RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 53

102K to 105K   out of 157.3K words

gaba Waya ji yake kamar kar ya tafi ya barta a garin, gara kawai ya tafi da matarsa, ko kuma ya zauna har zuwa sadda za a bashi matarsa.

Kamar ta san tunanin da yake yi, sai ta kalli hannayensu da ke ma?ale da juna. Kafin ta mayar da kallon kan fuskarsa, a kunyace ta sakar masa murmushi.
"Kayi ha?uri, sati biyu ne fa kacal. Kuma na maka al?awarin in sha Allah duk sadda ka kira za ka same ni a waya. Ka kwantar da hankalinka, ka je, Su Mummy na jiranka."

Ya kasa cewa komai don tsananin sanyin da jikinsa yayi, hankalinsa a tashe. Hannunta da yake cikin nasa ya Waga yakai bakinsa, ya sumbata a hankali sannan ya fice daga cikin Wakin da sassarfa.

Ko da ya fita, ta kasa bin bayansa don tsananin kunyar su Mummy da mutanen gida, yau dai hatta Karima da Yayyenta kunyar haWa idanu da su take yi. Don haka ta cigaba da zamanta a Wakin Baffa, zuciyarta cike taf da tunanin mijinta. Lokaci bayan lokaci ita kaWai sai ta saki lallausan murmushi, tana shafa bayan hannunta inda ya sumbata da tausasan laSSansa.

"Allah na gode maka."
Ta faWa a fili, zuciyarta cike da matsanancin farin cikin da baki bazai iya furta adadinshi ba.
[2/17, 10:59 PM] Fareeda Abdallah: Kamar yadda Mummy ta al?awarta ma zuciyarta, sai da ta sake ro?ar ma Hafiz gafara a gurin Innaye da Baffa. Ta ?ara tunasar da su komai fa na duniya yana faruwa ne bisa doron ?addarar da aka shirya faruwarsa tun kafin muzo duniya.
"Kuma idan kun duba, a yanzu komai da ya faru za mu iya cewa mafificin alkhairin da muke ta ro?a ne ako wane lokaci Allah ya tabbatar da faruwarsa a sau?a?e."

"Haka ne Hajiya. Daman mun yafe mishi, Allah ya yafe mana gaba Waya."
Baffa ya faWa da yanayin da ke nuna tun daga ?ar?ashin zuciyarsa yayi maganar.

Ita kuma Innaye cewa tayi
"Daman babbar damuwa da Sacin ran na yadda ya mayar min da ?a ?aramar bazawara ce, amma yanzu tunda Allah ya canja mata da wanda ya fi shi alkhairi komai ya wuce. Allah ya shirya mana zuri'a."

"Amin ya rabbi."

Kamar haWin baki, shi ma Alhaji Lurwanu gaf da za su bar ?auyen ya nemi ganawa da Baffa da Innaye a keSance ya sake ro?ar ma Hafiz gafara.

"Babu komai Alhaji. Wallahi har ga Allah mun yafe masa. Allah ya yafe mana gaba Waya."
Baffa da Innaye suka haWa baki gurin amsawa.

Kafin tafiyarsu sai da Hajja ta dam?a komai na gyaran jikin Zulaikha a hannun Umma Laraba da Aunty Balira.
"Amana! Ga amana nan na dam?a muku. Kuma kun san dai amana maci amana maye Wan'wuta ne inji yara. Ban yarda ko dai dai da rana Waya a tsallake yi mata gyaran nan ba, duk abinda ya ?are kafin kwanaki sha huWunnan ke Balira ki ranta kuWi a siyo. Duk abinda aka kashe idan kun zo zan biya ki, ?wandalarki baza tayi ciwon kai ba ?ar nan. Al?awari na Wauka."
Maganganun da tayi ta jaddada musu kenan har suka fice daga cikin gidan zuwa gurin motocinsu.

Duk sun riga sun sani kunya ce ta hana Zulaikha fitowa suyi sallama, shi yasa babu wacce ta matsa da son ganinta tsakanin Mummy da Hajja. Ita kuwa Karima a Soye ta shige Wakin Baffa tayi ma Zulaikha tsiya son ranta kafin ta fito daga Wakin tana ?yal?yala dariya.

Basu bar ?auyen Fa?o ba sai ?arfe shidda saura kwata na yamma. Sun rabu ne ko wane Sangare zukatansu cike da matsanancin farin ciki. Su Mummy basu wani tayar da hankulansu kan yamman da suka yi ba, saboda sun sani komawarsu Abuja bazai yiwu a ranar ba, in dai ba so suke suyi tafiyar dare ba, wanda sam Hajja baza ta bari ba. Sun tsara za su kwana a Kaduna, washe gari suyi sammakon wucewa Abuja.

Shi kuwa Alhaji Lurwanu da yake yana da harkokin da zai gabatar a Kaduna, ba ma a washe garin zai koma Abuja ba.
Labarin da Hafiz ya samu na aurar da Zulaikha ga Ya Kamal Wan gidan Mummy ba ?aramin farin ciki ya jefa zuciyarshi a ciki ba. Ko kaWan ranshi bai Saci, domin shi daman babu soyayyar Zulaikha irinta aure ko kaWan a zuciyarsa.

Ba ma kamar da ya samu labarin yafe masa da iyayensa suka yi daga bakin Abba Lurwanu da Mummy. Bayan uban faWan da yasha, ?iris ya rage ya karSi tukwuicin mari daga gurin Abban, saboda Sacin ran yadda irin wannan muhimmin al'amarin zai faru amma ya Soye masa.

Shi dai ha?uri yayi ta basu cikin ?an?an da kai, har zuwa sadda suka tabbatar mishi da su Baffa sun yafe masa, komai ya wuce, da fatan zai kiyaye gaba.

Samun waWannan daWaWan labarai guda biyu da bai taSa tsammanin jin su a irin wannan lokacin ba yasa Wan sauran zazzaSin da ya rage a jikinsa ?arasa fecewa. Sai ga shi ya mi?e garas, da ?warin jiki yayi ma su Mummy rakiya zuwa gurin motocinsu yana ta zabga musu godiya kamar zai ari baki.

Da yake a lokacin da suka je gidan Bintu tana asibiti, shi yasa duk bata san abinda ke faruwa ba sai da ta koma gida ya labarta mata.

?arara Sacin rai, hassada, ?yashi, ba?in ciki suka bayyana a fuskarta jin irin cigaba da Waukakar da Allah yayi ma Zulai a lokacin da bata taSa tsammani ba. Ta san Mummy Saudah tun da daWewa, Ogar Hafiz ce a gurin aiki, babbar macece hakima da ta tara Wumbin abin duniya, don ma dai ba ta da girman kai ko kaWan.

Ta kuma san Kamal, babban Wan Mummy da ya auri Zulai, haWaWWen gaye ne da ya tara dukiya mai yawa sanadiyyar aikinsa, kuma an mutu an bar musu gadon dukiya mai yawa.

A ta?aice saboda irin alfarmomin da suke ci ta sanadiyyar Mummyn ita da Hafiz yasa sadda Karima ta gama Karatunta na aikin jinya ta shiga ta fita har sai da ta samar ma Karima gurbin aiki a asibitinsu.

Yanzu shi kenan Zulai ta samu Waukaka? Ta faso gari kenan za ta goge duk wani ?auyanci da jakanci haWe da dabbanci su bar jikinta?
"TaSWijan! Shi kam a ina ya haWu da ita ne haka har aka haihu a ragaya?"
Ta tambayi Hafiz Win fuskarta babu walwala ko kaWan.

A ta?aice, ya bata labarin irin zaman da Zulaikha tayi a gidan Mummy na tsawon watanni.

A fili ta taSe baki
"Amma kuwa dai ya ji kunya, ya kuma yi faWuwar ba?ar tasa. Ace duk wayewa da gayu haWe da aji irin tasa ya rasa yarinyar da zai aura sai ?ar ?auyen ?ayau kuma jahila da?i?iya irin Zulai. Gaskiya ya ci baya..."

"Me kike nufi kenan Bintu?"
Hafiz ya tambayeta da Sacin ran da ya bayyana a fuskarsa tun da ta fara maganganun da ke nuna ba?in cikinta ?arara.

"Me nake nufi kuwa Dear? Kawai dai abinda ke raina na faWa, kai ma kuma kasan ai gaskiya ne."
Fuuu ta mi?e tsaye ta Wauki jakarta za ta wuce sama.

Da saurin gaske ya janyo ta ya dawo da ita baya sannan ya dan?wafar da ita akan kujera.
"Kar ki manta, abinda yayi Zulan da kike kira ba?auyiya, jahila kuma da?i?iya shi yayi ni Hafiz da kike aure. Domin ita Win ?anwata ce, jininmu Waya, ?auyenmu Waya, ashe ke ma baya kika ci da kike aure na?"

"A'a da banbanci fa My dear... banbanci mai nisan gaske ma. Kai ai ka daWe da shigowa birni, ka waye, kuma ka yi zuzzurfan ilimin boko. Idan ma ba ka faWa ba babu wanda zai kalleka yace kana da jiSi da wasu ?auyawa can... Amma dai duk inda ka nufa ni ba haka nake nufi ba, idan ka ji haushi Allah ya baka ha?uri."
A karo na biyu ta sake Waukar jakarta da nufin wucewa sama, ba tare da ta yarda ko fuskarsa ta kalla ba.

Domin Allah ya sani labarin irin cigaban da ya sami Zulaikha ba ?aramin ba?anta mata rai yayi ba. Ta zaci zai sake dakatar da ita a karo na biyu, sai taji bai janyo ta ba har ta fara haurawa matattakala.

Shi kuwa Hafiz tsananin mamaki da girgizar da kalamanta suka jefa shi a ciki ne yasa ya kasa sake ce mata komai, har ta Sace ma ganinsa. Duk da farin sanin da yayi ma halayen Bintu na son harkar wayewa da birnanci da nuna ilimi, abu ne da bai taSa tsammani ba ta iya tsayawa a gabansa ?e?e da ?e?e ta faWi munanan kalamai irin haka akan Waya daga cikin ?an ?auyensu ma ba Zulai da ta kasance jininsa ba.

Ya daWe zaune a gurin maganganunta suna wujijjiga shi, zuciya da mugun sa?e-sa?e sai ga shi cikin ?an?anin lokaci ta fara shigo mishi da wasu irin tunanika mabanbanta da juna. Duk yadda yaso yayi watsi da tunanikan da yake yi, ya kasa, a dole suka samu matsuguni a zuciyarsa suka yi darshe-darshe, ya cigaba da Sata lokaci a gurin yana sake raba Waya biyu a kalaman Bintu.

Daga ?arshe dai, tattara tunanin komai yayi ya aje gefe Waya. Ya mi?e tsaye, har ya nufi hanyar da zai sada shi da Wakunan barcinsu sai kuma ya canja shawara, yana ji a ransa in dai ya haura sama suka yi ido biyu da Bintu tabbas zai cigaba da tuhumarta kan kalaman da ta faWa masa ne. Shi kuma a halayensa ba mutum bane mai yawan mita da son maimaita magana Waya. makullin motarsa da yake ajiye nan kusa da shi ya Wauka ya fice daga falon.


***** *****


A cikin kwanaki goma sha biyu da suka biyo baya, Baffa ya sa an gama shirya ma Zulaikha Wakunanta da ke Sangaren Kamal da kayayyaki na gani a faWa cikin rufin asiri. Duk kuwa da yadda Abban Imam Win yace baya bu?atar komai, sam-sam Baffa ya ?i yarda da haka. Kuma wani abin sha'awa da burgewa shi ne kayayyaki kalar ?an birni aka zuba mata, dai-dai ruwa dai-dai tsaki.

Wani kyawun hange da Baffa yayi shi ne, bai tura ?a?ansa Kaduna suyi siyayya ba don gudun kar a sayi abinda bazai dace da Wakunan Zulai a Abuja ba. Alfarmar Abba Lurwanu ya nema, ya tura mishi da kuWi naira na gugan naira har miliyan Waya da cewa matar Abba ta shiga kasuwa ta sayi duk abinda ya dace, Duk da Abban yayi-yayi Baffa yabar kuWinsa shi zai ma Zulai komai na kayan Waki matsayinsa shi ma na uba, amma Baffa ya ce yayi ha?uri, Wawainiyar da yake da Sangaren Hafizu da su iyayensa ma ya isa haka.

Ko da Hafiz ya samu labarin halin da ake ciki hankalinsa a tashe ya kira Baffa. Domin a saninsa tun da ya fara aiki shi ke da alhakin yima ko wacce daga cikin ?annenshi kayan Waki, kuma ko Zulai in banda Allah baiyi aurenta da Mudan ba a wancan lokacin har kuWin kayan Wakinta ya biya, fasa auren da aka yi ne yasa shi karSan kuWinsa.

Ko da ya gama ro?on Baffa cikin ?an?an da kai da taushin murya kan a barshi ya Wauki ragamar shirya mata Waki kamar sauran ?an'uwansa ?arara Baffa ya faWa mishi ya fi so yayi ma Zulai komai da guminsa.

"Ba kuma don wai na raina ?o?arinka bane Hafizu, ko kuma wai don har yanzu ina jin haushin abinda kayi, a'a! Ko Waya ba haka bane."
Baffa ya ?ara da faWa mishi haka don kwantar masa da hankali.

?an shiru yayi yana jin babu d?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? aWi a zuciyarsa. Sai kuma ya ce
"To Baffa don Allah a barni in Wauki ragamar yi mata gara, tunda dai hidindimun da yawa. Don Allah Baffa."

Kamar Baffa zai ce a'a! Sai kuma ya ce ba damuwa. Yana iya yin Wan daidai misali ba na ?arya ba.

Sai dai abinda Baffa bai sani ba shi ne, kuWin da ya bayar na kayan Wakin da za'a siya mata kaso Waya ne bisa uku na abinda aka kashe. Abba Lurwanu ne ya cika kuWin, matansa suka shiga kasuwa aka yi mata siyayyar kaya masu kyau.

Bayan an kai kayan gidanta kuma washe gari suka je da manyan ?a?ansu mata aka ?arasa shirya mata gidanta. Yayi kyau sosai.

Duk da Baffa ya gargaWi Hafizu kan kayan gara bai ji ba, kuWi ya kashe sosai duk don dai ya fanshe takaicin kayan Wakin da bai mata ba.

Ana jibi biki, su Aunty Balira suka yi shatar mota aka loda musu cincin, dubulan, alkaki, nakiya, manshanu, da sauran ?ananun tarkace daga Innaye suka tafi da shi gidan Zulai.

Tarba ta mutunci da girmamawa suka samu daga Mummy da mutanenta. Zukatansu cike da farin ciki, sun ci, sun sha, sun yi nak da ?ayataccen abinci na girma. Haka suka dinga santin Sangaren Zulai da kayan da aka zuba mata.

Kayan ciye-ciyen da suka je da su daman tun daga Fa?o Innaye ta sa an raba komai kashi huWu ne. Biyu na Mummy, Waya na Zulai, Waya na Hajja. Haka su Mummy suka karSi kayan suna murna, zuciyarsu da fuskarsu Wauke da bayyanannen farin ciki, kamar anyi musu kyautar duniya. Sha tara ta arziki aka haWa sake haWa ma su Aunty Balira a matsayin tukeuici suka juya da shi.

Washe gari kuma ana gobe tarewa Mummy ta haWa manyan mata guda shida, danginta biyu, dangin Abban Imamu biyu, ?awayenta biyu, suka hau jirgi zuwa Kaduna, daga can suka Wauki mota da haWaWWun akwatunan lefe guda shida zuwa Fa?o, sha?e da haWaWWun kayayyaki.

A Sangaren su Innaye ma sunyi musu tarba daidai ?arfinsu, haka aka rabu zukatan ko wane Sangare da farin ciki, babu raini ko wula?anci balle kallon banza daga mutanen Mummy har suka bar Fa?o. Farin cikin wannan kaWai ya ishi Innaye da sauran dangi.

"Wani hanin ga Allah baiwa ne. Ke kam Zulai kin dace da miji da iyayensa, Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a Wayyiba."
Ire-iren maganganun da ke fita daga bakunan ?an'uwa da abokan arziki kenan.

Tun ana gobe biki, gidan Baffa yake dan?am da mata, sai sauke girke-girke ake yi ana Wora wasu tukwanen. Washe gari kuwa tun ?arfe goma na safe manyan motocin Waukar amarya da danginta har motoci takwas suka faka a ?ofar gidan Baffa.

Kuma basu takura kowa ba, domin umarni ne daga Abban Imam, har zuwa ?arfe uku na rana kafin aka gama shirya amarya da ?an rakiyarta suka kama hanyar tafiya Abuja.

[4/2, 6:12 AM] Fareeda Abdallah: ******


Cikin ?an?anin lokaci nan da nan sai gasu a cikin Abuja, wajen karfe shida da rabi na yamma. Tafiyar da ko kaWan Amarya da tagawarta basu ga nisan ta ba.

Fuskar Amarya wasai, sai ?an ?ananun ?wallan da tayi na sake rabuwa da su Innaye a karo na biyu. Amma babu irin kururuwar nan ko ?uncin zuciya mai bayyana ?arara auren dole aka mata, tana cikin farin cikin albarkar da su Baffa sukai ta sa mata. A gefe da gefenta kuma ga Yayyunta da za su raka ta har Wakin mijinta. Bayan sun iso kai tsaye gidan Mummy Sauda aka wuce da ita, kamar yadda aka tsara sai an gama duk bukukuwan a gidan sannan za a wuce da ita gidan mijinta.

A wannan sha'anin ne su Aunty Rakiya suka ?ara tabbatar da lallai fa ?an birni masu kuWin ma suna suka tara, ba ko wasu masu arziki ne masu wula?anta ?an ?auye irin Bintu ba.

A bikin Zulai, kwanaki biyun da suka yi a Abuja gidan Mummy komai za'ayi ana saka su gaba-gaba matsayinsu na dangin Amarya. Duk wani shagali da aka yi sai da aka kai su gurin kuma a masauki na musamman.

A tai?aice dai, an girmama su iya girmamawa. Wani abin mamaki shi ne har aka gama bikinnan na kwana biyu Bintu ko le?e bata yi ba, tana can gida ta Wora ma kanta ciwon ?arya har da su ?arin ruwa don kawai kar Hafiz ya ?ullace ta.

Shi kaWai yayi ta zirga-zirgan zuwa gurin ?an'uwansa. Ko da ya faWa musu Bintu ba lafiya, fatan samun sau?i kaWai suka yi mata suka shashantar da maganar.

Wani abu da ya sosa zuciyar Hafiz amma ya danne bai musu ?orafi ba shi ne, yadda ganin yawan waWanda suka zo bikin daga can ?auye yasa shi suSutar bakin yi musu tayin ya rage wasu suje gidanshi su kwana.

"Wa? Mu? Allah suturi bu?wui... Ai gidan Bintu shi ne ramin kura sai ?a?anta... Idan ka ganmu lahira kaimu aka yi Hafizu. Ai ko sha'ani ake yi a gidanka mun daina zuwa mu kwana Hafizu."
Ire-iren maganganun da ?an'uwansa sukai ta yaSa mishi kenan.

"Uhmmm! Hafizu kenan. Ai kai da kanka ka ture wannan damar da aka mi?a maka na zuwan ?an'uwa gidanka su sake. Ban san dai ko can gaba ba, amma a yanzu ko sha'ani ake a gidanka sai dai muyi maka fatan alheri ta waya, babu wacce za tayi gigin zuwa balle har ta ?unshi takaici da ba?incikin da ba shi kenan ba."
Cewar Aunty Balira.

"Yo wai ko da ka ganmu da yawa aka ce maka muna takure ne anan Win? Ai surukan Zulai sai dai muyi musu fatan alkhairi, wadataccen gurin kwanciya suka samar mana da wadataccen abinci, kai baka ga har wani kumari muka ?ara a cikin kwana guda da zuwanmu ba? Mun gode Allah a yanzu ba kai kaWai bane a binni, ga gidan Zulai nan, na san ko za mu zo muzo gobe jibi mu sake zuwa baza ta taSa gajiya da mu ba. Ai ranar naka sai naka."
Aunty Rakiya ta yaSa mishi maganganun.

Haka ya fice daga gidan zuciya cike da ?unci amma ba shi da halin tofawa balle har cibi ya zama ?ari. Sai kuma a wannan lokacin ne ya fara tunanin to ko dai Bintu tayi ma ?an'uwanshi wani wula?anci ne lokacin sunan Aadil? Idan ba haka ba waWannan ba?a?en maganganun duk na menene? A ganinsa guje ma auren Zulai kaWai bazai sa su dinga nuna tsangwamar zuwa gidanshi ?arara haka ba.

Su dai ko a jikinsu, bayan fitarsa ma walwala da warwasawarsu suka cigaba da yi.

Washe gari da wuri Mummy tasa Hibba ta sake tsantsara ma Amarya rantsattsiyar kwalliya aka Wauketa da danginta sai gidan mijinta da ke unguwar Aso rock.

?an'uwanta sai hangame

35 / 53