Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
yi ittifakin zuri'arsu ba sa barin namiji salin alin, ga tabbaci ma ina gani ba iya mijinta ta gama da shi ba, hatta kurwar Abbanku tana karkashin ikonta. Shi ne kuma ake son sai an ha'da da kai ka'dai da Ubangiji ya ba ni! Wallahi da hakan ta faru gara a ce ina kushewa".
Ya ce, "Yanzu Umma a yadda nake din nan har ki yi tunanin zan so Guduyo?
Ban da farar fata mene ne da ita ne, ai ni sam ba na son 'yan lukutayen mata, ba sa burge ni. Kawai dai ina son na samu damar da zan rika ganin surarta, domin tana matu'kar kidima ni".
Ihu Umma ta fasa tana cewa "Shike nan ta faru ta 'kare, ashe da gaske kana shaye-shaye Gudale? Ni ka furtawa wannan 'kazamar kalmar?".
Ya mike ba tare da ya ji wata fargabar komai ba ya ce, "Ni irin wannan abin naki ne yake ha'da ni da ke, to idan ban fa'da miki damuwata ba, wa zan fa'dawa ya fahimce ni? Ba na son ta, ban ta'ba raya zan so ta ba, amma idan ba zan rufe ki ba, da gaske ina son ganin ta, ai abin ki yi murna ne, Gudalenki ya zama man".
Salati kawai Umma take yi tana 'karawa tana cewa, "Haka za ka yi mini?"
Ya fice ya bar ta cikin bacin rai iri-iri. Shi kuma bai ga laifinsa ba, to idan mutum bai fa'dawa uwarsa damuwarsa ba wa zai fa'dawa a duniyarsa? Washagari da hantsi ya sake tarar da iyayen nasa. Kusa da Abba ya zauna a nutse tamkar gaske ya ce, "Abba fa'da mini don Allah kana da shekaru nawa ka auri Umma?".
A matu'kar sanyaye Abban ya ce, "Ina da shekaru ashirin da biyar Mahaifina ya ce ya gaji da zamana haka, shi ne kuma ya za'ba mini ita, a dalilin ya saba da mahaifinta wajen saye da sayarwar dabbobi".
Kai-tsaye Sadik ya ce, "Shekaruna ashirin da shida next month Abba!".
Ido sosai dukkansu suka zuba masa, sun kasa gane me yake damun tilon 'dansu, ba a buge yake ba, amma kuma sun tabbatar ba a cikin hayyacinsa yake ba.
Da mamaki Abba ya ce, "Aure kake so ke nan?"
"Ya ka'da kafadarsa ya ce "No! Ina dai son na gane irin adalcin da tsohonka ya yi maka, mahaifinka yana da hangen nesa, ina yi maka ta'aziyyar rashinsa Allah ya jikan sa."
"Amin summa amin."
Abba ya tsinci kansa da furtawa cikin ru'du.
Tsawon lokaci yana kallon Sadik sannan ya nisa ya ce, "Ka fara koyon sana'a, idan na gamsu ka mayar da hankalinka akan sana'ar sai a je ma nemo maka auren a inda ka ga yarinyar".
A sanyaye Umma ta ce, "Abdallah da Babangida kai ka samo musu mata fa Abban Yara".
Da sauri ya ce, "Su ma sai da na ba su damar su kawo zabinsu, sai da na ga ba su da niyyar kawowar ya sa na zabo musu da kaina, suka karba kuma babu musu. Har yau din nan ba wanda ya kunyata ni."
"Shi ma ai ba zai kunyata ka ba". Ta fa'da a tunzure.
"Allah Ya sa! Amma dai ya kawo wacce yake so da kansa, domin shi da su ba 'daya ba ne".
Daga Umma har shi duk sun san magana ya fa'da musu shi yasa suka yi tsit.
Sadik ya mi'ke yana cewa, "Ni dai ka samo mini aiki, ka riga ka san ni ba zan iya sana'a ba, tunda Allah ya sa na yi karatun".
Ya sake cewa, "Ka samo mini matar, ba zan ba'da maka 'kasa a ido ba, amma dai Abba plz! Bari ka ji ra'ayina, ba gajeriya ba, sannan ba mai jiki ba. Yar shawalwala, doguwa, fara, mai dogon gashi, wacce ta kammala karatunta na jami'a. Bayan haka ta kasance yar attajiri ce, ba na son a kwaso mini 'yar talakawa su zo su cika mini gida tamkar yadda dangin Umma suke yi, idan za su zo. Babu lissafi sai su 'dungumo da yawansu tamkar gidadawa".
Cikin wani irin yanayi Abba ya mi'ke. Sanin da Sadik ya yi duka za a kawo masa yasa shi kwasa a guje, ya fice.
# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?
Page 7&8.
Ya koma ya zauna cikin 'kunan rai mai yawa ya ce, "Ba zan fasa fa'da miki kin lalata rayuwar yaron nan saboda dalilinki na jahilci. Amma da'din abin ke ma ba jin dadinsa kike yi ba".
Ta yi shiru tana wasi-wasin sakawa Gudalenta hannu aka yi, ai da baya mata irin wannan sha'kiyancin, sannan idan Abbansu na guri ko kwakkwaran motsi ba ya yi saboda shakkarsa da yake ji. Amma a kwanakin nan hatta Abban bai tsira ba.
A fusace ya bar mata falon zuwa cikin 'dakinsa.
Na fito harabar gidan na hango shi ya fito kusan a guje, a fili na ce, "Ko sai yaushe zai daina fitinar da Abba zai daina kai masa mahangur'ba?"
Domin idan har na gan shi cikin hanzari sosai, ko gudu gudu ba shakka Abba ne ya kai masa wawura.
Haka kawai sai na ji ina son tsokanarsa kamar yadda na saba. Na saka sauri, na rufa masa baya, har mashigar bangaren samarin gidan.
Ganin zai 'kule ya saka na bude murya na ce "Yaya Sadik na dauko maka turmin ne?"
Ya juyo a fusace ya ce mini, "Kan uwarki za ki dauko mini. Munafukar banza, kullum idonki na kaina, na rasa irin wannan mayata. Wallahi saboda ke zan fara shan Lahaula! Ashe 'dan uwanka ma yana bin diddiginka, yana burin ganinka a uku?"
Na maze tamkar ban ji zafin furucinsa ba, na ce, "Na sani ko zai maka amfani idan zaka yi sana'ar da ka 'kware ta 'ketara katanga".
Takaici ya kama shi, ya juyo da gudu, ni ma na kwasa a guje, da iyakacin 'karfina nake gudun domin kuwa idan na yi saken da ya cim mini abin da zai biyo baya ba mai sau'ki ba ne.
Abba na tsaye fitowarsa ke nan ya hango muna tseren gudu, dalilin da ya sanya Yaya Sadik juyawa, ba tare da na lura ba.
Dole ta gabansa zan wuce, na ci burki a gabansa cikin matsanancin haki, da kuma nutsuwar na tsira. Domin na sani iyashegen Gudale bai da tasiri matu'kar Abba na wajen, ilai kuwa da na tsugunna sai hango Yaya Sadik na yi ya juya cikin gudun fanfalaki zuwa wajensu.
A matu'kar fusace Abba yake ce mini, "Ashe har yau 'din nan ba ki daina zuwa wajensu ba?"
Jikina ya sabe da rawa, saboda sanin da na yi ya sha mini togaciya akan na kiyayi zuwa wajensu. Da kakkausar murya tamkar ba Abba ba, ya ce, "ki kiyayi Sadik, zai ji miki rauni, ba sa'anki ba ne, ba kuma shi da nutsuwar da zai ji nauyin wargaza miki rayuwarki, ki taya mu kulawa da tarbiyarki".
Daga hakan ya wuce ya nufi 'kofar da za ta sada shi zuwa cikin tafkeken kongonsa da a yanzu gefe 'daya ya zama wani irin lambu, mai dauke da lemon tsami, na za'ki, goba, kashu, fasadabir, har da mangwaro, ga kuma su zogale da duk sauran ganyayyaki da su aka fara shukawa. A hakan kuma tamkar ba a yanki komai ba saboda tsananin girman wajen domin asali filaye biyu ne manya a ha'de.
A sanyaye na mike na yi wajen Umma domin lokacin da suke gudanar da aikin abinci ya yi, kasancewa ta mai son koyon dabarun girki-girke ce ya sanya ni yin 'kawance da masu aikinta, musamman masu hidimar abinci. Duk da cewa ba ta sakar musu ragamar abincin gaba'daya.
Duk da yadda nake ganin tana 'daure fuska idan na shiga kicin ba ya hana ni tsayawa na saka ido, har ma na kama wani abin, musamman idan na tabbatar Abba na nan, idan kuwa ba ya nan ba ta jin nauyin cewa na fita bavta son kinibibi da nunkufurci, shin me yasa ba zan koya a wajen uwata ba?
Ba na fishi domin gobe ma zan sake shiga, a dalilin Ubangiji ya yi mata baiwar iya sarrafa girki, fiye da zato. Sannan kullum abinci kala uku take yi, biyu na rana, ga kuma na dare, na daren ne ma ban cika tsayawa ba, domin ta fi yin tuwo saboda Abba.
Matu'kar ba miyar kuka za su yi ba, Baba Delu sai ta san yadda ta yi ta kira ni domin na ga yadda za a sarrafa nau'in miyar da za su yi. Saboda tana jin da'din girmama ta da nake yi, sannan tana son a ce an 'karu da ita, tana son ganin yarinyar da take da burun koyon girke-girke.
Mafi yawa idan na koma wajenmu, sai na gwada abin da na koyo, shi yasa na yi sa'a na tara kalolin abinci masu yawa, da na iya sarrafa su, don ma boarding school nake yi ta cinye mini lokutana.
*Kina bu'katar dukkan nau'in sutura masu kyau, zababbu kuma masu sau'kin farashi?*
*Kina bukatar siyar da furnitures din ki?*
*Kina bu'katar siyan furnitures din hannu da basu ji jki ba?*
*Albishirinki A AMYAS NEWLY & FAIRLY USED.* *Zaki samu dukkan abin da kike so cikin farashi mai sau'ki.*
*AMYAS NEWLY & FAIRLY* *komai da ruwanka ne domin hatta Talabijin da fridge, inji wanki, da dukkan dangin electronics zaku samu a wajensu. Sababbi ko tuwaris masu quality*
*Dan haka ku tuntu'be su àkan wannan lambar dan tabbatar da nagartar kayansu. 08083909947*
A hakan na cinye hutuna, na tattara na koma bisa rakiyar Yaya Al'amin da Yaya Sadik. Yaya Abbas ya tu'ka Abba zuwa wani daurin aure Dutse, domin ba wanda Abba yake yarda ya tuka shi, matu'kar ba Yaya Abdallah ba sai Ya Abbas domin a nutse yake yin tu'kinsa kai akan komai ma mai nutsuwa ne kwarai da gaske.
A hanya sai takalar Autan Umma nake yi don dai na samu ya kula ni.
Amma ya yi funfurus, tamkar ba da shi nake yi ba.
Yaya Al'amin da ya kasance direba, ya tunzura ya ce, "Wai ke kam wacce irin yarinya ce ne? Tunda ga Kano kike yi masa magana amma har yanzu da muka iso Zariya bai ce miki kanzil ba. Hakan bai ishe ki isharar cewar ba ya cikin sukunin da zai kula ki ba? Ki 'kyale shi mana ya ji da damuwarsa".
Yana rufe baki Ya Sadik ya juyo ya ce mini, "Ina jin ki, ai dai kin san laifi kika mini kan laifi! Amma ba ki san ki ba ni ha'kuri ba. Ranar nan Sakina ta nemi yin munafunci a tsakaninmu, yanzu kuma ga wani zai sake shiga, ki daina ba su damar shiga tsakanin zumuncinmu, saboda haka ma na yafe miki mun shirya. 'Yan ba'kin ciki sai su rungumi taransifoma".
Yaya Al'amin ya ce, "Su waye 'yan ba'kin cikin?"
Ba ja'inja Yaya Sadik ya ba shi amsa da cewa, "Kai da Sakina mana! Babban burinku ku ga mun sami matsala da Guduyo, to abin da ba ku sani ba, duk yadda kuke gadarar ku ne mafi kusa da ita, ni kuma zumuncina da ita ya fi 'karfin ku ce za ku shiga cikinsa, domin mutum kunyata zai yi".
Sanin halinsa da Yaya Al'amin ya yi yasa shi fa'din, "Allah ya bar zumunci" A ta'kaice.
Har muka isa Kaduna hira muke yi sosai, amma da zarar Ya Al'amin ya saka baki, ba kunya zai ce ya yi masa shiru! Tamkar dai shi ne Babba.
Suka ajiye ni, muka rabu cikin alhini, Ya Sadik ya mini al'kawarin in sha Allah zai halarci bikin (Graduation Ceremony) da za mu yi.
Na kalle su dukkansu na ce "Ba ku ba ni komai ba".
Ya Al'amin ya juya ya shiga mota yana cewa, "Ke ro'ko ba ya miki nauyi ne?"
Yayin da Ya Sadik ya zura hannu a aljihunsa ya fito da sabbin kudi masu yawa, ya zaro 'yan dari biyar guda hudu ya ce, "Ungo na sammiki, domin zance za ni shi yasa na samo sabbin ku'di kin san suna 'kara aji da kwarjini".
Wannan maganar ta yi matu'kar razana ni, na yi nadamar ro'kon da na yi, da ya zama sanadin da na shiga wani irin tashin hankali da bugun zuciya. Ya lura da canjin da na samu, amma ya waske da fa'din, "Ki yi karatu sosai, ban da kawance da kawayen banza. Sannan ki kula da salla domin ita ce komai a rayuwar mumuni".
Ya shige mota suka tafi, suka bar ni cikin zullumi da fargaba. Yaya Sadik kam duk tsiyarsa ba ya wasa da salla, wannan dabi'ar ce ta sanya yake samun sassauci a wajen Abba, yakan ce duk wanda ya ri'ke salla da sannu Ubangiji zai canja dabi'unsa zuwa kyawawan dabi'u.
Na fi kwana uku ina cikin damuwar budurwarsa da ya ce mini zai je zance, haka siddan na ji na tsane ta tun ban gan ta ba. Na san ina sonsa, amma ban tabbatar ba sai a wannan lokacin da na ji zancen wata a bakinsa.
Da 'kyar na cire wannan maganar a raina. Na fuskanci karatuna, don kuwa jarrabawar 'karshe zan rubuta, idan na samu tasgaro, ni ce nake da asara. Na tafi ba jimawa Yaya Sadik ya koma Jami'ar Bayero don yin Ph.D dinsa.
Ya Al'amin kuma ya samu aiki da gidan Talabijin na 'kasa reshen jahar Kano (N.T.A KANO).
Ya Abbas kam ya riga su samun aiki, ya jima yana aiki a Federal College of Education Kano(F.C.E).
Yayin da Ashir take aiki a Asibitin Malam tunda Pharmacy ya karanta.
Haka rayuwar ta ci gaba da gurgurawa har ranar bikin gama makarantar mu ta zo.
Kusan kowa ya zo mini wannan bikin, hatta iyalan kawun Gusau sun zo, bare kuma Antin Zariya da muka fi kusanci.
Sun ji da'din zuwan kuwa, domin na karbi kyautukan karramawa har guda uku. Na kar'bi na dalibar da tafi kowa 'da'a, na karbi na wacce ta fi kowa iya lissafi. Sannan na lashe kyautar dawowa makaranta akan ka'ida, ma'ana ba na 'karin hutu.
Murnar da na gani akan fuskar ahalina ya matu'kar sa ni nisha'di da rawar kai.
Ina fatan Allah Ya saka sakamakon jarabawa da muka kammala ya fi hakan sanya musu farinciki.
Yaya Sadik ne kawai yake fadin "Akan me ban lashe Turanci da su Chemistry ba?" Wai ban yi kokarin a zo a gani ba.
Kwana biyu tsakani muka kammala gaba'daya, direban Antin Zariya ya zo dauka ta a dalilin ta roki su Abba za ta dauko ni na yi kwanaki uku a gurinta sai mu taho tare, saboda za ta zo aiki na sati guda a ma'aikatarsu ta Kano.
Sosai na ji da'din zama duk da ba zan iya tuna yaushe na zo mata ba, saboda ta fi zaman Abuja. Sannan ni kaina ban cika barin gida ba, idan kuwa har ba na gida to ba na wuce gidan Sakina. Ko gidan 'kanwar Mama da take zaune a 'Danladi Nasidi nan din ma ba sosai ba, na fi dai 'karfi a gidan Sakina."
Ba wani jimawa WAEC ta fito, sosai sakamakona ya burge kowa, domin A1 guda uku ne a ciki sai B2 da B3 ko C babu, balle aje ga zancen D ko F.
Haka result din JAMB ya yi kyau domin kuwa ya zarce 200.
Wannan sakamakon shi yasa ba wahala na samu gurbin karatu a Jami'ar Bayero.
Inda na tsinci kaina zan karanci (Human Anatomy) bangaren likitanci ne.
Ba cece kucen da ba a yi ba, kafin na fara wannan karatun, saboda mafi yawa an fi son a aurar da ni, ni kuma na kafe a kan ba ni da saurayi, bisa hudubar Sakina.
Kan dole Abba da Yaya suka shafa mini lafiya.
Na fara karatun cikin dokokin masu yawa.
Mafi yawa tare muke tafiya da Ya Sadik, idan kuma ba shi da lectures da safe idan yan mutuncinsa na kusa zai bar komai ya kai ni. Idan kuwa 'yan tsiyar suna kusa na kira layinsa sama da sau goma bai 'dauka ba. Ko kuma ya 'dauka ya balbale ni da sababi a kan shi ba direbana ba ne, ba kuma shi nake yiwa karatun ba.
Haka zan kwantar da murya na ce, "In sha Allah za ka ci moriyar karatun nan, ka sake daurewa dai, ai na sani kana 'kokari".
Wataran na yi sa'a ya fito ya kai ni, wani lokacin kuma ko nafi 'kuda naci zan ha'kura na 'kyale shi. A haka na kammala shekarar farko, karatun kuma yana tafiya yadda ya kamata, domin point 'dina ya yi nauyi.
sosai.
A wannan shekarar wani attajiri a gaban layinmu ka'dan ya nemi tayar mini da hankali wai so na yake yi, matarsa ce ta rasu ta bar shi da yara biyar, ba wani babba ba ne amma dai ya kai shekaru arba'in da biyar ko da shida.
Kai tsaye Abba ya tunkura da maganar wai a ba shi izini tare da al'kawarin ba zai hana ni karatuna ba.
Daga Abban har Baba sai murna suke yi wai mutumin kirki ne, kowa ya san shi, mai kokarin ri'ke iyali ne, ai ko na yi tsalle na dire na 'ki amincewa. Tun zuwan farko na fa'da masa gaskiyar magana ban amince ba, duk kuwa da bavshi da makusa, ba kuma wani tsufa a tare da shi. Kawai ina ganin yadda 'kawayena suka auri mai iyali suke artabu, kullum cikin fitina ba ga matar gida ba, ba ga yaran gidan ba, kullum sai an yi maka sanadin 'bacin rai, ko kuma a yi ta bin ka da bi-ta da 'kulli, duk wani alherinka ba za a gani ba, amma komin 'kankantar laifinka sai ya zama abin yayatawa, abin tattaunawa abin kaicon kuma har da sharri za a 'hada.
Na sani wacce za ta ri'ke masa yara yake nema. Indai da adalci ai kamata ya yi ya nemi wata bazawara mai hankali, ko widow wadanda suka riga suka san matsalolin aure, suka kuma haifa su ma, amma rashin adalci ne zai sa a ce na amince, zaman aure zan yi ko rainon da babu godiya?
Ba karamin takaici su Abba suka ji ba, da na 'ki amincewa, suka dinga fa'din sai na fito da wanda nake so domin ai da ma da sharadin ba sai na kammala karatun zan yi aure ba, aka bari na fara karatun. Haka na ba