Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   30 / 61

87K to 90K   out of 180.1K words

wanka bai yi ba domin jallabiya ce a jikinsa idonsa a jirkice tabbacin ya afa 'kwayar. Na ce "Yaya Gudale amma ka ce mini ba zaka sake sha ba fa"
Ya bagarar da maganata ta hanyar cewa "Wai baku fa'dawa Abban likitan ya ce zaki iya yin 'yan harkokinki cikin lura ba?"
Na ce "An fa'da masa! Ya sani".
Ya ce "To sai yaushe ya ce zaki dawo?"
Na girgiza kai na ce "A a ban sani ba gaskiya".
Ya jijjiga kai ya tashi bai ce komai ba.
Da kansa ya shiga wajen Umma ya debo abinci ya dawo.
Yana ci yana maganganun tsageranci. Wai shi ya gaji da wannan kasafin, haka kawai a dauko masa matarsa babu iznininsa, sannan ta samu sau'ki an ki mayar da ita, dan kawai gadarar auren ha'di ne. Ya tabbatar da 'yar wani wajen ne da ba'a yi masa hakan ba.
Na yi shiru domin dai bani da bakin magana! Mussaman da nasan yana cikin yanayin da zai iya yin komai.
Sai da ya tabbatar Abba ya kammala karya wa sannan ya fita.

*Falon Abba*

Bayan sun gaisa suka yi shiru na tsawon lokaci.
Gudale ya katse shirun da cewa "Abba Halimatu ta samu sau'ki sosai".
"Eh na sani Sadik" ya amsa masa a takaice.
"Ya yi shiru. Can ya ce "To yaushe zata koma?"
"Sai ta 'kara warwarewa"
Daga hakan ya kame bakinsa ya tsuke.
A sanyaye ya ce "To" ba dan ya so ba".
Ya tashi ya fice ba tare da ya sake cewa uffan ba.
Yayin da Abba ya bishi da ido yana ayyana abubuwa masu yawa a ransa.
Abubuwan da ya ji da kunnensa Sadik din yana fa'da zai yi hukunci a kansu.

***
A kasalance ya dawo dakina ya zauna gefen gadon yana ta 'kunci.
Bai bu'da mini ba, nima kuma ban tambaya ba, domin na da'de da fahimtar idan yana cikin wannan yanayin, bai cika son ma na yi masa magana ba.
Bare kuma yanzu ya ha'du da bacin rai.
Ya gama zamansa tsawon lokaci ya fita ba tare da ya sake yin magana ba.
Har karfe biyar ina ta zuba idon ganinsa amma shiru, sai dai na sani yana can yana barci tunda ya sha abun da dole sai ya yi wannan barcin na asara.
Bai zo ba sai washagari. Wajen Umma ya karya a gurguje ya shigo muka gaisa a dalilin ya yi latti.
Da daddare da ya shigo mini! Ya kaikai ce ido ya ce "Ki dinga 'kwarara jikinki ko dattijon nan zai gane kin warke".
A hankali na ce "Ai yanzu kowa ya kalle ni yasan na samu lafiya tunda an kiyaye ka'idojin da aka gindaya mini a asibiti".
Ya ce "To idan Abba yana gida ki dinga fita kina zagaya wa, dan gaskiya na gaji".
Na yi shiru, na kasa cewa komai.
Ya zuba mini ido sosai ya ce "Ban gane ba".
A hankali na ce "Na ji".
Ya ce "Amma dai kin sani bana so a mini shiru ko".
Kai tsaye na ce "Yi ha'kuri dan Allah! Na ji zan yi".
Kan dole na tsiri fita idan Abban na gidan, haka idan nasan ya fito zan je mu gaisa.
Da kansa ya ce "ki dinga hutar da kanki Halima! Bar biye son zuciya, daure ki kula da lafiyarki, domin sai da ita kake da amfani".
Kunya ta kama ni da na gane Abba ya fahimci manufar wannan shige da ficen nawa.
A haka aka cinye sati, kafin nan kuma Yaya Sadik ya sake tuntu'bar Abba akan yaushe zan koma tunda na ji sau'ki sosai. Ya sake bashi amsar so yake na warware sosai.
Rannan dai ta 'kure masa ya zo mini a sanyaye.
Ya zuba mini ido tsawon lokaci har sai da kallon ya ratsa mini dukkan jikina, gane hakan da ya yi sai ya yi gyaran murya! Ya ce "Na gaji da zamanki a gidan nan ki fa'dawa Abba da bakinki cewar kin warware".
Zuciyata ta harba na ce "Ba zan iya fa'da masa ba Yaya Sadik! Ka ga kwanaki ma ya gano zaryan da ka ce na dinga yi".
Ya daure fuska sosai ya ce "Ba zaki iya ba kika ce?"
A hankali na ce "Kunya! Da nauyi zan ji, ka fahimce ni dan Allah".
Ya mi'ke tsaye ya ce "Ai shikenan! Tunda dai ban isa na baki umarni ki yi mini biyayya ba. Biyayyar miji kuma wajibi ne matu'kar ba zunubi zai sa ayi ba".
Na kalle shi na ga ransa ya baci matu'ka da gaske.
Da rawar murya na ce "kar ka yi fishi! Ka sani dai kullum farin cikinka shine kan gaba a wajena".
Ya hassalo ya ce "makaryaciyar banza! Ta ina ne kike mutunta farin-cikin nawa? Ai da hakan ne ina ce miki ga yadda zaki yi. To kawai zaki ce mini, amma kin zauna ina fa'da, kina turje wa sannan ki ce mini yayyyen".
Ya marairaice murya yana kwaikwaiyon abin da na ce din.
Daga hakan ya fice ya buga mini 'kofa da tsananin gaske.
Na yi sukuri ina mamakin wannan al'amarin, kawai Gudale ya so yi mini jidali ne. Banda haka ta Yaya zan iya cewa Abba zan koma gidan mijina?
Bai jima da fita ba Sakina ta shigo, da alama daga asibiti ta zarto nan.
Muka gaisa ta kalle ni ta ce "ko wani wajen na yi miki ciwo ne?"
Na girgiza kai na ce "'Kalau nake".
Ta jima tana nazarina ta nisa! Ta ce "ko ba kya jin da'din zaman ne? Na sani akwai takura".
Nan ma na ce "Ni ban takura ba, komai yi mini ake yi".
"To so kike ki koma wajen Na Moriki ya dinga jijjiga ki ko?"
Kunya ta kama ni. Na fara yi mata kuka tare da cewa"Bana son haka Maman Nana".
Ita kuwa ta zarce da cewa "Ai na ganshi a waje yana ta kumfar bakin ya gaji da ri'ke kin da ake yi! Ashe kema kin gajin kenan, bayan dan lafiyarki Abba ya tsare ki".
Na ha'de fuska na ce "To ai ni na ji sau'ki, komai zan iya yi. Gara na koma kar damuwa ta yi masa yawa".
Mamakina mai tsananin gaske ya kama Sakina ta rasa me zata ce mini.
Ta mi'ke tana cewa "Ai sai ki fa'dawa Abba hakan".
Na ru'ko hannunta na ce "Haka ma Yaya Gudale ya ce mini, amma kunya nake ji! Ko zaki taimake ni ki fa'da masa?"
Ta fisge hannunta ta nuna ni da yatsa ta ce "shashar banza marar hankali! Ni kike fa'dawa hakan?
Wlh Halimatu ki dawo hayyacinki wacce irin jarabta ki Gudale ya yi ne hakan? Duk wahalar da kika sha a sanadin rashin sassauta miki da ba ya yi, shine kike son sake komawa ya 'balle aikin da aka yi miki ko? Dama kin bi a hankali kin kula da lafiyarki domin idan baki da mamora jingine ki zai yi ya samo mai mamora".
Hawaye ya balle mini Na ce "Fata dai na gari lamiri ne".
Ta girgiza kai ta juya ta nufi 'kofar fita, ba tare da ta ce komai ba saboda ta fahimci na riga na bari soyayyar Gudale ta rinjayi komai a wajena ta yadda zan iya rufe ido na yi komai.
Har ta bude handle din kofar sai kuma ta dawo.
A sanyaye ta ce "Sadiya! Kar ki sake ki yarda da maganar Gudale da ya ce ki fa'dawa Abba zaki koma 'dakinki. Nima da na fa'da miki gatse ne. Kar ki yarda, ki yarda da hukuncin Abba! Komai zai yi babu son zuciya a lamarinsa. Kar ki yadda ki yi koyi da dabi'un Gudale na rashin kunya da rashin kawaici. Idan har zamansa da ke bai sa ya koyi ha'kurinki da sanyin halinki ba, ashe kuwa bai kamata ke ki yi koyi da munanan dabi'unsa ba".
Jikina ya yi sanyi ina gasgata gaskiya Sakina ta fa'da.
Amma babbar damuwata na tsani fishin Gudale! tayar mini da hankali yake yi. Sannan na tsani na ganshi a cikin damuwa, yanzun nan zan nemi nutsuwata na rasa.
Ni da kaina na sani akwai nauyi sosai na tunkari Abba na ce zan koma dakina. Sai dai ko zan iya jarumtar jure fishin Autan Umma?.
Na sani yanzu haka ma fishin da yake yi da hukuncin Abba ya fara shafa ta. Tunda shi matu'kar zai ce ga yadda za'a yi na ce ba hakan ba, to fa shikenan na ci mutuncinsa na raina shi.
Na kalli Sakina ina hango tarin soyayyata da tausayina a idanuwanta. Na goge hawayen na ce "shikenan ba zan fa'da ba! Amma ki taya ni addu'a kada na kasa jurewar na fa'da din".
Cikin lallashi ta ce "Banda ma baki da wayo, ai ba zai samu damar ce miki ki yi wannan 'danyen aikin ba. Shi ya je ya fa'da mana".
Da sauri na ce "Tun yaushe ya fa'da masa? Kawai Abban ne mun rasa gane manufarsa".
"To ke dai mace ce! Ba ruwan ki, ki zuba ido ki bar Gudale ya yi abin da yaga dama kada ki bashi tallafin ki".
Na ce "To".
Ta jima a dakin, tana ta hilata ta, tare da hannunka mai sandar idan mace ta bari soyayyarta ta rinjayi ta Namiji al'amarin da take fuskanta mai nauyi ne. Baya ga haka ya dinga yin iyashege kala kala kenan.
Da na gaji na ce "Wato dai Maman Nana so kike na daina son Yaya Gudale?"
A hankali ta ce "Ba nufina haka ba! Ina so dai ki danne shi a ranki, ki yi masa biyayya, ki sauke dukkan hakkinsa da ya rataya a kanki, amma matsananciyar soyayyar da kike masa barta a ranki! Yawaita addu'a kada ta zamo miki sanadin wahala a hannunsa".
Na ce "Wato dai gani kike yi ni ne na mutu akansa, shi ba ya sona?"
Nan da nan ta hauro ta hau zabga mini zagi, tana fadin "ki je ki biye masa tunda dai ke ba kya kishin kanki."
Ni kuwa na zum'bura baki ainun duk da nasan bata son na yi mata hakan.
Ta fita ta bar ni ina 'kunkunin ita ma ai tana son mijinta. Akan me zata ce kar na nuna wa mijina soyayya?

Washagari da safe ina ta jiran shigowar Gudale amma shiru, sai jin fitarsa na yi, ba tare da ya shigo mini ba. Haka da rana bai dawo ba.
Na yini cikin zullumi, ban sake shiga damuwa ba sai da daddare ya zo gidan ya ci abinci a wajen Ummansa ya gama abin da zai yi ya fice ba tare da ya neme ni ba. Duk da ina jin yadda ya dinga 'daga murya dan na ji ya zo gidan bu'katar ganina ne baya yi kawai.
Ina jin ya fita hawaye ya balle mini. Na dauki wayata na dinga doka masa 'kira amma bai dauka ba, duk kuwa da na kira ya kai sau goma.
'karshe ma sai ya kashe wayarsa gaba'daya.
Na kwana cikin damuwa. Washagari ban ji zuwansa ba, sai da zai fita ne na jiyo shi, shima na sani dan na gane ya zo ne, ya sanya ya yi abin da zan fahimci ya zo.
Wayarsa na dinga 'kira ba 'kak'kautawa har na gaji dan kaina. Na dinga tambayar kaina me na yi da na cancanci ya yi mini dogon fishi irin haka?.
Sai dare ya waiwaye ni, kafin lokacin kuwa duk na yi zuruzuru.
Ya zauna yana kallona, na gaishe shi a sanyaye ya amsa yana cin magani.
Tsawon dakika talatin kafin ya kalle ni ya ce "Na ga kina ta kiran wayata lafiya?"
Na kasa bashi amsa domin ina bu'de baki kuka zan fashe da shi.
Bansan me ya hana ya yi mini sababin shirun da na yi masa ba.

Ya nisa ya ce "Idan kika kira sau daya, sau biyu, ba zaki gane ina cikin wani uzziri bane? Sai ki ta kirana rututu tamkar 'kina kiran yaroh?"
Hawaye ya balle mini m. Jikinsa ya yi sanyi sosai. Ya ce "menene abin kuka Guduyo?"
Ganin sosai nake kukan mai dauke da ajiyar zuciya, sai ya sassauta ya ce "goge hawayenki ki fa'da mini dalilin wannan kukan.
Na jima kafin kukan ya tsaya mini. Na ce "Me na yi maka da zaka dinga zuwa gidan amma ba zaka dinga shigo wa kana duba lafiyata ba? Sannan na kira ka a waya ba zaka dauka ba, ba kuma zaka biyo ba?"
Ya daure fuska ainun ya ce "Ai nasan kina lafiya ne! Ba zai yiwu na ce ga abin da nake so ki yi mini, ba ki ji nauyi ko kunya ba kika ce baza ki yi ba. Kinga kuwa kar ki saka ran kullum sai na zo ganin ki, tunda na gane ni ka'dai na damu da son kacenwarmu tare".
Da sauri na ce "Amma dai Yaya Sadik kasan idan akwai abin da nake son na kasance da shi a doron 'kasa ai kai ne".
Ya mele baki ya ce "Ni ban sani ba, tunda a baki ne. Da hakan ne har zuciyarki ai da ba sai na ce ki yi wa Abba magana ba. Da kan ki zaki nuna kin warware zaki koma dakinki ki cigaba da neman lahirarki. Amma saboda kin fi son zaman nan din , shiyasa ba kya fitar da na ce ki dinga yi idan Abba na kusa. Kuma shiyasa kika ce ba zaki iya fa'din kin ji sau'ki ba.
Ni kuma abin da baki sani ba, na nemowa kaina mafita. Ba zan sake cewa ki koma ba, na zuba ido a cigaba da nuna mini iyaka akan hakkina. Sai dai ki sani ke za'a janyo wa. Kuma 'kin bani ha'din kai da kika yi da sunan kunya wallahi kwabar ki ce zata yi ruwa. Domin aure zan 'kara, ai idan a waje na nemo auren ba za'a mini abin da ake mini...".
Kafin ya rufe baki na fashe masa da kuka sosai ina cewa "me na yi maka? "
"Menene baki yi ba Guduyo? Yau kwana biyu na ce ki samu Abbanki ki ce kin ji garau, Kika bijire mini".
Cikin kukan na ce "To zan fa'da masa shikenan?"
Ya matso jikina sosai ya ru'ko dukkan hannuwanna ya ce "That's my *Hala*! Yanzu na ji da'di na kuma gane kin damu da damuwata. Yaushe zaki fa'da masa?"
Na ce gobe da safe, tunda yanzu dare ya yi".
"Yauwa na gode miki sosai! Yau zaki kwana cikin yardar Ubangiji tunda na yarda da ke."

Cikin rauni sosai na ce "Ka fasa yin auren?"
Ya sake ri'ke hannuna ya ce "To me zan yi da shi, dama ai zan yi ne dan na samu mai mini biyayya, tunda kin dawo hanya ai tuni na kore tunanin yinsa".
Da'di ya yi matu'kar kama ni, na murmusa sosai. Yayin da ya yi amfani da hakan ya jagwalgala ni son ransa. Gaba'daya a cikin shau'ki muke, ko dan an dauki lokaci mai yawa ba'a hadu bane?.
Da kyar muka rabu, yana ta mitar shi an tauye shi, shi ya ake so ya yi ne?.

Washagari kuwa na murje duk kashedin da Sakina ta yi mini na kada na bawa Gudale tallafi akan hukuncin Abba.
Na same shi da kaina a falonsa. Na yi sa'a Umma ta je ganin likita asibiti.
Bayan mun gaisa sai kuma na kasa cewa komai.
Da kansa ya gane ina da magana ya sassauta ya ce "fa'da mini damuwarki Halimatu na magance miki ita yanzu".
Murya na rawa sosai na ce "Dama dama na warke sosai, kuma zan iya yan harkokina".
Tsawon lokaci kafin Abba ya ce "Ai na sani Halimatu! Sai dai na yi mamaki da kika fi gamsuwa da ra'ayin mijinki akan na ubanki. Na tabbatar Sadik ne ya turo ki, ki yi mini wannan rashin kunyar, dan haka na yafe miki. Amma ki sanar masa cewa Ni da na cuce shi, na bashi ke akan dole ba dan yana so ba. Na fasa auren na ku, ma'ana bana so yaci gaba da wanzu wa, idan har ina da hakkin akan sa sai ya sakar mini ke".
Ai kuwa na dage na fasa masa kuka ina cewa "Kar kashe mini aure Abba dan Allah".
Ya yi shiru yana kallon irin yadda hawaye yake tsere a idona.
Ya sassauta ya ce "Nutsu ki saurare ni da kyau! Sau biyu ina jinsa yana fa'da miki na cuce shi, da na bashi aurenki akan dole. Matu'kar ban karya masa wannan lagwan ba, ba zaki samu lafiya ba, duk sadda kika kuskure sai ya fa'da miki dole aka yi masa ba son ki yake yi ba. Kuma 'karya yake yi, idan kuma gaskiya yake fa'da shikenan zan yi adalci na gaskiya.
Ki yi ha'kuri ki bani dama, sai Sadik ya fahimta zan bashi ke ne akan yana so, amma na gaji da zaman alfarmar da yake yi da ke".
Cikin kuka na ce "Abba! Sai kukan ya sake kwace wa.
Bai katse ni ba, sai da na yi mai isata na yi shiru dan kaina.
Na ce "Abba idan ban koma ba aure zai yi".
Na fa'da murya na rawa.
A kufule ya ce
"Ya jima bai yi ba, ya auro uku rana 'daya Halima! Ina ro'kon ki arziki, ko wannan ce biyayya ta karshe da zaki mini, kar ki bi bayansa ki kunyata ni, ki bari ya gane ke din kina da daraja, dole kuma ya kalli wannan darajar a yayin zaman aurenku. Ina nufin sai ya yarda ba dole na yi masa ba. Idan ba ya son ki, to ya dawo mini da ke salin alin. Ina da wandanda zan bawa su rike mini ke cikin soyayya da mutunci".
Jikina ya yi sanyi 'kalau, kunyar Abba ta kama ni, na yadda ya tabbatar mini na yi masa rashin kunya. Ga kuma ro'kon da ya yi mini kada na kunya ta shi. Amma gaskiyar magana dukkan zuciyata na ga tunanin kada a matsawa Gudale, ya tunzura ya sake ni, na shiga uku.










# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?*
*kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*.
*Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.*
*Sister Zainab 08039315577*.



*SDK*
*57-58*.


Maganganu masu taushi da sanyaya zuciya Abba ya dabaibaye ni da su, har ya samu kaina na gamsu na amince zan yi biyayya na zauna tare da shi! Har zuwa lokacin da komai zai yi masa yadda yake so.
Ya mi'ka hannu ya ce "ki fita harkarsa, ki daina daukar wayarsa bare ya hargitsa miki

30 / 61