Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   52 / 61

153K to 156K   out of 180.1K words

baki isassen ku'din da zaki sayi tufafin da zaki sanya da duk abin da zaki bu'kata?"
Na ce "Eh cikin mamaki.
"To kada ki sake yi mini maganar kayan Baby, domin ya fini, ko ta fini yawan iyaye wanda na bayar ma ai kara na yi musu, buga ki fa'da wa Yaya Abdallah ko Al'amin ko Abbas, ko kuma Ramlatu. Idan gaggawa kike yi marar kunya marar kawaici.
Na yin sakare ina tu'ajjibin Yaya Gudale! Duk yadda nake ganin na karance shi, amma kullum yana sake fahimtar da ni, har yau ban kammala gane shi ba, bare na fahimce shi.
Na ja gauron numfashi sosai.
Na ce "Ai shikenan idan Abban ya zo a na'de shi a zanin ai".
Ya murmusa ya ce "Hmmm maketaciya kawai, waton dai da gaske kike mata biyar zai biyo".
Na kuwa tuntsire da dariya na ce "Ai hakan ne gaskiyar magana.
Ka sani kai ko sai an yi maka bakwai kafin Wakilin ya iso ma".
Ya mak'e kafa'da tare da cewa "Innalallaha ma'assabirin. Aniyar moda ta bi randa".
Ya fice da sauri. Yayin da na daga murya na ce "A dawo lafiya".

*Munubiya*
Ta fito ta ci kwalliya kamar mai zuwa party ba dubiya ba. A hankali take takawa tamkar ta manta tsawon mintinan da ya kwashe yana zaman jiranta a mota.
Da kansa ya dinga kallon agogon wayarsa, yana ta nazarin Guduyo bata ta'ba yi.masa irin wannan yaukin ba. Ya sake tuna wani zuwa da suka yi gidan Sakina, mintina biyu kawai ya yi yana jiranta, ya yi tafiyarsa ya barta. Sai dirban gidan ne ya dawo da ita.
Ya kalli yanzu ya shafe minitna sama da talatin a zaune. Ta kuma fito babu wani alamun ta yi laifi, tamkar dai wani kaskantaccen direba.
Kafin ta iso gare shi, Umma ya hango Umma ta fito.
Gaisuwar da Munu ta yi mata ya yi matu'kar tsayawa Gudale a rai.
Domin cewa "Umma barka da lokaci ya kike?"
Wannan gaisuwar da mafi yawa matasa suke yinta gaskiya raine ne ba ka'dan ba.
Shi a karan kansa baya son wanda ya girma ya ce masa ya kake?
Bare kuma ace matar aurensa ta cewa uwarsa ya kike?
Tabdi jam.
Ransa ya baci sosai.
Ya fito daga motar yayin da ita kuma ta tunkaro shi tana cewa "Har na fito, sai na tuna ban yiwa Maman Amnah sallamah, acan na shantake, kasan idan ina gabanta manta komai nake yi tsabar yadda take da kirki da shiga rai".
Ai kuwa ha'kurinsa ya kare ya damk'e ta sosai yana fa'din "I hate you Munubiya."
Ya girgiza ta sosai ya saketa. Ta hanyar tunkuda ta gefe guda.
Ta kafe shi da ido ta ce "Zaka San ka ci zarafin jami'ar kare hakkin d'an Adam"
Umma da take gefe ta ce "Ku bi a sannu dai".
Takaicinsa ya sake girmama.
Ya fito ya fice kofar gida.
Yayin da Munu ta ja uban tsaki ta wuce ciki a fusace ainun.

Bansan wainar da suke toya wa ba, a tsakanin Umma da surukurta da kuma Gudalenta, amma dai na fahimci akwai jikakkiya a tsakaninsu da suke ta faman nukunukunta.
Ranar 25 ga wata December aka sake Ciro mini kyakkawan jaririna sai dai dan tsurut ne ba auki irin Babansa.
Sosai Gudale ya yi murna. Sai dai duk yadda yake zumudi bai iya daukar yaron ba. Da gaske yake yi bai iya daukar jarirai ba.
Da murmushi akan fuskarsa ya ce "Guduyo duniya! Waton dai yanzu kika yi niyya".
Na murmusa bance komai ba.
A take ya yi masa huduba da Abubakar sunan Abba, kuma sunansa".
Karin farko da na yi jego Yaya Gudale bai bata mini Rai tun a asibiti ba.
Haka nan kulawa da tattali mun samu tamkar ba Gudale ba.
Dan kuwa bai yarda ya koma wajen Munu gaba'daya ba.
Kwanaki biyun nan haka yake yi, idan ranar girkina ne, dakinsa zai shige ya yi kwanciyarsa.
Da na yi masa magana, ya ce haka ya ke so, hakan kuma yaga dama.
Da kansa ya zab'awa yaro inkiyar Aman.
Wani irin gata da tattali yake yiwa yaron, amma ni ban ji ya dara su Amnah a zuciyata ba. Mussaman ma Afra da nake ganin ko yara nawa zan haifa zata cigaba da zama mowar y'ay'a.
Duk da dai ban ta'ba bari hakan ya bayyana ba, ina kuma yawaita addu'a kada na fito da soyayyarta fili ta yadda zan janyo mata gaba a tsakanin yan'uwanta.
Domin kalubalen da iyaye suke haifarwa a tsakanin y'ay'ansu ba ka'dan bane. Am sani dole akwai Wanda zaki fi so a cikin yaranki. Amma kada ki fifita shi akan yan'uwansa, kada ki daukaki lamarinsa sama da nasu, kada kuma ya zama su bakya shawara da su ta yadda kowa zai fahimci an kin fi son wance ko wane, abin kaicon kuma sai kiga ko haihuwa Suka fara yi anfi son Yayan wanda shine mowar.
Wannan ba k'aramar fitina take haifarwa da kiyayya ba.
Allah dai ya shiryemu ya sa mu fi karfin sake saken zuciya da kuma sharrin shaidan.

Watan Aman uku ya yi kubibi da shi duk da dai ba wani girma ya yi ba, yanayinsu daya da Amnah domin itama haka take har yanzu sai dai doguwa ce har yau bata canja ba, komai na Sakina shine a jikinta, yayin da Aman ya ke kama da Gudale sosai. Afra ce ta yi ruwa biyu, idan muna tare ace kamata ta yi, idan tana tare da Gudale ace da shi tafi kama.
Daidai lokacin ma fara.kosawa da jarabarsa akan Aman, domin duk ranar da na kuskura ya ganshi da rigar da ya sanshi da ita to ga ba lafiya, shi kullum sabuwar riga ake bude masa.
Tun ina ganin zai gaji ya daina har na ha'kura na gasgata ba zai gaji ba.
Da ya ji kukansa ko yana sama zan ganshi a sukwane.
Idan ina yi masa mitar a goyon su Afrah bai yi wanann zumudin ba.
Yana bani amsa da cewa "Ai shi ban sha wahalar laulayin cikinsa sosai ba, shiyasa nake taya ki raino, amma cikin Afrah ai ba karamin azaba kika roka mini ba. "
Na ce "A a Yaya Gudale to ita kuma Amnah da baka yi laulayin ba gaba'daya fa?"
Sai ya waske da fa'din "ai ita yar fari ce wannan kuwa Abba ne"
Tun ina yi masa kawaici, ina biye masa a rainon Aman har na fara gundura, muka fara samun sabani sosai.
Komai na yi ban iya ba. Ba dama yaron ya yi kuka zai fara rikecewa shima, yana fa'din da gayya na ki rarrashinsa so nake kawai na bata masa rai.
Abin ya fara damuna domin na riga da na fahimci so yake ya lalata mini yaro kamar yadda tasa uwar ta yi masa gatan da babu kwaba a cikinsa.
Ko Amnah na goyawa yaron idan ya gani babu lafiya ya dinga sababin za'a kayar masa da yaro, wanne shashanci ne hakan zan bawa yar tatsittsiyar yarinya goyon Abbansa?
Jiki na rawa zai karbe shi, yana shafe shi, yana duddubawa ko an matse shi.
Na fara gajiya domin na fara kai wa gejin ha'kurina.
A daddafe yaron ya kai watanni takwas, gatan da yake ga ni a wajen Ubansa ya wuce duk tunanin me tunani. Domin kuwa komai na yaron mai girmane a wajensa.
Har ta kai da kansa yake yi masa wanka bisa dalilin idan ni nake yi masa yana kuka, to ya fahimci sabulu nake shaka masa.
Dan haka ya hutar da ni yi masa wanka.
Bansan ya iya harkar raino ba sai akan Aman.
Sai dai wani Ikon Allah duk yadda Gudale yake yi masa, shima kulaficina ne da shi.

Daidai lokacin kuma Munubiya ta fara gazawa da rashin samun dama a wajena. Ta fara yi mini barazanar ko ta tsiya tsiya ce sai mun yi
soyayya ita Bata tana son abu bata same shi ba, ta fahimci bansan alheri da rarrashi ba.
Kuskuren farko da ya faru shine ban ta'ba fa'dawa Yaya Gudale matsalata da Munu da bakina ba, sai dai idan ta yi katobara akaina a gabansa ya taka mata burki.
Amma ni ban ta'ba nuna masa akwai boyayyen abin da take nufina da shi ba.
Al'amarin da ya fara rikita komai.
Domin watan Aman goma Sha daya muka yi wani kazamin rikici.
Da daddare wajen goma da rabi na dare.
Ba zato na fito daga wanka daure da towel a lokacin kuma yana gida yana dakinsa na wajena.
Kawai sai ganin Munubiya na yi ta fado dakina cikin wata irin rigar barci fan darinka tsirara.
Ba wata wata ta shammace ni ta rungume ni tsam tsam. Na dinga kicin kicin k'watar kaina a dalilin ban son tawul din jikina ya subuce mini.
Ilahirin jikina sai rawa yake yi, zuciyata sai bugawa take yi fiye da k'ima.
Na fara kai mata mari ina zaginta.
Amma ko dar ita sai kokarin kai wa sassan jikina cafka take yi, ni sai na ga tamkar a buge take.
Kamar jifa sai gashi a bakin kofar dakin.
Ya tsaya cak yana kallonmu, amma dukkan fishi da bala'in duniya duk ya tattaro ya yabawa fuskarsa.
Yayin da Munu take fa'din kin fi shi komai.
Kin fiye mini shi.

*Ko kunsan hakan yana faruwa in reality?*
*Ko kunsan ana lalata yanmata ta wannan hanyar mussaman a makaratu?*
*Mu yawaita addu'a, mu yawaita istigifari*.
*Allah ya tsare mu, ya tsare mana zuri'a*.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Ummu Muhammad collections*
*Tana sayar da dukkan nau'in sutura masu kyau zababbu kuma masu sau'kin farashi*
*Tana sayar da takalma da jaka masu kyau*
*Tana ha'da lefe*
*Tana ha'da kayan haihuwa*
*Tana sayar da Data*
*Tana yin adashe, Kuma fasihiyar Tela ce*
*Tuntube ta a wannan lambar 08063358662*
*Siyan na gari aka ce maida ku'di gida"


*SDK*
*91&92*
Tashin hankali ba'a saka masa rana.
Domin wani irin shak'a Gudale ya yiwa Munu.
Amma ita kuma tana ri'ke da ni gam gam.
Dan haka ya ha'da mu tare ya dinga kai mana bugu ta ko ina.
Ba k'aramin gigita ta ya yi ba kafin ta sake ni.
Tawul d'ina ya fa'di, na yi tsirara.
Sakwan kusan biyar ban iya sunkuyawa na dauko tawul din ba, tsabar yadda na muzanta.
Tozarcin duniya ya lullube ni, wani irin kukan ba'kin ciki nake yi mai girgiza zuciya sosai.
Na kalli yadda ya yiwa Munu jina-jina.
Yayin da bakinta bai mutu ba.
Fa'di take "matsalon wofi. Baka iya komai ba sai k'ifadi. Bana sonka, na fa'da matarka n nake so, kaddara ce ta baka ita, bata dace da d'an tsurut irin ka ba".
Ni kaina ba k'aramar wahalar gaske na sha ba, bare ita da ya zage dukkan karfinsa ya jibge ta.
A take kuma ya rangad'a mata saki.
Duk yadda take jin jiki sai ta k'yal-k'yale da dariya ta ce "Saki daya na ragwaye ne.
Ya tunzura ya ce "Na kara miki".
Bakinta na jini ta ce "Ai idan baka cike ta ukun ba, ya tabbata raba mana kwana kake da uwarka, ai ni abin da nake yi yafi naku tsabta, ban ta'ba cin karo da uwar da take kishin d'anta irin taka ba".
Ya kuwa sake yin kanta yana kai mata duka kan jiki, kan k'arfi da dukkan iyawarsa.
Yana fa'din "Na cike Miki, tanbadaddiya tsinanniyar Allah da mala'ika Jibrilu".
Da abin ya ta'azzara na ji tsoron kada ka ya yi kisan kai na kokarta na sanya riga, na saka dukkan karfina na ri'ke shi, yayin da nima ya dinga kai mini duka muryarsa a zafafe tamkar ya ha'diye zuciya yake cewa "Ni Kika yiwa hakan Guduyo?"
Na hau barin baki, ai kuwa ya hankada ni, na kifa akan gado.
Ya fita, na bishi da sauri domin na firgita da yanayinsa sosai.
Wayar Sakina na kira, na fa'da komai da kuma halin da Munubiya take ciki.
Na zauna a falo ina addu'ar Allah yasa kada Munu ta mutu mu shiga uku.
Ba a Jima ba sai ga su Yaya Al'amin da Yaya Abbas, tare da Sakina.
Cikin hikima ta gyara mata jiki. Duk jinin da ya bata mata da jiki, wanda kuma zai ja hankalin mutane sai da Sakina ta goge shi.
Ta bata taimakon gaggawa ta farfado.
Ta dinga sakin maganganu babu jin nauyi bar kunya.
Tashin hankalin da muka ga ni ba dan ka'dan bane.
Domin kuwa washagari sassafe sai ga jamian human Rights sun kawo sammaci.
Abin takaici kuma har da Umma suka gaiyata.
Muna kallo suka tafi da Umma da Gudalenta.
Bamu san ahalin su Munubiya kara da kiyashi ne daukar marar sani. Domin kuwa duk amincin dake tsakanin Umma da Momi a wannan rikicin bai yi tasiri ba.
Momi mahaifiayar Munu ta rufe ido ta manta duk sabo da kawancen da yake tsakaninsu. Suka daure su, domin sun riga sun shirya wa rikicin sosai, sannan sun saki makudan Ku'di Dan abi kadin cin zarafin da aka yiwa diyarta.
Bata bada aurenta dan bata son yarta ko dan ta gaji da ita ba.
Ba kuma inda aka ce a kama mace a daketa tamkar jaka.
Hukumomi daban daban ta dinga gurfanar da Umma da Gudalenta.
Har Amenesty sai da suka shiga case din.
Duk yadda Umma take ganin suna da kudi, a wannan al'amarin bai yi tasiri ba.
Wula'kanci sosai uwar munubiya ta jagoranci aka yiwa su Umma. Wannan shi aka cewa *SABO DA KAZA*.
Kwanakinsu shida sannan aka sako su bayan Antin Zaria da Yaya Abdallah sun shiga sun fita, an kashe mahaukatan kuda'de.
Kuka ba irin wanda Umma bata yi shi ba.
Dan kuma rashin tsoron Allah sai cewa take yi "Ta tabbatar wannan abin aikin magauta ne".
Shi kuma wata irin gaba ya dauka da ni mai tsananin gaske.
Idan zan kwana ina yi masa magana ba zai ce mini kanzil ba.
Gaba'daya ya firgice sai ramewa yake yi a tsaye.
Mun kai wata a hakan na rasa inda zan tsoma raina domin hukuncin ya yi mini tsananin gaske.
Da k'yar Sakina ta sasantamu, bayan ta shawo kansa ya fa'da mata ai nima na so ha'intarsa ne, tunda ban ta'ba fada masa tana mini hakan ba, bayan maganganun da bai yi zaton da gaske take yi ba. Da ta dinga fa'da a gabansa yana taka mata burki
Tana tafiya ya kalli idona ya ce "Tun a wananan ranar na tsane ki.
Idan na kalle ki, sai na tuna yadda na ganku ke da kawar shedanar taki.
Wai da idona na ga wata tana kai wa abin da na girma da sonsu cafka?
Ai na sani ba wannan ne karon farko da ta yi miki hakan ba.
Me yasa baki fa'da mini ba?"
Hawaye ya goce mini na ce "Baka gasgata ni ba kenan? Akan idonka na girma amma baka fahimci abin da zan yi da wanda ba zan iya yinsa ba?"
Ya ce "Dan adam kuma akwai abin da ya kai shi saurin canjawa da butulci ne?"
Haushi mai tsananin gaske ya turnike ni kwarai da gaske.
Na mi'ke na ce "Allah ne shaidar komai".
Na koma daki na zauna ina fashewa da kuka.
Duk hakuri da kawaicin da na wanzu ina yiwa Yaya Gudale a zamantakewarmu ashe duk baya ga ni?
Idan wani ne ya ce mini Yaya Gudale zai zarge ni zan karyata.
Domin ko shi da nake ta zaman ha'kuri da shi, matu'kar ba ganinsa na yi turmi da tabarya ba, ba zan ta'ba zarginsa ba. Kome zan ga ni, kome za'a ce akansa kuwa.
Tun a lokacin zuciyata ta yi wani nauyi, da rauni a dalilin gajiya da halayyarsa da kuma takaicin yadda ban aminta a idonsa ba.
Gaba'daya zaman namu babu da'di a dalilin ya ja ya dake ba zai saurare ni ba.
Na rasa gane inda ya ajiye ni.
Domin dai ita Munubiya ya skaeta, amma Ni m bai sake ni ba sai faman gana mini azaba yake yi.
Kwana biyu bani da gas, na fa'da ya kai sau uku.
Amma ta tafasa bai ce ba.
Idan da wutar NEPA zan yi maza maza na mana girki ni da yarana, domin na sha ajiyemasa ko kallon abinci ba ya yi bare ya bu'de. Idan kuwa babu sai dai na zuba ido.
Sai da aka yi kwana biyar sannan ya yi refiling din.
Aman kawai ya ke kulawa amma ni da Afrah tamkar ya
Wurgar da mu.
Rannan ya dawo ya tarar da Aman babu wando, Pampers na cire masa, yaron ya fito falo a guje tunda shekararsa guda kenan.
Tun kuma Yana da watanni takwas ya fara tafiya, yanzu tafiyar ta yi kwari.
Aikuwa sai ganinsa na yi sabe da shi a zuciye.
Yana zuwa sai kawai ya dauke ni da wani irin mari! Afrah ta yi maza ta ce "Lah Ba kyau duka a face inji Islamic teacher din mu fa. Ta kalli yadda hawaye ya goce mini ta ce "Kawai ki fa'dawa Sister dinki ta zo ta rama miki.
Tana nufin Sakina kenan. Domin duk a zatonsu yayata ce, ba tasa ba.
Ya kuwa damk'ota itama ya faffala mata marin.
Ya fice da shi a kafa'darsa.
Tun a wananan ranar na kudire kuwa na yaye shi.
Washagari kamar almara sai ga Sakina da kawarta, wai duba yaron abokiyar aikinsu Suka je bayan layinmu, shine ta biyota ta gaida Umma.
Ta kasa samun nutsuwa da yadda ta gan ni.
Bayan kawar ta tafi ta dawo ta tisa ni a gaba.
Na kwashe komai ina kuka na fa'da mata.
Ta jima bata ce komai ba.
Kafin ta ce "Da zaki iya da kin bar wananan tak'adirin Halimatu. Farin cikinki bashi da yawa a gidansa.
Ki yi ha'kuri, ki daina bari son zuciyarki yana rinjayar ki akan sha'aninsa."
Hawaye ya balle mini.
Ta mi'ke ta ce "ki tsananta addu'ar zabin Allah a zamanku. Duk yadda nake son taimakonki sai da hadin kanki na dari bisa dari.
Amma ki sani fa har ku tsufa a hakan zaki kasance a hannunsa. Tunda ya riga ya fahimtar da ke shi din dabiunsa irin na *Sabo da kaza* ne ke kuma kin nuna masa *Damo* ce ke akan dabiun nasa".
Ta mi'ke har ta kai bakin kofar dakin sai ta tsaya ta juyo ta ce "Ko zaki zo mu tafi?"
Na girgiza kai na ce "Abba! Ya ce "Na yi ha'kuri".
Ta dawo ta ci d'amara da mayafinta ta ce "Idan kika kuma sako mini maganar Abba akan al'amarinki sai na ci gidanku.
Marar hankali! Shasha kawai. Ke bari ki ji Abba ba dan ya haife ni ba. Amma adali ne, da ace tun waccan marin kin bani ha'din kai da bai sake d'aga miki hannu ba.
Amma dake kin mayar da kanki banza ina tabbatar miki Namoriki sai ya siyo dorina saboda ke."
Ta tafi ta bar ni.
Tun ranar na kasa samun lambobin Sakina idan zan kwana ina kira ba zan sameta ba. Da na duba ta a WhatsApp sai ma fahimci ta yi blocking dina ne.
Bansan me ta cewa Antin Zaria ba, tunda har Afrah ta fa'da mata Dady ya mare ni jini ya fito a hancina. Sai kawai ganin Junaid muka yi ya iso Kano da sassafe tunda jirgin safe ya shigo.
Shine babban d'an Antin Zaria, aure ma yake shirin yi a lokacin. Wai Mamanshi ta turo ya tafi mata da Amnah. Sakina kuma ta zo da kanta

52 / 61