Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
"Umma mutum yana da ikon sakawa wani ciwo ne?
Bani ka'dai bane, da akwai maza da suke yin laulayi.
Na sani kuma da zabi za'a bawa Guduyo ba zata yarda na dinga wahalar da nake yi ba.
Ki dinga yi mana addu'ar na samu lafiya, ita kuma ta sauka lafiya".
Idan ta ji hakan sai ta yi gum. Tana jin takaicina kamar ta shak'e ni.
Cikin sa'a bai dauki lokaci mai yawa ba, ya warware.
Komai kuma yana ci babu zabe.
Ban ta'ba jin dadin aure ba sai a wannan lokacin. Ba wai baya bata mini ba, ba wai da'di nake ciki a kullum ba.
Amma akwai mutuntata wa a tsakaninmu. Sannan bani da matsalar komai, duk abin amfani bani da matsalarsa. Haka nan bangaren sutura ma babu laifi. Abu mafi da'di sassaucin da Umma ta yi. Ta rage yi masa famfo a kaina, tunda shima ba ya yarda ya tattauna matsalata da ita.
Dan haka ba kasafai muke samun sabani ba.
Ya canja wa Afrah makaranta. Ya daidaita ta da Aman. Komai tare yake yi musu, ko fita zai yi matu'kar ba wajen aiki bane to tare zai fice da su. Hankalina ya kwanta sosai. Ban damu da saurin fishinsa ba, tunda na yi sa'a indai na yi tuba zai ha'kura.
A hakan har watan haihuwa ya tsaya aka ciro mini kyakkawan jaririna mai kama da Aman.
Komai na Gudale ne a jikin yaron.
Murna kan murna Gudale ya yi fadi yake "Baban Gusau ne wannan. Sauran ki Baban Yara ".
Na murmusa na ce "Maman Kebbi fah?
Tunda na lura so kake
yi sai ka jera sunayen yan gidansu Abba".
Ya murmusa ya ce ai kuwa domin so nake nima nawa autan ya zama Baban Yara ne".
Na ce "Gashi kuma na gama. Haihuwa biyar duka c.s abin a jinjina a tausaya mini ne".
Ya yi dariya ya ce "Ke kya fara?
Baki haifo mini Sakinata ba?"
Na ce "Sakinarka ko tawa?"
Ya ce "Karfin hali fa take gwadawa nan duniya Sakina ba wanda take so kamar ni har ya'yanta kuwa".
Yana rufe baki ta shigo da murmushi a fuskarta.
Nan da nan kuma sai ya waske yana fa'din "Wa zai yiwa Sakina takwara kuma ana zaune kalau? Haka siddan yarinyar ta kwaso halinta. Tunda dai na haifo photo copy dinta ai ya isa ta gode mini.
Jiya da naga hoton Amnah a status din Antin Zaria har tsorata na yi da yadda kullum take sake juyewa tana komawa tamkar Sakinan Guduyo sarkin shiga tsakanin soyayya".
Na jima ina kallonsa, ina mamakin yadda ya murde tamkar ba shi ya gama kwarzanta ta ba, yana fatan na haifo masa baby girl ya sanya sunanta.
Amma tana shigowa ya waske shi a dole bai damu da ita ba.
Ta sake murmusawa ta ce "Autan Umma ina ce mun shirya?"
Ya ha'de rai ya ce "Ni fa duk wanda ya fifita wani a kaina babu aminci a tsakaninmu.
Idan kina son na yafe miki to ki daina kwashe soyayyar da kike mini kina bawa Guduyo".
Ta kyal-kyale da dariya tana fa'din "Gudale ka samu duniya Allah yasa lahira tafi hakan. Ni na taba ganin mai kishi da matarsa irin ka?
Ka ce Al'amin ba zai sota sama da kai ba, hakan kuma aka yi, kan dole ya zabe ka ya bar ta, yanzu kuma ka ce nima ba zan fi sonta akan ka ba? Wannan adalci ne?"
Ya matsa kusa da ita ya mika mata yaron ya jingina barin jikinsa a kafadarta ya ce "Saboda duk cikin yan'uwana na fi sonku. Dan haka zan ji ba'kin ciki mai yawa idan kuka fi son wani a a kaina. Tare muka ta so ke ce babbarmu akan me wata da ta zo daga sama ta kwace mini ku, kuma ayi zaton an so zaman lafiya da ni?"
Daga ni har Sakina muka yi dariya.
Na ce "To fa'da masa ya bar ni na yi zumunci da Farisa, nima ita ce kawata kuma yar'uwata amma sam baya barina na je gidanta, Yaya Ashir ai dan-uwana ne, kuma ni ban ta'ba sonsa ba tun da. Bare yanzu da bana ganin kowa a gabana sai Dadin Afrah."
Ya murmusa ya ce"shikenan ku yi zumuncinku, Ashiru ma na yafe masa zaluntata da ya dinga yi muna yara. Al'kawari na yi babu ni babu shi, amma jiya Baban Yara ya saka na yafe masa na dawo da zumuntar da na yanke da shi".
A wannan karon Sakina ce ta yi dariyar tana cewa "Idan baka yafe masa ba, me zai rage shi?"
Hidima sosai Yaya Gudale ya mini, wannan ce haihuwar da aka yi masa ya yarda shi aka yiwa ya yi dukkan hidima, dan ko haihuwar Aman da ya samu namijin da yake kulafaci cewa ya yi indai iyayen yaron ba zasu yi hidimar ba na d'aure musu shi a d'ankwali.
Amma wannan kam kan jiki kan k'arfi yake yin komai.
Tuni kuma ya yiwa yaro huduba da Musa. Da kansa kuma ya ce Arif za'a dinga kiransa.
Baban Gusau ya yi murna sosai.
Ya taho takanas ya kawo raguna biyu da kayayyaki masu yawa.
Iyalinsa ma sai da suka zo ganin mai sunan mijinsu.
Bare kuma Farisa da take gari.
Hankalina ya kwanta sosai. Ba abin da yake damuna.
Sai matsalar Yaya Gudale na saurin hasala, ban isa ya ce yana da bu'kata na bijire ba, idan kuwa na bijire ya dinga kunci kenan da tashin hankalin ai dan ya fa'da mini sirrin zuciyarsa ne na ba zai sake yin aure ba shine nake tak'ama.
Ina laifin ya yi ha'kuri, na yi har sati biyar?
Ban samu kwanciyar hankali ba sai da na koma kwana a dakinsa.
Na riga da na gane shi komin shirina da shi, komin kyautata masa da zan yi matu'kar zan yi nesa da shi a shimfida to kuwa zai shafe idonsa ya manta komai na alherina. Shi dai babban alherin da zan yi masa da zarar ya zo da bu'katarsa na bar komai na tarairayaye shi. Shikenan na mutuntata shi, ina kuma son shi.
Akasin hakan kuma zai zama dalilin da zai ce na raina shi, ban damu da shi ba. Shikenan sai ya zama sanadin da zai sa ya yi mini fishi sosai.
Ni kuma an jarrabe ni da k'yamar ganin fishinsa. Idan ya botsare mini gigicewa nake yi har sai na shawo kansa sannan nake nutsuwa.
Ban Jima da haihuwa ba. Auren Junaid da y'ar tsohon Gwamnan Kano ya taso.
Shirin biki ake yi na attajirai kuma yan boko.
Irin tanadin da ake yiwa bikin ka'dai ya isa a gane bikin manya ne kuma yan boko.
Anyi shagali irin wadda ba zai yiwu na fa'da ba. Antin Zaria da mijinta Kano suka dawo tunda duk danginsu suna na dan haka anan za'a yi bikin.
Tunda ga kan bikin dangin amaryar dana ango anyi shine cikin farin-ciki da wadata.
An bawa kowa damar ya shiga dakin taro, babu shamaki. An kashe dukiya sai fatan alheri kawai.
An kai amarya jiya, sai kuma kwarya kwaryar liyafa da mai d'akin Gwamna mai ci ta shirya a gidan gwamnati, wannan kam an takaice adadin mutane saboda yanayi na tsaro.
Muna sashen Umma ana ta aiki.
Sai ga Anti Maimuna ta shigo da hadaddiyar envelopes a hannunta
Ashe Katina ne guda shida a ciki.
Gudale ya shigo, muka yi magana ya karbi mukullin gida wai ya manta nasa a office.
Har ya fita sai kuma ya dawo ya shige ciki wajensu Umma.
Bai wani jima ba nima na shiga dan kwantar da Arif da yake bayana.
Ai kuwa sai tashin hayaniya nake jiyo wa daga dakin Umma.
Muryar Anti Maimuna sai rawa take yi, tana fa'din 'Umma ta saka baki Gudale ya bata katin ya zata yi da kawarta data yi mata waya ta shirya ta zo ta ajiye mata katin?"
Yayin da shi kuma ya rantse ba zai bayar ba.
Umma ta ce katin guda nawa ne shin?"
A raunane ta ce "shida ne, amma tun acan Antin Zaria ta cire daya ta rubuta matar Abdallah.
Dan haka saura biyar
Ni, Juwairiya, Ramla, Sakina, shine dayan zan bawa k'awata. (matar d'an majalisa ne ita ma).
Ya zo ya dauke ya ce na matarsa ne.
Tunda matar Abdallah zata je ai ta wakilci yan kofarsu, idan aka bata ita ka'dai, to Farisa fa?ai duk matsayinsu daya a gidan".
Ya hassalo sosai ya ce "Tabbas matsayinsu d'aya.
Amma ke kuma na fiki matsayi ko?
Tunda kika raba muku a tsakaninku kin gamsu su Ramla ya zama dole su je, to ni kuma fa?
Nawa na dauka, bani kuma da ra'ayin zuwa dan haka matata ce zata je mini".
Rikici ya kaure ta fara kuka tana fa'din "Umma ta saka baki mana".
Umma ta yi k'undubalar cewa "Gudale bata ka ji, kubutar da ita jin kunya".
Nan da nan ya ce "Umma a wula'kanta ni, ta hanyar cire ni a jerin yaran gida sannan ki bi bayanta?
Inda ka'ida za'a bi ai kamata ya yi na samu biyu, amma d'ayan ma sai a hana ni saboda ba ni da k'ima, ko saboda bani da alaka da gidan?
Wallahi tunda ta dai-daita mini mata da wata a cikin gidan nan to bazan bata ba, ko gaban Antin zamu je ai na sani ta lissafa da Guduyo, amma ita tunda bata son ta shiyasa zata kyautar da nata a kawarta.
To Wallahi sai Guduyo ta je bikin nan, sai dai ita ta ha'kura ta bada nata, ko kuma ta tozarta ba matsalata bace."
Anti Maimuna ta fashe da kuka tana cewa "Ya wula'kanta ta saboda ni".
Yayin da shima yake cewa "ita ta wula'kanta shi tunda kawarta ta fi matarsa.
Umma kuwa da ke har gobe bata son fishinsa ta kasa yi masa fa'da.
Suna ji suna ga ni ya fito da katin nan.
Ni kuma tuni na fice na shiga ana cigaba da aiki da ni.
Ya fito ya kira ni.
Ba sukuni ya ce "Anjima ka'dan ki dawo ki shirya zan kai ki govt house."
Na ce "To".
Ya tafi ya bar ni, da sake saken zuciya.
Damuwa ta d'aya yadda Anti Maimuna zata sake tsananta mini.
Dama yaya lafiyar kura?
Dole Anti Maimuna ta bawa kawarta ha'kuri.
Ba karamin da'din halarta bikin nan na yi ba a dalilin ganin Anti Sa'adan Mk.
Ita ce a gaba a kawayen uwar ango.
Bata halarci ragowan events din ba, a dalilin sai jiya ta dawo daga Egypt raka Hajiyar Bichi ganin likita.
Na kallesu suna high Table ita da Antin Zaria.
Sun yi matu'kar kyau, ba wanda zai ce sun zarce shekaru arba'in.
Ilimi da gayu ya samu muhalli.
A yanzu haka Sa'a ita ce shugaba a kungiyar kare hakkin mata da yara.
Sannan tana da gidauniyar lauyoyi mai zaman kanta wacce ita ce take jagoranta.
Na dinga kallonsu ina fatan Nima na zama kamarsu. Manyan mata sun kewaye Antin Zaria.
Ba abin da yafi ilimi Dadi.
Ga Amnah na gefenta bata yarda ta barta a ko'ina. Kowa gani yake autar ta ce tunda duk kama suke yi.
A wannan lokacin na ji sha'awar na koma na yi masters dina ya kama ni.
Ko ba zan yi aikin ba, zurfafa ilimi abu ne mai matu'kar amfani. Ga dai Anti Sa'a, na tuno sadda Yaya Gudale ya hana ni aiki, har misali da ita Antin Zaria ta yi mini, ta ce itama mijinta hana ta aiki
ya yi, amma ta yi ta zurfafa iliminta. Dan haka nima zan yi kokarin zurfafa ilimina duk da dai na sani sai na jure jidalin Gudale a dalilin baya kaunar ya shigo gida bai gan ni ba tamkar yaro mai shan nono. Gashi bata aikin har yau amma tana da hanyoyin samun ku'di daban daban, ga kuma kungiyoyin tallafawa mata da marayu da take jagoranta.
Haka aka gudanar da walimar nan cikin ilimi da nutsuwa.
Haj Sa'adah Mk ita ta yi bayani a madadin uwar ango.
Duk yadda ake kwarzanta dadin muryata na tabbatar ta Anti Sa'a ta kere tawa. Gashi a gayance cikin gogewa da ilimummuka daban daban take maganar.
Nasiharta ta fi karkata a yiwa Amarya nasiha da kuma gujewa sharrin kawaye. Bayan haka sai gode wa kokarin miji. Ta kuma ja hankalin angon akan ya zama adali mai yin sassauci akan amaryarsa domin ta bar kowa nata tana zaune da shi."
Kowa ya dinga murmushi a dalilin jawaban nata babu son zuciya, ba kuma ta ja shi ba.
A takaice ta yi shi bai gunduri kowa ba.
Tana kammala wa dakin ya dauki tafi raf raf. Duk yadda dakin ya ha'da zakwakuran manyan mata sai da kwalliyar Iyah Basiru ta yi matu'kar birge kowa.
Ta zama big madam abin alfaharin miji da y'a'ya.
Mussaman da a yanzu burin Baban d'anta Jawad yake daf da cika domin ana tsakiyar shirye shiryen kaddamar da jirgin da ya siya mata, ya kuma sanya masa D'an iya airlines.
Ban sake tsinkewa da lamarin Antin Sa'a ba sai da mijinta ya zo daukarta.
Muna harabar gidan gwamnati dankareriyar motar ta shigo. Shi yake tukin da kansa.
Ya fito duk da shekarun girma sun hau shi yana nan a tsaye da karfinsa da lafiyarsa. Mussaman da yake rayuwar ta yi albarka, an cimma dukkan buri.
Matashin saurayi ne ya fito a gaban motar.
Ina jiyo Anti Sa'a tana fa'din yanzu Malam baka taho mini da twins ba?"
Ya murmusa ya ce "Na fa'da miki ba zan koma gida ba."
Amir ya ce "Mami dan Allah ki zo mu tafi, tun safe Malam yana ta yawo da ni, na gaji, ina son kuma na je naga ko Mamana ta sha maganinta".
Sa'a ta kalli yaron da tarin kauna duk da har yau bata ta'ba fa'da masa ita ce Uwarsa ba.
Ta ce "To Amir, bani mintina uku mu yi sallama da uwar bikin".
Ina kusa da Antin Zaria ta iso suka dan rungume juna suna yin sallama da fatan alheri.
Tana cewa Anti ta yi kokarin zuwa kafin ta wuce domin zasu yi bikin kaddamar da Dan iya airline da kuma katafariyar jami'ar da Mk ya kwashe shekaru goma yana gininta.
Anti Zaria ta ce "zan zo In sha Allah? Oh burin Jawad dai ya cika, jirgin nan na cikin ransa. Àllah ya sanya albarka. Sannan ki fa'da wa oga a bani vacancy na mutum biyu dan su yi aikin koyar wa.
Sa'a na dariya ta ce "Duk da dai kinsan har yau din nan ra'ayinsa shine akan gaba, amma bana jin zai tankwabar da bukatarki".
Ta rakata har gaban Mk, ya yi mata murna, ita ma ta yi godiyar ta ga sakonsa.
Sannan ta yi masa murnar Cigaban da ya zo musu, ta kuma gabatar da bukatarta.
Cikin yakana ya ce" daga yanzu zuwa ko yaushe duk tsayin zamani kina da alfarama a makarantata. Kada ki ji komai."
Ta yi godiya ta ce "A gaida Farida".
Ya bata fuska ya ce "Ai baki gayyace ta wannan bikin ba, bayan duk kokarin da ta yi, duk wadancan events din ta zo tunda k'awarki bata nan, amma saboda son kai a wannan sai kuka ware mini ita".
Dariya saosai Antin Zaria ta yi ta dinga fa'din Afuwan ".
Yayin da Sa'adah ke gefe bata ce komai ba.
Ta kalli Amir ta ce "ka gaida Mamanka da kyau".
Ya amsa da "zata ji Anti".
Suka shiga mota, Mk na tu'ki, Sa'a na gaba, Amir kuma na baya a zaune.
Charting yake da Jawad.
Zuwa yanzu ya san Sa'a ce ta haife shi, amma bai nuna ya sani ba tunda daga ita har Mk ba wanda ya zaunar da shi ya fa'da masa.
Farida kuma har yau din nan soyayya take nuna masa gangariya fiye da Amira.
Dan haka shima yake tare da ita, yake son Amirah fiye da su Jawad ko dan sun sha nono guda ne?
Amma baya iya danne kaunar Sa'adah matu'kar suna tare, ya dinga yin abubuwa na soyayyar jini, ita kuma tana lallaba shi.
Amma komai nasa da dukkan al'amarinsa bata shiga.
Farida ce uwarsa har gobe.
Ha'kuri da juriyarta ya sanya ta cigaba da zama tauraruwar Mk. Har kuma yanzu idan ta murde masa rasa sukuni yake yi, shiyasa yake kaffa kaffa da abin da zai sa ta tunzura. Duk da yana motsa mata kwanji idan zata zo masa da son rai, wani zubin kuwa kan dole yake ha'kuri ya bar ta domin rikici a jininta ne, bare kuma ya hadu da kishi.
Shi kuma sonta da tsoron fishinta a ransa ne, ba zai canju ba.
A hanya ya ce "Burinki ya cika, Jawad ya siya miki jirgi"
Ta kyal-kyale da dariya ta ce" ya ce fa tare ya siya mana."
"Ya kyabe baki ya ce "Wannan shine yaudara. Tun yana kankani kika kitsa masa maganar da ya gimamata a zuciyarsa.
Ai kallonku nake yi ke da shi kawai. Kuma wai har kuna iya kalubantar nafi son su Amir".
Ta waiwaiya ta ga voice note yake yiwa Jawad, hankalinsa baya tare da su, ta dawo da hankalinta kan Mk.
Ta ce "Malam! Mu bar maganar nan sai mun je gida kada ya ji me kake cewa yaje ya fa'dawa uwarsa ta zaci kamar sun dame ni ne, dan yanzu idan ta ji wannan maganar idan ta tisa ni a gaba da tsokana cikin dabara sai gidan ya yi mini zafi.
Tunda a fili zaka nuna ni ce Babba. Ha'kuri kawai zaka ce na yi".
Ya murmusa ya ce "Akan me ba zan baki ha'kuri ba, kin shige zuciyar mijinta kin yi kane kane kin bar ta a sakade ai dole ki yi ha'kuri da ita kema. Ba zai yiwu a mata duka biyu ba".
Sa'a ta fashe da dariya tana cewa "Allah ya so gidan kowa daban, da ina nan tana mini kisan mummuke, kai kishi da irinsu Farida sai an shirya matu'ka gaya. Allah ya so ni, ya hore mini kai".
Shima ya fashe da dariya ya ce "kinsan kuwa zanci gaba da nuna ban fahimci ita matsokaniya ba ce".
"Eh ai Amarya ce da bata laifi a wajenka".
"Ke kuma uwargidana kuma zuciyata gaba'daya ba".
Amir da yake jinsu ya ce "ita kuma Mamana hantarka ce ko?"
Suka fashe da dariya dukkansu uku.
A haka har suka isa gida suna hira cikin nisha'di.
*Madallah da Mk da ahalinsa*
Fatan alheri ga ahalin *HALIN YAU*.
Yadda ya kawo ni da kansa haka ya dawo ya dauke ni. Afrah da Aman na gaban motarsa suna ta cin inibi.
Ina fito wa ya ce su koma baya su zauna.
Da kansa ya fito ya bu'de mini motar, ya karbi Arif sai da na zauna sosai sannan ya miko mini shi sannan ya rufo mini kofar.
Muna tafe cikin farin-ciki, duk Wanda ya ganmu sai ya yi sha'awarmu.
Duk macen da ta gan ni a hakan ga miji ga y'ay'a reras ha kuma wadata sai ta yi sha'awata ta yi fatan Ina ma itama ta samu hakan ba tare da tunanin irin kalubalen da na tsallake, nake kuma fuskanta ba.
Tunda dai har a yanzun da muke zaune kalau ha'kuri nake yi kan ha'kuri.
Sau'ki kawai na samu.
Sati daya da bikin Antin Zaria