Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   42 / 61

123K to 126K   out of 180.1K words

"Na gode! Shake mini wuya take yi."
Ya bu'de fresh milk din ya ce "To ga mutumin sha ya sanyaya miki makoshi Sadiyayye. Da hausata da na ki fa'da miki ai. Amma ke da Abba baku fahimce ni dai-dai ba. Gashinan ai tun lokacin baki huta ba, ba ki barni na huta ba".
Ban ce komai ba. Ya sake kwantar da ni a jikinsa ya ce "kin yi sallah ne?"
Na daga masa kai tabbacin na yi.
"To muje na taimaka miki ki yi wanka ki ji da'di a ranki, tun safe fa kike cikin wannan yanayin."
Ya tara hannunsa a daidai bakina ya ce "zubo dukkan bacin ran da yake zuciyarki na je na wurga shi ruwan can na sallari".
Hawaye ya balle mini a dalilin takaicin da yake sake cusa mini da sunan rarrashi.
Abin da kuma yake yiwa kulafaci ba zai samu ba duk azinarsa kuwa".





# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee ✍️.
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wanannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.

*SDK*
*73&76*

Duk rarrashinsa ban yarda na tashi ba, bare na shiga daki Kamar yadda ya so.
Ya ha'kura ya tafi, ya kyale ni.
Har tsakiyar dare ina falo kan sallaya. Sallah kawai nake yi ina kuka gaban Ubangijina.
Wannan daren ya yi matu'kar tsauri a gare ni. Domin tsintar kaina na yi ina addu'ar a karbi raina na huta.
Kamar yadda ban yi barci ba, haka shima bai yi ba. Domin sintiri ya yi ta yi tsakanin dakinsa zuwa falon.
Ya zauna ina sallame wa ya ce "kada ki sake tayar da sallah Guduyo. Kin sani aikin da zaki yi mini yafi sallar nan da kike yi lada da kusanci wajen mahaliccinmu.
Na miki iya laminin da zan iya yi miki".
Na kalle shi na ce "Ba zan iya ba! Na roke ka, ka barni na samu sukuni".
Ya hassalo sosai ya ce "kafaffiyar yarinya kawai! Dan ma kin samu ban ta'ba nuna miki komai ba. Nifa dama ba wai ina gamsuwa bane. Bare yau da kika sanya masifa a ranki duk kin wani zama ragajab".
Na murmusa na ce "Allah ya yafe maka".
Ya yi kwafa ya wuce Amma ba hakan ya so na yi ba. Na sani so ya yi na fashe da kuka ina tambayar ba'asin da gaske yake yi ko kuwa dan ya yi fishi ne?. Daga hakan kuma sai ya samu abin da yake so.
Na tada Sallah na rabu da shi.
Sai dai ina idar wa na kife ina gunjin kuka.
Duk da na sani Gudale ya fa'da mini maganar dan na yi ba'kin cikine ta yadda zuciyata zata yi bindiga.
Saboda na sani idan baya gamsuwa da ni ba zai dinga kidima idan mun kebe ba, ba zai dinga ajiye girman kansa dan ya samu yardata ba.
Na tabbatar ko da bana zuwa wajen Faseelat dan samun nagartattun supplement din da suke kara mini daraja. Ina cikin sa'idan mata.
Amma saboda zai yi aure ya rufe ido ya kalli tsabar idona ya ce mini baya gamsuwa da ni. A fili na ce "Tirkashi".
Wani irin kishi mai dagargaza dukkan confidence ya dinga shiga ta.
Na dinga kuka ina ambaton Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun.
Wajen k'arfe hudu ya sake dawowa ya tarar da ni akan sallayar ya ce "yanzun kin samu sukunin zuciyar ko kuwa?"
Ba ja in ja na ce "Ubangiji ya saukaka mini Alhamdulillah".
"To taso muje".
Na yi yake na ce "Kai da baka gamsuwa menene na wannan bibiyar ne? Na ce bana so, bana ra'ayinka".
Ya kuwa mike yana fa'din "Amma kin sani dai daga yanzu kina cikin tsinuwar malaiku dan kuwa ina cikin fishi mai tsananin gaske da ke".
Na ce "Na tanadi katon carbi na yin istigifari mai yawa".
"Guduyo laifin da kika yi cikin saninki shi zaki yiwa istigifari? Ai ni kika sabawa, kuma kin sani sarai Allah baya yafe laifin da ka yiwa wani".
A hanzarce na ce "Indai kai na yiwa laifin dan Allah samu waje ka yi ta kwashe mini karama, dan kuwa indai sai na amince da kai to kuwa ba zan rabauta ba a yau dai"
Ya juya yana cewa "Na barki Guduyo! Na bar miki abinki ki jika ki sha. Ni da nake shirin daukar sabo tsukakke ma".
Na bishi da ido kawai, wani ikon Allah sai ban ji komai ba domin kuwa na san takaicin ban bashi bane ya sanya yake ta sakin maganganun daza su iya haifar da babbar matsala idan ba'a yi taka tsantsan ba. Maganganun sun shige ni, sun zauna a zuciyata.
Washagari har ya fito cikin shirin fita ina zaune ba alamun gyangyandi.
Ya zauna ya ce "Ina son mu tattauna maganar jere ta yadda zamu rufe maganar gaba'daya.
Next week zasu zo jere. Na so na bata gidanta daban ta yadda zasu yi jerensu sosai, sai Umma ta nuna bata son hankalina ya rabu gara na ha'de iyalina waje guda. Yarinyar kuma ta amince.
Yanzu ki za'ba sama kike so ko kasa?"
Na sake yin yak'e na ce "Duk inda ka bani zan kar'ba ai kai ne maigidan".
"To ki za'bi sama kin ga zaki dinga yin exercise, sannan ita ta roke ni, 3 bedroom take so".
Na ce "hakan ya kamata tunda Yar babban gida ce. Ubanta da yan'uwanta masu fa'da aji ne".
Ya yi sororo ya ce "magana kika fa'da mini Guduyo? Daga na tambaye ki dan kada ki sake kai k'arar ban baki zabi ba, shikenan sai ya zama bak'ar magana?"
Na girgiza kai na ce "To me na fa'da wanda ba gaskiya ba? Ita ai ka ji ra'ayinta, ta amince ka ha'da mu, sannan kana son bata dakuna uku, tunda haka take bu'kata. To ni kuma ko garden ka kai ni ai zama zan yi kasani, tunda ni ba yar kowa ba ce".
Ya mi'ke yana cewa "Allah ka'dai yasan adadin mugun halinki da nake ha'diye wa. Ace ba dama ka taro mace daga gabas, sai ta nausa ta yi yamma?"
Ya koma daki ya dauko wayarsa.
Har ya kai kofar fita. Na bu'de murya na ce "Daga asibiti zan wuce gidan Maman Nana"
Da sauri ya ce "Capital No! Ban barki ba".
"Gaskiya ina son zuwa Gudale".
Ya juyo da mamakin yadda na ce Gudale gatsal.
"Neman masifarki ya kare a kanki Guduyo. Duk sadda nake rarrashinki a lokacin kike botsare wa".
Ya fice bayan ya ja tsaki mai tsananin gaske.
Na kifa kaina a jikin kujera ina wani irin kuka mai dauke da shessheka.
A gurguje na yi wanka na shirya. Kai tsaye wajen Abba na shiga, na tabbatar yanzu yana falo tunda har yanzu yana nan da dabi'ar jira a gama zuwa gaishe shi kafin ya shiga ya kwanta.
Na tsugunna gabansa bayan na gaishe shi. Na kasa tashi. Cikin tarin 'kauna marar algus ya ce "menene matsalar ki Halimatu?"
Cikin rishin kuka na ce "Abba zaka iya dakatar da auren, ka taimke ni ka hana shi, zan iya mutuwa a dalilin bugawar zuciya, ina sonsa, ina son na mallake shi ni ka'dai".
Ya yafito ni, na rarrafa na isa daf da shi.
Ya saka hannunsa a kaina. Ya ce "Yi salati Halimatu ki ji sanyi a kirjinki".
Na dinga nanata salatin har na dan samu sau'kin suyar da kirjina yake Yi"
Ya yi gyaran murya ya ce "Saurare ni da kyau Halimatu! Bu'de dukkan tunaninki, bu'de zuciyarki! Ubangiji ne ya halasta masa k'arin aure matu'kar yana da hali kuma yana da ra'ayin hakan.
Idan na hana shi damar da Ubangiji ya bashi tabbas na yi son zuciya, na kuma yi wa shari'a katsalandan."
Na fashe da wani irin kuka a dalilin isharar da maganar Abba ke yi mini cewa auren Gudale babu fashi.
Bai hana ni ba, sai da na yi kuka sosai.
Na dago na ce "Mutuwa nake son yi, ina zan saka kaina Abba?"
Ya mi'ke kafafunsa ya ce "Saka kanki anan Halima ki yi kukanki son ranki".
Na kifa kaina kuwa na dinga kuka hawaye na sauka kan kafafunsa.
Cikin rawar murya ya ce "Ubangiji a sassauta mata kishin da yake neman kassara zuciyarta da tunaninta. Allah ka san dalilin da yasa aka k'ulla wannan auren idan an yi da mugun nufi ne. Na rok'e ka, ka tsare mini Halimatu, ka hana zaluncinsu yin tasiri a kanta.
Idan kuma daga gareka ne, ka ha'da zuciyoyinsu, ka saka ta zama adala kuma jagora a gidan".
Ya yi shiru yana jin yadda jikina yake bari.
Ya sake sassauta wa ya ce "Ina ro'konka ya Allah ka wanke zuciyar Halimatu daga kishi mai sanya wa a halaka, kishin da zai sanya ta yi zalunci, da kishi mai sanya kunci, a sassauta mata ya Ubangiji".
Wani ikon Allah sai na ji wani irin sauki da afuwa yana shigata. Na dako fuska jage jage da hawaye.
Ga mamakina sai na ga shima kwallar yake yi.
Cikin alhini da tausayi ya ce "Bu'de kunne ki ji ni sosai kada ki yarda dan mijinki ya k'ara aure ki yanke masa dukkan kauna da buri. Matu'kar bai wula'kanta ki ba, ba laifi bane k'arin aure. Kar kuma ki manta aljannarki zata fi samuwa ne idan kin yi masa biyayya. Kada ki kuskura ki bari fishin zuciya ya sanya ki zalunce shi. Kada ki bari ki bawa wata damar da zata karbe miki miji, duk abin da take da shi Ubangiji ya yi miki shi.
Kada ki ji tsoron karawa da kowacce mace, domin Ubangiji ya halicci kowa cikin kyakkawar siffa. Babu mummuna, kowa mai kyau ne, Ubangiji baya kuskure, idan an fiki anan, sai kiga kema kin fi a wani fannin, babu kuma wanda yafi wani a wajensa sai wanda yafi tsoronsa yafi kyaun zuciya.
Idan an fiki kyaun sifa yi kokari ki yi fintikau a kyaun zuciya."
Na yi shiru ina sauraronsa da dukkan nutsuwata.
Ya numfasa ya ce "Ki zama adalar uwargida Halimatu! Kada ki yarda ki yi kissar da mata suka fi kware wa ta tuggu. Fa'di magana anan, fesa a can sai kiga mace ita ka'dai ta cakalkala al'amura masu yawa. Kada ki yi kulunboton da miji zai zalunci wata matar saboda ke. Kada ki gallazawa abokiyar zamanki. Domin duk halittar da kika ga ni a doron kasa akwai manufar halittarsa. Ubangiji yana kishin bayinsa mussaman wadanda aka zalunta.
Ki ji tsoron Allah! kada ki yi zaluncin da sakayya zata dawo miki ta inda baki yi zato ba.
Duk matar da ta samu dama ta gallaza wa abokiyar zamanta ko y'ay'an da ba nata ba. Billahillazi Halimatu matar nan bata cin bulus. Ki nutsu ki yi duba na tsanake. Duk wacce ta uzzirawa wata lah shakka sai an uzzirawa nata yaran idan ta aurar da su.
Mafi yawa kuma idan shekarun girma ya zo mata sai kiga komai ya kubuce mata, gidan ya yi mata kunci, hakanan a jarrabe ta da tashin hankali a cikin ya'yanta da lafiyarta."
Tari ya sarke shi, sai da ya huta ya ce "ki sake duba duk wacce ta yi ha'kurin cutarwar miji, ko na kishiya a karshe sai kiga ta yi karfi a wannan gidan, domin Ubangiji ne yake bata kariya da kansa, ba kuma zata wula'kanta ba. Ina miki sha'awar kyakkawan karshe Halimatu. Sai dai bana son ki yi ha'kurin da yake na cuta ne, ko na rashin sanin ciwon kai. Idan kinga da cin mutunci to kawai ki ha'kura a maimakon ki shiga hanyar bata da sunan samun kan miji".
Murya na rawa na ce ",Na gode! Na kuma ji duk abin da ka ce, zan kiyaye".
Ya daga dukkan hannuwansa biyu sama ya ce "Allah ka saka Halima cikin bayinka da kake karba daga garesu, Ubangiji kasan yadda nake son aurenta ya dauwama! Ina rokonka ka hore mata mijinta, a cika zuciyarsa da soyayyarta mai tsayawa a rai, mai kuma naci, a baibaiye shi da tausayi mai hana zalunci, a sanya ta zama shugabar matansa har a aljannah".
Na ru'ko hannunsa na ce "Ameen Abba! Ubangiji ya ji ka, madallah da kai".
Ban San dalili ba sai kawai na sake kifa kaina a jikinsa ina kukan da bana ciwo bane, kuka ne mai shauki, ina ayyana ko mutane nawa ne irin Abba a wannan duniyar?"
Daidai nan Baba ya shigo, ganinmu a hakan ya sanya ya yi turus.
Ya samu gefe ya zauna.
Ya ce "Kinsan dai bashi da cikakkiyar lafiya, amma sai ki zo ki tayar masa da hankali? Haka jiya kika yi, yau ma kin dawo, alhalin kinsan wannan koke koken zai iya sanya wa ya yanke hukunci na son rai. Ansan kishiya babu da'di to akan ki aka fara ne? Bana son rashin hakuri gaskiya".
Abba ya ce "yi kukanki Halimatu ni kuma ina ta roka miki Ubangiji ya sanya wannan ne kuka mai tsanani da zaki yi a dukkan rayuwarki".
Baba ya zauan a kasalance. Na dago na kalli Abba da tarin kauna irin wadda nake yi wa mahaifina.
Ya mini wani irin murmushi da har yau bai bace mini ba.
Ya ce "ki yawaita addu'a, ki yawaita istigifari".

Na isa asibiti muka yi kicibus da Sakina sama sama muka gaisa ta zille a dalilin bata yarda mu yi doguwar magana saboda takunkunmin hana ta fa'da mini auren Gudale da aka yi.
Kusan a tare muka tashi. Na bita muka tafi a motarta.
A hanya na ce "oh Maman Nana har da ke a cikin masu boye mini Gudale zai yi aure?"
Ta dan razana sai kuma ta ce "Na rasa yadda zan yi ne, ina jin tsoro ne, gani nake yi zuciyarki zata iya buga wa".
Na dan yi yake na ce "Ba komai Maman Nana jiya Abba ya fa'da mini, zuciyata ta kusa tarwatsewa tabbbas! Domin ko runtsawa ban iya yi ba. Amma dazu da safe Abba ya sanyaya mini ita, ya kuma roka mini sassauci a wajen Ubangiji! Alhamdulillah na samu sukuni sai dai har yanzu kirjin ya yi nauyi sosai."
Da karfi ta ce "Alhamdulillah! Allah ya a kara miki juriya, In sha Allah manufar da aka cusa masa auren ba zai samu ba, da ikon Rabbani".
Nan da nan jikinta ya yi sanyi tabbacin bata so ta fa'di hakan ba.
Ni kuma na waske tamkar ban fahimci komai ba.
Na sani ko a gabana Umma ta yi mini rashin kyautata wa ba yadda zan yi da ita.
Domin dai matar Abba ce! Matu'kar ba zan iya cin mutuncinsa ba, dole kuwa matarsa ta wuce cin mutuncina.
Sannan ita ce ta haifi Antin Zaria, baiwar Allah da bata taba nuna mini banbanci tsakaninta da sister's dinta ba. Hakanan ita ce uwar Sakina. Ita ta haifar mini Gudale sannan kakar su Amnah ce. Kenan tana da tarin alfarmomi masu yawan da bazan iya yin fito na fito da ita ba. Duk yadda na kai da rashin ganin girmanta sai dai na barshi a raina, amma taci tudun da bazan iya keta ta ba.
Na riga na gane k'addara ta yi mana wani irin dauri irin na huhun goro, tunda nima kullum a cikin takaicina take.
Na numfasa na ce "Abba ya fahimtar da ni alamura masu yawa a yau din, na gasgata dari bisa dari babu son zuciya a tare da shi. Na kuma daura damarar bawa Yaya Gudale dukkan support din da mace ta gari zata bawa mijinta a yayin da zai kara aure. Ki taya ni addu'a na zama adalar uwargida".
Jikinta ya mutu sosai ta ce "Na gode miki! Ni kuma idan har kika yi hakan na miki al'kawarin duk runtsi ina tare da ke. Abba ya ro'ke ni, na tsaya miki, kada na bari ki wula'kanta, na kuma tabbatar masa duk abin da zan yi dan ki gamsu kina da yar uwa mace zan yi. Zan kuma yi dukkan kokarina na ganin aurenki bai tabu ba. Da bakinsa ya tabbatar mini har aka daura aurenku baya so. Amma tunda kika haihu, ya tabbatar soyayyar da kike yiwa Namoriki mai girma ce. Ya tabbatar mini kullum sai ya ro'ki Ubangiji ya wanzar da aurenku muddin rai, ya baibaiye zaman naku da kwanciyar hankali da albarka
Ya ro'ki ko bayan ransa kada na bari ki wula'kanta a hannun Namoriki'.
Hawaye ya balle mini na tausayin Abba! Cikin wasiyyar da yake fa'da a bayyane, al'amarina ne akan gaba. Duk Wanda suka yi hira mai tsayi sai ya ce "kada a bar Sadik da iyawarsa a dinga saka masa ido, kada a kuma ayi fishi a yanke zumunta da shi, saboda halayyarsa. Sannan kada a bari Halimatu ta yi ha'kurin da yake na cuta ne.
Har yau din nan ban san wani halitta da yafi Abba karamci da son dinke zumunci ba. Madallah da mutane da suke kokarin kyautata zumunci, madallah da mutane masu danne son zuciyarsu. Madallah da mutane masu sassauci da afuwa mussaman idan an zaluncesu.
****
Muka isa gidanta na shige dakinta na kwnata ba jima wa barci ya yi gaba da ni. Barcin da ban yi ba shine yanzu ya gwada mini fin karfi.
Sosai na yi barci domin sai kusan magariba na tashi, ina bude ido na ga Yaya Gudale yana tsaye tabbacin shi ya tashe ni.
Ban ce komai na duro na shige bandaki. Ina fito wa na yi shimfida na tada Sallah, duk da na ganshi a zaune dirshan a bakin gadon.
Na idar ya kalle ni ya ce "Na ce kada ki zo, amma saboda gardamarki sai da kika zo ko?"
Ban kula shi ba illah iyaka na kafe shi da kallo mai tsananin gaske.
"Tashi mu tafi".
Ya fa'da da sigar umarni.
Na mike shima ya mike.
Ido cikin ido na ce "Ba inda zani kwana zan yi"
"Kinsan Allah! Ba zaki kwana ba, akan me haka kawai ki baro dakinki ki ce zaki zo nan ki kwana?"
"Ina da abin yi ne, kuka zan yi a jikinta, idan na kammala gobe zan dawo".
"Saurara! Bana son shirmen banza kin ji".
Dai dai nan Sakina ta shigo ta same mu a tsaye.
Ta ce "A a ya haka kun yi cirko cirko tamkar zakaru".
Ban amsa ta ba na ce masa "Idan zaka tafi yi tafiyarka, amma ba inda zani".
Ya kalli Sakina ya ce "yanzu a gabanki take mini wannan wula'kancin amma kin kasa tsawatar mata?"
Kafin ta bashi masa na yi fit na ce "Idan ta ce na bika tabbas zan bika sai dai da ikon Ubangiji sai ka ha'du da bacin rai a hanya".
Nan da nan ya ce "Shikenan sai ki zauna ki kwanan amma ki sani tilas kika mini domin kuwa na sani tunda kika mini baki lah shakka sai na hadu da tsautsayi. Gobe zan dawo na dauke ki. Aniyar moda kuma tabi randa"
Ya fice da sauri.
Yayin da Sakina ta kyal-kyale da dariya tana cewa Guduyon Gudale sha

42 / 61