Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   56 / 61

165K to 168K   out of 180.1K words

rikita kwanyar mai sauraronta".
Na kashe wayar ina cewa "Ashe zance ka zo".
Sakina da take zaune kusa da ni. Ta ce "daukar ki ya zo yi?"
Na girgiza kai tare da cewa "Zance ya zo wai".
Ta kyal-kyale da dariya tana cewa "Allah ka shirya mini autan Umma. Sai ki shigo da shi falon Baban Nana".
Hakan kuwa ya shigo cikin kwalliya ta sosai, na kalle shi Ina ganin tamkar saurayin ne na gaske.
Domin bashi da wani girma, mafi yawa gani ake Amnah kanwarsa ce tunda tsayi ne da ita.
Na koma wajen Sakina tamkar zan dauko masa wani abu.
Ya jima yana zaune yayin da ni kuma na biye Sakina muna dariyarsa.
Mintina goma sha biyar sai ga kiransa ya sake shigowa wayata.
Na dauka ya ce "Ranki ya da'de ina ta jiran ki, bani da jarumta akan al'amarinki fa."
Na kashe wayar na fita.
Na same shi ya harde kafa daya kan daya yana kallon talabijin.
Na zauna nesa da shi sosai.
Na gaishe shi da kyar.
Shi kuma ya amsa da sakakkiyar fuska.
Ya kaikaice zama ya ce "Kasaitar Ubangiji yawa ne da ita Guduyo. Kullum na zauna sai na yi ta lalubo dalilin da ya saka nake ganin girman gidanmu idan ba kya cikinsa. Bana fahimtar rashin kowa a gidan, amma ke ko zarce lokacin dawowa daga B.U.K. Kika yi sai na ji damuwa mai yawa.
Ashe kin shiga zuciyata kin yi kane kane.
Wani irin so nake yi miki mai wuyar samuwa ko a duniyar littafan tatsuniya".
Na ta'be baki tabbacin ban gamsu ba.
Ya mak'e kafa'da ya ce "kin san am always positive. Ba sai kin gasgata ni ba, domin ni na gamsu ke ce duniyata.
Ina tashi daga nan ma wajen Baban Yara zanje na tsugunna na yi masa godiyar bani ke da aka yi.
Abba ya so ya ganni a gurfane a gabansa ina yin godiyar bani ke da ya yi.
To yanzu zanje na yi masa godiyar a gaban wakilinsa."
Na tura baki gaba na ce "Baka tambayi izinina ba, ka dauko mini mota. Ina ce tun jiya ka bani kyautar ta?"
Ina rufe baki ya zabura ya fita daga yanayin salamar da ya yab'a a fuskarsa.
Ya dawo a Gudalen Umma.
Ya nuna ni da yatsa ya ce "kin ci uwar k'arya kin kwana da yunwa Guduyo. Ina ce baki yarda kin yi mini abin da nake so ba?
Ai cewa na yi idan kika yarda zan baki, kika k'i yarda din, sai kuma dan ke ce uwar son banza sai ki ce kin ci kyauta! To ki sake lale".
Na mike na daure fuska na ce "To shikenan".
Na fara tafiya da nufin barinsa.
Da sauri ya ce "ki dawo Halah! Barina a wajen nan zai zama sanadin da ba zaki rabauta ba."
Na dawo ina cin magani.
Ya sassauta tamkar ba Tak'adiri Gudale ba.
Ya ce "kin amince yau komai zai dai-daita, kin amince komai zai wuce, ya zama kamar ba'a yi ba?"
Na ki tamka masa, ya iso kusa da ni ya ru'ko hannuna ya ce "pls mana Halah! Ki ji tausayin dan-uwanki. Nine fa Baban Afrah! Na ci arzikin kasancewata ubanta".
Na ce "Kai da baka so ta ba, me yasa zaka nemi kamun k'afa da ita?"
Ya ce "Hmm! Ba zaki gane bane, amma Wallahi yarinyar ta shiga raina, hotunan ta sun fi na kowa yawa a wayata.
Ba zamu tsaya cecekuce da tone tone ba.
A mini ha'kuri yanzu. Ki huce, na yi al'kawari a gaban Baban Gusau ba cin mutunci a tsakaninmu"
Na yi shiru.
Ya koma ya zauna yana lalubo wanccan yanayin, ya kashe murya ya ce "Zan tafi yan mata sai yaushe kuma?"
Na kyal-kyale da dariya domin kwarai da gaske
ya dage shi ala dole hira yake yi.
Na ce "kana da mata ne?"
Ya ce "Ina da mata da yara uku.
Amma matu'kar kika bani hadin kai daga kanki na rufe kofa. Wannan al'kawari ne na yi miki shi, da zan dauwama ina rokon Allah ya bani ikon cika wa."
Dadi ya ratsa ni, amma ban bari ya bayyana ba.
Na ce " idan kana sona, ka je ka saketa sai ka zo mu fahimci juna".
Ya zabura ya mike ya na cewa "wuyar sha'aninki ya kai k'urewa uwar Amnah. Ke an fasa zancen ma, zo mu tafi gida haba. Ina dalilin ina ta rarrashi kina sake nausa wa jeji?".
Dariya ta so subuce mini. Na juya na yi wajen Sakina.
Kememe ya ki shiga wajenta ya gaishe ta.
Wai sai wani lokacin.
Kuma a hakan yake so ta bani ha'kuri.
Ya kuma za'bi gidanta amma ya kasa gaishe ta. Kai zuciyar Gudale sai Àllah.
A hanya muna tafe sai cewa yake yi "Ba kyau ka bawa wasu damar daza su shigo matsalar gidanka.
Ya sassauta ya ce "kinsan dai abin da kike yi mini haram ne ko?
Zan miki albishir matu'kar kika mance komai mussaman a yau din nan to zaki rabauta domin duk bacin rai da kika saka ni, to kuwa na yafe miki.
Sannan duk al'kawarin abubuwa da na ambata zan miki suma sun zama wajabat, har motar nan kuwa".
Na cuno baki na ce "Bana so."
"Nifa tunda ka mare ni akan yaron da na haife shi cikin wahala ka fita a raina.
Tunda shi kake so, kake kuma muradi to ka je na bar maka shi.
A hargitse ya ce "Na fara gajiya da gaske Guduyo. Ko dai ki ha'kura cikin girma da arziki, ko kuma ki ha'kura da tsiya tsiya tunda baki san rarrashi da ban ha'kuri ba.
Na yi murmushi na ce "Zan ga yadda za'a yi kuwa".
Ya hassalo ya ce "Guduyo me yasa sai kin kure ni ne?
Idan ina kaunar ki ga raunina shega nake.
Amma tunda kika hade da Sakina komai ma zaki saka na yi.
Aman din da kike ta fishi akansa, Wallahi tunda kika gudu ban sake waiwaiyarsa ba. Komin kukansa bani da sukunin rarrashinsa. Nan duniya Umma ce kawai ta fiki a wajena."
Na ce "Sakina fa?"
Ya girgiza kai ya ce "so na kauna na jini tabbas bani da kamar Sakina, ta zarce komai da kowa a wajena. Kar ki yi mamakin kuma Al'amin ne zai biyo mata baya a wannan fagen sannan ku members ku biyo baya.
Amma a so irin na bege, na burgewa, na jiyar da juna da'di, ba wacce zata kai ki, balle ta fiki".
Murmushi ya subuce mini.
Hakan da ya gani ya sanya ya ce "Dan Allah Guduyo mu kwanta tare kin ji?"
"Ba zan kwanta da kai ba, idan na yi ciki kuma ka dawo da wula'kancinka, bare kuma ace na haifo mace?"
Da sauri ya ce "Darajar kura'ani ba wannan maganar a zuciyata.
Ni yanzu bawa ne mai godiya sosai.
Na gamsu Ubangiji ya bani damammaki a rayuwa amma na kangare masa. Na shiga jirgin tuba da nutsuwa.
Ina tabbatar miki a yanzu ba abin da nake so irin na ga na fara yi miki laulayin ciki. Na k'osa na gan ki da Baby."
Na ce "Hakane! Amma ban yarda ba, kaga har yau Umma bata sona da kai, tunda k'ememe ta ki mayar da ni dakina. Ina kan bakana har sai ka kawota gabana ta roki arzikin na zauna da kai lafiya, ta kuma sanya albarka a zaman namu".
Na dago na kalle shi yana mini wani irin lalataccen kallo ya tumbatsa tamkar zai fashe.
Ya ce "Wallahi Tallahi kin yi ka'dan ki ce na kawo Ummah gabanki! Har abada tafi karfin hakan, ba kuma zata yi arahar da zata zama hakan ba. Kar ki yaudari kanki Guduyo. Umma uwata ce da ban ha'da darajarta da komai ba. Kar ki nemi wuce gona da iri kin ji. Kin ce sai ta je Gusau zaki dawo, ta je. Kin ce sai ita zata dawo mini da ke, ta bawa Sakina umarnin ta dawo da ke. Yanzu kuma ki ce sai ta zo gabanki ta ro'ki arzikin ki zauna lafiya da ni? Tabdi jam. Ashe kuwa baki fahimci rayuwar nan ba. Ba zata zo gabanki da nufin durkusawa ba, har abada Guduyo.
Amma na yarda zamu je gabanta ta sanya mana albarka ki ji da kunnenki. Yau ne rana ta karshe da zaki kafa mini hujja da Umma. Ki bari, bana so, ba sa'ar ki ba ce, ba kuma zan dauki wannan iyashegen ba, if not zamu samu mummunan rikici"
Ya fa'da a matu'kar kufule.
Jikina ya yi sanyi a dalilin tsananin fishin da na gani a tare da shi.
Tsawon lokacin mun yi jugum jugum tamkar masu zaman makoki.
Shine ya fara hucewa ya ce "Ni na manta wannan maganar na shafe ta.
Yayin da na daure fuska na turo baki sosai ina kunkinin ni ban shafe ta ba.
Ya kasa daure wa da shiruna ya ce
"Pls Guduyo ki manta komai, kinsan dai na yi k'ok'ari fa, gaba'daya na sauke komai, raunina ya gama bayyana a gabanki, to ki huce hakanan".
Har muka isa gida rarrashi yake yi da campaign.
Fadi yake "idan da abin da kike so ko sha'awa fa'da mini sai mu biya na siya miki."
Yayin da na ce "Bana son komai."
Na shammace shi na shige dakina na rufe kofa.
Washagari da safe na fito da nufin yi masa karin kumallo.
Ina cikin soya masa dankali, ya fito, ya tsaya a bakin kicin din.
Wani irin kallo yake mini na takaici tsantsa.
A hassale ya ce "Mandiya hamshak'iya, wai ke kafaffiyar yarinya ko?
To ki je ki jika abinki ki sha. Bazan sake cewa ina so ba. Bare ki yi ta tozarta ni, komai mutum ya yi dan kansa. Zan zuba miki ido komai zaki yi, ki yi, amma Allah na ganin komai."
Na juyo ba alamun damuwa a tare da ni. Dan na sake k'ular da shi sai na murmusa na ce "Na kammala abin karin kumallo kada ka fita baka karya ba".
Ya kuwa tunzura ainun ya ce "Idan kika kuma bani abinci sai na kwashe miki karama Halimatu! Kinsan dai bakin miji tamkar na mahaifi ne.
Ki bari yunwa ta kassara ni ai baki da asara".
Ya juya fuu ya fice da sauri.
Wajen Umma ya nufa ya tarar da ita zaune da Antin Zaria suna hira.
Ya gaishe su a sanyaye, tare da cewa har kun tashi ne?"
Anti Zaria ta bashi amsa da cewa "Ai da yau zamu wuce to an sami matsala bamu samu tickets ba. Sai jibi kuma."
Umma ta kafe shi da ido tana nazarin irin ramewar da yake sake yi a kullum.
Ta kasa ha'kuri ta ce "Wai menene matsalarka ne?
Ina ce tunda ta dawo kuma shikenan sai ka sauke masifar da ka sanya wa zuciyarka hakanan."
Ya numfasa cikin kunya da nauyi ya ce "Umma so nake ki bani dama na kawo ta gabanki, ki sanya mana albarka, ki nuna kina kaunar zaman ta cikin ahalinki, ki kuma sassauta kamar yadda muka yi da ke shekaranjiya."
A hassale ta ce "Wato sai anyi hakan da ta kwantar maka da hankali?
Wannan yarinyar ta zame mini kadangaren bakin tulu. Ban da kaddara me za'a yi da haularsu?"
Ya marairaice ya ce "Ki yi ha'kuri Umma! Ina sake baki ha'kuri kaddara ce ta ha'damu, ita ce uwarsu Aman. Ki taimke ni ki sassauta, ki karbeta Ubangiji zai baki ladan masu ha'kuri. Ke din farar uwa ce Umma. Ba abin da baki yi mini ba, ba gatan da baki yi mini ba, duk ba wanda na manta."
Ya durkushe gabanta guiwa biyu ya ce "Sake nuna mini soyayya ta hanyar yin ha'kuri da al'amarin Guduyo. Ina miki al'kawarin a tsaye nake akan k'afata, bata isa ta ta'ba mini ke na barta ba, bata isa ta wula'kanta ki ta kwashe k'alau a hannuna ba.
Ta sani ke ce abu mafi daraja a wajena. Ina son ki mini adalci Umma ta hanyar yin hakuri da matar da Ubangiji ya za'ba mini, sake daure wa, ki mini wannan alfarmar".
Ta share hawayen idonta ta shafa kansa ta ce "ka kawota zan yi hakan! Allah ya tsare mini kai. Allah ya kawar da dukkan abin da babu alheri a cikin rayuwarka. Aniya bi aniya In sha Allah".
Antin Zaria da itama k'walla take yi ta hau fa'din "Ameen Umma! Ai kin gama yi masa dafa'i daina tsoron komai akan sa Ubangiji ba zai juyar da addu'arki ba".
Ya dinga godiya sosai tare da al'kawarin duk runtsi ba zai bari a fi karfinsa a gidansa ba.
Ba abin da Umma take kauna irin ta ce ya nemi Abida da take gabanta a yanzu.
Amma da ta tuna irin tozarcin da Munubiya da uwarta suka yi mata sai ta tsorata.
Ta kuma sani kanwarta Adama uwar Abida ita ce take ta fa'di tashin kawo mata taimakon yadda za'a yakice Baban Yara da iyalinsa a jikin Abba amma basu samu nasara ba.
Ta sani kuma matu'kar ya auri Abida sai an mallake mata shi, ai hatta ita kanta sai ta koma karkashin ikon Adama.
Kan dole ta ha'kura tana kukan zuci, tana hirji da nadamar yadda rayuwa bata zuwa mata yadda take so.
Har yau da shekarun tsufa suka cimmata bata samu cikar burikanta ba.
Bata ga Safiya a uku ba, bata ganta a kaico ba. Sai ma cigaba da a kullum take ganinta a ciki.
Dukiyar mijinta da ta sanya ta d'agawa da kyashi, kusan rabinta ta Gudale ce. Yayin da ya kasance y'arta ce matarsa kuma uwar y'ay'ansa.
Kuka ya goce mata sosai tana yi tana fa'din "Allah na yi tuba! Sai dai har abada babu aminci a tsakaninmu, na ajiye makaman fa'da da Safiya da ikon Ubangiji.
Amma matu'kar da kulunboton da ta yi, to ba zata mutu ba sai ta hadu da sharrin bebayen aljanu darajar manzon Allah".
Antin Zaria ta kasa jurewa ta fashe da dariya hawayen tausayin uwarsu kuma na gangarowa a fuskarta mai cike da kamala ta ce "Bebayen aljanu kuma Umma? Menene manufar hakan?"
Cikin kuka Umma ta ce "Azaba zasu yi ta gana mata, duk juyin da za'a yi kuma baza su magantu ba.
Kafin a ankare sai ta ji jiki fiye da yadda na ji".
A wannan karon hatta Gudale sai da ya fashe da dariyar sosai.
****
Ina zaune a falo wayata ta hau Kara ina dubawa na ga Yaya Gudale ne.
Na dauka. Ga mamakina sai cewa ya yi anjima ka'dan zan shigo Allah ya sa kina gida?"
Na dake na ce "Sai ka zo".
Na kalli kaina tsab nake, cikin kwalliya.
Ba jima wa kuwa ya iso.
Shiru shiru bai shigo ba.
Kafin na yi wani tunani sai kawai wayata ta hau kuwwa.
Na dauka ganin shine sai cewa ya yi "Na iso ina wajen gate".
Na dauki mayafi na fita, na tarar da shi zaune a mazaunin direba, ya sanya wa fuskarsa bakin glass da yake yawan sawa idan yana cikin rashin sukuni
Na bu'de motar na zauna. Muka gaisa, ya zuba mini ido sosai.
Ya numfasa ya ce "Sai yawo kike yi mini da hankali Halimatu! Zuwa yanzu ya kamata ki y'anta zuciyata daga zullumi, ki kuma hutar da gangar jikina daga kewa. Kinsan dai ni ban iya tsilla tsilla ba. Ina jiye miki tsoron kada na fa'da tarkon da zai zame mana fitina. Na gaji, ina bu'katar ki sosai".
Na dauke kai na ce "Ai kaine har yanzu baka iya magana ba, da ka fara ma sai ka bantse".
"To ba sai ki yi hakuri da ni a yadda nake ba.
Ban iya karya ko munafunci ba. Dama kuma ban miki al'kawarin zan zama yadda kike so ba, na dai yi alwashin babu cin mutunci a tsakaninmu.
Yanzu ki koma ciki ki ha'da mini ruwan wanka.
Ki tanadar mini abinci yunwa nake ji. Sai ki shirya zaki raka ni unguwa".
Na fita na fara tafiya, sai ji na yi yana cewa "Guduyo".
Na dawo na tsaya. Ya miko mini leda mai dauke da tambarin Oriflame.
Na karba na yi godiya sosai.
Na shige na ajiye ledar a falo, na wuce dakinsa na shirya masa ruwan wanka kamar yadda ya bu'kata.
Na dawo kicin na shirya masa abincin.
Ina ta tunanin gara da na yi girkin ban biye shi da ya ce kada na sake bashi abincina ba.
Na dawo falo na bu'de ledar ina ganin tsadaddun turaruka sai shower gel din da nake amfani da shi, da ya ji ina fa'da wa Sakina ya k'are.
Ya shigo fuska a daure tamkar ba shi ba.
Na yi masa sannu ya amsa. Ya wuce dakinsa.
Ya fito sanye da jallabiya mai asalin kyau da tsada.
Ya iso falo, ya zauna na ajiye ledar na ce "Nan zan kawo abincin?"
Ya dauke kai ya ce "Eh.
Na wuce ina mamakin wannan fishin da yake yi.
Na kawo masa.
Na zauna ina cigaba da ganin kayan.
Ya kalle ni ya ce "Wa ya kawo miki wadannan turarukan masu daraja haka?"
Na yi sakare ina tunanin me zance masa.
Na dauke kai na ce "k'anin Sakina ne".
Ya basar sai kuma ya ce "Allah dai ya sa kin fahimci manufar wannan alherin nasa".




*Na gode sosai da ha'kurinku*
*Na gode da fatan alherinku*.
*Surayya Dee* ✍️
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *YABOWA DA JINJINA*
*na matu'kar yabawa da jinjina ga SDK comments group, mussaman masu yin sharhi babu gajiyawa, bayan saka ku'dinku da kuka yi, wajen siyan ticket din karanta labarin, sai kuma kuke sake k'arfafa mini guiwa ta hanyar yin sharhi mai ma'ana.*
*Na gode muku sosai! Ubangiji ya sanya albarka a dukkan sha'aninku*

*SDK*
*97&98*.
Na waske ban ce komai ba.
Muna zaune aka fara kiran maghrib ya mike ya fice tare da cewa "ki shirya ina dawo wa zamu fita".
Bai jira amsata ba ya rufo k'ofar.
Bai dawo ba sai da aka sallaci Isha.
Yana dawowa ya tisa ni a gaba har wajen shashinmu ganin gaban Baban Yara zai kai ni sai na nemi turje wa tare da cewa "Ba inda zani ban yi niyyar shiga ba yau".
Ya d'aure fuska ya ce "Billahillazi sai kin je".
Na fara hawayen takaici na ce "ka daina mini wannan wula'kancin Yaya Sadik! Akan me zaka dinga zuwa gaban iyayenmu kana maganganu masu nauyi da rashin ta ido?"
Ya mak'e kafa'da ya ce "kafiyar ki Guduyo. Kukanki kuma ba abin da zai hana. Na gaji da halinki, na gaji da neman yardar ki, na k'osa da wannan maganar, na gaji k'warai da gaske.
Ke kuma baki shirya yin sassauci da afuwa ba. Da ace Abba na nan da tuni na sake gurfanar da ke a gabansa.
Amma tunda baya nan sai na kawo ki gaban Baban Yara na kuma bu'de maganar k'arara."
Na kalle shi ba alamun wasa ko zolaya a tare da shi.
Hawaye ya goce mini na ce "Na rok'e ka kada ka mini hakan, dan girman Ubangiji".
Ya kankance ido ya ce "Zan bar maganar ne ka'dai matu'kar zaki yarda komai ya wuce a tsakaninmu, zaki samar mini nutsuwar da nake bu'kata."
Na daga kai na ce "Na yarda".
Ya rike hannuna ya ce "To mu je, amma idan kika yaudare ni zaki ga karshen rashin kunya a gobe".
Muka yi sashen Umma.
Muka tarar daga ita sai Abida. Antin Zaria

56 / 61