Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   20 / 61

57K to 60K   out of 180.1K words

sannan ba jinnu bane"
"Wato dabba ne ko?"
Na yi shiru.
Ya nisa ya ce "Ni kika kwatanta da dabba?"
Jikina ya yi sanyi na ce ba fa dabba bane.

Ya ja tsaki mai'karfi tare da cewa "Duk iyashegen da kike ji da shi, sai na sauke miki shi wallahi.
Zan je na tambayo menene *Ayu* sai na gano ma'anarsa sannan zan dauki mataki".
Na yi maza na ce "Amma dai idan ka tashi neman ma'anar kar ka saka sunana a ciki".
Ya ce saboda kinsan al'amarin bana mutunci bane kenan?".
Ya yi kwafa ya kashe wayarsa.
Kan dole ya je ya bu'de kofar, ya tarar da Iman diyar Anti Ramla dauke da basket din kayan karin kumallo.
Ta duka ta ce "Uncle ina kwana? Ga shi in ji Antin Zaria".
Ya karba, ba tare da ya ce mata uffan ba. Ta juya ta tafi, a dalilin an ja kunnenta kar ta sake ta zauna.
Ina daga daki ina jinsa yana karya wa, kamshin abincin ya shiga har dakin.
Na kasa ha'kuri, na fita.
Bance masa komai ba na dauki plate ina kokarin zuba wa kaina.
Sai da na gama zuba ferfesun 'kafar sa da soyayyen dankali, ina 'ko'karin zuba shayi.
Ya kaikaice ya ce "Amarya mai aji jira take akai mata abinci har daki, a lallabata, ta ci, yayin da ita kuma take nuna kunya da yauki".
Maganar ta shige ni amma sai na waske na ce "Rai dai! Da sannu kunkuru zai je inda zomo ya je."
Ya tabe baki ya ce amma kuwa sai an kosa bai isa ba".
Na koma daki, ina kokarin mayar hawayen da yake yun'kurin zubo wa.
Da yake bana wasa da cikina, tas na cinye, na kora da lafiyayyen shayin da ya sha kayan ha'di.
Na dauki plates din, na je na kwashe wanda ya yi amfani da su, har basket din na kai kicin duk da bamu cinye ba. Tsaruwar falon da kicin din ba karamin burgeni suka yi ba. Hakika an narkar da dukiya mai yawa wajen kawata mana gida. Ubangiji ya saka dukkan iyaye da alheri.
Na zo wucewa ina kallonsa yana kallon 'kirjina da 'dinkin kayana ya sake fito da su sosai.
Na wuce a raina ina cewa "lallai kuwa kunkuru zai jima bai isa inda zomo yaje ba"
Da na rasa me zan yi, na dauko tsintsitar kwakwa na share kafet din, haka na share tayals din da ita, saboda bansan inda aka jefa ta laushin ba. Na gangara na share falon, saboda na ga Gudale ya tashi.
Na hada ruwa na yi moping.
Kamshi ya cika gidan saboda a ko'ina na saka turaren masu mabanbanta kamshi, dan haka sai suke bada wani nau'in kamshi mai da'din sha'ka.
Da na kammala na wanke hannuna, ja dauko ledar supplement dina na fitonda guda na hadiya.
A raina ina karfafawa kaina guiwar na cigaba da tsuma kaina ta yadda duk sadda na tashi daga Amaryar buzuzin zai ki'dime a kaina.
Ni da kaina na shaida ingancin maganin saboda yadda nake jin sauyi mai yawa a marata madallah da kayayyakin *Faseelat*
*07039269802*

Na zauna a falo ina kallon wata tasha da ake tseren motoci.
Ban Jima da zaman ba ya fito sanye da farar shadda mai kyau sosai.
Sai sheki yake, ga kamshi tamkar dai angon gaske.
Bai cika saka kaya haka ba, kullum a cikin kananun kaya yake, shiyasa a kwanakin nan ya sake yi mini kyau a dalilin shigar manyan kayan da yake yi.
Kallo daya ya mini ya dauke kai ya wuce bai ce 'kala ba.
Na bi bayansa da ido, ina jin soyayyarsa na sake bin dukkan sassan jikina.
Bayan azahar ba jimawa, sai ga tawagar mutanen gidan mu.
Tunda ga kan Antin Zaria, har cousins din mu na Gusau da kebbi.
Aka dinga hira cike da nishadi, gefe guda ana jimami gobe war hakan kowa yana daf da isa inda ya fito.
Bikin aure da ha'da zumunci yake.
Yammaci sosai duk yan'uwa sai jan kunne suke ta mini, tare da nanata mini hakuri shine mabudin dukkan nasara.
Antin Zaria ta mi'ke tana cewa ragowan jama'ar ya kamata kuma su tafi.
Kafin su tafin sai ga Abba, Baban Gusau da Yaya da kuma Maman Kebbi.
Tare da Yaya Sadik da kuma su Yaya Al'amin da Abbas! Abin mamakai har da Yaya Ashir.
Dukkanmu muna 'kasa a zaune, yayin da iyayenmu suke zaune Kan rantsatsiyar kujerar falon.
Bayan an yi addu'a. Abba ya fara yi mana jawabi mai dauke da rauni da kashe jiki.
Ya ha'da mu dukkanmu, ya dinga mana wasiyya da mu ri'ke zumunci, mu yi hakuri da duk wani kalubalen da yake cikinsa, Ubangiji da kansa ya wajabta yinsa, shiyasa yana cikin abubuwan da shaidan yake shiga cikinsa ya yi kane kane, ya jefa gaba da kiyayya a tsakanin 'yan-uwa.
Ba dan komai ba, saboda ya sani zumunci ka'dai idan ya bari muka ri'ke shi, muka inganta shi, da sannu zai zame mana sanadin shiga aljannah.
Shi kuma ba hakan yake so ba, abokan zama yake nema a wuta, shiyasa ba abin da yake sanya shi farin-ciki kamar idan ya yi galaba akan tarwatsa aure, da sanya bawa shirka, da kuma jefa kiyayya a cikin zumunta.
Ya yi shiru tsawon lokaci, har kowa ya ji tamkar ko ya kammala ne.
Ya nisa ya zarce da cewa "Bayan haka ina son na fa'da muku, mu yanzu ka'dan ne ya rage mana a cikin wannan duniyar, domin ko Autan mu ya kai shekaru sittin din da Annabi ya ce mafiya yawan al'ummarsa zasu rayu ne a tsakanin sittuna au saba'una, kalilan ne suke zarce hakan, yayin da yawa basa kai wannan shekarun ma.
Dan haka ina sake jaddada muku ku yi ibada, ku yawaita istigifari, sannan ku zama bayi masu yawan godiya.
Ina sake jan kunnenku ku zama masu sassauci, masu dauke kai ga wanda ya yi maka izgilanci da gangan, da sannu Ubangiji zai maka sakayya, ku zama adalai a cikin iyalinku".

Ya sake dakatawa ya numfasa sannan ya cigaba da maganganu masu ta'ba zuciya domin da yawa duk kwalla ne a idanuwanmu.
"Sadik! Sadik! Sadik".
Sau uku ya 'kira shi yana amsawa.
Ya kaurara murya ya ce "ka ji tsoron Ubangiji ka yiwa kanwarka kuma matarka adalci, ka sassauta mata, ka Kuma gane ita din mace ce, mace kuwa Ubangiji bai yi ta a mike ba. Annabi ya ce mana a karkace aka yi su, dan haka mu yi hakuri mai yawa da sha'anin su.
Ka sani mun baka ita ne, ba dan mun gaji da ita, ko dan ka zauna da ita bisa alfarma ba.
Cikin soyayya da adalci zaka ri'ke ta, ka yi mata sassauci a inda ta kuskure maka, ka yaba mata idan ta yi abin kyautatawa. Kar ka zalunceta, kar musguna mata, idan na kama da wannan laifin ka sani nima ba zan sassauta maka ba. Ina ro'kon Ubangiji ya sanya alkhairi mai yawa a aurenku, ya baku zuri'a mai albarka wacce zata yiwa musulunci da zumunci hidima".
Dukkan falon suka amsa da "ameen".
Haka su Baban Gusau, da Maman Kebbi suka sake tofa albarkacin bakinsu, kuma dai duk maganganun suna nuni damu zama masu ha'kuri da ladabi a duk inda zamu tsinci kanmu a rayuwa.
Daidai nan Sakna ta nemi izinin zata shiga gida karban wani sako.
Ta fita da sauri, ina kallon yadda Abba ya bita da kallon kauna, irin sahihiyar kaunar da Uban yake yiwa managarcin 'dansa.
Ba jimawa kuwa ta dawo wasu mata uku, suna biye da ita da manyan tires an nade su da poil papper.
Suka ajiye, suka gaisa da mu sannan suka tafi.
Ta dauki tire daya ta bawa su Abba.
Daya kuma ta bawa su Yaya Al'amin, yayin da dayan kuma namu na mata.
Hadaddiyar fried rice ce da ta ji hanta sosai, ga kuma hadin ganye.
Kowanne tray da cokulan roba a kalla guda bakwai a ciki.
Ta kira Farisan Gusau suka yi kicin suka de'bo ruwa da lemo sai da suka rabawa kowa sannan suka zauna aka Fara cin abincin.
Addu'ar albarka ba wacce iyayenmu basu yiwa Sakina ba.
Hatta Antin Zaria sai da ta ce "wato dai Sakina idan ban yi da gaske ba, sai kin 'kwace girman nawa kamar yadda kika kwace mini fada a wajen su Baba da Yaya".
Aka dinga dariyar maganar.
Sosai Sakina ta mayar zaman ya zama wata irin walima mai da'di da sanya nisha'di da son a tabbata a cikin wannan yanayin na farin-ciki da kaunar juna.





*Umm Muhd collections*
*Tana sayar da hand bags da takalma na kece raini*
*Tana dinkin manyan mata yan kwalisa*
*Tana ha'da lefe*
*Tana ha'da kayan haihuwa*
*Tana da mayafai gangariya*
*Tana da duk nau'in sutura*
*Tana da zababbun kayan kicin*.
*08063358662*.




# Team Gudale#
# Team Guduyo#
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.

*Umm Muhammad collections*
*Sharrariyar mai sayar da dukkan kayan sutura da kuma takalma da jaka masu kyau da sau'kin farashi*.
*Bayan haka tana ha'da lefe dai dai da aljihunku*.
*Tana ha'da kayan haihuwa*
*Sannnan kwararriyar tela ce da ake yayi*
*08063358662*.
*SDK*
*39-40.*



Zaman nan bai tashi ba, sai daf da maghrib!
Bayan Antin Zaria ta dauko sauran kayan da ta rarraba a wajen dinner, ta bi duk Wanda yake wajen ta bashi hadaddiyar jaka mai dauke da kofin shayi na tangaran da tawul masu dauke da sunana da na Yaya Sadik a jiki.
Su Abba kawai ta ce nasu na cikin gida.
Suka dinga tafiya, suna barina, sai lokacin na ji kewa ta dirar mini.
Da tuni ina cikinsu.
Farisa ta gyara falon, ta wanke tires din yayin da aka zubar da cokulan.
Ta kammala ta tafi ta barmu.
Sakina ce kawai ta rage bata tafi ba.
Ana idar da sallar sai ga Yaya Sadik ya dawo da sauri tamkar wanda ya yi mantuwa.
Kai tsaye ya shigo dakin da muke zaune, mun idar da sallar tana ta fa'da mini abubuwan da zan dinga yi na janyo hankalinsa kaina.
Ya na'de hannuwansa a 'kirji ya ce "Sakina! Na tambaye ki mana?"
Ta kalle shi sosai ta ce "Ina jin ka".
"Me yasa kike da kisisina ne?
Bayan duk kazallahar da kika yi dazu kika sanya aka dinga kwarara miki addu'a ke ka'dai tamkar ke kawai suka haifa. Hakan ba ishe ki ba, sai kin zo kina koya mata makircin da zata kai ni 'kasa ko?"
Ya fa'da cikin daurewar fuska.
Ta sassauta ta ce "wato addu'ar da suka yi mana dukkan mu bata yi maka ba, wacce aka mini ne ta tsaya maka a rai?"
Ya basar ya ce "To tashi ki tafi na sallame ki, daga nan har watanni shida kar ki zo, kin sani dai daga ni har ita 'kannenki ne ba yayyenki bane bare ki yi ta yi mana zarya".
Ta murmusa ta ce "Na Moriki magidan ci".
Ta dauki dankwalinta ta daura, tare da yafa mayafi.
Ta kalleshi ta ce "Idan har ka yi halin girma ba zaka ganni a gidanka ba har sai ranar da Halimatu ta haifo little Sakina. Ina fata ba'di iyawar hakan".
A tunzure ya ce "wa zai yi miki takwarar?
Ga uwata, ga kuma Antin Zaria! Yo da na saka sunanki ba gara na sawa yarinya sunan rana ba. Haka kawai na je ta debo Halin ki na rasa yadda zan yi da ita.
Matu'kar kuwa zan saka sunanki ki tabbatar lami ko Attine za'a ce mata tunda alhamis aka haife ki".
Ta dinga dariya sosai tana cewa "To ita ai ba lallai ta zo alhamis din ba, indai an yanka mata rago da sunan Sakina, sannan a school zata amsa Sakina Sadik Moriki ai magana ta kare".
Ya harareta ya ce "Dan me zaki batar da sunan Abba?
Bayan yaran da zan haifa ne kawai zasu yi bearing da sunan sa kamar yadda Umma ta ke fa'da mini".
Ta girgiza kai ta ce "*Sakina Sadik Abubakar*. Shike nan?"
Ya daga kai tamkar dolo tare da cewa "shikenan sai dai ki sani ba a farko ba, domin so nake Abba da Baban Gusau su fara zuwa".
Yana rufe baki ta mi'ka masa wata takarda da alamun risit ne.
Domin ta kosa da wannan maganar ta shiririta.
Ya karba ya duba, ya ce abincin da muka ci 'dazu ne ya lashe har dubunnai haka?"
Ta ce "Eh na tura maka lambar asusuna ta what'sapp, sai ka tura mini ku'dina domin rufa maka asiri na yi. Bai kamata ace iyayenka da danginka na kusa sun zo babu komai a gidanka ba".
Ya kuwa zabura ya ce "Kuturu! Ai kuwa kin ci uwar 'karya kin kwana da yunwa Sakina. Wato ni zaki yiwa bariki?
Ki ciyo mini bashi, sannan ki nuna ke kika yi da aljihunki, ayi ta sanya miki albarka, sannan ki zagayo ki ce na biya ki ku'di?"
"Eh mana ai dama haka Annabi ya koyar washagarin tariya idan da hali ango ya shirya 'yar walima. To kuma na ga an cika maka gidan saboda soyayya da gata. Sai kuma a bar mutane su tafi bakinsu a bushe alhalin Ubangiji ya bada damar da za'a yi fiye da hakan".
"Sakina! Ya kira ta a tunzure ko ke ce 'kuda wajen naci ba zan baki ko kwabo ba. Ban saki ba, ban aike ki ba, ke ko maganar kika sake tayar wa sai na je gaban Abba da Baba na fa'da musu wannan wayon na ki, kinga sai su janye albarkar da suka saka miki tunda ba dan Allah kika yi ba.
Ni dai kam ban san wata halitta mai tsananin bariki irin ki ba".
Dariya ta kama mu, na maze ban yi ba, domin idan na yi din sai sai ta zamo mini wani abin daban. Yayin da Sakina ta kyale-kyale sosai. Ta ce "Kai yanzu akan kudin da bai gama rufa dubu arba'in ba kake wannan dagewar?
To shikenan an bar maganar, amma ka sani bashi ne, bashi kuwa sai mai imani ne yake biya, ka shaida ban bar maka ba, zaka biya tilas".
Haka ya tisa ta a gaba suka fita yana nuna mata dan'kareriyar motarsa da take filin gate an rufeta da tanfol.
Daga rakiya bai dawo ba, sai da ya yi sallah.
Yauma haka muka kwana ba tare da kowa ya san ma'kwancin 'dan-uwansa ba.
Da safe da na tashi, na shiga madafi a dalilin na ga kicin 'din akwai komai na bu'kata.
Dan Haka na fara shirin yin samosa da meat pie tunda hatta nikakken nama na gani a cikin madaidaicin freezer din.
Na sani kuma duk hikimar Sakina ce tunda ta san bana gajiya da yin snacks.
Kafin goma na safiya na kammala.
Da yawa na yi. Na na'de shi cikin leda na saka a fridge na soya wanda nasan zamu karya da shi.
Na tafasa shayi na zuba a cikin flask.
Na kai su kan dining.
Na gyara kicin din sannan na wuce zuwa 'daki, na kade gadon na share. Falon dai ban share ba saboda a yammacin jiya Farisa ta yi masa kyakkawar shara, kuma tun lokacin ba a sake zama a ciki ba.
Dan Haka kawai na fesa air freshener bayan na jona burner na saka turaren wuta.
Na yi wanka, na shirya cikin atamfa coffee sosai.
Doguwar riga ce na kashe daurin dankwali na yi matu'kar kyau.
Cikin 'dar 'dar na bu'de ragowan dakunan da suke cikin falon amma banga shi ba.
Na tabbatar yana sama.
Cikin dauriya na hau saman na tarar da kicin a farko sannan na shiga falon da aka shirya shi sosai.
Na rasa wanne dakin zan shiga a cikin guda biyun.
Na yi shahada na murda kofar dakin dake bangaren dama.
Ai kuwa ina turawa na tarar da tafkeken daki tamkar nawa na 'kasa.
Komai na dakin a shirye tamkar na mace.
A jikin madubin na ganshi a tsaye yana taje sumarsa, ya shirya cikin kananun kayan da suka karbe shi.
Duk da ya ji shigowata, hakan baisa ya
Juyo ba.
Na shiga ka'dan na sassauta murya sosai na ce "Ina kwana? Na kammala abinci, kai nake jira"
Ya juyo ya ce "je ki fara cin abinki".
Ban tanka ba, na fito, ba tare da na ji komai ba. Illah iyaka dai na 'daura damarar sauke nawa hakkin da ya rataya a kaina.
Na zauna kan dinning table din na fara karyawa hankalina a kwance.
Ina cin samosa ina korawa da shayi.
Ba wani jimawa ya sauko, bai yi magana ba, ya ja kujerar nesa da ni, amma wacce zamu zama opposite.
Na dinga rawar jikin zuba masa a plate da 'ko'karin ha'da masa shayi.
Ya dakatar da ni tare da cewa "Ke bana son kinibibin banza ni kuturu ne ko kuwa yaro ne 'kan'kani?"
Na tsame hannuna na ce "Ba ko 'daya yi hakuri".
Da kansa ya yi komai, ya kammala ya mi'ke ya fice ba tare da ya ce mini uffan ba.
Hawaye ya cika mini idona. Ina jin wacce irin amarya ce ni?
Na zari tissue na goge ban bari ya zubo ba.
Na hau saman na gyara masa, na wanke ban'dakin.
Na bulbule masa wajen da turaruka daban daban.
Na ga agogo sha'daya da kwata.
Sai kawai na 'doro alwallah, na tada walaha.
Na da'de ina rokon Ubangiji ya kara mini ha'kuri ya kuma sanya soyayya da tausayina a zuciyar mijina.
A kan darduman barci ya sace ni, saboda tunda na tashi da asuba ban koma ba.
Ban farka ba, sai da na ji ana 'Kiran sallah.
Na yi salati ina ambaton istigifari.
Ban ji yunwa ba sai wajen uku.
Na shiga kicin na tsaya ina tunanin me zan yi ne?
Sai kawai na ji waya, na fito da sauri na dauko.
Cikin sa'a na ga Aziza ce take cewa tana harabar gidan.
Da sauri na bu'de mata kofar. Muka rungume juna.
Ta dire kayan hannunta sannan ta koma ta dauko kwandon da ta ajiye a bakin 'kofar.
Shinkafa da miyar kaji Mama ta zubo mana.
Ga kuma hadin salad, na ce aikuwa kamar kun san tashi na yi zan 'dora girki."
Tare muka zuba, muka ci, ta dauko mana ruwa da lemo a kicin.
Sosai na ji dadin zuwan Aziza.
Sai da ta shiga ko'ina sannan muka adana kayayyakin da ta kawo mini.
Karfe biyar ya dawo, dawowarsa ya sanya Aziza tafiya duk da shima ya ce mata ta yi zaman ta.
Amma ta'ki, ta tafi.
Yana zaune a kujera ya 'dora 'kafa daya kan 'daya.
A hankali na ce "Na kawo maka abinci nan ko kuwa zaka je wajen cin abincin?"
Ba tare da ya kalle ni ba ya ce "Wai ke kam dole sai kin yi mini magana ne?
Abinci kawai na iya ci. Baki san ki yiwa mutum abin arziki ba, sai abinci?
To abinci, ko ina na je ci zan yi, yanzu haka ma a 'koshe na ke".
Na yi sororo na kasa gane wannan maganar tasa inda ta dosa.
Na ce "me kake so na yi maka, ka fa'da mini, a shirye nake na yi maka komai matu'kar hakan zai sa ka gamsu ba abin da nake so irin ka daina wannan fishin. Ka daina nuna mini halin in

20 / 61