Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
barka ka haihu da wata, tunda uwarsu tasan kan dukiyarka da take hannun d'anta. Wai ace har bayan Abbanku yana kushewa ma sai da aka yi kulunboton da ya yi mini abin da kullum sai na yi hawaye?
Ka shekara talatin har da d'oriya amma abar wasiyyar kada ka kula da abin da yake mallakinka ne, sai dai wani?
Komai zaka yi sai an sani, kome kake so sai ka yi y'ar murya kuma akan abin da yake naka ne. Sannan ace kada ka ha'da dukiyarka da ta shakikanka amma kuma an damk'a ta a hannun wanda zai iya shatale cigabanka ta hanyar yin mugunta, tunda kullum idan ya so zai iyawa cewa asara ake tafkawa babu kuma mai kalubalantarsa".
Da kunnena na ji wannan bitar da ta zaunar da shi take yi masa.
Na kuma ji ya bata amsa da cewa "Umma Idan akwai Wanda na shaida babu son zuciya a lamarinsa to Abba ne, ya riga ya san ban iya kasuwancin ba, ya fahimce ni irin fahimtar da ke baki yi mini ba.
Umma duk tarin dukiya matu'kar aka ce dauka za'a yi kullum, ba karuwa zata yi ba to la shakka wataran wayar gari za'a yi aga babu ita. Abba ya san dukkanmu kowa da iyalinsa, ya guje mana samun b'araka ne bayan babu shi akan abin duniya. Tunda ya sani kowacce tana da miji da y'ay'anta. Sannan su bai ce ga yadda zasu yi da nasu kason ba, kema bai ce ga yadda zaki yi da naki kason ba. Ni kuwa da yake ta tattala ni, har bayan babu shi to zan yi kokarin na ga na tsaya akan duk abin da ya ce ko da kuwa ya ci karo da ra'ayina".
A hassale ta ce "Tunda baya nan, ai sai ka raba biyu ka bawa Antin Zaria ta siya maka hannun jari daban daban, Allah barshi rabin Abdallah sai ya dinga juya maka tunda dai sun zame mana kaska."
Ya daure fuska ya ce "Umma dukiyar nan da kike ganin na sameta Wallahi bana sonta, na karba ne dan Ubangiji da kansa ya raba, ya kuma shirya ayi hakan. Wanda ya tara abarsa ya tafi ya barmu da ita, da ace zan rasa komai, Abba ya dawo zan fi son hakan. Amma tunda ba zai dawo ba, to ina tabbatar miki yadda ya ce na yi da dukiyar da ya yi ta tattalawa da taimkon Yaya Abdallah, har na gajeta to kuwa hakan zan yi. Ba zai zama na'kasu ba, idan na yiwa Yaya Abdallah yar murya tunda ai wahala yake yi mini, kuma yayana ne na sosai. Sannan ai yasan da Antin Zarian amma ya ambaci Abdallah.
A fili Umma ta ce "Mai Ashafa bala'in duniya! In sha Allah sai mun tsaya ranar gobe k'iyama".
Nan ma ba fargaba ya ce "Umma ina guje miki daukan alhakin da zaki je lahira idan an tsayar da ku din da kike fata ki kasa yin nasara domin dai baki da hujja akan tarin zarge zargen da kike yi masa.
A yanzu ba abin da ya dace da ke irin ki rungumi istigifari don ki samu ki iske Abba cikin aminci ku cigaba da rayuwa a aljanna".
Ta kuwa fashe da kuka tana cewa "In sha Allah! Sai dai ka tsananta addu'ar kada ayi mini kulunboton da a lahirar ma zan kasa ganinsa. Ai ni kam ina cikin masifar duniya."
Ya ru'ko ta yana shafe mata hawaye, yana cewa "Ki yi shirun ki Umma! Gudale da duk abin da ya mallaka na ki ne, kuma har na daina numfashi zan ta yi miki addu'a, duk mai nufinki da sharri kansa zai koma".
Na sulale na koma tunda dama zuwa na yi na gaishe ta, na ji wannan maganar dan hakan sai na koma wajena. Ba tare da na bari sun gan ni ba.
Daki na shiga na kwanta zuciyata sai rawa take yi. Anya kuwa Umma ba zata yi nasarar kashe mini aure ba?
Hawaye ya goce mini, ina fa'din Innalillahi lillahi wa inna ilaihir Rajiun.
Wani ba'kin ciki ya tokare mini na yadda kusan kullum sai Umma ta zagi kakana bawan Allan da ya haifi wadanda suka fita.
Abin kaico kuma ba akan komai ba sai zato da zargi.
Yanzu kuma ta ce na hana Munubiya haihuwa. Duka duka auren da bai rufa shekara daya bane za'a fara lissafin na hana ta haihuwa?
Na tuna rannan zamu fita tare da Munubiya ta'aaziyar Baban abokin Yaya Gudale da ya rasu, da muka dawo na ce muje mu gaida Umma kai tsaye ta ce ba zata je ba, ta yi wucewarta tabbacin da gaske take yi. Banda alhinin mutuwar Abba da ya karya dukkan zafin kan Yaya Gudale ai da tuni ya sallamata, tunda a yanzu idan zata fita bai isa ta nemi iznininsa ba. Har kuma yanzu bata shiga kicin da nufin yin girki, sai dai yan aikinta har biyu da ta Jere a saman.
Duk masifar Gudale akan yan aikin sun matsa masa, a takure yake ya ha'kura ya zuba ido. Ba dan komai ba saboda Umma.
A hakan dai muke rayuwa Umma ta shata layi sosai, a dole take gaisawa da yaran gidanmu, Babanmu kuwa yaki yarda da gabar da take son yi da shi, domin yadda duk safiyar duniya yake shiga ya gaida Abba, hakan ita ma kullum sai ya je ya gaishe ta ya duba ta.
Sai dai ko ka'dan bata ganin karamcinsa, asalima ga ni take yi dan suna da ku'di ne, ta manta ko Abba bai bashi koami ba, yafi karfin abinci da sutura da bu'katar yau da kullum, bare kuma kason da ya samu ya kusan yin kankan da nata, ga kuma yaransa kowa ya kawo k'arfi, Antin Zaria kuma bata fasa alherin da take yi masa ba, asalima sai ta ha'da har kulawar da take yiwa Abba akansa.
Abba ya yi watanni shida da rasuwa Yaya Gudale ya fara murde mini akan fita aiki, a farko da lallashi yake yi, yana cewa "kinsan dai ba abin da kika rasa, tunda na yi hakuri na yi biyayya, kema yanzu ki yi hakuri ki mini biyayya, ki ajiye aikin nan. Kin sani Guduyo bana so, bana kaunar na shigo wajenki ban ganki ba, ki ajiye aikin, idan komai ya kankama na business, zan fa'dawa Yaya Abdallah a yanka miki albashi, duk dai ba zai kai wanda Gwamnati take baki ba".
Dariya kawai nake yi ina cewa "Aikina ba dan iya ku'di bane kawai, ceton rai ne, sannan idan baka wajena yana debe mini kewa da damuwa."
Tun yana maganar jifa jifa har ya dawo kusan kullum sai ya yi, a dalilin Umma tana yawan nuna masa tunda baya ra'ayin matarsa ta yi aiki bai kamata ya yi hakuri ya cutu ba. Kuma Munubiya ma ta fa'da a gidansu a samo mata aiki tunda matarsa tana yi, ba zata yarda da digiri biyu a kanta ba amma tana gadin gida idan mun fice aiki.
Wannan zugar ta Umma sai ta yi tasiri a zuciyarsa, ya fara murdewa, muka fara takun saka da shi, rabon da mu yi irin wannan zaman na doya da manja tun kafin rasuwar Abba. A dalilin nasihohinsa da mutuwarsa ta sanya nutsuwa da tausayina yin tasiri a zuciyar Gudale, amma tsohuwar nan sai da sake tunzura mini shi.
Sanin da na yi aikin nawa ne bata so itama akaran kanta domin ina hucewa uwata takaici, sannan Munubiya bata kere ni ba, shine take son yin mini sanadin rasa wannan damar. Ni kuma sai na bijire na ki yarda na ajiye.
Shikenan sai abubuwa suka fara yin tsami, babu fa'da a tsakaninmu, amma sam bana Jin da'dinsa.
Sai ma ta gwada masa wata dabara ta fahimtar da shi ai mace mai aiki tana taimakon namiji tunda ai shima ya yi mata alfarma da ya barta take fita kullum tana cud'anya da maza.
Dake tasan kishinsa da k'yamar aikina da ya yi, sai ta daina zagin Malam mai Ashafa tunda wataran yana taka mata burki, kuma maganar bata tasiri, tunda bai daina gaida Mama ba, bai daina mua'amalantar su Yaya Al'amin ba. Sannan aurena bai mutu ba. Bugu da kari ya sake ninka mua'amalarsa da Baba.
Kullum a cikin fa'da masa take kayan kwalliya ya sauka akansa, hatta tufafi ma sai ya bushi iska, amma ita Munubiya ya yi kokari ya fitar da ita kunya, ya kuma k'ara kawaici akan ta tunda dai tana mutunta ra'ayinsa.
A wannan lokacin kullum sai na yi kukan rashin Abba! Mussaman da Anti Maimuna da Anti Juwairiya suka bi ra'ayin uwarsu suke yakata da dukkan zuciyarsu. Bayan ra'ayin uwarsu sai na fahimci har da kyashinmu da suke yi suna ganin tamkar nan gaba zamu fi su k'arfi a family.
Har ta kai jallin akan dole suke hulda da yan gidanmu, irin gaisuwar nan ta dole. Baba kawai suke gaisarwa shima bai isa su kai masa matsalarsu ko su shawarce shi akan wani lamarinsu ba.
Anti Ramla ce ita tun filazal a tsakiya take, bata kyautata mini, amma kuma bata musguna mini, bata kuma bada goyon baya a musgunawar da ake yi mini, haka nan tana gaida iyayena cikin mutunci duk da bata jan doguwar hira yayin gaisuwar.
Yayin da Antin Zaria da Sakina suke tare da mu dari bisa dari.
Rashin samun goyon bayan wadannan mutane biyu shine sa'ar da Abba ya yi zumuncin da ya yi ta kashedin a ri'ke shi da girma bai ruguje tun bai jima a k'asa ba.
Har yau, har gobe ina girmama Antin Zaria da Sakina mutane ne da suka gaji karmaci da arziki a wajen Ubansu. Mutane ne da idan Ubangiji ya albarkaci family da irinsu to yana wahalar gaske zumuncin wannan dangin ya rushe gaba'daya. Domin ko ka yi niyyar yin wani abu na tsiya idan ka tuno su, sai kawai ka ha'diye dukkan musgunawar da waninsu yake yi maka saboda nauyinsu.
Ina cikin wannan yanayin na rashin da'din mu'amala da Gudale, Munubiya da ta fahimci hakan sai itama ta murde musu, ta ki basu goyan bayan su musguna mini.
Anti Maimuna ta ka'da ta raya ta zama uwar dakinta amma sam ta ki haka Anti Juwairiya, ko bikin dan gidan Umma Adama ta Yola da zasu je, ba wanda ya fa'da mini sai Sakina.
Umma kuma ta sanya Munubiya a gaba suka tafi tun saura kwanaki biyar bikin.
Daga baya su Sakina suka bi bayansu bayan ta yi ta bani hakuri ta ce "Ko gobe idan na Moriki zai tafi kada ki yarda ki bishi, ki yi zamanki, ki koyi jarumtar barin inda ba'a son ganinki".
Ido cike da k'walla na rike hannunta na ce "Madallah da Sakinan Abba".
Ai kuwa suna dawowa Munubiya ta zo ta baje mini irin tsiyar da suka tafka da Anti Maimuna wai har da dambe suka yi.
A tsorace na ce ai kuwa dai baki kyauta ba Yayar mijin naki?"
Ta ta'be baki ta ce ato ina ruwana da ita, ai ina da ilimi ke da kike yar'uwarsu kuka rayu gida guda suka ki, suka juya Miki baya, suka zabi wata akan ki sai kuma na yi tunanin ni ba zasu yi mini fiye da hakan ba?
Ta girgiza kai ta ce never ever in history.
Kawai fa daga ta zuba mana abinci ta ce na sauko mu ci abinci, na ce mata Ni bana cin abinci da wata, wai shikenan na yi mata rashin kunya har tana cewa duk gatan da suke yi mini har zan ce mata wata, ashe bani da mutunci?
Ni kuwa na ce mata a wajenta na koya".
Na kame bakina na tsuke na ce "Allah ya rufa asiri"
Ta amsa da amin. Bayan ta ce "kaf gidan nan akwai marar mutunci ne irinta? Da har zata ce wani bashi da shi?"
Dai-dai lokacin kuma ta kwanto jikina tana cewa "Kamshinki da'di Maman Amnah! A hakan tamkar kin waye, amma idan na ga yadda kike barin jiki akan Dan-ummansa sai na yi ta mamaki.
To menene wani abin burgewa ne a tare da shi da kika daukake shi har hakan?"
Zuciyata ta tsinke mussaman da ta kai kanta yake shafar kirjina cikin hikima.
Na mike dukkan jikina na bari na ce "Bana son irin hakan Munu! Kada ki bari na wanke amincin da zuciyata ta yi da ke".
Ta kashe mini ido cikin rashin damuwa ta ce "Me na yi to Maman Amnah? Kinsan kin fi shi haduwa? Kin fi burge ni akansa?"
Na dauki salati cikin firgici na ce "Allah ya shirye ki.
Hawaye ya balle mini. Cikin kuka na ce "Wayyo Abba daga tafiyarka na fahimci bangon dana jingina ya zube, yau ga wata katuwar masifa tana tunkaro ni, ba wanda zai bani k'afarsa na yi kuka, ya kuma fahimce ni, bare a gasgata ni. Inna lillahi wa inna ilaihir Rajiun".
Ta mike tana fa'din "calm down mana, da zaki nutsu ki yi tunani zaki ga ba abin da yafi hakan da'di, ba kuma zaki sake kwana da takaicinsa ba, to me zai dame ki, kina da ku'dinki, ba kya bu'katarsa fa'da mini inda iyashegensa zai yi tasiri. Kin ga ni yana mini gadara ko isa?"
Ta girgiza kai ta ce "saboda yasan baya gabana, hatta uwar tasa ma ni bata gabana na yi aure ne kawai dan an matsa mini, amma mene ne a cikin auren ban da takaici da rashin y'ancin kai.
Dama fata nake na haihu ko sau daya ne, Alhamdulillah na samu ko yanzu na ga damar kashe auren sai na zagi uwarsa".
Zuciyata ta buga, ciki ne da Munubiya? Nan da nan na dinga a uziya da shaidanin da zai tunzura ni, tunda dai nasan Gudale na mua'amalantar ai kuwa idan da rabo ciki zai samu.
Na kalli cikin idonta na ce "Bana ra'ayin hakan Munubiya! Bana so, kada ki janyo mu yi rikicin da za'a jimu".
Ta mak'e kafa'da tare da cewa "Na gaji da zagaye zagaye Halima! Ina son ki sosai. Idan kuma kin k'i, to ban ki a jimu a gidan radio ba.
Tunda na dora ido akan ki ban sake yi miki kallon kishiya ba sai abin kaunata. Zan yi komai dan na raba ki da lusarin mijinki Mumys boy, domin ke din kin wuce ace ana mulkar aurenki, kina da daraja kin wuce irin wannan kaskancin."
Na koma na zauna ina ta ambaton Allah yayin da ita kuma ta wuce wajenta cikin kwanciyar hankali.
A gigice na kira Sakina a waya na fa'da mata komai.
Ta yi shiru domin ita ma ba karamin gigita ta yi da wannan maganar ba.
Tsawon lokaci bata tanka ba, har sai da na ce "Kina jina kuwa?"
A hankali ta ce "Ina jin ki Sadiya abin ne ya ki'dima ni, kaina ya kulle kwarai da gaske. Ki bari zan yi tunanin abin da zamu yi".
Na ce "To".
Washagari a asibiti Sakina ta dinga jinjina girman al'amarin, ta ce "Ba mutunci ne da yarinyar ba, zata iya burma ki, kawai shammatar ta zaki yi, ki dinga nadar maganganunta a waya saboda su zame miki shaida. Amma idan kika fito Kika fa'da za'a iya cewa sharri kika yi mata".
Na yarda da shawarar Sakina.
Amma na yi matu'kar janyewa Munubiya, duk da ita ta 'ki yarda ta yi fishi da ni irin yadda na yi da ita.
Muna cikin wannan yanayin Munubiya ta fara wata irin jinya.
Sosai take galabata, Gudale da daddare ya shigo mini, ba walwala ya ce "Gobe ki wuce da Munubiya asibiti ta ga babban likita".
Na amsa da cewa "To Allah ya bata lafiya".
Ni na jagoranci kai ta asibiti, na tsaya kuma ta ga likita, aka mata komai muka dawo.
Ashe lokacin ma cikin ya shiga wata na biyar an kuma tabbatar mana yan biyu ne a cikinta kamar yadda scanning ya nuna.
Tattali da gata ba wanda Umma bata nuna Mata ba, hatta Gudale da bai wani daukaki lamarinta ba, samun cikin Nan da yadda Umma ta sakankance maza zata haifo ya yi d'oki, ya ajiye abubuwa masu yawa yana nan nan da ita.
Abin yana mintsini na. Duk sadda Umma take fa'din Munubiya ce zata haifo magajin Abba, sai na daga hannuna sama da nufin na yi addu'ar kada Allah ya sanya ta haifi namijin, sai kuma kunyar Ubangiji ta kama ni. Sai na fasa yin wannan addu'ar, sai kawai na ro'ki a cire mini damuwarsu a raina, ya kuma shirya mini yarana, ya tsare mini su.
Tana warwarewa sai ga takardar samun aikinta da Ma'aikatar Human right, ashe anan mahaifiyarta take aiki sai dai na ji ana cewa tana daf da yin ritaya.
Ga mamakina Gudale bai damu ba, amma kuma ni yak'i biyuwa mini ta da'din rai a dalilin aikina. Ya dauke wa kansa siya mini kayan kwalliya ko Undis, hatta gas idan ya kare kafin ya yi refeling sai na da'de ina fama, wani lokacin ya yi bayan ya gama wulakancinsa, wani lokacin ya jido mini gawayi, wani lokacin kuma ya bawa banza ajiya ta. Sai dai na yi da aljihuna.
Makaranta da ya saka su Amnah ya kamata ace wacce tafi wannan ya saka su, amma duk ban ce komai ba, ban yi yun'kurin yin korafi ba, mussaman da aka yi dace makarantar suna da kwararrun Malamai, ta zama raina kama.Z
A hakan kuma rannan mun shiga wajenta ni da shi da sassafe, ta kalle ni ina sanye da labcoat ta ce "Aikin ma'aikatan jinya ai sai dai kawai ayi shiru amma tsiyar da ake yi yafi na ko'ina. Barin ranar da za'a a kwana, ai lusarin mijine kawai zai dauki wannan kazantar.
Nan da nan raina ya baci irin wanda bai ta'ba baci da Umma ba.
Dake a cikin fishi nake sai ha'kurina ya kwace a kanta. Ba fargaba na ce "Allah dai ya tsaremu ni da Sakina, dake a waje daya muke ai".
Ai kuwa wannan maganar ta girgiza Umma ta fashe da kuka tana fa'din na jefeta da bak'ar magana.
"Amma ba laifina bane laifin Gudale ne da ya mayar da ita banza har na zageta akan idonsa. Sakina kuma ta ga karshen bijire mata da take yi a kaina.
Gudale ya yi tsam ya kasa cewa komai amma ya tumbatsa da fishi.
Na fito na barsu ina rayawa a raina ta saka ya sake ni. Duk gudun zuciyarta da nake yi bata ga ni, amma Munubiya da take fa'da mata kowacce magana gatsar ita take lallabawa.
Tana ta danne cin kashin da take yi musu dan kada ta kunyata.
Na wuce asibiti, a ranar bamu yi kwanan dadi ba, domin gaba'daya ya tunzura ainun.
Ya dinga kumfar bakin tabbas na raina shi da na mayar wa Umma