Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   48 / 61

141K to 144K   out of 180.1K words

shiyasa na bar mata shi, ni ban kullace shi ba, amma dai kam yaje ya rike wacce ya za'ba a kaina, Amaryarsa ba ruwana da ita tunda bata yi mini laifi ba. Shi da ya mini, shine ba ruwana da harkarsa, tunda dai bai ma yarda ya tozarta ni ba".
Abba ya ce "Ai kuwa dai wannan shine hukunci na gaskiya ku tashi ku je."
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *83-84.*

Nan da nan Gudale ya ce "Amma dai Abba sai da na ce A mini adalci, ka yiwa alfarmar Malam Zubairu Rahimuhullah. Ka yiwa Guduyo irin fa'dan da zaka yiwa Sakina idan mijinta ya kawo maka karar tana cutar da shi".
Jikin Abba ya yi matu'kar yin sanyi. Ya ce "yau har da Ubana ka nemi kafun k'afa da shi? To maganar ta kare kuwa".
Ya kalle ni da tarin kauna ya ce "ki yi hakuri! Annabi ya ce Madallah da mutanan da suke yin afuwa idan an zaluncesu alhalin suna da ikon ramawa. Darajar miji yawa ne da ita, ina ta fa'da miki Annabi da kansa ya ce shine lauyanku ranar Gobe, ki tuna kuma dokokin dake cikin aure Allah ne ya shimfida da kansa dan haka biyayyr da aka wajabta muku ku yiwa miji, ba mijin zaku dinga kallo yayin biyayyar ba. Ubangijin da ya wajabta yin biyayyar zaku dinga kallo a farko."
Na fara kuka ina cewa "Allah Abba ina ha'kuri sosai amma shi baya ga ni, sai ya yi ta kure ni. Kuma abin haushin sai ya nuna ma baisan ya yi laifi ba bare ya bada hakuri".
"Ato idan bai gyara ba watarana zai zo gabar da zai kure kin ya rasa mai shawo masa kan matsalar ai".
Nan da nan Gudale ya fara gyaran murya. Yana cewa "uhum uhum Abba dan Allah kar ka ce komai kawai a taimake ni dai a kashe wannan maganar a bata ha'kuri, amma kada a mini bakin da zan sake yin wani kuskuren, a kuma jarrabe ni da rasa wanda zai mini maganin matsalar".
Na gallasa masa harara na ce "Wato Abba ne zai bada ha'kurin laifin da bai ji ba, bai ga ni ba."
Ba kunya kuwa ya ce "Ato ba shi ya haife ni ba?
Ina ce jiya har ce miki na yi na ci darajar Abba, amma kika yi funfurunfus to yanzu gashi nan a gabana a gabanki ya ce ki bini, ki yi ha'kuri da ni, da sannu Ubangiji zai hore miki ni".
Na sandare tsabar ki'dimar da na shi na kalaman Gudale.
Ya sake shayar da ni wani sabon mamakin ta hanyar cewa "Ai kin bani mamaki Wallahi! Yo wannan kallon ba shine zai sa na ki fa'din kin ki manta komai saboda alfaramar Abba ba".
Na girgiza kai ina cewa "Allah abin godiya da baka zo a mace ba."
Abba ya ce "Rabu da shi. Bai isa ya burma ni ba. Nima hakan ya ta'ba mini ai, a gabana ya nemi ha'da fitina tsakaninmu da Yaya ta Kwalli."
Ya kuwa bata rai ya ce "Abba dole Guduyo ta dinga mini gashin kuma. A gabanta ake nuna mini kasawata. Zan tafi, ka bata umarni na karshe mai karfi akan ragaitar da nake yi a hannunta, tunda tasan kai din farin Uba ne."
Abbaya girgiza kai ya ce "Ubangiji ya ganar da kai, ya shirya ka. Guddi tashi kuje! Nasan na isa da ke, shima tabbacin hakan ne ya sanya ya kawo mini wannan al'amarin gabana, to ya zanyi tunda na riski wannan zamanin?"
Kunyar Abba ta rufar mini mussaman da na ga shima kunyar ce ta hana shi kuzari.
Kaina na kasa na ce "Na ha'kura har zuciyata Abba! Ya ci darajarka".
Na mike da sauri yayin da Gudale ya ce "Ina ganin tala jaurar duniya a wajen Guduyo ana son Uba da farin ciki, amma ba'a son dansa da kwanciyar hankali. To dai shine ya haife ni, gara na dinga fa'da miki dan ki dinga raga mini".
Na tafi ban tsaya ba, amma ina jinjina girman iskancin Gudale.

*Abba*
Ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya ce "Sadik sai na mutu zaka zama mutum sak?"
A sanyaye Gudale ya ce "Na yi tuba Abba! Abin ne yafi karfina, a mini afuwa yadda aka saba".
"Na yi maka Sadik Allah ya shirye ka. Sannan ina sake jan hankalinka akan yarinyar nan. Kar ka zalunceta da gangan. Idan ka ci amanarta in sha Allah kaima ba zaka ga da kyau ba. Ban da ma zuciya ba a ganinta bare a hukunta ta, ina salahar zuciyar Halima ina daukar tirka tirkarka? Har yau din nan ban ta'ba jin ta yi korafin rashin kirkin da uwarka take yi mata ba. Kana sonta, amma ka kasa sanya aminci a tskaninta da uwarka. Akan idona Saudatu take jagorantar a wula'kanta mini diyar Ibahim, yar wani, tafi yar jinina. Ai Wanda ya ce Allah ya huta. Sai kuma Ubangiji ya damk'e wa Halimatu kai, ya cusa maka sonta ta inda baku yi zato ba. Wallahi duk ranar da ka yi kuskuren sakin yarinyar nan daga kai har uwarka sai kun rasa sukunin zuciya da na gangar jiki. Idan kuma ka Cigaba da musguna mata da gayya, kaima ka dinga ganin sakayya ta inda baka yi zato ba kenan".
"Abba kana son ka dinga yi mini baki dai".
Gudale ya fa'da cikin rauni sosai.
Ba baki bane gaskiya ne Sadik! Wataran sai ka yi bitar kalamaina. Wataran sai ka yi hawayen rashina, watarana sai ka duba ko ina baka ganni ba, bare har na fa'da maka gaskiya ka yi zaton na yi maka baki ne."
Gudale ya sake yin kasa da kai ya ce "Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana mai albarka, ina yi maka fatan aljanna Abba."
A daki ya tarar da ni ya rungume ni, na dago ina hararsa na ce "Ka gama yin mini sharrin sannan ka yi zaton zan kula ka?"
Ya kuwa ruga kamar yaro yana fa'din "Da zafi zafi ake dukan karfe ai yana falon bai koma ciki ba, bari na je na tabbatar masa ba karya na yi ba, bai isa na ci darajarsa ba."
Sanin da na yi da gaske komawar zai yi, zai kuma iya yin rantsuwar da Abba zai gasgata shi, hakan ya sanya na bishi a guje mun fita kofar falon na cafko rigarsa "Ina cewa bana son haka, ka ga ka bari".
Yayin da yake zillewa yana fa'din "Na rantse sai ya ji, ai kuma na gaji da kafiyarki".
Na fara dariya dariya, kuka kuka ina fa'din "Dan Allah ka bari ka ga dai ba abokin wasanmu bane".
Yana kokarin kwace wa ya ce "To yau sai ya zama abokin wasan, gobe sai ya koma Abban".
"Na ce dan girman Ubangiji ka bari bana so".
Ya zuba mini ido ya ce "Tom na fasa amma wallahi anjima kika yi mini wula'kancin da kika saba, ina tashi zan koma gabansa zan bude maganar sosai. Wallahi ba zan ji kunya ba".
Na d'aga kai na ce "Shikenan na yarda."
Dai dai nan Sakina ta shigo gate din namu ganina rike da shi, ya sanya ta ce "Oh lamarinku sai ku".
Yayin da Gudale ya bata rai ya ce "Da y'an bani na iya sun gane sai su daina shiga tsakaninmu ko Guddin Abba?"
Na cuno baki na ce "A a wallahi! Dole mutum ya yi kishin nasa ai".
Ya wuce yana cewa "Allah sai kin yi tuba akan wannan bayar da ni da kika yi a gaban Sakina".
Sakina ta tuntsire da dariya mai karfi tana fa'din su Namoriki an kamu da gaske".
Ya k'i kulata a dalilin haushinta yake ji.
Daren wannan ranar ya shiga cikin tarihi a rayuwar aurenmu, domin duk nau'in soyayya ba wacce Gudale bai mini ba. Hadin kan dana bayar ya sake armasa lamarin. Tsananin ki'dimar da ya shiga ya saka ya saki baki, cikin rawar murya yake fa'din "Ki daina mini waccan horon, komai zamu yi ki daina juya mini baya, ya kike son na yi ne?".
Na ce "ba ga matarka can ba, mai tsukakke ba irin nawa k'ofar Dan... "
Da sauri ya danne mini baki ya ce "Billahillazi haushin wula'kanta ni da kike yi ne, amma k'arya ne tsagwaronta. Da kina sona ba zaki kyautar da kwanakin da zan yi miki ba, na ce miki ina so ne? Abin ba karamin k'ona mini rai ya yi ba. Shiyasa nima na rama, amma saboda kinsan ni mayenki ne shine kika yi ta gasani na satittika masu yawa. Ina ro'konki arziki kada ki sake mini irin wannan gashin k'umar dan Wallahi zan iya zuwa gaban dukkan iyayenmu na fa'da musu azabar da kike gana mini."
Cikin wata irin murya da ba zanci zan sake yiwa Gudale ba na ce "To ai baka gamsuwa kuma bani kake so ba".
Jikinsa na rawa ya kamo kunnena ya rada mini "Wallahi ina sonki sosai Guduyona kema kin sani, aikin da kike fita kullum ne yake neman kassara ni."
Ya fa'da muryarsa na karye wa alamun kuka ne ya nemi kwace masa.
Jikina ya mutu, ya rungume ni hawayensa na diga a gadon bayana. Wannan kukan da ya yi mini sai ya zama tamkar an saka mini kyamar aikin.
Na dinga rarrashi ina bashi ha'kuri tare da cewa "nan bada jimawa ba komai zai daidaita.
Shikenan sai muka shirya na dinga tattala shi, ina kaffa kaffa da abin da zai ha'do mu.

A wannan lokacin na ga sintirin da mata suke yi a gidan ya yi yawa, yammata da zawarawa.
Ba abin da Munubiya take matu'kar so irin ta rungume ni, rannan na dawo daga aiki kawai ba zato a filin gate ta rungume ni ta shafo bayana har zuwa mazaunaina. Nan da nan jikina ya dauki rawa na zame ina kallonta.
Ga mamakina bata nuna ta yi wani abin ba.
Ta dinga yi mini barka da zuwa da wani irin kallon da bai kamata ta yi mini irinsa ba. Tun ranar sai na fara janye mata, na fara kaffa kaffa.
Ita kuwa sai ta yi kamar bata gane ba, ta cigaba da zuwa wajena, tana sake jan Afrah a jikinta. Ga kyautar da take yawan yi mini na abubuwa masu daraja ta sake ninka wa.
Abin da fahimta ba wani damuwa ta yi da Gudale ba, domin zata iya baro shi a samanta ta zo ta zaune mini, tana mini wani irin kallo da shagwaba shagwaba da suke matu'kar sanya ni a faragaba da zullumi.
Idan na yi yun'kurin fa'dawa Gudale sai na fasa, domin dai bani da hujja gamshasshiya.
A matu'kar tsorace nake da ita domin idan baka iya kama barawo ba, shi ya kama ka, sai dai na tsananta addu'ar Allah ya raba ni da sharrinta ya kawo mini mafita cikin ruwan sanyi.
Ina cikin wannan zullumin jikin Abba ya tsananta. Aka kwantar da shi a Asibitin Malam.
Duk wanda yaje wajensa sai ya yi hawaye domin duk yadda yake cikin ciwo sai ya ce "ku ri'ke zumunci, ku sadar da shi ko da kuwa ku an yanke muku. Idan ya kalli Babanmu sai ya ce "Ka yi hakuri da Sadik kada a bar shi da kansa, kuma kada halinsa ya sanya a yanke zumunta da shi.
Kowa a family nan bashi da sukuni domin sosai Abba yake jin jiki. Haka kawai na dinga shiga fargaba mai yawa, domin na sani Abba ne jigo a zaman aurena. Yanzu idan ya mutu ya bar ni a wananan halin na gaba k'ura baya damisa ya zan yi ne?
Umma bata sona, tana fatan ta samu hanyar wula'kanta ni fiye da wula'kancin da take yi mini a yanzu sannan ga kishiyar da alamunta suka nuna lesbian ce, kuma ta k'yasa ni.
A wannan tsukun hawaye baya yanke wa a fuskata, a fili nake yin addu'a ina cewa "Allah ya tashi kafadunka Abba".
Ranar juma'a 7 ga watan biyar da hantsi Abba ya amsa kiran Ubangiji.
Mutuwar da ta yi mini wani irin mahangurba.
Ina tsaye akan Abba ya cika, farin ciki daya da nake yi masa, ya yi salati yafi cikin carbi, sannan da zai cika ya samu damar cikawa da kalmar.
Amma duk da hakan zubewa na yi na suma tsabar kidima.
Na bude na ga ana shafa mini ruwa.
Sakina tana kuka ta rike hannuna muka fice daga dakin, zuwa lokacin tuni an wuce da gawarsa domin a gaggauta shirya shi.
Cikin Sa'a aka kammala ha'da shi aka fice da shi zuwa masallacin murtala idan an idar da sallar juma'a za'a sallace shi.
Irin kuwwar gidan yake yi, ni sai nake ganin tamkar dukkan flowers da bishiyoyin gidan sun taya mu kuka da alhinin fita da gawar Abba. Domin gaba'daya gidan kaurewa ya yi, yayin da Ubangiji ya basu ikon busawa da karfi sosai.
Idan na ce sai na fa'di irin dukan da mutuwar Abba ta yiwa ahalinmu to bata lokaci ne mai yawa.
Amma dai kam ko ban ce komai ba kowa ya san an mini mutuwa ba ka'dan ba.
Abba mutum ne har da rabi, ya wanzar da rayuwarsa gaba'daya a neman halak da kuma tiritiri da zumunci.
Ina kuka Ina fa'din "Allah ka jikan Abba, ka bashi aljannar da ka tanada dan masu sada zumunta".
Kowa a cikin dangi sai ya mini ta'aaziya ana fa'din sannu da rashi Halimatu, hakan kuma ba k'aramin karya mini zuciyata yake yi ba.
Gudale idan na ganshi sai na ji tausayinsa yana kama ni domin kuka yake yi fiye da na yan'uwansa mata. Fuskarsa sanye da ba'kin glass amma hawaye sai dai aga yana zuba.
Amma a hakan zai leko ya tasa ni a gaba ya ce sai na ci wani abu, hawaye bai yanke masa ba, cikin karfin hali yake fa'din "Sannu Guduyo, daure ki sha ko kunu ne, nasan yadda kike ji, to amma ya zamu yi ne?"
Tsawon kwankin makoki kowa a ki'dime yake.
Haka mahaifina a tsawon kwankin da na shafe a duniya ban ta'ba ganin sa cikin ki'dima irin a kwanakin mutuwar Abba ba. Haka Mama dan har ina rasa wanda yafi kuka a tsakaninta da Umma.
Amma tunda mutuwa dole ce ba kuma yadda za'a yi mutum ya dawo, haka aka tattara aka ha'kura, muka bishi da addu'a.
Sai dai kam ni da Gudale mun shafe kwanaki arba'in mutuwar tana yi mana wani irin bugu.
Wani lokacin ma shi da kansa yake bani hakuri yana cewa "Na sani an miki mutuwa Guduyo amma ki yi hakuri in Sha Allah zan yi kokarin na maye miki gurbin Abba wajen kyautata wa, zan iyakacin kokarina na kiyaye amanarki da ya yi ta bani, da ikon Ubangiji ba zan yi abin da yake ta jin tsoro ba. Ro'kon da zan yi miki dan Allah idan na kuskure miki kada ki tsananta fishi, kinsan dai yadda Abba ya yi ta jaddada yadda yake son aurenmu ya wanzu.
Nima na miki al'kawarin ba zan tsananta ba, a sadda kika kuskure mini".
Na fashe da kuka yayin da ya Jani jikinsa idanuwansa jawur yana goge mini hawaye amma ya kasa sake bu'de baki tsabar yadda zuciyarsa take zabalbala.


*Ina yi mana ta'aaziya*.
*Ni kaina ina cikin alhini, ayi ha'kuri da wnanan.*
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS*
*SUNA RENTING KAYAN AMARE*
*SUNA SAYAR DA SUTTURUN MATA ZABBABU, NA ALFARMA, DA KAYAN KICIN*.
*SUNA SIYAN KAYAN FURNITURES KO ELECTRONICS NA HANNU*
*SUNA KUMA SAYARWA*.
*SUNA SAYAR DA FILI DA GIDA*.
*SUNA BADA HAYAR GIDA*.
*KOMAI DA RUWANKA NE AMYAS GASU DA SANIN DARAJAR CUSTOMER. KAYANSU KUMA MASU INGANCI NE KUMA MASU RAHUSA NE*.
*08083909947*.


*SDK*
*85&86*.


Kafin arba'in din Abba duk abin da ya mallaka an kamalla lissafinsa da taimkonsu mahaifina da kuma Baban Gusau.
Yaya Abdallah da shine akan dukiyar komai ya ajiye shi har zuwa lokacin da za'a yi rabonta ga magada.
Tabbas munsan Abba yana da arziki, mun sani kuma me alheri ne domin hatta ma'aikatan gidanmu sunsan irin kyauta da alherinsa, ban da aiyyukan alheri da yayi ta yi na fili dana boye, masallaci da islamiyoyi da kuma rijiyoyi da ya yi ta yiwa kansa tanadin gobensa. Don kuwa har ga ni muke yi yana yin alheri fiye da yadda arzikinsa yake.
Amma sai bayan da ya mutu sai aka sake fahimtar wani darasi a rayuwar Abba.
Na farko sai da ya mutu kowa ya fahimci irin tarin dukiyar da ya tara.
Duk yadda ake tunanin Abba ya wuce nan. Ubangiji ya bashi wata irin dukiya amma sai bai nuna wata d'agawa ko alfahari ba, ko kuma ya yi ta hak'ilon sai an sanya shi sahun manyan attaijaran k'asa.
Na biyu kuma abin da ya yi ya sake sanya kowa cikin jimami da hawayen da baya yanke wa.
Littafi guda da ya da'de yana rubuta wasiyyar yadda za'a yi masa.
Ya rubuta tun shekaru uku da suka wuce da aka ga ni a rubuce.
Ya raba dukiyarsa gida uku da kansa.
Kaso biyu na magadansa ne, ahalinsa kenan.
Kaso d'ayar kuma da kansa ya rarraba a tskanin yan'uwansa da yasan ba zasu gaje shi ba.
Wanda sanadin hakan kowa sai da ya mallaki dukiya me yawan gaske.
Sai kuma wak'afi da ya yiwa kansa.
Sai kuma Yaya Abdallah da ake ta akilon juya ku'din da shi.
Irin abin da ya bashi a rubuce ko zai shekara goma bai fita da sunan neman ku'di ba, to lah shakka zai ci abinci zai sanya sutura zai kuma dauki nauyin iyalinsa. Sai kuma ya jaddada idan an raba gadonsa to lalle kada Gudale ya hada nasa kason dana yan'uwansa mata, kowa ya rike nasa gudun samun rikici akan dukiya.
Sannan bai yarda ya jagoranci dukiyar da ta zama tasa ba, ya cigaba da aikinsa, Abdallah kuma ya kular masa da ita, domin idan akwai amintaccen da Abba ya gasgata Yaya Abdallah ne.
Umma ba karamin kad'uwa ta yi da wannan lissafin da aka zaunar da su ana yi musu ba.
Hakan kuwa Baban Gusau da manyan lauyoyi da Malamai suka yi rabon kamar yadda shari'a ta tanadar.
Gudale ya ja dukiyar da ta mayar da shi wani irin hamshak'in attajiri na gaske, sai dai ko ka'dan bai yi murna, ko zumudi ba, haka nan ko kobo bai dauka ba, ya mi'kata kacokan ga Yaya Abdallah kamar yadda Abban ya ce shine zai cigaba da juya masa, sai dai komai an yi shi akan tsari da shaidu.
A kafatalin Ya'yan Abba mutuwar tafi kidima Gudale, kuma shine wanda ya dade bai warware ba.
Wani lokacin sai Sakina ta bar gidanta ta zo ta zauna da shi.

*Watanni hudu*

A hankali kuma har komai ya daidaita aka cigaba da harkoki.
Sai dai kullum ta Allah Abba yana ranmu, yana samun adduoinmu babu kakkautawa.
Yayin da Umma ta fita takaba sai kuma al'amuranta suka fara ta'azzara a dalilin Munubiya bata samu ciki ba, kullum sai ta zaunar da Gudale ta ce "Yaushe zasu

48 / 61