Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
ina miki fatan ki samu sassauci a dukkan abin da nake jiye miki tsoro".
Sai a lokacin na ce "Ameen".
Ta kafe ni da ido tana mini kallo mai tsananin gaske.
Ta girgiza kai ta yi 'kwafa.
Ta fice ta bar ni.
Maimakon na yi nazarin maganganunta, na auna su, na gano girman soyayyar da take yi mini ta ninka wacce nake yiwa Gudale. Sai kawai na shiga hakaito kyaunsa, kwalliyarsa, hatta rashin kunyarsa burge ni take yi.
Na hango 'dan tsurut din bakinsa mai dauke da fararen ha'kora tamkar kankara.
Na sake ha'kaito sumarsa da take cike fam, gata 'baka wuluk, sannan ake gyarata tamkar sumar mace.
A rayuwata ban ta'ba ganin namijin da shagwa'ba take yi masa kyau irin Gudale ba. Duk girmansa idan yana gaba Umma sai ka rantse yaro ne da bai da'de da yaye ba.
Ita kuma bata fahimtar ya girma ta dinga lallaba shi kenan, sannan komai yake so sai ta yi masa.
Har a lokacin bai wuce ya kwanta ya yi matashin kai da cinyarta ba, ba kuma zata motsa ba, dan kar ta tashe shi.
Idan su Sakina na fa'dan ya bar musu uwa ta huta da hidimarsa haka nan.
Ita ce take cewa "Ku bar mini autana ya yi yadda yake so. Duka duka nawa yake ne? ai ni idan ba gani na yi za'a aurar da 'dansa ba, ba zan gane ya girma ba."
Shikenan sai suka koma zuba musu ido.
****
Kwanci tashi har aka kwashi sati biyu da zartar da hukuncin aurenmu. Amma har lokacin ban ga sassauci daga wajen Yaya Sadik ba asalima na jima ban ganshi ba.
Ranar litinin sassafe na fito dan tafiya makaranta, na ganshi tsaye shi da Yaya Al'amin.
Na karasa kusa da su, na gaishe su.
Yaya Al'amin ne kawai ya amsa, amma shi sai ya dauke kai.
Hakan da yayi ya ta'ba Yaya Al'amin kwarai da gaske.
Da daddare ya zo, ya shiga 'dakin mahaifiyarmu, sannan ya 'kira ni.
Sai da ya rufe 'kofar sannan cikin murya kasa kasa ya ce "Halima! Da ke da Sadik 'daya ne, wallahi ba wanda ya fi wani a wajena, amma zan fa'da miki gaskiyar magana, ki samu Abba ki nuna masa ba Kya son wannan ha'din gara a mayar da auren ki kan Ashir. Ina tabbatar miki Abba adali ne ba zai kalubalence ki ba. A gabana Sadik yake nuna wa an yi masa dolen auren ki, ba ya jin kunyar idona".
Idona ya ciko da hawaye, ina jin wani irin abu na taso mini.
Cikin kuka na ce "Yana sona fa! Laifi na yi masa, kuma zamu shirya ne".
Ya kalle ni sosai ya ce "shikenan Halima good luck".
Ya fita da sauri.
Na goge idona ina 'kunkunin ina son abina, ai ni zan zauna, ba wani ne zai yi mini zaman ba.
Washagari na dawo daga makaranta muka yi kicibus da shi a harabar gidan.
Na gaishe shi, ya bagarar tamkar yadda yake mini tun sanda ban yarda na biyo shi daga gidan Sakina ba.
A hankali na ce "Yaya Gudale! Ya kamata ka huce hakanan, ai dai ka sani kafi Sakina a wajena, to menene na wannan doguwar gabar haka? Dan Allah mu shirya haka nan".
Ya mini kallon wulakanci ya ce "ke kam kin ji jiki wallahi! Ashe ba zaki kame kanki ba? Wallahi na tsani mace marar aji".
Ya yi tsaki ya wuce ya bar ni.
Jikina ya yi sanyi sosai, na dinga auna maganarsa, maimakon na ji raina ya baci, sai na tsinci kaina da jin takaicin kaina na kama ni, me yasa ban zama mai aji ba? Tunda Yaya Sadik mai aji yake so.
Na kudire duk inda aji yake zan nemo shi dan na burge shi.
Amma matsalar a kansa ne bani da ajin kawai, shin zan iya kamewa akan lamarinsa?
A wajen na 'daga hannu ina fa'din "Allah Yaya Sadik mai aji yake so, ina ro'kon a sanya na zama kamammiya a idonsa da zuciyarsa, Ubangiji a cika masa kirjinsa da soyayyata."
Ranar jummaa Abba ya bukaci dukkan ahalin gidanmu su zo yana son ganin su.
Bayan la'asar aka zauna.
Ba bata lokaci ya sanar musu aurena da Sadik ya gabato.
Aka yi addu'a da nasihohi, sannan ya sallami kowa bayan ya ce Al'amin da Ashir su maida hankali suma, tunda sun girmewa Sadik din, duk dai ba wani fiko ne mai yawa ba.
Bana mantawa a cikin 'dakina na bangaren Ummah! Sakina ta zaunar da ni tana cewa "ki fa'dawa Abban ya canja miki Na Moriki da Ashir.
Sadik fa ba zaki iya da shi ba Halimatu! Ina jiye miki tsoron kar ki shiga damuwa".
Na zum'bura mata baki sosai, na kasa cewa komai saboda yadda nake Jin tamkar na rufe ta da duka. Dan kawai ita ta yi auren ku'di, mijinta bashi da wani kyau, duk da ita din ko a cikin kyawawan mata sai ance mai kyauce saboda yadda kyaunta ya shahara.
To ni nafi son kyakkawan namiji, dan gaye, marar nauyi, sannan ma'abocin son cin da'di koba komai nima ai zan ci.
Amma an tisa ni gaba ana ta cewa ban dace da shi ba, da sauran surutai marasa kan gado.
Ta zuba mini ido ta ce "Ni Kika zum'burawa baki haka?
Na dauke kai na ce "Ato ni na gaji da wannan maganar gaskiya, gashi nan kin janyo mini 'bacin ransa, tun abinda ya faru a gidanki har yau bai sake kula ni ba. Kuma ai nice zan yi zaman ba wani ne zai taya ni ba, kowa ya iya allonsa ya wanke kawai".
Ta yi matu'kar razana ta ce "wato tun ba ki je hannunsa ba, kin fara yin koyi da rashin kunya da rashin mutuncinsa ko?
Tabdi lallai kuwa! Ai shikenan ki wanke allon lafiya".
Ta mike ta bar ni cikin bacin rai mai yawa.
Ni kuma ina ganin idan ba hakan na yi mata ba, ba zata shafa mini lafiya ba.
Na yarda da Yaya Gudale da yake cewa kazallaharta ta yi yawa.
Shikenan Abba ya dinga shirin aurenmu tamkar dai ba'a ta'ba aurarwa ba sai akanmu.
Sakina ya 'kira ya dam'kawa ma'kudan kuda'de akan ta shiryo mini lefe. Da sauran gyare gyraen amarya.
Kan dole ta ajiye fishin da take yi da ni.
Ta kira ni bamu zame ko ina ba sai gidan abokiyar karatunta fasilat hazikar jakadiyar *G.H.T*.
Da murna *Anti Faseelat* ta 'karbe mu, ta kalle ni ta ce " ya naga Amarya ba kya glowing? duk kin yi duhu, har wasu 'kuraje nake ganin suna neman 'bata miki fuska?"
Sakina ta ta'be baki ta ce "gata nan wata'kila streess din makaranta ne, sannan ta 'dorawa kanta damuwa, ba shawara ba komai ta canja mai din da take amafani da shi.
Da murmushi Fasilat ta ce "kwantar da hankalinki Amaryarmu, bayan gyan jiki har mai zan baki ki matsa akan man na asali sai farar fatar ki ta dawo tamkar ta larabawan Jordan".
Ni dai bance komai ba.
Sai da muka sanyaya ma'koshinmu sannan ta yi mana iso zuwa dakin da kayayyakin suke ajiye.
Ta kalle ni sosai ta ce "tunda fatarki fara ce sannan dry ce zan baki seti mai matu'kar kyau ki fara amafani da shi kafin bikin". Ta dauko wani kit din mayuka da tarkacensa, a ido ma ka'dai abin sha'awa ne.
Ta sake za'kulo wani 'dan karami ta ce "ki ha'da da wannan, domin sai an hada da shi ake samun abin da ake bu'kata".
Na kar'ba ina juyawa.
A hankali na ce "Anti na gwada shi bai yi ba".
Da sauri Fasilat ta ce "Ba wanda ya dace da fatarki aka baki ba, wata'kila na masu oily skin aka baki. Ki tambayi Sakina! Kayana masu kyau ne, sannan sai nasan ainihin kalarki kafin na baki shawarar wadanda zaki shafa".
Na girgiza kai cike da gamsuwa.
Sakina da ke haushina take ji, bata ce 'kala ba.
Ta dai kalleta ta ce ki bata kwalli da jan baki har da powder".
Ta hado dukkan abin da Sakina ta ce.
Na sake nutsuwa ina duba wani supplement da yake yaki da kowanne irin sanyi da yake addar mata ba yanmata ba, ba matan aure ba. da kuma wanda amare zasu fara kafin auren.
Ga wani irin lubricant mai kyau da daukar da nutsuwa Wanda ta ce sai anyi zan fara amfani da shi.
Duka Sakina ta ce "Ta zuba su a leda.
Yawan ku'din bai damu Sakina ba, saboda ta gasgata *Fasilat* da kayanta.
Hatta basir din da ya sanya mijinta a gaba aka kasa samun maganinsa, wani maganin na *G.H.T.* ya sha ya dace.
Ku tuntu'be ta a wannan lambar. *07039269802*.
Siyan na gari aka ce maida ku'di gida.
Na yi zurfi a tunanin yadda Anti Sakina tasan manyan mata da kasuwancinsu, shiyasa komai nata na daban ne, to baka samunsu barkatai a ko'ina, na kuma lura gogewar fatar Sakina tana 'damfare da yadda take tu'amalli da mayukan oriflame. Mussamna da yake ta hadu da wanda tasan sirrikan mayukan da zasu kar'bi kowacce launin fata, tana zaba mata wanda zasu yi daidai da ita.
Wani Mai da *Aisha lame* ta za'ba wa Sakina a dalilin fatarta oily ce ba 'karamin fito da zahirin kalarta yake ba. Mussamna da yake ya dace da farare masu oily skin irinta.
Ni da kaina na gamsu ban san wata jakadiyar oriflame da tasan kalolin mayunka da zata hada maka su gyrara ka tamkar Kawar Sakina ba.
Duk Wanda ya yi mua'amala da ita zai so ya dauwama yana tu'amalli da kayanta.
Tuntu'be ta kan wannan lambar dan samun mayukan da suka dace da fatarki.
*07033662633.*
Ranar biyan bukata rai ba'a bakin komai yake ba.
Haka Sakina itama ta sayi nata kayayyakin gyaran auren a wajen jakadiyar *G.H.T Fasilat* ta yi mana sau'ki sosai.
Ina jin Sakina tana ce mata, zata dawo ta siya mini wanda zan tare da su
Da murmushi Fasilat ta ce "sannan ma dangin supplement din da zai daidaita ta, ya fiddo da zahirin shape dinta sun iso. Bayan bikin kuma sai mu duba yiyuwar yi miki rigista da su. Domin na shaida kin gane sirrin da ke cikin kayan *G.H.T*.
Kin gane abu mai daraja farashinsa daban ne, haka nan aikinsa ma na daban ne".
Sati 'daya kawai na yi, amma na yi matu'kar canjawa, kyaun fatata ya bayyana, zahirin farinta ya fito, ta yi laushi tu'bus. Ni da kaina bana gajiya da kallon kaina.
Tafin hannuna ya yi laushi sosai saboda kullum hand lotion yana jakata.
Hatta Mama sai da ta ce idan na san bleaching nake yi na kiyayi kaina.
Na yi dariya na ce "Haba dai Mama duk yadda nake da farin nan sai na ha'da da Wanda zai lalata mini halittata?
Kawai dai fatar ta samu mayukan da suka dace da ita ne, shiyasa take fitar da asalin kalar da Ubangiji ya yi ta. Ni da kaina bansan haka nake da kyau ba sai yanzu.
Wani abin mamaki ni da kaina na ji dadin marata, wannnan farin ruwan da nake zubar mini lokaci zuwa lokaci ya kau, haka 'kai'kayin da nake 'dan ji from time to time ya tafi gaba'daya. Madallah da kayayyakin *G.H.T* mussaman wanda aka siya ta hannun jakadiyar da kamfanin ya gamsu da kokarinta da sau'kin kayanta.
*Madallah da Faseelat 07039269802*
*Madallah da jakadiyar G.H.T da bataq 'kwangen sayar da man da ba zai karbi fatar mutum ko kayan da baza 2su gyara zamantakewar auren mace ba*.
*Lol Gudale ne ya ce a nemo zakkwakuran masu Gyaran mace in and out*🤪
*Ni kuma na Nemo wandanda suke tested and trusted*.
# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee.
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
*SDK 31-32.*
*Muna ha'da lefen Guduyo ne*
*So zaku yi ta ganin shahararrun 'Yan kasuwa, da masu gyaran amare.*
*Idan kuka bibiye su zaku tabbatar kayansu zabbabu ne, Kuna masu sauki ne*.
*Kunsan dai supplements din da Iyah Basiru take amfani da su gangariya ne*
*Shiyasa ta gamsu da Faseelat 07039269802 mai gangariyan kayan kamfanin G H.T.*
Na fito sanye da shu'diyar shadda mai duhu doguwar riga, da aka 'kawata da duwatsu masu ruwan hoda.
Na yafa mayafi kalar duwatsun. Na yi wani irin kyau saboda yadda nake she'ki da glowing.
Jikina a cike rugu rugu da ni, komai ya cika dam, tamkar zai faso riga.
Mama ta ce "Sakinan zuwa zata yi ta dauke ki?".
A hankali na ce " ta ce Idan ta iso waya zata yi mini na fita, sai mun dawo zata shigo".
Ai kuwa ina rufe baki wayata ta hau 'kara. Ina dubawa na ga ita ce.
Na fita ina cewa Mama "sai mun dawo".
Na shiga gaban motarta ta ja muka wuce.
Bamu zame ko ina ba, sai sabon titi gidan 'kankara.
Gidansu *Umm Muhd collection* na dinga mamakin yadda Sakina take sanya suturun da bana ganinsu a jikin kowa ashe ba a kasuwa take siyayyarta ba, a gurin matan da suke zana kayansu da kansu ne, su kuma yi oder su kaitsaye.
Sanin kowa ne galibin matan da suke business da jarinsu da wahalar gaske ka ga irin kayansu a kasuwa.
*Umm Muhd collection* tana cikin jerin irin wa'dannan yan kasuwar.
A farko Sakina bata fahimci kayanta ba, Amma aminiyarta da suka hadu a dalilin karanta littafanta *Surayya Halin Yau* tana yi mata shunenta shikenan ta yarda da gaske kayayyakinta unique ne. Mussaman da ta jarraba ta gani.
A yanzu haka Sakina tana cikin WhatsApp group dinta, tana ma karban kayayyakinta ta siyar mata tare da dogayen rigunnan da Sakinan take saidawa.
Takalma na za'ba asalin Italians masu tsananin kyau. Haka jakunkuna ma qualatitives ne.
Na gasgata, na kuma shaida kyau da sau'kin kayan Umm Muhd. Domin duk yadda *Sa'adan Mk* take da high tana siyayyar takalmi da jaka da kayayyakin kicin na alfarma kuma zababbu a wajen *Umm Muhd collection*
*08063358662*.
Bayan haka tela ce da ta shahara.
Ba a dauki lokaci mai yawa ba Sakina ta kammala shirya mini lefe na garari.
Siyayya ta Fisabidillahi ta yi.
Ta kaiwa Abba ya gani, ya yaba mata kwarai da gaske.
Ya umarceta da ta kai gidan Yayar Kwalli, ita kuma sai ta shirya yadda za'a kawo.
Ya dinga sanyawa Sakina albarka, yana alfahari da ita cikin ya'yansa, a dalilin halin girma irin nata.
Kwanaki kadan ta shiryo ita da jama'arta suka kawo kaya.
Kayan da kowa ya kalla ya san an salwantar da dukiya mai yawa.
Duk kayan cikin akwatin zababbu ne.
Kuma masu daraja ne.
Kayan costumes ka'dai ya isa a ha'da wani lefen, domin duka kayan oriflame ne, amma daga wajen jakadiyar su *Aisha lame* da ta goge a wajen sanin nau'in mayukan da zasu da ce da kowacce irin fata. Kai ka ce Damatology ce, ko kuma wacce ta yi digiri a custumalogy.
Haka nan atamfofi da lesinan ciki selected ones ne, kowa yasan order mata ta sha ban ban da sauran gama gari.
Mafi yawa a wajen *Amyas newly & fairly used* aka samo su.
Idan kina bu'katar latest atamfofi da laces kawai tuntu'be ta a wannan layin na tabbatar zaki yaba ki kuma gode mini, duk da ita komai da ruwanka ce, ko kayan 'daki kike bu'katar canji duk tana da ruwa da tsaki a harkar, haka nan idan zaki siyi kayan daki sabbi ko na hannu masu kyau cikin rahusa duk ta shaharar a wannan fagen za kuma ki sameta da cika al'kawari kedai kawai tuntu'be ta. 08083909947.
Har bikinmu ya zama saura sati uku babu jituwa ko ka'dan a tsakanina da Yaya Sadik! Ya rufe kofar sulhu, ya tsananta sosai.
Ana haka Abbah ya ce masa ya dauke ni mu je mu yi test.
Kai tsaye asibitin Malam muka je.
Bamu 'bata lokaci soasai ba, aka kammala.
Sakamakon gwajin jini na gynotype ya nuna ni A.A. ce yayin da Yaya Sadik ya kasance A.s. sai na Hiv da sakamakon mu ya nuna dukkan mu positive ne ma'ana bamu da 'kwayar cutar.
Mun fito, muka hadu da Sakina, ta kalle mu ta watsar. Jikina na rawa na shiga gaisheta, a dalilin na matsu ta gama hucewa da ni.
Yayin da Gudale ya yi gaba, ba tare da ya ce mata uffan ba.
Muka fito tare tana duba results din namu.
Ta miko mini tare da cewa "kun kai ga barka! baku da matsalar komai, ina yi muku fatan alheri".
Na kasa amsawa, bansan kuma dalilin ba.
Ta wuce da alama round take yi.
Na bu'de murfin motar zan shiga, na ji kamar muryar Yaya Ashir ya ce "Sadiya".
Na juya da sauri ai ko shine ba kama ba ce.
Na amsa da sakakkiyar fuska.
Na gaishe shi, ya amsa da walwala yana tambayar me na zo yi asibiti?
Na kasa bashi amsa, ya m'iko hannu ya karbi file din hannuna.
Ya dudduba ya mayar da su fuska ba walwala.
Ya numfasa ya ce "fatan alheri! Tare kuke da Sadik kenan? I thought da Abbas kuke na ga motar Abba ce, nasan kuma Abbas kawai Abba yake bawa motarsa".
Ya 'Dan rankwafa ka'dan ya ce "Sadik girma na shirin hawa kanka amma ba zaka gane rayuwa ba. Ina 'dan-uwanka kuma Yayanka amma ba zaka fito mu gaisa ba?".
Kai-tsaye ya bashi amsa da cewa "Ai ba dan ni ka tsaya ba, tunda har ka bada tabbacin ka dauka Abbas ne.
Ita dai da take kanwarka kuma masoyiyarka, sai ka sake na'de kafar wando ka yi ta zazzago mata kalaman 'kauna. Ni kuma ka yi ta watso mini na kuruciya da kiyayya".
Ya kammala maganar tare da jan tsaki mai tsananin gaske.
Ganin hakan ya sanya na shiga motar jiki a sanyaye saboda yadda naga dukkansu ransu ya kai 'kololuwar 'baci.
Yaya Ashir ya ce "Na rantse maka ba dan a asibiti bane da kaga abin da zan yi maka, har kullum ina jaddada maka ni ba Al'amin ko Abbas bane da kake musu iskanci son ranka. Banda dai aure 'kaddara ne, me babbar mace irin Sadiya zata yi da kai? 'Dan mitsili da kai sai hancini da 'kifa'di".
Yana rufe baki ya nausa cikin asibitin ya barmu a wajen.
'Kafafuwana har rawa suke yi, tsabar tsorata da halin da Yaya Gudale ya shiga.
Sai numfarfashi yake ya rasa inda zai saka ransa.
Ya jima kafin ya kalleni idonsa jawur tamkar gauta ya ce "A gaban ki Ashiru ya tozarta ni, amma kika kasa kare ni ko?
To bari ki ji ina tabbatar miki sai dai a tsine mini amma sai dai auren ya koma kansa.
Me za'a yi da matar da za'a ci mutuncin mijinta amma ta yi farin-ciki da hakan?
Na gane dama soyayya kuke yi, to huta roro na bar masa, dama shi ya dace da kumbusa irin ki".
Murya a dusashe na ce "Ka yi hakuri ka sani dai babu ruwana, ni kaina ji na yi tamkar na