Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   50 / 61

147K to 150K   out of 180.1K words

martani a gabansa.
Yayin da ni kuma na ki tankawa, duk yadda nake jin zuciyata tamkar ta fashe a dalilin yadda ni yake bude mini wuta idan na kuskure amma bai isa ya yiwa Munu hakan ba. Har yau din nan basu yarda sun fito da maganar damben da ta yi da Anti Maimuna ba.
Ya kalle ni ya ce"Kin mayar da ni mahaukaci ko Halimatu? To na rantse miki sai kin bar aikin nan kome kike ji da shi kuwa".
Murya na rawa na ce "Ai kuwa ba zan bari ba Sadik! Ita wacvar matar da ke kana sonta kana tsoronta ai ta fara aikinta, ba kuma izninka amma baka ce komai ba".
Ya murde mini kunne ya ce "Ko a Rivers State zata tafi kullum da sunan aiki ba zai dame ni ba, amma ke ko a kofar gidan nan zaki dinga yi ba zan yarda ba. Dama na yi hakuri ne, amma tunda baki fahimci ha'kurin da nake ta yi miki ba, kika mayar wa da Umma magana Wallahi magana ta kare, ai komai zata ce sai ki yi hakuri ki duba ita din uwata ce, amma tunda kika iya irin wannan wula'kancin to kuwa magana ta kare. Na dakatar da aikin ki"
Na yi murmushi hawaye na zuba na ce "Bai dakatu ba, ba kuma zai dakatu ba Yaya Gudale."
Washagari kuwa na yi ficewata, ina bakin A&E a tsaye sai ga Yaya Ashir, ya tsaya muka gaisa, muna cikin gaisawar suka zo shi da Umma ya kawota ganin likita.
Hatta Ashir da ya gaida Umma bata amsa, bare kuma tawa gaisuwar. Shi kuwa Gudale ya kallemu ya watsar bayan ya sanya gilashinsa.
Zuciyata ta tsinke na tabbatar abin da zai biyo baya ba mai sau'ki bane.

*Hanyar komawarsu gida*.
Umma sai fa'di take "To gashi dai ana maka hira da Mata har da kyakyacewa. Na fa'di gaskiya kuma ta zage ni ta hanyar nunawa y'ata ma hakan take, akan idonka kuma. Wallahi ban da nasan ba a barka haka siddan ba, to kuwa lah shakka da na sallamaka, ranar tashin kiyama sai Ubangiji ya yi mana hisabin wahalar da gatan da na rayu ina yi maka amma ka bijire mini, kake kuma zaune da matar da zata kalli idona ta mayar mini da magana a gabanka."
Ta dinga goge hawaye da tissue.
A hankali ya ce "Ki zuba ido Umma zan dauki mataki fah".
Ta rakakkabe murya ta ce "Matu'kar baka tsaida aikinta ba. Billahillazi sai dai na sallamaka, zan fita daga dukkan sha'aninka Wallahi".
Da yamma na dawo na tarar da shi a falona tunda dama a wajena yake.
Idon nan nasa tamkar garwashi. Na wuce na yi dakina.
Ya biyo ni yana fa'din "Hamshakiya ishasshiya! Yau zaki ga karshen kafiyarki".
Ban kula shi ba. Ya sake hassala ya ce "Da uzinin uwar wa kika fita?"
Sai lokacin na ce "Kada ka sake ka sako uwata a wannan maganar ".
Ya kuwa fusata ya ce "Na sako uwar taki dan uwarki, Ina ce ni a akan idona kika yiwa tawa Uwar rashin kunyar?"
Hawaye ya goce mini na ce "Bani da kaico Yaya Gudale dan ka zagi Mama, nasan zugo ka aka yi, kuma mai zugar ma bata tsira a wajenka ba, ashe kuwa dan ka zagi uwar wani ai ba abin na yi ba'kin ciki ba ne.
Ai kuwa ya dauke ni da mari. Yana huci ya ce "Kin yi k'arya Wallahi! Halima ba zaki rabauta ba, na ce kada ki je aiki, kika take maganata, kika fice ko?
Sannan kuma na je na tarar da ke da Ashiru kuna barbad'a
Ashe Umma gaskiya ta fa'da. Amma kika rufe ido kika yi mata rashin kunya saboda kina ganin kin isa.
To sai ki je, ki auri Ashiru domin ba zan iya cigaba da zama da ke, ba kya mini ragayya akan uwata ba, sannan ba zaki girmama ra'ayina ba. Na datse igiyar aurena d'aya akan ki".
Bai jira komai ba ya fice.
Bansan ya aka yi ba, na ji na fa'di akan gadona, k'irjina ya yi nauyi, ban yi zaton irin wannan hukuncin ne zai biyo baya ba".




*Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?*
*kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*.
*Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.*
*Sister Zainab 08039315577.*
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *SDK*
*87&88*.
Idan na ce zan bayyana irin yadda sakin nan ya buge ni, na yi k'arya amma wacce mijin da take so ya saketa ba da hakkinta ba ita ce ka'dai zata fahimci irin dimuwar da nake ciki.
Wani irin tashin hankalin da ban yi zaton zai ziyarce ni ba, ya mamaye ni.
Na dinga jin ashe lokacin da Gudale zai kara kara aure ba tashin hanki na shiga ba.
Yanzu ne nake cikin firgici mai yawa.
Na kasa tashi har aka idar da sallar maghrib ban iya motsawa ba.
Ina nan inda na zube har taran dare tamkar mutum mutumi.
Ga Afrah bata nan, Amnah ta jata suna wajen Umma.
Idona ya bushe a ranar na fahimci yin kuka ma ba karamin Rahma ba ne.
Take na tuno Abba! Na dinga tuna yadda yake fatan aurenmu ya dauwama muddin rai, ashe hakan ba zai samu ba.
A k'asa da shekara da mutuwarsa komai y subuce mini har da auren.
Tunawar da na yi da Abba ne, wani irin kuka ya goce mini.
Na dinga yi ina shesskar ajiyar zucy, ina jin inama na hadiye zuciya na mutu ko na huta da wananan masifar.
Na dinga tuno togaciyar da Mamana ta yi mini kada na sake na zama surukar Umma domin ba zan huta a hannunta ba.
Na gane wautar da na yi da nake ganin ba zan damu da matsalar Umma ba.
Ashe kuwa ita ce matsalar, domin ita take jan kaso sab'a'in da biyar na matsalar aurena.
Da k'yar na rarrafa na yo alwallah.
A ranar kam ban san me na karanta a karatun sallah ba.
Tsabar tashin hankali.
Na idar, amma ba kasa tashi akan abin sallar.
Kullum ta Allah na sani sai na yiwa Abba a addu'a a fili ko a boye. Amma a wannan daren kafin gari ya waye ban san adadin addu'ar da na dinga aika masa ba.
Na idar da sallar asuba barci ya dan sure ni.
Sai kawai na yi mafarin Abba da farin tufafi yana cewa "Alheri mai yawa ya tunkaro ki Halimatu! Daure ki mini alfarmar yin idda a dakinki, idan kuma ya nemi sulhu kada ki yi tutsu ba yin kansa bane, zuga ne da kuma sharrin zuciya, kada ki barshi a wannan halin, idan har kin kasa jure zama da shi, babu wacce zata zauna mini da shi, ni kuma so nake ki zame masa garkuwa har a aljannah".
Daga haka ya dinga yin murmushi yana tafiya da baya da baya cikin murmusshi.
Yayin dana dinga mi'ka masa hannu Ina cewa zan bika Abba! Ka tafi da ni".
Bai ce komai ba amma ta girgiza kai alamun ba zan bishi ba.
Koda na tashi ban manta mafarkin ba. Jikina ya sake sosai.
Na kasa yin katabus, zufa sai karyo mini take yi tamkar ba sanyi ake yi ba.
Har k'arfe takwas na safiya ina ta saken saken shin na tafi ne, ko kuwa na zauna na yi idda kamar yadda Abba ya ro'ke ni?
Kaso mafi yawa na zuciyata yafi rinjayar mini na zauna.
Dan hakan sai na zabi na zauna din, ina kuma fatan mu shirya domin bansan son Gudale bai yi rauni a zuciyata ba sai a ranar.
Domin da na tuna ya sake ni sai zuciyata ta buga, zufa ta dinga karyo mini tamkar wanda na yi tseren gudu a lokacin zafi.
Na kasa kunne na ga fitarsa amma har goma ta buga ban ji motsin ba, na leka ta windo amma na ga motocinmu duk suna nan tabbacin bai fita ba.
Kuma ranar aiki ce.

*Gudale*.
Yana kwance a dakinsa abin duniya ya rufar masa, zuciyarsa ta ki kwanciya, mafarki ya yi Ashiru ya zo neman auren Guduyo.
Ya ganta ta ci kwalliya tana zaune a yar bukkar da Abba ya gina a harabar gidan dan hutawarsu shi da Baban Yara.
Sai murmushi take yi.
Yayin da Ashiru yake fa'din "Ubangiji baya kuskure Halimatu! Bayan dogon lokaci dana dauka ina dakon soyayyarki, sai bayan da na cire rai da samun ki, sai Ubangiji ya juya al'amura, gashi zai cika mini buri.
Zan yi komai dan na same ki, zan yi rikici da duk wanda ya nemi nuna mini ana barin halak dan kunya, a yanzu ke din ta mai rabo ce.
Tunda wawan mijinki ya bar ki kika fito daga gidansa, ya sake yin wautar bari kika kammala iddarki to kuwa zan fafata da shi dan na tabbatar na yi masa kwalelenki kamar yadda ya yi mini a karon farko.
Halimatu ta murmusa dimples suka lotsa.
Abayar da take jikinta bata boye tudun kirjinta ba. Hannayenta dauke da lalle da ya sake kawata ta.
Ta ce "Yaya Ashir kai me zabina, ka daina sako maganar Sadik domin tuni na rufe babinsa, dama kaddarar zan haifa masa su Amnah ne, ka daina bata ranka akan wannan sakaran".
Dai dai nan ya farka. Fargaba me yawa ta kama shi, da ya tuno ya saki Guduyo fa da gaske. Nan da nan ya zabura ya duro daga kan gado yana cewa "Tabbas mafarki ba gaskiya bane, amma sau tari yana iya zama gaskiyar. Ashiru zaka yi abin da yafi haka shegantaka ma. Domin na tabbatar babu Allah a harshenka bare a zuciyarka, baka k'i na mutu ka zo zawarcin Guduyo ba".
Ya dauki waya ya kira Sakina bugu biyu ta dauka. Kafin ta ce komai ya fit ya ce "Sakina maganar da Guduyo ta fa'da miki na janyeta, ki kira ki fa'da mata."
Cikin rashin sanin manufarsa ta ce "Bamu yi waya da ita ba, rabona da ita tun jiya a asibiti, har yanzu kuma bamu yi waya ba, na kira duka layukanta a kashe, lafiya kuwa yau bata zo aiki ba?".
Ya waske da cewa "shikenan sai anjima".
"To ina ta tafi?
Tunda bata fa'dawa Sakina ba ya tabbatar bata fada wa kowa ba.
Wani irin al'amari ya dinga mamayarsa, amma idan ya tuna kukan da Umma take yi, ya sake hango yadda ya ganta tsaye da Ashiru babu fargaba ko nadamar ta karya dokar da ya saka mata, sai ya ji ransa ya kai koluluwar baci.

*Dakin Guduyo*.
Ina zaune hawaye yana ta zubo mini, sai kawai na ganshi a bakin kofar dakin ya yi turus wata'kila bai yi zaton zai gan ni a ciki ba, domin a hanzarce ya turo kofar.
A sanyaye ya shigo dakin ya zauna akan front drower. Ya da'de yana kallona cikin rashin abin cewa.
Yayin da na yi karfin halin ha'diye kukan da nake yi.
Murya ba amo ya ce "Baki tafi ba guduyo?".
Nima tawa muryar babu amo na ce "Ina nazarin inda zan tafi ne, tunda kasan ai Baba ba zai bar ni na zauna masa a gida ba, tunda kai kullum mai gaskiya ne a idonsa".
A hankali ya ce "Ki ajiye aikinki Guduyo bana so, bana so, bana so."
Murya na rawa na ce "Idan na ajiye so kake na dinga bin dangi ina yar murya ko? Ni ba aure ba, ni kuma ba ga abin da zan dogara da kaina ba."
Ya sauko ya tsugunna a gabana ya ce "Kishinki nake ji mai yawa. Tabbas akwai Yar tsama a tsakaninmu da Ashiru, amma ban tsane shi ba, sai da ya bari na fahimci yana son ki, amma ke kin kasa gane iya gaisuwa kawai na amince ki yi da shi, na tsani doguwar hirar da babu hijabi a tsakaninku."
Baki na rawa na ce "To ai yanzu tunda ka sake ni, ba ruwana da fa'da mini wannan maganganun, kai ma kuma babu ruwanka da aikina".
Ya sassauta ya ce "Idan kin yarda ai shiryawa zamu yi Guduyo, ko barci fa ban yi ba, kalli yadda na sake kankance wa mana daga yammma zuwa yau".
Wata irin salama ta shige ni, na tabbatar ko ban yi mafarki da Abba ba, ba zan iya yin turjiya mai yawa ba, kawai dai zan yi jarumtar da ba zan nemi sulhu da kaina ba.
Hawaye ya goce mini, na kifa kaina akan guiwata na dinga yin kuka mai dauke da gunji saosai.
Ya rikice yana cewa "Ki yi ha'kuri kin ji! Ki taimke ni, ki ajiye aikin nan, zan nemo miki wani, zan yanka miki albashi, kin sani Abba ya tara mana dukiya me yawa, so yake kuma na rayu da ke".
Wannan maganar sai ta sake tsananta kukana.
Cikin kuka sosai na ce "To ai kasan da hakan ka rufe ido ka sake ni, alhalin ban yi maka komai ba".
"Nan da nan ya harzuko ya ce "Baki mini komai ba kika ce? Shin Ashiru wai matsayin su daya da Al'amin ne a wajenki? Ke nifa rungumar da Al'amin ya miki ma fa ha'kuri kawai na yi Billahillazi! tunda shari'a bata sanya takunkumi akan hakan ba, na kuma sani har duniya ta na'de babu aure a tsakaninku. Amma ina tabbatar miki Ashiru a yanzu haka bai ki na mutu ba".
Na kasa cewa komai saboda yadda ya fitattike.
Tsawon lokaci muka yi tsit, tamkar mutuwa ta gilma.
Ya nisa ya ce "Ina son mu shirya yanzu Guduyo! Ki yiwa Allah ki ha'kura da aikin nan, na rantse miki ba zamu ta'ba samun zaman lafiya da ke ba matu'kar kina kan ra'ayinki".
Ganin yana lallashina sai na dan ja zare ka'dan na ce "Ba dai ka rabu da ni ba?
To kawai mu rufe maganar haka nan".
Ya sassauta ya ce "Ni na riga da na huce Guduyo, kinga dai Abba da yanan ba zai ji da'di wannan bak'ar kaddarar da ta sauko mini na furta wannan kalmar ba.
Mu rufe a tsakaninmu, ba sai kowa ya ji ba.
Na zum'bura baki na yi shiru
"Kawai ki ajiye musu aikin sai mu yi zamanmu lafiya, kuma tafiyar da baki yi kin bar ni ba, na yi matu'kar gode miki, na kuma sake girmamaki Allah ya yi miki albarka".
Bansan meyasa ba, nake jin matu'kar Umma tana d'oron k'asa bazan ta'ba samun kwanciyar hankali da Gudale ba.
Na yi imani da Allah ko kaffara ba zan yi ba, ita ce ta yi mini sanadin tsinkewar igiyar aurena ta hanyar sake tunzura shi.
Hawaye ya goce mini, na kasa cewa komai.
Ya ce "Zaki ajiye din?"
Na tsinci kaina da cewa "Eh".
Nan da nan ya rungume ni, yana cewa "Na gode sosai, Àllah ya kore shaidanin da yake tsakaninmu.
Na janye, na mayar da ke".
Na yi shiru illah hawayen da ya k'i yanke mini.
Ya ce ", Amma dai kinsan bana son irin wannan kukan ko?"
"Ai kuwa kuka ya same ni, akan abin da bai kai ya kawo ba kawai ka sake ni, idan kuwa haka ne ba za'a dauki lokaci mai yawa ba zaka haramta mana zaman gaba'daya".
Jikinsa ya yi sanyi ya ce "ki daina yi mini mugun fata Guduyo! kaddara ce ta hau kaina da wani irin zazzafan kishi."
Na kafe shi da ido na ce "menene matsalarka da Yaya Ashir ne? Yanzu gaisawa da shi
sai ya zama sanadin mutuwar aure dan kawai darajar aure ta fa'di warwas, alhalin kuma shi din dan-uwana ne. Kawai dai an zugoka ne, an kuma saka ka datse mini aikina dan kawai ba'a son a ganni cikin walwala alhalin ba a kaina aka fara aikin ba".
Ya zabura ya ture ni daga jikinsa, ya nuna ni da yatsa ya ce " Billahillazi zan yi miki dukan da ba zaki fahimci komai ba tsawon lokaci mai yawa. Baki da mutunci Guduyo! A gabana kike ta zagin Umma? To ta yi zugar tabbatacciya marar mutunci. Dama fa hakuri na yi, akan idona kika ce bana ganin mutuncinta, ina zaginta, to mu kaddara ma ina zagin nata amma ke kuma kin ci uwar karya kin kwana da yunwa ki zageta ki kwashe kalau a hannuna.
Na mayar da ke tabbas, ko kina so, ko ba kya so kin maidu, kuma ki tashi ki shirya na raka ki, ki bata hakuri."
Nan da nan na sake zum'bura baki, na juya fuskata tabbacin ba zan je ba kenan.
Ya mike ya ce "Tun jiya nake cikin tashin hankali saboda ke, amma sam ke baki gane ba, kuma Wallahi ko zaki shide sai kin je."
Ya fice ya bar ni da bacin rai mai yawa.
Bai jima ba sai gashi ya dawo da belt. Na zabura na mike na ce "Na rantse idan ka dake ni da wannan abar zaka yi nadama."
Ai sai kawai ya ce "Zan doke ki ne ba a matsayin miji ba, a matsayin yayanki da za'a tura gidan aurenki ya ladabtar da ke idan kika nemi zubar mana da tarbiyar gida".
Na sha kune na ce "uhum uhum".
Ya nuna kansa ya ce "Ban isa ba ko Guduyo? Babu wata alfarma da zaki iya yi mini ko?
To bari laifin da kika yi mata ya zama sanadin da zata tsine mini, idan ya so na lalace na kasa yin albarka, idan kuma hakan ta faru ai ke ce a ciki, tunda ya'yanki ne zasu fi kowa yin asara".
Na ce ba y'ay'ana kawai ba, na munu fa? Sannan ita meyasa ka barta take yin aikin?"
Ba fargaba ya ce "Saboda ita ina sonta, ina kuma jin tsoronta, ke kuma bana son ki, na kuma fi karfinki ina ce shikenan?".
Idona ya ciko da 'kwallah takaici tamkar na ha'diye zuciya na mutu.
Haka ya tisa ni a gaba amma muna fitowa falo ya yar da belt din.
Muna isa kofar shiga bangaren Umma zuciyata ta tsinke, saboda tuno Abba da na yi, sannan kuma zuciyata tana ganin bai cancanci na bata ha'kuri ba alhalin bata nufina da alheri.
Mun zo daidai windon dakinta, na juya da sauri ai kuwa ya damko ni yana fa'din "Idan ba zaki yi saboda ki taimake ni ba, to ki girmamata saboda matar Abba ce, bata ha'kuri saboda shi"
Shikenan na bishi muka shiga cikin gidan.
Bamu zame koina ba sai ciki dakin Umma.
Na zauna daga gefe a kasa yayin da Gudale ya zauna a bakin gadon.
Na gaisheta ta amsa da k'yar a kuma wula'kance.
Shima tasa ba walwala ta amsa masa.
Tsawon lokaci ba wanda ya sake yin magana.
Gudale sai kallona yake yi. Cikin karfin hali na ce "Umma ki yi hakuri akan abin da ya faru jiya, baki fahimce ni bane, kallon uwa nake yi miki, matu'kar ba

50 / 61