Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 61

39K to 42K   out of 180.1K words

wato *Moriki & Brothers*. Gudale ya dinga tunanin shin mutane nawa ne masu tsananin son 'yan-uwansa irin mahaifinsa, hatta dukiyarsa yana jinginata tare da yan'uwansa ne. Rahamar Allah ta tabbata ga 'yanuwa masu son zumunci da sadaukawa irin Abba.
Ya nutsu sosai yana sauraron albishir din da za a yi masa.
Gyaran murya ya yi sannan ya ce, "Sadik a tsarina ba na so na yi maka aure ba tare da kana tsaye da kafafuwanka ba, ma'ana sai kana da aikin yi ko sana'a. Ba don komai ba sai nauyin da zai hau kanka ba ka'dan ba ne.
Sai dai kuma duk yadda na so ba haka Ubangiji ya tsara ba.
Ban zaci nan da ba'di ma zan amince a nemo maka aure ba, saboda ban yarda da nutsuwarka ba. Don haka ba zai yiwu a dauki yar mutane a ba ka ragamar kulawa da tarbiyarta ba".
Zuciyar Gudale ta harba da tsananin gaske, bai yi zaton aure za a yi masa ba, shi yasa a canke-cankensa bai hakaito aure ba.
Ya sake yin kasa da kansa yana jin faduwar gaba na sake tsananta a gare shi, shin wace ce yarinyar da aka zabo masa?
'Yar wane attajiri ne?
Sannan ta yi daidai da taste dinsa?
Yana cikin wannan yanayin ya ji Abba ya zarce da cewa, "Amma daga jiya na 'dan sami 'kwarin guiwar ba ka aure, da ma kuma na yi imanin lamuranka ba za su tabarbare gaba'daya ba. Tunda ka yi sa'a ka daina wasa da Sallah, tsawon shekaru biyar ke nan na gaskata ka akan salla komai tsananin yanayin sanyi ko na damina ba sa hanaka yin salla a jam'i musamman sallar Asuba. Annabi ya ce, "Salla tana daidaita sha'anin mumini, tana kange shi da aikata munana ayyuka da dabi'u.
Gafarar Allah ta tabbata ga muminai masu jingine ababen shagala, da zarar sun ji liman ya ce, "Haiya alal Salah".

Daga nan kuma sai Abban ya numfasa ya ce, "Ka saurare ni da kyau, ka kuma nutsu. A baya ka ce mini ka ba ni damar na samo maka mata kamar yadda na yi wa 'yan uwanka ko?"
Kai kawai Gudale ya 'daga masa, saboda yadda yake cikin ki'dima da sanyin jiki.
"Madalla!" Abba ya furta sannan ya zarce da cewa, "To idan Ubangiji ya kai mu 2 ga watan goma na wannan shekarar, nan da watanni biyu masu zuwa za ka zama ango. Zan sake yi maka albishir da cewa kwabonka ba zai yi ciwon kai ba. Komai ni zan yi maka har kudin kunshi da na kawayen amarya, fatana dai ka ri'ke mini ita da kyau. Idan ka yi mini hakan ni kuwa ba zan gaza wajen yi muku komai ba. Da kanka za ka gane ba abin da nake so tamkar kai da iyalinka".
Murmushin jin da'di ya 'kwacewa Gudale. Hakan ya sake faranta ran Abba.
Don haka ya yi 'kundubalar cewa, "Halimatus-Sa'adiya na za'ba maka ta zame maka mata kuma uwar ya'yanka. Na san za ta yi daidai da tsarin daka lissafa mini".
Sosai kan Gudale ya daure ya kasa fahimtar wace ce Halimatu da aka ba shi ya aura. Rashin fahimtar da Abba ya gani a tare da Sadik din sai ya hutar da shi tsananta tunani ya ce, "Ina nufin 'yar uwarka *Guddi*."
Wata irin dariya ta kama Gudale, ya dinga tintsirawa ba kakkautawa. Ba komai ya sa shi dariyar ba irin yadda Abba ya ce, *Guddi!* Ko mene ne abin wahalar fada a *Guduyo* tamkar mutum zai ce gudu sai kawai ya 'kara da yo shike nan fa.
Can kuma ya nutsu ya ce, "A gafarce ni Abba! Yadda kake son fa'din sunan ne ya sanya ni dariya. Amma saboda Allah Abba ta ina Guduyo ta dace da wacce na siffanta maka?"
Cikin rarrashi Abba ya ce, "Halima fara ce, doguwa, sannan tana da gashi".
"E amma ba ta kammala karatunta ba, sannan ba 'yar attajiri ba ce".
Abba ya nuna kansa ya ce, "Ka raina arzikina ke nan? Don kuwa ai ni ne ubanta ba wani ba." Ya fa'da a tunzure ka'dan.

Ganin hakan ya sanya Gudale diriricewa yana cewa, "Amma dai a gaban Umma sai da na ce maka 'yar shawalwala nake so ba wai bunkusa ba. Sannan gaskiya ni ba ita ba ce zabin raina ba".

"Ita ce zabin Allah a gunka, ka sanya hannu biyu ka karba, ban yi zaton za ka iya kunyata ni ba, su Abdallah ko tari ba su yi ba, suka karbi zabin da na yi musu cikin farinciki da godiya mai yawa. Shike nan tashi ka tafi zan musanya mata kai da Abbas ko Ashir tunda ita na isa da ita na sani ba za ta yi mini musu ba. Bare su kuma da nake da tabbacin ko wuta na ce su fa'da ba za su kunyata ni ba, za su na'de kafar wando ne kawai su fa'da. Ba abin da zan cewa 'ya'yan yan uwana sai fatan alheri. Tabbas ko ban haihu ba, na sani ba za su bar ni na koka ba, tunda suna yi mini biyayya fiye da ta 'dan da na haifa".

Kuka kawai Gudale ya saka masa tamkar sanda yake yaro 'dan karami, sannan ya 'dora kansa a kan kafafuwan mahaifin nasa
Sosai Abba yake nazarinsa yana kuma jin soyayyar 'dan nasa tana nema ta kasa sarrafuwa a lokacin.
Tsawon mintuna sannan ya fahimci kukan shagwaba da iyashege kawai ya sanya shi a gaba yana yi masa, domin bai ji dumi a cikin hawayen nasa da yake diga a kan kafarsa ba, hakan ya sanya ya gane ba kukan ba'kin ciki yake yi ba.

A tausashe ya ce, "Na ce ka tashi ka tafi tunda ba ka amince da hukuncina ba, shi ne za ka sanya mini kuka? Ban yi fishi ba ai, tunda Ashir yana nan, na tabbatar shi zai karba babu hamayya, kai kuma ka je ka nemo zabinka, damarka ce ba zan hana ka ba".
Sai a lokacin Sadik ya 'dago kyakkawar fuskarsa hawaye yana tsere, shi da kansa bai san dalilin zubarsu ba amma ya yi amannar ba na bakin ciki bane, ba kuma na farinciki ba ne.
A sanyaye ya ce, "Abba na ce maka ba zan karba ba ne da kake ta faman jingina wa Ashir matar da kake 'kirarin ka ba ni? Ka sani kuma babu jituwa a tsakanina da shi, tunda ya fahimci kana daukaka lamarinsu, shike nan sai yake neman wuce gona da iri, sau nawa Baba yana mana shari'a da Ashir? Duk lokacin da wani abu ya hada mu baya jin nauyin ya daga hannu ya zabga mini mari! Bayan da watanni kawai ya girme mini. Ko Al'amin da Abbas da muke gida daya ba sa yi mini wannan wulakancin, amma shi saboda gadarar Yayar 'Kwalli sai ya dinga tozarta ni alhalin na fishi karfi a gidan nan tunda shi 'dan mace ne."
Kafin Abba ya yi magana Sadik ya sake zarcewa da fa'din, "Ka daina nuna mini sun fi ni a wajenka, ina jin haushin hakan, ka daina jingina wa Ashir Guduyo! Sosai abin ya yi mini ciwo a zuciyata, domin ba ta dace da mai mugun hali irinsa ba. Sannan har zuciyata na sake jin ba na son sa, ai na sani son ta yake yi, to ko don na tabbatar na yi masa kwalelenta, ba zan tankwabar da umarninka ba, mugu kawai, masu zuwa cin arziki amma sun zame wa halastattun 'yan gida 'karfen 'kafa".
A nutse Abba ya ce, "Wato dai ba da kyakkawar manufa ka karbi auren ba, saboda kawai akwai yartsama a tsakaninka da Ashiru ne dalilin karbar?"
Da sauri ya amsa da cewa "Saboda kai na karba Abba! Don ka ji a ranka ni ma ka isa da ni, ina fatan duk lokacin da na kawo zabina ni ma za a yi mini adalci albarkacin biyayyar da na yi, idan kuma ita ce ka'dai aka 'kaddara mini, shike nan".
Sosai kalaman suka faranta ran mahaifin nasa, ya dinga sanya masa albarka, da nema masa tsari daga dukkan abin 'ki.
Domin bai zaci zai amince cikin sau'ki ba, musamman da ya san halin 'dan nasa na gardama tamkar mutanen farko.
Ya numfasa ya ce, "Na gode maka sosai Gudalena".
Karon farko da ya ji mahaifinsa ya kira shi da wannan sunan, sannan har ya kara da fadin nasa.
Da mamaki ya daga ido yana kallonsa. Murmushi Abban ya yi ya ce, "To ko ba nawan ba ne na Umma ne kawai?"
Farincikin da Gudale ya tsinci kansa a ciki ba zai misaltu ba, har ya dinga jin anya ya taba shiga yanayin da ya saukar masa da farinciki bayan yana cikin rudani sosai.
"A fili Abba ya ce, "Ba mahalu'kin da zai haifi 'da ya ce ba ya son sa sai dai ya guji halinsa, ko da kake ganin na fi son su Abdallah akanka ai ba hakan ba ne. Ubangiji da kansa bai daidaita 'dan cikinka da 'dan Dan-uwanka ba. Saboda yadda ya yi kasafin rabon gado da kansa, ta yadda ya nuna karfin jini. Sai dai kuma ayoyi daban-daban da hadisai masu yawa da suka yi ta nuna mana girman zumunci da kyautata shi, Ubangiji ya wajabta mana yin ibada, aure da kuma inganta zumunci. Amma muna cikin wani irin zamani da mutum bai san kowa ba sai 'ya'yansa, kadan ne suke daidaita 'ya'yansu da na yan'uwansu a fuskar mua'amala. An sani ba zai yiwu su zama 'daya ba amma ka ba su 'kofa da fuskar da za su ji a ransu cewar kaima Babansu ne, za su iya tunkararka da dukkan matsalolinsu, za su yi dariya a gabanka a yayin da suke cikin farinciki, haka nan za su yi kuka akan kafadarka a lokacin da suke cikin firgici ko 'bacin rai. Idan kuma Ubangiji ya azurtaka sama da su ka ji a ranka cewar ba iya kai da 'ya'yanka ne za ku ribaci wannan dukiyar ba, domin su ma suna da hakkin zumunci a cikinta. Allah Ya kan dauki mutum a cikin zuri'a ya bun'kasa arzikinsa da manufar ya zama bango a cikin wannan Ahalin.
Mutane ka'dan sun fahimci manufar Ubangiji akan arziki da damar da ya basu ta rayuwa, sai su yi ta aikata alheri da kuma kyautata zumunci, yayin da wasu da yawa suke halaka ta hanyar daukan ra'ayin ri'kau na kowa ya tashi ya nema da kansa bayan kuma dole sai wani ya daga wani, kafin a kai ga gaci".
Jikin Sadik ya yi sanyi ya 'dan fahimci mahaifin nasa ka'dan! Ya kuma rage jin haushin damar da ya bawa zumunci.
Da Abba ya lura irin wa'dannan maganganun suna tasiri a zuciyar Sadik, fiye da fa'da, sai ya 'kudire zai dinga yi masa matashiyar su akai akai, har Ubangiji ya bude masa zuciyarsa ya fahimci rayuwa dai-dai ba yadda ya fahimceta a yanzu ba.
Dan hakan sai ya datse wancan hanunka mai sanda da yake yi masa, ya dawo kan batun da yasan zai sanya shi farin-ciki.
Da tarin soyayya ya ce "Ya ya labarin motarka kuwa? Baka ce mini komai ba tunda aka kaita wajen gyara".
Kai-tsaye Gudale ya ce "Nifa bana sonta Abba dan haka ma ko tuntubar bakaniken ban sake yi ba".
Cikin hikima ya ce "Ai Shikenan mai sunan Baban Nana Aisha(R.A.)! Ka yi nazarin wacce kake so, sai na yi maka oder, Ina fatan ta iso kafin lokacin bikinku. Waccar 'dinma ai bata fi wattanni biyar da saya maka ba, za'a gyarata sosai sai a barwa Halimatu saboda zuwa makaranta.
Tunda kana daf da kammalawa, sannan aiki zaka fara ba da jimawa ba, baka da lokacin kaita da daukota, kuma ba zai yiwu iyalinka ta dinga jaurar hawan adaidaita ba tunda Ubangiji ya bada yadda za'ayi".
Kan Gudale ya fasu saboda yadda Abba yake lalla'ba shi. Kafin ya yi magana ya ji murya Abba ya sake cewa "Ka nutsu sosai ka fa'da mini dukkan abin da kake so, komai yi maka zan yi dan ka gane ba ni da wanda ya kai ka balle ya fika. Abin da nake so da kai yanzu, ka 'dan fara samar da fahimta a tsakaninka da Halimatu duk da na sani kai da ita tsakaninku sai Allah! Amma zan so ka canja alakar shiriritar da take tsakaninku zuwa kyakkawar manufa mai cike da soyayya da mutuntawa".
Gudale ya saki ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "gaskiya ni Abba raina ni zata yi, bata da kunya, kawai ka fa'da mata da kanka, amma ka ja mata kunne ni wlh inta ce zata raina ni, ko yi mini yanga bubbugeta zan yi, sannan na ganar da ita rigarka kawai ta shiga".
"Tunda ta shiga rigata, na gode maka, na sani kuma watarana zaka gode mini, ka kuma yi mini Addu'a akan zabin da na yi maka.
Tashi ka je, Ubangiji ya yi maka alabarka".

AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS*
*Masu bukatar siyan fili ko gida*
*Masu bukatar gidan haya*
*Masu bukatar siyar da kayansu Dan su yi canji duk ku tuntu'be su*
*Sun shahara Akan kasuwancinsu saboda sauki da kuma kyakkawar alaka tsakaninsu da customers*
*08083909947*.

Ya mi'ke yana cewa "Na yi godiya sosai! Godiyar mota nake yi fa, zan je na duba wacce zata fi dacewa".
Ya fice Uban yana binsa da addu'ar shiriya, yana fatan wataran ya zo ya tsugunna ya yi masa godiyar bashi Halimatu da ya yi.





# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee.
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.


*SDK27&28.*

Barci sosai na sha tunda na idar da sallah na koma a dalilin bani da darasi sai karfe biyu. A makare na tashi na lalubo wayata na kalli agogo, da azama na tashi na shiga bayi na yi brush a gaggauce, hijabi kawai na zura, na doshi falon Abba, saboda nasan yana dab da komawa cikin dakinsa dan haramar fita tunda sha'daya ta wuce.
A 'dan dogon coridon da ya raba falon Umma da na Abban muka yi kicibus da Yaya Sadik, ya fito daga falon.
A fusace ya wuce ni, na 'dan daga murya na ce "Ina kwana?".
Bai amsa ba. Da yake hankalina ya yi gaba sai ban sake maimatawa ba.
Ina shiga falon, na tarar da Abba ya mi'ke yana shirin shigewa daki.
Ganina ya sanya ya koma ya zauna.
Ya amsa gaisuwata cike da kulawa kamar kullum, sai dai walwalar da na gani a tare da shi, ta sha banban mussaman da na ga Gudale daga wajensa ya fita. Sau tari indai ka shiga wajen Abba bayan fitar Gudale ba zaka samu walwala a tare da shi sosai ba, dan haka sai na dinga mamakin wannan annushuwar da yake ta faman yi mussaman yau da har ha'koronsa nake gani saboda murmushin da yake yi mai yawa ne.
Na taya shi murmusawa amma kuma mamaki nake yi sosai.

Da farin-ciki ya ce "Kinga Sadik yanzu?"
Na 'daga kai tare da cewa "mun ha'du da shi zai fita, Ni kuma na shigo".
Ya ce "Madallah! Maganar ki ya gama yi mini. Ba kunya, ba komai, ya ce mini na bashi ke ya aura, har na dinga mamakin da ban fahimci kun shirya kanku ba tuntuni".
Na yi 'kasa da kaina, karon farko a rayuwata da na ji Abbah ya yi maganar da ban gasgata ba, domin na yi imani Gudale ba zai ce masa yana sona ba, tunda bai ta'ba furta mini ba, bai kuma fa'dawa Sakina da Yaya Al'amin ba.
Kafin na ce "wani Abu sai jin muryarsa na yi yana cigaba da cewa "Na fa'da masa ya nemi amincewar ki, amma ya ce Na taimake shi na fa'da miki da kaina, domin idan a bakinsa ne zaki mayar da al'amarin wasa, bayan haka yana jin tsoron kada ki 'ki amincewa ki kuma raina shi".
Take na sake yarda da zatona, wannan Shirin Abba ne dan kawai ya tabbatar da waccar maganar da na fa'da na ce dama ya za'ba mini Yaya Sadik.

A hankali na ce "Abba ba ya sona gaskiya, da wasa yake yi".
Ya zuba mini ido na tsawon lokaci kafin ya ce "Ashe auren ne ba kya so, shiyasa kowa ya zo sai kin bada uzziri.
Ina ce anan kika ce ba kya son Abbas da Ashir?
Gara Sadik da su, yanzu kuma Sadik din ya zo sai ki ce wani abu daban shin menene damuwar ki ne, fa'da mini matsalar ki Halimatu".
Murya ba amo na ce bana son ka 'dora farin-cikina akan nasa ne, na sani Abba dukkan mu 'daya ne a wajenka. Amma ba zan so a yi masa dole ba".
Ya nisa ya ce "Ba wani dole da zan yi masa, ya amince, kema kuma kin ce kin ji kin gani magana ta 'kare."
Kai-tsaye na sake cewa "eh da gaske gara shi akan su Yaya Abbas".
Na sani mamakina ne ya sake kama Abba dan haka sai ya buge da yin wani irin murmushi tare da cewa "je ki, zamu zauna da sauran iyayenku ina fatan nan da lokaci ka'dan ayi komai a kammala".
Na fito, na shiga dakin Umma dan na gaisheta saboda ina son na tafi shahshinmu, domin na sake na yi murna son raina. Wai ni ce nake shirin zama Mrs Gudale sai nake ganin abin tamkar almara.
Da sallamah na shiga cikin dakin na tarar da Gudale kinshige'de a bakin gadon Ummah. Yana ta danne danne a rantsatsiyar wayarsa, amma ko amsa sallamata bai yi ba.
Na dan yi jim! Ina son na tambaye shi Umma Ina jin tsoron wulakancinsa.
Na daure na ce Yaya Gudale! Ina kwana, ina Umma?"
Ya ajiye wayar a gefensa ya tashi ya zauna sannan ya mini wani irin lalataccen kallo ya ce "Tana cikina! Daga yau idan na kuma jin kin ce mini Gudale sai na yi 'kasa kasa da ke, 'koshasshiya kawai".
Kafin na ce komai Umma ta fito daga bayi da alamun alwallah ta yi dan yin walaha.
Ganinmu tare ya sanya ta sake 'daure fuska tamkar an fa'da mata mugun abu.
Na risina na gaisheta ta amsa a gajarce, tana shimfida abin sallah ta tayar ba tare da ta kalle ni ba.
Jikina ya yi sanyi saboda wula'kancin da ta yi mini yafi na kullum.
Na fita ina jin wani iri a raina, amma murnar da nake ciki sai ta sanya ban damu ba, bare na gane irin tasirin da Umma zata yi a gidan aurenna.

*Kina fama da ulcer?*
*Kina fama da bushewar ni'ima?*
*Kina son fatarki ta yi kalar butter*?
*Kinsan Sa'adan Mk bata amfani da kowanne irin supplement sai na manyan Mata kuma ingantacce*
*Ki tuntu'bi Faseelat a lambar domin

14 / 61