Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
da ha'kuri a kan zan kawo.
Yaya Sadik kuwa ya dinga fa'din "Ai kuwa kin yi wa kanki attajiri irin Alhaji Anas a ce yana son ki ki ce ba kya son sa? Bayan kyakkawan mutum ne ga nagarta?"
Na bashi amsa da cewa, "Ba na son sa tunda dai ni zan zauna, ba wani ne zai zauna mini ba".
Ya tabe baki ya ce, "kyakkawan da shi fiye da ke?"
Na 'ki tankawa, domin so yake ya samu damar da zai yi mini cin mutunci. Daidai lokacin shi ma ya fara son wata Nusaiba Lawal Makole a gabanmu ka'dan suke Islamiyya 'daya muka yi. Babanta attajiri ne kwarai da gaske. Daliba ce a ECOSAT, tana karantar Lab Science.
Siririya ce sosai, sannan doguwa fara. Ta dai dace da muradinsa. Kullum ni yake damun na samo masa lambar wayarta, mafi yawa a hanyarmu ta zuwa makaranta ko dawowa zancenta yake yi, ba ya la'akari da yanayina da yake canjawa matu'kar zai sako maganar Nusaiba.
Haka kuma ba na ta'ba bari hirar ta yi tsayi, zan yanke
ta, ko na bar shi ya yi ta abarsa shi ka'dai.
# Team Sabo da kaza
# Ana tare.🤝
# Surayya Dee
✍️.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?
Page 9&10
*Fatan alheri ga marubuta Iyayen dakina masu wankakkiyar zuciya*
*FADILA LAMI'DO*
*BINTA ABBALE*
*Na gode sosai da kokarinku kan rubutuna*.
*Allah ya kara muku basira da daukaka*.
Ranar Talata, a ranar da na kammala rubuta jarrabawar 'karshe ta zango na biyu ma'ana 'karshen aji biyu (Second Semester), tana cikin jerin ranakun da ba na mantawa. Ba don komai ba, sai don dalilai guda biyu.
Na farko, wani irin al'amari ne ya faru da na kasa tatance shi. Domin jarrabawar 8-10 nake da ita.
A ranar kuma Yaya Sadik ne kawai a gidan, daga Yaya Al'amin har Yaya Abbas sun yi je Moriki ta'aziyyar rashi da aka yi, har da Yaya Sadiq Abba ya ce su tafi amma ya 'ki ya ba da uzirin yana da test. Ba irin 'kiran da ban yi masa a waya ba, amma da yake 'yan tsiyar na kansa bai 'dauka ba, tunda ba shi da darasi a wannan lokacin. Na kalli agogo na ga kafin na fita na samu abin hawa zan iya makara, don haka na manta dokar hana ni zuwa shashensu.
Da na duba harabar gidan na ga ba kowa, sai kawai na doshi gurin nasu. Na shiga da sallama na tarar da shi a kwance idonsa biyu. Amma ya yi la'kwas tamkar ruwa ya cinye shi. Daga bakin 'kofar na tsaya tunda a tsorace nake a dalilin karya dokar da na yi.
Na marairaice na ce, "Ka rufa mini asiri Yaya Sadiq ka kai ni, na yi maka al'kawari daga yau ba zan sake matsa maka ba. Zan fa'da wa su Abba ko mai Adaidaita ne a daukar mini".
Ya yi shiru tamkar ba da shi nake ba.
Na bu'de baki da nufin sake ro'kon, ya 'daga mini hannu alamun na yi masa shiru.
Na kame bakina tunda nema nake yi a gunsa.
Cikin murya marar amo ya ce, "Kasala ke damuna, 'kafafuna ciwo, ke komai ma ciwo, ga sanyi nan sosai nake jin sa har cikin 'kashi.
Zo ki mini tausar 'kafafuwana idan na ji dama-dama wata'kila na iya tu'kin".
Ba tunanin komai na 'karasa na fara yi masa tausar, ban yi da yawa ba, ya dinga wani irin nishi, ya mi'ke. Ba zato kawai na ji ya 'kan'kame ni da 'karfin gaske. Yana wani irin abu, can kuma ya yi wani irin al'amari mai kama da gurnani, jikinsa ya saki sosai, ya sake ni.
Ina bakin gadon ina fama da 'barin jiki da kuma tsoro, domin boxer 'din jikinsa bai iya hana abin *da ya feso shafa ta ba.
Kafin na ce wani abu, sai jin sa na yi cikin tsawa ya ce, "Fitar mini a 'daki, ni kam ba an hana ki zuwa nan ba?"
Jiki na rawa na 'dauki 'dankwalin da ya zame a hannu ban ma iya 'daurawa ba.
Sai da na je bakin 'kofa na juyo, na gan shi ya mi'ke, ya doshi ban'dakin cikin 'dakin, na 'daga murya na ce, "Zacka zo ka kai ni 'din?"
Kai kawai ya 'daga mini alamun e.
Na dinga fa'din "Na gode sosai!
Sai dai me? Haka na fita 'dankwali a hannu saboda tsananin ki'dima. Ina fita din kuma, Abba ya hango ni, ba kuma yadda zan yi na koma ko na 'buya.
Saboda fili ne sosai ba wata ma'boya.
Ya ja ya tsaya, ni ma na tsaya a inda nake, cikin rawar jiki na samu na 'daura 'dankwalin na gyara zaman Lab Coat din jikina. Na karasa gabansa na tsugunna ina gaishe shi cikin rawar murya irin ta rashin gaskiya.
Fuska a 'daure ya ce "Me kika je yi can wajen?"
"Abba makara zan yi shi ne na ro'ki Yaya Sadiq ya zo ya kai ni, jarabawa zan shiga ne".
"Amma ban sha fa'da miki matu'kar ba shi da darasin safe, ki dinga tafiyarki ko kuma Al'amin ko Abbas wani ya kai ki ba?"
"Ka fa'da Abba! Ka yi hakuri".
Ya nisa ya ce "Sadiya! Na 'dago na kalle shi, da sauri na mayar da kaina 'kasa ba tare da na amsa 'kiran ba.
Saboda yadda na ga tashin hankali a fuskarsa.
"Na Sha fa'da miki ki daina zuwa wajensu, kin 'ki, na fa'da miki gaskiyar magana Sadik fa zai iya yin komai, domin ba shi da kunya bare ya ki nauyi".
Yana rufe baki na ce "Addu'a za ka yi masa, bare ni ba ya mini rashin mutuncin".
Ya jima yana kallona ya nisa ya ce, "Ke nan dai na yi 'karya?"
Da sauri na hau rantsuwar ba hakan nake nufi ba.
Ya nisa ya ce, "Ni na haifi Sadik ashe kuwa a ce ba na son sa, ko ba na yi masa kyakkawan zato, ko addu'ar shiriya bai taso ba. Amma hakan ba zai hana na fa'di gaskiyar lamari ba. Ina jin tsoron abin da zuwan ki wajensa zai haifar mana, yau ne karo na uku da nake ganin kin fito daga wajensu, idan har ba mantawa na yi ba, tun kina sakandire nake ta jan kunnenki akan ki kiyayi Sadik amma kin 'ki ko?"
Na kasa bu'de baki na kare kaina, domin ni kaina a cikin ru'du nake a dalilin matsar da na sha a hannunsa, duk da dai iya rungumar ce kawai.
Karon farko da na ji Abba ya ce shi ya haifi Yaya Sadik.
Ya nisa ya sake cewa, "Ki fita harkarsa, sannan lallai ki turo mini wanda kika aminta da shi, hankalina ba zai kwanta ba, har sai na ga mun rabu salin alin da ke".
Ya shige wajensa ya bar ni a wajen, na bi shi da ido ina raya daga tattakin da ya zame masa 'ka'ida ya dawo.
Meeting sosai suka yi a kaina, Abba da Baba har Yayar 'Kwalli ta zo. Dukkansu bakinsu 'daya aure suke son yi mini kafin hutu ya 'kare. Tunda za mu yi dogon hutu.
Na dinga jin kunyar Abba na sani wani irin kallo yake yi mini. Sannan na san ba zai bayyana musu ya gan ni na fito a wajen samari da sassafe kai babu kallabi ba. Cike da ladabi na ce, "Ni ban shirya da kowa ba, amma ku 'dan yi mini ha'kuri na 'dan lokaci 'kalilan".
Yaya ta amsa da cewa "An ba ki lokacin Halima, sai dai ki sani ba mai yawa ba. Domin ba zai yiyu mu zuba miki ido da sunan karatu ba. Matu'kar ba ki turo wanda kike so ba, ba shakka Anas ne mijinki".
Na 'daure fuska sosai don ta fahimci cewa ba na maraba da shi har cikin zuciyata.
Haka na tattara na wuce gidan Sakina! Domin har yau 'din nan ba ni da inda nake zuwa na sake, na yi komai kaina tsaye irin gidanta, ko gidan Umman 'Danladi Nasidi ba na sakewa irin haka. Duk kuwa da mace ce mai son zumunci da inganta shi, komai yi mini take yi, idan har ina gidan matu'kar abu 'daya take da shi, to babu shakka sai dai ta hana Aziza 'diyarta ta ba ni, tana fa'din ai ita ce babba sai ta yi hakuri, duk kuwa da kwanaki ashirin ta ba ni kacal.
Aziza na cikin mutanen da nake jin su har cikin raina, kusan a cousins 'dina na family din mahaifiyata na fi son Aziza haka na fi son mahaifiyarta a duk tarin 'yan-uwan mahaifiyata duk da yawansu kuwa, tunda 'ya'yan mahaifinsu yawa ne da su tamkar tsaki, iya wadanda na sani ma su ashirin da uku ne. Ban da wanda suka rasu, su goma kuma a gurin mahaifiyarsu, biyu sun rasu tun kafin a haife ni, yayin da 'daya ya yi hatsarin mota ya rasu a shekarar da na shiga sakandire.
Saura su bakwai, mazansu uku, mata hudu, duk suna cikin Kano ban da guda 'daya da aure ya kaita jahar Ondo cikin garin Akure, Anti Kulsum kuma ita ce autarsu.
Na isa gidan Sakina ban same ta ba, tana asibitin Malam inda take aiki, na shiga 'dakinta da a nan nake yin masauki na ajiye kayana, na fito na shiga kicin na hau bubb'de warmers 'din da suke kan drowers 'din kicin din.
Na dauko plate na fara serving kaina babu 'keta domin ina cikin jerin mutanen da ba sa wasa da cikinsu musamman idan na samu kaza ko kifi.
'Yan aikinta guda biyu sai murnar zuwana suke yi, suna ta yi mini barka da zuwa cikin farin-ciki da girmamawa domin sun san zan 'dauke musu aikin abinci.
Bayan karatuna ba abin da yake sanya ni nisha'di irin girki, ina son na yi girki, ba na gajiya da 'dorawa da saukewa.
Shi yasa har su Nana yaran Sakina, murna suke da zuwana. Domin kuwa duk abin da suke son ci ba na gajiya wurin girka musu.
Da yamma Sakina ta dawo ta tarar da ni.
Ta ta'be baki ta ce "Ai ban sa rai za ki zo ba, tunda wancan hutun ba yadda ban yi da ke ba ki zo ba, kika shafa wa idonki toka. Saboda na Moriki ya hana ki."
Na dinga dariya ina cewa, "Ba fa shi ba ne, Abba ne ya hana ya ce na zauna a gida kawai".
Ta galla mini harara tare da cewa, "Ashe ba a gabanki ya ce duk yadda nake nuna isa a kanki zai nuna mini ban isa ba? Idan na ga 'kafarki a gidana a wancan lokacin to na isa 'din. Idan kuwa ban gan ki ba, to na kama kaina na tsaya a iya hurumina. 'Kiri da muzu kika kunyata ni, ai ni kuma kallon ki kawai nake yi".
Na yi shiru a dalilin ta fi ni Gaskiya. Ta dinga cashe mini tana cewa "In dai na Moriki ne, ina zaune zan ji ku a rana, domin ba mai iya masa sai Mahallicinsa".
A fili na ce, "kafatanin danginmu baibai kuke kallon Yaya Sadik. Amma idan akwai mutum mai da'din sha'ani ai shi ne".
Wani irin kallo ta bi ni da shi mai matu'kar ratsa jiki, ta kasa hadiyewa ta ce, "Shin Halimatu mene ne tsakanin ki da na Moriki ne?"
A sanyaye na ce, "Ba komai fa, sai zumunci da kika sani."
A gigice ta zauna ta ce "Halimatu! Har sau biyu, plz ban da na Moriki, kar ki bari ki fa'da tarkonsa, ba za ki kwashe 'kalau ba. Zuciyarki mai taushi ce, mai hakuri ce, mai kuma sadaukarwa ce. Gudale 'kanina ne da na saki gora ya kama, ke nan nan duniya ba abin da zai yi na 'ki shi, ko na janye jinin da ya hada mu."
Ta nisa sannan ta ce, "Amma wallahi bai fi ki a wajena ba, don haka zan fa'da miki gaskiyar magana irin su sai gogaggun mata, da suka san yau suka san gobe, suke tafiya kan 'yancin da turawa suka ba wa mace. Amma ke kam 'yar yarinya da ke, da yanzu ne kike cikin shekarun kuruciya, ina tabbatar miki wahalar da za ki sha ba ka'dan ba ce, domin son ki ya fi nasa yawa, har yau 'din nan ba ni da wani tabbacin yana son ki. Ko yana son naki shi kansa bai sani ba. Na san dai a duk lokacin da ya 'kyalla ido ya fahimci ba kya gida ya dinga bibiyar inda kike ke nan, amma hakan ba zai zama hujja na yana son ki ba. Tunda zai fa'da miki maganar da ta zo masa ba taunawa a gaban kowa. Ba ya jin damuwa ma idan ya saki kuka, ashe kuwa bai kamata ki bari ki makance , ki so shi har irin haka ba".
Jin na yi mata shiru, ta zuba mini ido tana kallon yadda na tunbatsa da fishi.
Ta nisa ta ce, "Halimatu akan Namoriki?"
Na ce, "Ni ba na son irin haka gaskiya, ni ban ce miki ina son sa ba, kin zauna kina ta sukar lamarin, yo idan haka Allah ya tsara ya za a yi? Na dauka ko kowa zai kushe ke za ki 'kaunaci lamarin".
Na zum'bura mata baki ainun.
Ta yi matu'kar ka'duwa. Tsawon lokaci tana kokawa da numfashinta.
Ta nisa ta ce, "Har haka al'amarin ya yi girmama? Namoriki akwai ja'irin bawa".
Na 'ki tankawa, ta sake cewa ki musanya shi da Abbas, ya fi shi nagarta, ya fi shi hankali, sannan yana da abin yi, bayan haka kuma ba wani son sa kike yi ba, sosai za ki ji dadin zama da shi".
Tana rufe baki na ce, "Wallahi ko a 'kafa aka daura mini shi sai na subuce na tsere. Ai ni din nan da kika gan ni ba na son namiji mai jiki, ba na son shiru-shiru, wanda zai ta gana maka azabar duniya ana 'karyataka. Idan ba ki sani ba, ki sani Aziza yake so, har na fa'da mata, sun fara magana kuma".
Ta yi galala tana saurarona, a tunzure ta ce, "Ashe dai ya koya miki irin iyashegensa, ban da iskanci har ina wani jikin a-zo-a-gani a tare da Abbas? Kawai dai ki ce kin fi son 'dan 'kyamo ta yadda zai ma'kal'kale ki tamkar 'dan biri".
Na dinga dariyar da ta 'kular da Sakina tamkar ta rufe ni da duka. Kafin mu yi magana muka ji ihun Nana da kaninta Na'im suna fa'din "Ga mai kama da anti Halimatu." Na kai idona kan talabijin 'din ina kallon yarinyar da suke fa'din muna kama fara ce sosai kuma 'yar duma-duma. Sai dai na fita bu'dewa ta 'kasa duk da ita ma na ga hawa take yi sosai.
Sakina ta daka musu tsawar su yi mata shiru, ai kuwa nan da nan suka yi tsit da su.
Maimakon ta bar maganar, sai ta sake cewa, "Ina son na ja hankali! Kar ki yi gan-gancin da Namoriki zai fahimci you are in love with him, domin kuwa ba 'karamin takaici zai cusa miki ba".
Na 'daure fuska na ce "Ni fa ban ga dalilin tsananta wannan maganar ba Maman Nana! Domin dai ban ce miki komai ba, hasashe kike yi".
Ta girgiza kai ta ce "Ai shike nan! Na san dai Namoriki dabi'unsa tamkar irin na *Sabo Da Kaza* ne da ba zai hana a yanka a cinye ta ba. Na fa'da miki gaskiya, na fita ha'kkin zumunci".
Na mike ina guna-gunin ta bari ya furta yana so din mana kafin ta fara wannan jawabin mai kama da 'kafar ungulu.
Ta bi ni da ido, mamakina tamkar ya kashe ta a zaune.
Washegari da yamma sai ga shi a gidan Sakina tamkar jifa, wani iri na gan shi tamkar ba Gudale sarkin ado da ginshira ba.
Ya yi 'kerere a kicin inda nake aikin yin dambu, na kalle shi na ce, "Kamar ba ka da lafiya?"
Ya watsa mini kallo da idanuwansa da suka birkice, ya ce, "A'a asibitin Nasarawa ne a kaina 'yar rainin sense."
Na ja bakina na tsuke. Na ci gaba da aikina.
Ya kalle ni ya ce, "A tsaye za ki bar ni ne?"
Na janyo wata irin kujera da suke zuwa ha'de da turmi na kai gabansa tare da cewa ga abin zama".
Da saurinsa ya ja da baya tamkar ya ga wani mugun abu.
*Alkalamin Surayya Dee*✍️
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?
*Mai bu'katar karanta wannan labarin ya tura ku'din karatu 500 a wannan asusun.*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar 08032773332*
*Note*
*Shimfi'dar labarin shine farkon littafin! Dan haka wacce bata karanta shimfida ba ta koma ta Karanta*.
*Page 11&12*
Ya ce, "Ashe ke muguwa ce, kuma ma'ketaciya?"
Mamakinsa ya kama ni ina son gane me na yi na 'keta da zalunci?"
Na kalle shi na ga da gaske tsoron kujerar yake yi.
Na ce, "me na yi maka da ka jingina mini wadancan siffofin?"
Da kumfar baki ya ce mini "Wato so kike na yi ta haifar 'ya'ya mata ko?".
Ya sake shayar da ni wani sabon mamakin fiye da na farko, na kasa yin ha'kurin maganar ta bi ruwa na ce "Zama a kan irin wannan kujerar ne sababin haifar 'ya'ya mata?"
"E mana hakan na taso na ji ana fa'da shi yasa nake gudun kujerar tsugunno da kuke zama a kai, dan kar a zo a cika mini gidana da tarkacen mata".
Na yi sukuri cikin kasala, amma kallon sa nake yi ina mamakin kalaminsa da babu azanci ko tauhidi a ciki.
'Karin ta'ajibin da na shiga shi ne babu jahilci a tare da shi, domin tun ba ni da wayo suka yi sau'kar al'kura'ani mai girma, ban da littafan addini daban-daban da suka samu sani a cikinsu. Sannan kuma ilimin zamanin ma a yanzu haka yana daf da kammala Doctoring degree 'dinsa.
Ashe kuwa bai kamata ya yi amanna da irin wa'dannan maganganun da gidadawa, kuma jahilai suka kitsa su, wawaye suka aminta da su ba.
Na nisa na ce "Ba a yi wa Allah dabara dai, shi ne Yake sarrafa komai, da ikonsa komai Yake gudana".
"Allahu Akbar! Na fiki sanin hakan sai dai dole zan kiyaye duk abin