Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 61

24K to 27K   out of 180.1K words

na karaya.
Ya ce, "Ko a hanya kika nuna kin san ni sai na ci kazar ubanki. ya bugi 'kirjinsa ya ce, "Ni ne ba ni da zati ko Guduyo? Na rantse miki ba zan yarda ba, tunda na zo duniya ba wanda ya ci mini fuska irin ki".

Cikin rashin tsoro na ce, "Ina fuskar da zan ci 'din? Ai idan na ce zan ci fuskarka ba za ta ragu ba, domin 'yar masayau ce ba afki".
Ai kuwa ya dinga kawo mini duka ina karewa, ina sake cewa, "Wallahi yau na gane kai din mace ce da rigar maza! Domin duk namiji mai gwada 'kwanjinsa akan mace wallahi sakarai ne".

Ina rufe baki ya sakar mini gashi, ya kifa kansa a jikin sitiyarin mota, tsawon lokaci sannan ya dago da fuskarsa da ta hade da zufa da hawaye duk da sanyin AC da ya cika motar.
Yasa hannu ya zaro tissue a cikin kwalinta da take tsakanin kujerunmu.
Ya dinga goge hawayen takaicina. Na sa ci kallon sa na ga gaba'daya ya birkice.
Jijiyar kansa ta fito rada-rada idonsa ya yi jawur tabbacin ya kai 'koluluwar fusata.
A raina ban ji 'dar ba, domin ya riga da ya kai ni 'karshe da bakaken maganganunsa, idan ma ni lalatacciyar ce ai shi ne ya lalata ni, domin duk wani abu na iskanci cikin dabara shi yake fara nuna mini shi.
Na tuna da wayona da komai, ba a wani jima ba ma ya 'kankame ni ya mini tunbudin da ban san yadda ake yin sa ba sai a ranar.
Soyayya ta hana ni ganin laifinsa, bare na nuna masa cin zarafi ya yi mini. Na sake tuno lokacin da ban yi hankali sosai ba, amma na fara girma yake jana dakinsu yasa ni rawa, ko ya zaunar da ni akan cinyarsa da nufin ganin hotuna a wayarsa. Na yi tsaki a fili, a zuciyata kuma na ce wai mai wannan ta'asar ne yake jifan wani da lalata. Amma laifina ne da na amince ban ta'ba nuna masa ba na so ba.
Dole ya ce mini komai. Ba zato na ji ya danna mabudi, ni ma a gaggauce na bu'de motar na fice ina jin da na sake shiga motar nan gara na jingine karatun ga'badaya. Ina da hakuri akan komai amma na tsani a ta'ba mini mutunci.
Zagayawa na yi na samu inda ba kowa na zauna a gefe na ci kuka sosai domin ba karamin dafa ni kalmominsa suka yi ba.
Na tuna wai ni ce abin kunya a gare shi, ni ce ba zai iya nuna wa duniya ba a matsayin matarsa. Sannan kuma ni ce zan yi masa fyade.
Duk yadda haushinsa yake nukurkusa ta ban ji na daina son sa ba, bai fita a raina na can ba. Sai dai kuma wata irin jarumta ta shige ni da nake jin zan iya auren Munir.
Don haka ban 'bata lokaci ba, na zaro wayata karon farko da na 'kira Munir da kaina.
Ya katse ya 'kira ni. Na dauka na yi masa sallama, ya amsa cike da zumudi mai yawa.
"Ranki ya da'de! Ina fatan dai ba kuskuren kira na kika yi ba?"
Na saki yar dariyar da babu nisha'di a cikinta na ce, "Ba kuskure ba ne kai din Ustaz na yi niyyar kira, ba kuma kiran kawai ba, zan sanar maka ka samu lokaci ka je wajen Abba".
"Who am I today?" Ya fa'da cikin yanayi na farinciki.
Na yi shiru ina sauraron maganganunsa na murna.
Na katse shi ta hanyar fa'din "Zan shiga lakca".
Na katse wayar ina jin dole na tattara na bar wa Gudale filin gidan tun bai tuso ni a gaba da bala'insa ba.
Hawayen da ya yi ba zai zuba a banza ba, na sani akwai abin da zai shirya mini a gaba.
Na kuma sani da gaske ni kawai yake 'dagawa kafa, amma ko antin Zaria ma ba ta tsira ba. Wannan karon kuwa na sani ba zancen sassaci tunda ya fa'da da bakinsa.

*Kina neman kwararriya tela*?
*Kina bu'katar kyawawan takalma da jaka irin na manyan Mata?*?
*Kina bukatar samun zababbun suturu?*
*Kawai tuntu'bi Umm Muhd collection*
*Ina tabbatar miki zaki huce takaici*

Washegari kuwa Munir da yamma ya je wajen Abba suka tattauna. Kwanaki uku a tsakani na je gai da shi da sassafe kafin na tafi makaranta. Har na mi'ke da nufin tafiya ya tsayar da ni.
Ya ce, "Na yi binciken sirri akan wannan yaron domin na san ubansa duk da dai ba mua'amala muke yi ba.
Sai dai bayanan da samu a kansa ba mai da'di ba ne.
Ni ya ce mini ya ta'ba aure matar ce ta rasu tun ba su yi shekara guda ba. Yanzu kuma na sami bayanan da suke nuna mini tamkar shi din mai yin auren mutu'a ne. Tunda an tabbatar mini sau uku yana auren yana saki, duk aurarrakin nan kuma akwai rabo a tsakaninsu ma'ana yaransa uku daga uwaye mabanbanta."
Na dinga jin wani irin tashin hankali na ratsa ni ashe Ustaz kura ne da fatar akuya! Ni zai yaudara? Kafin na ce wani abin Abba ya ce, "Don haka ina sanar da ke ki rabu da shi ba mijin aure ba ne, makaryaci ne mai auri saki".
Ki nutsu sosai Ubangiji zai kawo miki wanda ya fi shi alheri tunda dai kin kafe ba kya son yaron kirki irin Anas".
Na sunkuyar da kaina 'kasa ina jin wata irin damuwa na rasta ni ba don komai ba, sai don yadda babban mutum da ya kai shekaru talatin da biyar a duniya amma zai iya karkace baki ya shirga 'karya don kawai ya cim ma burinsa.
Kaicon wannan halayyar tamu, kaicon son zuciyarmu da a kullum suke zama sandin shigar mu cikin 'kunci. Ko mene ne ribar da za ka samu idan ka yi 'karya don ka zalunci wani?
Babu sai damalmalewar al'amura.
"Tashi ki je, ki ci gaba d addu'a ni ma zan taya ki, amma ina jan hankalinki ki cire shi a ranki ba shi da nagartar da zamu ba shi aure. Ubangiji ya yi miki albarka, ya ba ki na gari".
Na amsa da ameen tare da yin godiya da kuma yi masa fatan inganci a lafiyarsa. Na fita jikina babu 'kwari. Ina fita na hango Gudale yana shirin shiga motarsa na dauke kai, ina jin ko ya ce na zo na shiga ba zan shiga ba, bare na san shi ma ba zai dauke ni ba.

Haka kwanaki suka shu'de ba tare da mun sake haduwa da Gudale ba, tsakaninmu sai daga nesa shi ma ba kasafai ba. A hankali sai na fara hucewa, kewarsa ta fara shiga ta, har na fara tunanin yadda za'a yi mu shirya.
Ran nan sai ga Sakina ta zo gida, daga asibiti ma take.
Muka yini cikin walwala a dalilin Umma ta je Yola.
Matu'kar kuwa tana nan ba na samun fuskar da zan shiga cikinsu a yi hira da nishadi.
Muna zaune a falon Umman muna cin shinkafa da wake da salak.
Gudale ya shigo ba sallama, yana gani na ya hade fuska tamkar ya ga gawa.
Ya zauna kusa da Sakina sosai ya jingina rabin jikinsa a jikinta, fuskarsa na kan kafadarta. Wani irin al'amari ya kama ni, shaukin kaunar su na diba na tamkar irin haka Yaya Al'amin yake so na. Kamarsu guda shi da Sakina, duk da kyan Gudale na tabbatar Sakina ta fi shi kyau.
'Ya'yan Umma kyawawan gaske ne matu'ka sai dai kyan Sakina ya zarce kwatance, tafi kowa kyau na ban mamaki. Duk iyashegensa 'kaunar da yake yi wa Sakina ba ta boyuwa, ita ce kawai za ta zage shi kanta tsaye bai rama ba.
Sai dai ya gama hargagainsa amma ba zai zage ta ba, haka nan ita ce zai daina yi wa magana ya dawo ya fara yi mata ko ba ta neme shi ba.
Da sauri ta ce, "Na Moriki jikinka zafi fa".
A shagwabe ya ce, "Umma! Idan na shigo ban gan ta ba, sai na ji tamkar na yi ta rusa ihu, sai na je wajen Mama nake 'dan samun nutsuwa. Gaskiya zan hana ta tafiyar da ta wuce kwanaki biyu".
Dariya ta yi ta ce, "Sai ka ce mai shan nono? To me za ta yi maka ne wadda ba za ka iya yi wa kanka ba, komai kake so Mama na yi maka, ga su Dala mai aikin abincin Umma, sannan ni ma komai ka ce kana so yi maka zan yi".
Da wata irin murya mai rauni tamkar ba Gudale ba ya ce, "A'a Sakina ko ba za ta yi mini komai ba, na fi jin nutsuwa na shigo na gan ta a gidan nan, ina jin dadi idan ta gan ni ta bar komai ta tarairaye ni".
Sakina ta murmusa ta ce, "Haka ne! To ka dinga jin maganarta ka daina sa ta bacin rai".
Yana jikinta ya ce, "Ban son irin haka Sakina kin sani! Wai duka wata nawa kika ba ni ne?"
Dariya ta yi ta ce, "Ai kai ne babba da shekaru sifili ka girme mini".
Ta bu'de jakar hannunta ta mi'ko mini mukullin motarta ta ce, "Halimatu dauko mini wata farar leda ina zaton akwai maganin malaria a ciki".
Na amsa na fice. Ban wani jima ba, na dawo dauke da ledar. Na mi'ka mata, ta bu'de ta duba ta fito da wanda ya kamata ya sha, sai da ta 'ballo masa, ta saka ni na 'bude ruwan roba na zuba masa a glass cup.
Amma fir ya 'ki sha ya kafe lafiyarsa 'kalau kewar Umma ce kawai ta ke damunsa.
Tsawon lokaci yana jingine jikinta, kafin ya yun'kura ya mi'ke, yana 'dan tangadi.

Ina tsaye ya zo wucewa ta kusa da ni, na sassauta murya na ce "Sannu Yaya Gudale".
Ba zato na ji saukar wan irin marin da ya katse mini ji da gani na wucin gadi.
Na durkushe saboda ki'dima, na fashe da kuka sosai.
A hanzarce Sakina ta iso kusa da mu tana tambayarsa ba'asin wannan uban marin da ya zabga mini.
Bai kulata ba, illa ya bu'de murya yana fa'din "Ashe ba ki ji kashedin da na yi miki na kar ki sake nunawa kin san ni ba?"
Ya yi hucin 'bacin rai, ya nisa! Ya ce "Bilhillazi idan kika sake yi mini magana sai kin ga tashin hankali! Na tsane ki, na tsani ko da jin muryar ki ne".
Da 'kyar cikin rawar muryar kuka na ce "Na yi nadamar abin da na yi maka plz kar ka yanke zumunci da ni Yaya Gudale".
"Tun ranar da kika ci mutuncina, kika tozarta ni, tun lokacin na tsane ki.
Ina gargadin ki ki fita harkata if not you will be in trouble".
Sakina ta yi sukuri tana nazartar mu, ta kalle ni ta ga na yi la'kwas hawaye na bin fuskata, na fahimci ta fi ni jin zafin marin da ya yi mini.
Ta mayar da kallon ta gare shi ta ce, "Namoriki akan me za ka mare ta? Kasan haramun ne duka a fuska musamman ma ta mace baliga".
Ya 'kan'kace manyan idanuwansa ya ce, "To ki fa'da mata ta kiyaye ni, na riga na cire ta a sahun 'yan-uwana! Matu'kar kuwa za ta mini magana wallahi sai na yi mata 'barin makauniya. Tunda na gane ba ta da kunya kuma ba ta da mutunci. Wai ni za ta kalli tsabar idona ta ce mini ba ni da zatin da cikakken namiji yake da shi, hakan bai ishe ta ba ta sake danganta ni da sakarai".
Sakina ta nisa ta ce, "Namoriki tsakani da Allah bai kamata ka tsananta wannan maganar har haka ba. Ko ni ba zan iya lissafa adadin yadda kake kushe Halimatu ba, za ta yi maka abin arziki ma amma sai ka gwasale ta. Hatta Guduyon da kake kiran ta da shi, ta amsa har yau din nan ba wanda ya san ma'anarsa. Kai ne ke ce mata kumbusa, Sadi bon bon, 'Katuwa, Tu'ke'kiya, Ra'kuma da sauran sunaye na iyashege. Duk da hakan kuma jikinta na rawa take kyautata maka, ni na san ba haka kawai za ta fa'da maka abin da ka ce ta fa'da din ba".
A tunzure ya ce, "Duk ina fa'da mata. Shin ni ban girme ta ba? Sannan duk sunayen dana ke fa'da din, fa'da mini guda 'daya wanda ba ta siffantu da shi ba".




# Team Gudale
# Team Gudiyo
# Ana tare 🤝
# Surayya Dee ✍️.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*


```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?


*Fatan alheri ga wadanan group din, mussaman wadanda suka bani support wajen sayan wannan littafin*
*Takorites*
*Janaftys*
*Khaleesat palace*
*Gwaram discussions*
*High class women*
*Da sauran groups daban daban*.
*Na gode madallah Ubangiji ya albarkaci kasuwancinku da 'ya'yanku*
*Gudale na jinjina muku, yana bu'katar addu'ar ku*😄
*Son so*🤝


*Ku'din karatu 500 ne. Biya ki karanta cikin nutsuwa da aminci*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*Ki tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.


*Page 15-16*

Sakina ta ce, "To ka sani ko ka siffantu da abin da ta ce 'din da gaske?"
Ya kuwa sake hasala ya ce, "Haba ai ko makaho ya shafa zai san Ubangiji ya kyautata halittata. Baya ga hakan ta ina na zama sakarai?"
Sakina ta dubi idonsa ta ce, "Ko ba sakarai ba ne kai, kana yin 'dabi'un sakarkaru domin kuwa babu shakka sakarai ne mai 'dabi'ar 'daga wa mace hannu. Ai namijin duniya ba a ganin 'kwanjinsa da sunan duka sai akan 'kato 'dan-uwansa amma ba mace mai rauni ba".

Ya yi shiru a dalilin maganar Sakina ta yi kunnen doki da tawa maganar da na fa'da ta tunzura shi har da kukansa.
Jin ya yi shiru, cikin muryar kuka na ce, "Dukana ya yi a ranar shi yasa na fa'da masa hakan, kuma Anti tunda na ba shi ha'kuri ai sai magana ta wuce. Zalina ya ci amma tuni na yafe masa, har ina yi masa magana saboda nasan illar gaba a shari'a".
Tausayina ya yi matu'kar kama Sakina ta sunkuyar da kanta 'kasa saboda yadda idanuwanta suka ciko, a dalilin ta riga ta yi amannar na fa'da komar Gudale. Ta gane na gama mutuwa a kansa, irin son da ba jan kunnen da zai yi tasiri. Ta fahimci duk wulakancin da yake mini zuciyata ba ta 'kullatar sa na tsawon lokaci mai yawa.
Ta nisa ta ce, "Tunda ta ba ka hakuri ai sai ka ha'kura, kai ma ka ba ta hakuri. Maganar ta wuce haka nan! Harshe da ha'kori ma ana sab'awa".
Ya nuna ni da yatsa ya ce, "Munafukar banza, a gidan uwar wa kika ba ni ha'kuri? Ina ce nunawa kika yi kin wuce ki yi haka?"
Sakina ta yi shiru tana ganin ikon Ubangiji. Ta kasa ha'kuri ta ce, "Yanzu ma ai ta ba ka hakuri Namoriki".
Da sauri ya ce, "Ba na son haka Sakina, ya za a yi yarinya ta yi wa na gaba da ita rashin kunya, kuma ki dinga ba ta kariya? Wannan sam ba tarbiya ba ce, ba gata kike yi mata ba. Na kuma rantse, sai ta tuba kafin na dawo da ita cikin jerin dangina".
Da sauri na ce, "Shike nan na tuba, Allah ya ba ka hakuri."
Ya wani dau'ke kai ya ce, "Ki ci gaba da rashin kunyar idan abin yi ne".
Sakina ta kalle shi ta ce, "Namoriki kai har za ka yi wa wani batun rashin kunya? Tabdi jam! Wannan shi ne wanzami baya son jarfa".
A zafafe ya ce, "Sakina ki ci gaba da yi mini irin haka. Na rantse miki zan ba ki mamaki".
Yana rufe baki ta ce, "Ai kullum sababbin mamaki ka ke shayar da ni".
Ya shige cikin 'dakin Umma yana yin gunaguni.
Yayin da Sakina ta 'dago ni daga durkuson da na yi.
Ta dinga rarrashi na, ni kuma tuni na daina jin zogin marin saboda ya yarda za mu ci gaba da mu'amala.
Hakuri ta dinga ba ni, tare da cewa, "Ki daina damuwa da lamarin Namoriki! Kin sani sarai manyan gidan ma ba hutawa suka yi da tsiyarsa ba. Ki kame daga kula shi".
Na daure fuska sosai na ce, "Me kike nufi ne Maman Nana? Zumunci za ki gille?"
Ta girgiza kai tare da cewa, "A'a wa zai raba zumunci, ko shiga cikin rikicin zumunta?"
Kai tsaye na ba ta amsa da cewa, "Sai mai son ya kunyata, ya kuma tsinci kansa cikin marasa rabon rahma a ranar gobe".
Ta zuba mini ido tana mini wani irin kallo mai tsanani.
Ni kuma na waske na yi tamkar ban kula ba. Ta yi wani irin gauron numfashi ta ce, "Halimatu ba ki dace da fuskantar 'Kalubale mai gigitarwa ba. Ba wani tasku a gurin 'ya mace irin rashin samun nutsuwa a gidan aurenta. Yau na gaskata da gaske kina son wannan yaron, sai dai a karo na biyu zan maimaita miki ba ki dace da shi ba."
Na 'daure fuska sosai tamkar hadari. Ta sassauta cikin rarrashi ta ce, "Ki yi amfani da iliminki, kar ki bari ki biye wa 'kawar zuciya, cizon yatsa ne zai biyo bayan hakan Sadiya".
Cikin gajiyawa da maganganunta a tunzure na ce, "Don Allah Anti kin ji Yaya Sadik ya ce yana so na ne?
Idan kuma kin fahimci irin jarabtar da aka mini a kansa ne kike mini haka, sai na ce miki ba ni da ikon daina son al'amarin da kike ganin aibu ne a wajenki".
Da matu'kar mamaki ta ce, "Wato a idona ne aibu ko?"
Ba ja-in-ja na ce mata, "E domin kuwa ni ban ga makusarsa ba, shi ba so na yake yi ba, bare ki dinga nuna mini ba kya son mu sake zama abu guda da ku".
Na fa'da da rauni sosai. Sakina ta hau tattara kayanta musamman babbar ledar kayayyakin sayarwarta ne a ciki, tunda 'yar kasuwa ce ta sosai. Domin mijinta Dubai da China yake fita yana shigowa da kayayyaki daban-daban.

Ta kalle ni ta ce, "Ni kika fa'dawa haka ko?"
Na dauke kai na ce, " To akan me za ki dinga sanyaya mini guiwa?".
Ta juya ta fita tana fadin, "Yi hakuri ba zan sake tsoma miki baki akan wannan matsalar ba."
Na yi sakare ina jin rashin da'din fishin da na gani a fuskarta. Amma kuma ba na jin zan bi bayanta don na ba ta ha'kuri.

Ina zaune shiru tsawon mintina uku, ina shirin mi'kewa Yaya Sadik ya fito daga dakin Umma, idonsa a 'dan birkice. Yana mi'ka tabbacin barci ne yake shirin kayar da shi.
Shudin wando ne iya guiwa a jikinsa,

9 / 61