Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
da cewa "Nine na baka aurenta, kuma tun wanccan lokacin na tabbatar maka nine ubanta.
Kowa anan yasan halinka, yasan ba dan ita ce matarka ba da tuni an fara kirga maaka adadin matan da ka aura, ka saki.
A ko'ina zan fadi gaskiya ko da hakan na nufin ta bata rayukan jama'a ne. Idan har zuwa yanzu da kuka shafe shekaru kusan biyar da aure kana ganin akwai na'kasu a cikin zamantakewarku to ka yanka duk abin da kake ganin ya yi maka daidai ni kuma zan fansheta. Domin ina matu'kar tsoron na mutu na barta a wulakantaccen hannu, ba ga kai ba, ba ga wadanda suke da tasiri akanka ba."
Umma ta sake muzanta.
Yayin da Yaya Sadik cikin rawar murya ya ce "Haba Abba! Haba Abba! A gabanta, a gaban Guduyo?"
Muryarsa ta karye ya yi maza ya saka fuskarsa a dukkan hannuwansa tabbacin hawaye ne yake neman zubo masa.
Dakin ya sake yin tsit kowa ya mayar da hankalinsa kan Uba da dansa.
Sai da ya ha'diye kukan ya dago ya ce "A gafarce ni! Amma gaskiyar magana an tozarta ni a bainar nasi Abba?
Kullum na zo gabanka da shaukin na zauna mu yi hira na ji da'di, baka duba hakan sai ka baibaiye ni da maganar Halima da girman hakkinta. Abubuwa da yawa da ake mini nake yin kawaici saboda kai, ba kowa ne za'a masa ya ha'kura ba.
A duniya na tsani matata ta yi aiki, amma haka siddan. Sai ga Ashiru ya samo aiki ya kawo dan kawai y musguna mini. Na nuna bana so. Ba a duba uzzirina ba, aka bank'ara ni akan dole take aikin. Ni ka'dai nasan adadin ba'kin cikin da nake ha'diyewa a dalilin wannan aikin nata. Duk na danne na kai zuciya nesa saboda ina tsoron fidhinka, ina son zama da ita. Duk da hakan kuma sai a tara mini jama'a har da wadanda basa nufina da alheri, da wandanda idan na mutu baza su ji nauyin shiga gonata ba, ace wai za'a fanshi matar da ban ce bana sonta ko na gaji da ita ba a gabansu. Me na yi dana cancanci a mini irin wananan tozarcin dan manzan Allah?.
Sai kawai ya fashe da kuka tamkar yaro 'kan'kani. Kuma kuka yake yi na tsantsar ba'kin ciki ba wai na iyashege ba.
Yana yi, yana cewa "An ci mutuncina".
Bansan ina matu'kar sonsa har lokacin ba. Domin ji na yi, na shiga wani irin tashin hankalin da bansan adadinsa ba ya sake rufar mini.
Bansan ya aka yi ba, na ce "Kuka kuma Yaya Gudale?".
Sakina da take gefena ta mintsine ni. Na yi maza, na kame bakina ina hirji ciki zuciyata.
A ranar na ga zahirin kauna domin shi kansa Abba sai da kukan Gudale ya ta'ba shi. Ya dan diririce, sannan ya yi ta karfin halin cewa "To menene na kuka kuma tamkar Amnah?".
Kowa na wajen sai da jikinsa ya sake yin laushi. Aka sake fahimtar jarumtar da Abba ya da'de yana yi akan al'amarin Gudale.
Domin wani irin chemistry ne ya yi aiki mai matu'kar tsayawa a rai, da sha'awar karfin soyayyar da ke tsakanin Abba da Gudalensa amma zumunci da kawaici suka baibaiye shi yake ta boye wannan soyayyar, sannan yake ta jan kunnensa a kaina. Ni dai bana gajiya da jinjina wa Abba. He is my role model.
Da rawar murya ya ce "Abba ai wallahi ban da dai ina da magauta a wajen nan da zasu iya yi mini vedio, da kuka zan yi irin wanda Amna ta dinga yi tana jinjira, dan ka gane tsananin ba'kin cikin da nake ciki".
Girgiza kai Abba ya yi ya ce "Share hawayenka ka bu'de kunne ka saurare ni. Wallahi da gaske nake ba zan saurara maka ba, matu'kar ka ce zaka zalunci Halimatu ko bana raye idan ka cuceta akwai wadanda zasu kalubalenceka domin a hannun Ubangiji na damk'a amanarta, na kuma baza mutanen da Ubangiji ya cika zuciyarsu fa alheri su sanya mini ido a zamanku. Matu'kar kana son ka zama namiji a gidanka kamar yadda kake fata, to kuwa ka raba kanka da saka mata a harkar gidanka".
"To na ji Abba! Amma ita Guduyon wacce irin nasiha kake yi mata a kaina? Ni bazan fa'di matsalata da ita a gaban Wanda basu ki yau ace bama tare ba.
Zan dawo daga baya na fa'da maka duk irin wula'kanta ni da take yi dan ka dinga yin balance wajen jan kunnenmu gaba'daya. Na rantse ba karamin cutar da ni take yi ba. K'arfi da yaji ta mayar da ni bafade".
Girgiza kai kawai Abba ya yi ya bar maganar tun kafin Gudale ya sake baro masa wata maganar da zata saka a kunyata ainun.
Wannan maganganun na Abba sun sake zame mini dan zani a wajen Umma domin ba karamin kullata ta sake yi ba, mussaman yadda a gabanta aka bawa Gudale zabin ya sake ni, amma ya kasa karshe ya buge da kuka.
Yaya da Baba suka tofa albarkacin bakinsu, su kuma sun fi jan kunnena, suna ta jaddada irin girman hakkin da miji yake da shi. Yayin da hakan ya yiwa Yaya Gudale da'di ya dinga fa'din "Na gode muku, ku fa'da dai yi mata matashiya domin gatan da ta samu ya saka ta manta."
*****
Kwanaki biyu Gudale ya share ni, a dalilin Abba ya tozarta shi saboda ni a bayyanar nasi. Ni da shi kowa harkar gabansa yake yi.
An kwashe komai na gidan, wasu na kaiwa Mama wasu kuma na sayarwa *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS*
*08083909947*.
Anyi sabon fenti. Ana gobe za'a zo jeren amarya. Sakina ta iso da masu shirya gida. Ba jimawa motar kaya ta iso.
Gudale ma yana gidan. Suka gaisa, aka fara shigo da kaya ana ajiye wa. Gudale ya ce "Sama za'a hau da su".
Sakina ta ce "Ban gane ba. Bafa kayan amarya bane na Halimatu ne".
"Na sani ai, tuni mun gama magana da ita ta ce tana son saman".
Nan da nan Sakina ta ci damara ta ce "Wannan shi ake kira gangan Namoriki. Tun fil'azal ai kasa na Guduyo ne. Sama naka, yanzu kuma da ka yi niyyar kara aure sai ka barwa Amaryarka samanka. Domin ina maka rantsuwa da zatin Allah komai kake nufin ya faru zai faru matu'kar ka nemi jan Wannan maganar".
Maimakon ya bu'de mata wuta yadda ya saba. Sai ya sassauta ya ce "ke dadina da ke bakya fahimtar al'amura Sakina. Na fahimtar da Guduyo mun kammalah magana. Na fa'da a gidansu yarinyar cewar kasa ne nata, so kike na koma na karyata kaina haba Sakina".
Ta make kafa'da ta ce "Wallahi ba zata dauki sama ba. Ko dai ka bawa Amaryarka sama ka koma ka karyata kanka, ko kuma ka samar mata wani waje.
Ya kallo ni ya ce "Yanzu Guduyo ba zaki bude baki ki sanar mata ke kika zaba ba, sai ki bari ta mini kallon marar kirki?"
Na dauke kai ba tare da na ce "kanzil ba, domin idan na ce zan kunyata Sakina tana iya nada mini duka sannan ta fita a dukkan sha'anina a yadda na ga ta tunzoro sosai.
Ransa ya baci ya ce "Dama an fa'da mini yanzu zaki ko yi munafunci ta yadda zaki dinga boye alherina kina yada sharrina. Banda haka me yasa kika nuna mini kin amince?. Dama yadda nasan ni ka'dai ne namiji da ya kwanta a cikin Ummah, hakan na gasgata zuwan da kika yi gidan Sakina kulle kullen mugun abu kuka yi.
Sakina b'ata tsaya b'ata yawun bakinta wajen fahimtar da shi ba ni ce na k'i ba, ita ce bata yarda ba.
Yayin da nima ban kware mata baya ba.
Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, waje ya fara d'aukar harami domin tuni aka shirya falo. Har wani wajen karatu aka fitar mini.
Zuwa yamma kuwa an kammala da ko ina, murna da daukin yadda aka gyara wajen ya yi matu'kar zangwaye kishin da nake jin tamkar na babbaka gidan.
Na dinga yiwa Abba addu'ar gamawa lafiya.
Kawai takaicin Gudale ne bai yi sassauci ba, mussaman yadda yake ta shirin yin biki cikin farin-ciki. Dan ya sake cusa mini takaici tunda ya ce nice na shiga tsakaninsa da ubansa.
A gabana yake waya da Umma tana zayyana masa abubuwan da zai yi dan ya fita kunya a idon yarinyar da danginta, ya daina barin komai sai ita ta yi ko su Anti Maimuna. Baya Jin kunyar rarrashinta da cewa komai ina yi fa Umma, kawai yarinyar ce take raina kulawar da nake bata, alhalin kuma tasan ina sonta. Ni gaskiya Umma bansan ya zan yi ba fa, na fara gajiya".
Yayin da ita kuma take cewa "A a ai hakan ma na samu, na kuma gode maka, an yi ban yi zaton ma za'a barka haka, ba tare da an sarrafeka ba. Ban da ina tsaye, ai da ko maganar aure ban isa na yi maka ba domin sai ka shafe kwanaki bakwai baka so ganina ba, tsabar yadda zuri'a gidan mai Ashafa zasu dinga rubuce ka a allon karfe, ko a tofe sunanka a ruwa ayi siddabarun da za'a ayi ta tafarfasa ka akan wuta. Ai masifar mutanen nan ba yar ka'dan ba ce."
Wataran ya ce "Amma kin mini al'kawarin ba ruwanki da maganar mutanen nan. Wani lokacin kuma ya celNa fa'da miki asiri zai ci ni, amma ba zai yi tasiri ba Umma".
Haka wadannan kwanakin masu tsauri suka dinga shudewa ba tare da na yarda da Yaya Gudale ba. Tun yana rarrashi da sauke duka girmansa, har ya fita harkata, tsakaninsa da ni sai bak'ar magana.
Ranar da ya rage saura kwanaki biyu aurensa, da daddare ya same ni a falo inda na mayar makwancina. Ya sassauta ya ce "Yau kam tura ta kai bango. Zo ki ji Y'ar Abba".
Na dauke kai na ce "Ina jin ka".
"Abin da kike yi mini fa ya wuce ka'ida. Ki dubi uban ku'din da Abba ya narkar ya siya miki gadajen da zaki dinga lalube masa dansa da kyau amma fir kin rufe ido kin kasa gano manufar wannan alherin nasa".
Na rasa yadda zan yi da takaicinsa, kawai sai na zabi na yi masa shiru.
Ya ce "Ko kizo ki mini abinda zaki rabauta cikin farin-ciki da walwala ko kuma ki yi a dole kuma babu rabauta a tare da ke".
Tsakin da ban yi niyya ba ya subuce mini.
Ai kuwa babu zato kawai na ji ya buge mini baki. Zafi sosai na ji. Cikin ba'kin ciki da kishi na ce "Allah ya isana".
Ai kuwa ya fusata ya ce "ni kika yiwa Allah ya isa Guduyo? Abin har ya kai da zagi? Na rantse miki ba zaki sake zagina ba, daga yau".
Gaba'daya ya birkice ya shak'e ni, na saci kallonsa na ga idanuwansa a jirkice suke tabbacin yau ya tuna baya ya dan jefa k'wayarsa, abin da na jima banga ya yi ba. Tsoro ya kama ni, dana san a cake yake dan ban biye shi mun yi musayar yawu ba. Bare har na janyo wa kaina masifar da bansan inda zata tsaya ba.
Wani irin murde ni ya yi tamkar ba dan tsurut ba. Ya sanya mini karfin da banyi zaton yana da shi har hakan ba.
Wata irin mua'amala ya yi dani tamkar da baiwar da bata da k'ima ko ka'dan. Tun ina yun'kurin kwatar kaina har na fahimci ya da'de yana mini wannan tanadin. Dan haka na ha'kura na sallama ya yi iyakar abin da yake ganin ya hukunta ni.
Tabbas na ji jiki, ya wahalar da ni, domin shi kansa tun yana yi dan ya samu nutsuwar da ya jima bai samu ba. Har ya koma yana yi dan kawai ya azabtar da ni.
Tsawon lokaci sosai kafin ya tashi ya barni a wula'kance.
Har asuba ina kwance, duk yadda na so na tashi na yi wanka kasawa na yi, dan tsananin ba'kin cikin halin da nake ciki.
Ina kallonsa ya fito ya tafi masallaci. Da rarrafe na isa daki, na yi wanka da ruwan zafi sosai.
Na dinga yin tsarki da ruwan zafi da kuma wani sabon cleansing cream na tsarki da Aisha lame jakadiyar Oriflame
ta bani shawarar amfani da shi tunda na haihu. Kuma sosai nake Jin da'dinsa, har infections yake yaki da shi.
Ina idar da sallah ya dawo. Ya kalle ni ya yi tsaki ya ce "ki ta wula'kanta ni saboda kawai ina miki kara ban ta'ba fito wa na fa'da miki ainihin yadda kike ba.
Alhalin yadda kike bukekiya haka wajen yake".
Na sandare, hawaye ya goce mini. Baki na rawa na ce "Ni Yaya Gudale?"
Ya nuna ni da yatsa ya ce "Ke Halima! Domin kin tashi ma daga Guduyon tunda duk sun yi yaushi sun zama tamkar jarirai shida kika shayar".
Ya yi shigewarsa ya barni da tsananin tashin hankali.
Da wuri ya fice, a dalilin yau zasu yi dinner.
Abba kuwa yana dawowa daga sallar juma'a sai gashi Yaya Abdallah ya rako shi har cikin falona. Duk yadda nake cikin damuwa hakan na daure na marabci Abba da murmushi da kanzagi.
Yayin da shikuma ya ji da'di, ya yaba da kawatuwar wajena. A fili ya ce "Wato Halimatu ina son Sakina! Ina alfahari da ita, ki taya ni sonta, itama babu son zuciya a al'amuranta. Allah ka so Sakina, ka tsare ta, ka yafe mata".
Na ce "Ameen Abba! Amma ni fa?"
Ya murmusa ya ce "Ho autarmu! To ai ba sai na fa'da miki ba, domin ke din uwa ce, kinsan kuma yadda karamin d'a yake da shiga rai."
Na yi murmushin da ya fito daga dukkan zuciyata, na ce "Ni da Yaya Abdallah wa kafi so to?"
Ya tuntsire da dariyar da ban ta'ba ganin ya yi irin ta ba.
Ya ce "Ashe kishi ne har haka da ke Sadiya?"
Nima na yi dariyar na ce "Kawai ka fa'da Abba"
Ya ce "shi na fi so. Kinsan shine babban d'ana".
Na gimtse fuska na ce "To ni da maigidan nan fa".
Ya ce "Kunnen doki kuke bansan wa yafi wani ba. Duk wanda yafi yiwa wani sassauci da afuwa a zamantakewarku to shi nafi so".
Na yi dariya na ce "Allah ya baka aljannar daya tanada dan saddikai Abba" .
Ya amsa da cewa "Ina ro'konsa ya sanya mu a rukuni daya da dukkan zuri'a, so nake mu makwabci juna a aljannar Halima".
Ya miko mini dan karamin akwati mai daukar ido.
Nasa hannu biyu na karba. Ina godiya sosai.
Ya ce "Bu'de mana.
Ina bu'de wa na ga wata irin dankareriyar sarka da zobe da kuma chain.
Na zuba ido ina kiyasin mahaukatan ku'din da ta ci.
Na yi kasa da kaina a dalilin raunin da ya shige ni.
Na dago na ce "Sannu Abba! Madallah da Kai".
Ya murmusa ya ce "ki yi farin-ciki, ki zauna a dakinki dan Allah. Amma idan akwai cutarwa kada ki yi hakuri. Allah ne shaidar yadda nake son aurenki ya yi k'arko, amma bana kaunar ki yi zaman kuttu.
Kinsan halinsa Halima! Na sani kina juriya, addu'ar da nake yi miki na Ubangiji ya hore miki shi, In sha Allah ba za'a juyar da ita ba".
Ya fita ba jimawa sai ga Yaya Al'amin da Yaya Ammar sun kawo mini katon fridge da injin wanki wai su suka siya mini. Ga akwatina uku kuma inji Baba wai kayar fa'dar kishiya ne ya fanshi Gudale. Basu wani jima ba suka tafi.
Na zauna na yi tsam da raina na ga irin tarin dukiyar da aka tara mini duk dan a sanyaya mini zuciyata. Amma zuciyar kullum sake tafasa take yi mussaman da a yanzu Yaya Gudale ya sake murdewa.
Na tuno motata da ta iso jiya. Na kalli tsadaddun frame da mahaifiyata ta siyo mini.
Na sake kallon akwatinan da Baba ya mini dan ya wanke mini takaicin lefen da Umma bata bari an yi da ni ba.
Akan kunnena ta cewa Sakina ko dankwali ba za'a siya mini ba. Tunda Abba ya kulle bakin aljihunsa saboda ni, komai ita take yi da taimkon su Anti Maimuna. Dan haka ba za'a mini komai ba, tunda ai nima an yi mini lokacin aurena.
Motar da aka canja mini ba karamin kidimata taa yi ba. Mussaman da na barwa Yaya Ammar tawa ta da.
Haka kayan dakin da aka sake mini, hatta Sakina sai da Umma ta ci mutuncinta. Domin so ta yi ta auro wacce zata kere mini a komai, sai kuma Abba ya fahimci manufarta, ya mayar da auren ya zame mini tamkar jari.
Ya dinga nanata a kular masa da zamana ko bayan babu shi.
Tabbas auren Yaya Gudale ya zo mini da tarin alfarmomi sai dai da yake an sanya mana k'yamar kishiya duk sai gatan da na samu bai wanke mini kishin ba, sai dai kuma na samu amincin kada a zo da sabbin kaya nawa sun tsufa.
Karamcin Abba! Da yadda ya damu da farin-cikina, da yadda yake rokon na kwantar da hankalina na zauna lafiya da mijina sun matu'kar zangwaye haushin Gudale da ya damfaru a raina.
Na k'udiri aniyar gyara kuskuren da nake yi, na gamsu k'arin auren da zai yi ba laifi bane.
Ina zaune sai ga Amnah ta shigo a guje, Momi ki bani takalmin da Maman Abuja ta kawo mini inji Umma zamu tafi wajen bikin Dady".
Na kalleta naga sai murna take yi. Na rausayar da kai na ce "To shiga ki dauko, yana dakinku ai".
Da gudu ta yi study room din da aka kirkirar mini. Tana cewa "Momi shine ba ki ce na zo na ga yadda aka yi miki gyara ba?"
Na ce "Ai yanzu kin ga ni".
Ta shiga dakin da yake nasu ne . Ina jin tana ihun murna nasan kuma sabon gadonsu da fenti ne ya fa'da'da murnarta.
Ta fito da takalmin a hannunta ya shiga dakina da yake makwabtaka da nasu.
Jim ka'dan ta fito ta ce "Mummy gaskiya yau anan zan kwana. Ki cewa Maman Nana a dawo da Afrah."
Na zare mata ido na ce "Maman Nana kika ce? Ke ba mamanki ba ce, Yayar tawa?
Ta kame bakinta ta ce "very sorry Mummy. Maman sallari to".
Na girgiza kai na ce "Ai bazan iya ba ".
To ni na fa'da Mata?"
Da sauri na ce" A a".
Ta falfala tana cewa "Na tafi Ummah ta ce kada na da'de kar a tafi a barni".
Na girgiza kai na dan yi murmushin da iya lebena ya tsaya. A fili kuma na ce "Umma duk nisanta ni da Amnah da kike yi dai ni na haifeta. Allah dai ya baki nisan kwanan da zaki ga sadda