Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
da ibada ya jikin naka?"
Lebe duk huciyar sanyi bakin nan duk ya yi wani iri tamkar bana Gudalen Umma dankwalinsa ba.
Cikin rarrashi ta ce "Ya maganar yarinyar kana leka wa kuwa?"
Ya ce "Ta ya ya zan dinga zuwa a hakan Umma? Dubi yadda na rame wuyana ya zama tamkar marikin lema. Ga lebena duk yayi babu kyan gani kamar na wani katon bagaujen kauye."
Ta sake sassauta wa ta ce "Ai na ga ka fara warwarewa ne, amma dai kuna gaisawa a waya.
Ya nisa ya ce "Muna waya sosai. Ni yadda ta matsa na tura ne ya fara damuna wanne irin al'amari ne hakan?".
Ta sake kwantar da murya ta ce "Baban nata ne ya matsa mata ta fitar da miji, ko ya bata wani da bata son sa. Tunda kai take so, shiyasa suke son magabatanka su je, aure sai sadda ka shirya ko kuwa?
Kasan dai tsakanina da uwarta alkunya ce".
Ya ce "To amma dai sai na sake wartsake wa".
Ta ce "To dai ka mayar da hankali, kuma na fa'da maka kada ka yi kuskuren fa'da mata, da zarar suka ji maganar bata riga da ta yi karfi ba, zasu shiga su fita, su lalata al'amarin.
Baban Yara ya sha yun'kurin Karin aure sai abin ya lalace, kai karshe ma Abbanku aka sihirce ya hana shi, shikenan maganar sai tashin zance.
To kaima hakan zasu yi maka. Kai ban da rabon wad'annan y'an matan da yake da zafi ta ina kamar ka, zai buge da auren wannan yarinya?. Rabo! Wato ba karamin al'amarine ba. Sai dai na gode wa Allah da ban hana ba, bare ya zama ajalina, ko su zo ta hanyar banza."
Ya ce "sai yanzu na gamsu bamu dace ba Ummah! Muguwar yarinya ce ta gaske. Duk wani law da zata tabbatar da ni a cikin tasku ta san shi. Amma duk an hadu ana mini kallon azzalumi, wai dan uwanka ma baka fita a wajen sa ba. Ai *HALIN YAU* din nake ciki Àllah kawai zai fitar da ni".
"Ta marairaice ta ce "Ai da idan ina fa'din mugun y'ancinsu baka yarda yanzu da ka zauna da su ai ka ga ni. Babbar godiyar da nake yi da basu samu galabar yi mini farraku da kai ba, saboda kullum na kai goshina a sujjuda sai na roka mana tsari da hatsabibancinsu".
Ya numfasa ya ce "Umma kin tabbatar ta kammala karatunta ko?"
Da sauri ta ce "Ta kammala digirinta na biyu ma. Kuma irin wacce kake so ce. Na tabbatar zata yi maka tunda ta yi mini. Sannan bata aiki, ta kuma yarda zata bi dukkan ra'ayinka. Kasan kai din Ubangiji ya kyautata maka halitta sannan kai ka'dai tilon namiji a wajen uwa da uba, wacce duk tasan ciwon kanta ai ririta ka zata yi, domin kai din kana da alfarmomi daban daban wata'kila ma ita ce uwar maza je".
Ya murmusa ya ce "Allah ya sa Umma! Da kuwa Guduyo ta ga karyar yi mini Addu'a, tunda ta gane ita din mai zafin yawu ce shikenan ta kunshe ni take ta gana mini azaba ta hanyar rattaba mini mugayen addu'o'i."
Ta saki tsaki ta ce "Wata'kila ma fa kambun baka ne da ita. Ni fa dama tun tana karamarta nake tsoron ta domin waddannan kwala kwalan idon ta nata yafi kama da na mayu ko masu kambun baka. Sannan matu'kar zata ce dama ayi kaza, to lah shakka abin nan zai faru ko ba yanzu yanzu ba. Sannnan na fa'da maka dama b'akin dake kan harshenta dafi ne, kada ka yarda ku yi fa'dan da zaka nuna mata kana son Amaryarka ta haifa maka maza, domin kuwa zata iya yi maka fatan itama tabi layinta tunda muguwa ce kuma azzaluma."
Maganar ta shige shi ya juya ya ce "Amma kada ki yarda aji kin jingina mata maitar nan kinsan shari'ar bata karewa".
Da sauri ta ce "Hakane, bare ni da basu ki na mace ba, tsabar yadda na tsare musu gaba. "
Ya ce "Ba zaki mutu ba sai kin ga auren Amnah".
Ta murmusa ta ce "Ai kuwa dai da har shampoo zan yi a kaina"
Ya dan motsa kumatunsa alamun murmushi tunda kurajen bakinsa basa bari ya bude bakin sosai bare har ya kyakayata.
Ya ce "To kuma yanzu ma ina cewa duk bayan sati biyu kike zuwa a miki shampoo din?"
Ta girgiza kai ta ce "Ina nufin Tocin"
Ya sake murmusawa ya ce "kurajen nan sun takura ni, ga dariya fal a cikina. To Umma kafin auren Amnah ai gashin na ki babu baki ko daya, tunda yanzu ma farin yafi yawa. Sannan gashinki tamkar kina shafa masa relaxer saboda bak'i da sulb'i. gashi nima haka nawa yake, abin da'di kuma har su Amnah duk kin sam musu."
Ta yi dariya ta ce "Ai komai nawa sai haularka sun samu domin Ubangijin da yake kyautata halittar ya sani da ina da ikon tsara komai yayin halitta to naka yaran sai sun fi na kowa".
Ya ce "na sani Umma! Na gode. Amma zan so, su fiki tsayi, sannan kada su dinga ajiye damuwowin mutane a ransu irin yadda kike yi".
Ta nisa ta ce "Hm nima ai dole ne, ba wanda zai fahimci halin da nake ciki sai wadanda suka shiga takalmina. A zo a same ka da mijinka amma komai ayi muku tare. Alhalin ba mijinku daya ba. Sannan a fifita 'ya'yan wata akan naka ai kowa ya ga wannan lamarin an san kulunboto ne yake aiki ba wai zumunci ba. Na buga na ka'da amma ban samu makarin wannan al'amarin ba har yau. Kai Uban su Safiya ya nema musu duniya sai dai kuma a lahira su yi kallo, dan kuwa ko sun tsallake siradi sai dai su samu gidan haya domin shi yafi dace wa da su a dalilin musgunawa bayinsa da suka yi ta yi".
Ya kame baki alamun mamaki ya ce "Umma wa ya fa'da miki akwai gidan haya a lahira?"
"Ba wanda ya fa'da mini, amma hakan ne yafi dacewa da su".
Ya girgiza kai ya ce "ki dai yi rikicin ki a duniya, amma a lahira kam wallahi walakiri bai san sanayya ba ko ka'dan".
"Tun kafin ka zo nasan da hakan Gudale. Amma zaluncin da mutanan suka yi mini sai dai mai samaniya ya mini sakayya. Amma batun yafiya babu".
Tsawon lokaci suna tare tana ta kushe Halimatu da uwarta da dukkan ahalinsu. Wata maganar ya kwabe ta, wata kuma ta shiga zuciyarsa, mussaman na k'arin auren da take ta haska masa wata'kila a jikin amarya yaran sa maza suke.
****
Cikin abin da bana mantawa shine ranar wata Talata a lokacin cikina ya shiga wata na bakwai har ya yi nisa.
Na kammala aikin gida, a ranar ban je aiki ba. Kawai na ji bayana ya kame, marata ta kulle wani irin ciwon da ban taba yin irinsa ba ya dabaibaye ni. Kafin wani lokaci da bashi da yawa na fita a hayyacina, na zube a tsakiyar falon ban sake sanin inda kaina yake ba. Sai bu'de ido na yi na gan ni a gadon asibiti, duk dangi suna kaina cirko cirko.
Hannu na kai na shafa cikina na ji wayam, wani irin al'amari ya daki zuciyata. Hawaye ya balle mini. Yaya Al'amin da yafi kowa kusanci da jikin gadon ya matso yana fa'din "Maimakon ki ce Alhamdulillah sai kuma ki fara da kuka? Menene yake miki ciwo?
Na girgiza kai na ce "Babu".
Daga nan kowa ya matso ana mini sannu, Yaya Gudale aka babbake a gaban Yaya Al'amin tamkar me son ya fahimtar da shi karfin kusancin da yake tsakaninsa da ni, yafi wanda yake tsakanina da shi, shikuma Yaya Al'amin din ya je gefe ya bashi guri. A hankali na fahimci tiyata aka mini aka raba ni da cikin jikina, shin da rai ko babu rai?"
Na rasa wa zan tambaya tunda ba wanda ya mini maganar.
Da safe ba kowa sai Umman Danladi Nasidi, Gudale ya iso da abin karya wa. Umma ta yi dabara ta fice. Ina zaune akan gadon. Tuni Umma ta goge mini jikina, ina sanye da doguwar riga marar nauyi.
Ya mini sannu, na amsa a hankali. Ya ce "Yanzu Guduyo menene matsalarki da har jininki ya yi mugun hawa haka?
Kowa a family sai kallon uku saura yake mini, hatta Abba da kyar yake amsa mini gaisuwa, dan girman Allah me nake yi miki ne?".
Na girgiza kai na ce "Babu komai".
Ya numfasa ya ce "Allah ya baki lafiya"
Na ce "Ameen".
Muka dan yi shiru gaba'daya. Na kalle shi na ce "Ina Afra take?"
Ya zuba mini ido ya ce "Tana wajen Sakina".
Na sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa, domin yarinyar tana da kulafucina, ko Umma ba yarda take da ita bare kuma Mama.
Amma tana yarda da Sakina, na sani kuma zata samu kulawa tamkar tana hannuna.
Na sake cewa "Bebin fa ko ta koma ne?"
Ya zuba mini ido sosai ya ce "waton kin hakkake dama mace ce a cikinki ko? Saboda baki fasa addu'a ba".
Na dan ta'be baki na ce "Ba haka bane saboda kawai na hakikan ce haihuwar jinsi gadonta ake yi".
Ya mi'ke ya ce "gado kamar Yaya?"
Ba fargaba na ce "Yaya Al'amin matarsa namiji ta haifa ga shi nan har yana rarrafe, kuma Yaya Abdallah sai da ya haifi boys guda biyu a farko sannan ya samu matan daga baya. Ka sake duba gidan Yaya Babangida mace aka masa a farko amma maza uku suka biyo bayan macen.
Yaya Ammar kuwa har yau macen yake fata bai samu ba. Kaga matayensu sun gado uwarsu ne. Dama kuma galibi anfi gadar uwar Mlmiji, shiyasa Antin Zaria bata haifi girl ko daya ba ba. Ga su Anti Sakina da Anti Ramla kowa mace daya ta haifa, boys dinsu sunfi yawa. Na gasgata wannan maganar yanzu saura uku kafin a samo maka boy, tunda mata biyar ka biyo rigis. Na gado tawa uwar mijin Ubangiji sarkin adalci".
Ya nuna ni da dan yatsansa ya ce "Ni kika yi wa wannan cin mutuncin?
Akan idona kika yiwa uwata gori?
A gabana kika nuna mini Yan uwanki sun gado uwarku. Ni ma tawa uwar na gado?".
Ban san me ya same ni ba, babu tsoronsa da nake ji na ce "Eh ko k'arya na yi?.
Ai na fa'da maka haihuwar girls a gidanka yanzu aka fara".
Idan na zauna da ke ko?"
Na make kafa'da na ce "your choice".
Ya girgiza kai ya ce "Anya allurar nan ta sake ki kuwa Guduyo? Ko kuma kin yi gamo da jinnil ashiq ne suke son su miki ingiza mai kantu?"
Idona da hawaye na ce "Ai na sani ba'kin cikin da ka yi ta kunsa mini dan cikin ya zube ne burinka bai cika ba, shine ka zuba mini magani a lemo to ka ci riba ka yi kisan rai, tunda an riga an busa mata rai, Allah ya jikan little Sakina. Allah ya sa ta zamo me cetona".
"Eh ai ke ka'dai kike da hakki a kanta, shiyasa zaki ce ta cece ki, sannan ni ba sunanta Sakina ba Wallahi, sunan yarinyata *Adama* sunan kanwar Umma ta Yola".
Na kafe shi da ido, ina rasa me zan ce masa dan na raba mana takaicin da nake ji.
Sai na murmusa na ce "Àllah ka jikan Umma Adama ka shaida na yafe mata, ka ajiye mini ita a makarantar *Annabi Ibrahim(A.S).* Ka kawo new Adama a kusa".
Ya kufula ya ce "Duk masifarki kin gama yi mini haihuwa, wannan yarinyar tabbas kin zame mini kadangaren bakin tulu. Amma na bar ki da mai Rumfa. Ranar tashin alkiyama a mana hisabi, tunda kika mini kazafin kisan kai".
Na murmusa na ce "ka dauki mataki tun yanzu kawai ka sauwakewa kanka zaman takura da zalunci".
Ya ce "Allah ya baki lafiya. Na tabbatar ba a hayyacinki kike ba Billahillazi. Gaki da yawan azkar Guduyo! wa'danne irin kafiran shaidanune suke neman susuta ki haka?"
Ya fice yana cewa "Kalu Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un".
Na murmusa na koma, na kwanta na ce "Allah ka saita tunanin wannan bawa naka".
Sai da na shefe sati sannan aka sallame ni, tun lokacin kuma bai sake yarda mun kebe ba, bare wata sa in sa ta ha'da mu.
Wata guda na warke, sai dan abin da ba'a rasa ba. Zaman mu ba yabo ba fallasa. Dama ya saba bani lokaci sosai idan na haihu tunda cs ake yi mini. Baya nemana sai na yi arba'in. Amma dai na sani a cike yake da ni a dalilin yana yawan cewa na ci mutuncinsa a akan idonsa tunda na yiwa uwarsa gori. To wallahi na jira sakamakon wannan katobarar dan kuwa ba zai bari ta bi ruwa ba.
Ana haka Abba ya fara ciwo a tsaitsaye, tun yana ganin likita anan har ya fara jaurar zuwa Egypt asibiti.
# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?*
*kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*.
*Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.*
*Sister Zainab 08039315577.*
*SDK*
*71&72*
Kowa yana cikin alhinin jinyar Abba! A dalilin an gano yana fama da ciwon mafitsara. Sosai yake shan wahala. Wani aiki da aka yi masa a Egypt ya dan samu sau'ki, har yana yan harkokinsa duk da dai baya fita, ya yi nisa.
Ganin sau'kin da ya samu ya sanya Yaya Gudale ya zartar da kudirinsa na a nemo masa auren Munubiya Baffah K'unci. Y'a a wajen attajirin 'dan kasuwan da ya yi shura. Sannan uwarta kawar Umma ce ta sosai. Kusan ma ita ta yi masa shunenta.
Na santa tabbas me kyau ce, kuma sirirya ce ta gaske. Sannan bata cika tsayi ba. Ta dai dace da y'ar shawalwala dai dai da tsarin Yaya Gudale.
Gaban Baba ya fara kai maganar aje a nemo masa aure a gidan Alh Baffah Kunci.
Ba ja in ja ya goya masa baya. Baba da kansa ya shirya komai, sai da komai ya kankama sannan ya sanar wa Abba.
A matu'kar sanyaye Abba ya ce "Bana son wannan auren da zai yi. Babu nagarta a gidan da ya kwaso auren. Da a ce gidan tarbiya ne ai ba zamu hana shi abin da Ubangiji ya halasta masa ba. Saboda dalili na son zuciya".
Baba ne ya dinga kawo misalai iri iri na bai kamata a soki lamarin aure ba. A bashi damarsa, abi lamarin da addu'a.
A kan dole Abba ya ha'kura. Aka kai ku'din aure, aka saka ranar aure wata biyu masu zuwa.
Baba ne kawai yake kan maganar kane kane, kuma wani ikon Allah bai fa'da wa Mama ba. Sai kuwa su Umma da mukarrabanta Anti Maimuna da Anti Juwairiya.
Umma kuma ta hana kowa ya fa'da mini maganar a cikin yaranta. Hatta Sakina sai da Umma ta yi mata gargadi. Duk da ta sani, amma ta kasa fa'da mini a dalilin kiyaye maganar uwarsu. Sai dai gaba'daya a susuce nake ganinta.
Karin abin da yasa ban samu labarin da wuri ba. Abba ya koma ganin likita kwanaki biyu da kai ku'din auren, suka tafi da Baba da kuma Yaya Gudale. A can suka tarar da Yaya Abdallah.
Mama bata sani ba, bare na ji. Dan haka ina zaune cikina kwarkwaro. Umma da su Anti Maimuna suna ta shiri bikin kece raini, suna ta hada kayan lefe na alfarma.
Sati hudu suka yi a Egypt, suka dawo. Sai lokacin na lura da kaffa kaffa da wayarsa da Gudale yake yi. Sannan da zarar ya dawo daga office zai tsala wanka ya fice. Tun ban damu ba har na fara kokwanto.
Saura sati biyu biki. Na je duba Abba. Ya zaunar da ni yake ta yi mini nasiha mai ratsa jiki. Tabbas jikina ya yi sanyi duk da dai tunda jinyar nan ta ci karfinsa ya ninka yin nasiha akan girman ha'kuri da kuma riko da zumunci.
Amma nasihar wannan ranar ta banbanta kwarai da gaske. Domin cewa ya yi "Na hore ki da yin ha'kuri Halimatu! Amma ban ce ki yi hakurin zalunci ba. Ko da na ce ban da kawo k'ara ai na fa'da miki ne dan na kubutar da ke auren Sadiki! Amma tunda Ubangiji ya kaddara mijinki ne kuma uban y'ay'anki ne ai sai da aka yi. Ina kuma gode miki sosai. Amma a yau zan tabbatar miki kada ki yadda da ha'kurin da kika san cutar wa ne a gare ki. Kada ki yarda ki dauki wula'kanci saboda ni, ko ki yi ta zaman takura saboda na ce babu kawo k'ara.
Na janye miki wanccan takunkumin. Sannnan ina son ki kara ha'kuri, yadda baki tayar da hankalinki akan maganar aurensa ba, ya sanya na saka Abdallah ya canja miki mota, gobe kuma na sanar da Sakina ta zo kuje ki zabi duk kayan da kike so, sai a fitar da na wajen ki, ki bayar, ko ki yi sadaka da su.
Na siyo miki sarka ma tana cikin kayana, bana son kowa ya ga ni. Shiyasa na boye miki ita. Sai ranar juma'a zan baki.
Na yi sakare cikin rashin fahimta da zullumi mai tsananin gaske. Wai waye zai kara auren ne?
Na gama lissafina, jikina ya dauki kyarma na dinga jin tashin hankali yana shiga ta. Duk yadda na so yin jarumtar hadiye tashin hankalin da ya ziyarce ni farat daya sai da na kasa. Na kifa kaina na dinga kuka a tafin hannuna.
Kuka nake yi na kaico iri iri. Kuka nake yi na takaici, ina ma ace na ji maganar Abba! Ina ma na ji kashedin mahaifiyata, ina ma ace na ji shawarar Sakina. Wai aure Gudale zai yi? Amma ban cancanci ya zaunar da ni ya fa'da mini da bakinsa ba? Bani da wannan darajar, ba dan Abba ba wata'kila da sai saura wata kenan zan samu mai fada mini tunda kowa yana girmama ra'ayin Gudale ne.
Kukan da nake yi, ya ta'ba Abba sosai ya kira ni a sanyaye cike kuma da soyayya da tausayi mai yawa.
Ya ce "Halima kukan na menene ko dai akwai matsala ne?"
Na girgiza kai na ce "Babu Abba! Tausayi kaina ne ya kama ni, da ace ka mutu da sai dai na ji ana shigo da amarya saboda bani da muhimmanci a wajen kowa. Dama ya'ya mata basu da daraja