin faWa ma wani daga Sangarensa ba, hatta Zulai da a yanzu suke very close da ita.

Bayan sati biyar da faruwar al'amarin ne Mahaifin Bintu ne ya kira Alhaji Lurwanu yake mishi ?orafi kan yadda bai kira shi a waya ya jajanta mishi kan abinda ya faru ba.

Mamaki mai girma ne ya kama Alhaji Lurwanu, da takaici sosai a muryarsa yake nuna damuwar yadda Hafiz Win ya iya sakin Bintu ba tare da ya kai mishi ?orafinta ba.

"Uhmmm! Shi fa Hafizu ba shi da laifi Alh Lurwanu. Gaba Waya laifin na Bintu, kuma ko ni ne a matakin da yake kai iya hukuncin da zan iya Wauka kenan zuciyata tayi sanyi-sanyi."
Ba tare da Sata lokaci ba ya kora ma Alh Lurwanu bayanin duk abinda ya faru.

"Ikon Allah! Amma kuwa in dai haka ne Bintu bata kyauta ba. Sai dai kuma shi Hafizu kamar ya yi gaggawa gurin sakinta. A sanina akwai hanyoyi da dama na ladabtar da mace, saki shi ne mataki na ?arshe-?arshe bayan duk an bi waWancan hanyoyin an kasa cimma matsaya.

Amma Alh Aminu (Baffa) ya sani kuwa?"

"To gaskiya ba na jin shi ma ya sani, don dai bai kira ni ba. Ko kai Winma dalilin da yasa na kira ka ganin yadda Bintun ta kasa ha?ura ta rungumi ?addara ne. To ya zanyi? Hannunka ba ya ruSewa ka yanke ka yar Lurwanu. Duk da dai ita ce ba ta da gaskiya, kuma har yau na kasa nuna mata a fili ina tausaya mata. A can ?ar?ashin zuciyata ina jin zafin yadda ta lalace, ta ?are, ta shiga cikin halin ?a?a-ni-kayi. Ko gurin aiki fa ba ta iya zuwa, a yanzu idan ka ga Bintu na rantse ba lallai ka gane ta ba.

Don Allah idan da hali kayi wani abu akan lamarin..."

"Yin wani abu ya zama dole Alh! Amma ina ro?onka alfarma Waya. Alfarmar kuwa ita ce don Allah yanzu muyi ma Hafiz uzuri, ka ga jibi idan Allah ya kaimu za'a Waura aurenshi... Muyi ha?uri, zuwa sati na sama idan mai duka ya kaimu da kaina zanyi takakkiya zuwa Ofis Win shi in ji ya za mu Sullo ma al'amarin. Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah komai zai zo ya wuce..."

"Ba damuwa Alh! Na gode."



******


Ta Wauki tsawon mintuna goma sha biyu hawaye masu zafi na sauka daga kwarmin idanuwanta.
Duk da hawayen da ke jerangiyar sauka daga idanunta, kallon fili da na idanun zuciyarta bai Wauke daga kyakkyawan

46 / 53