Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 61

102K to 105K   out of 180.1K words

kitifo dan ki gane irin tasirin da kike da shi a zuciyata ko?"
Na dinga rantsuwar ban san komai ba , ya yarda da ni.
A farko tamkar zai botsare sai kuma ya janyo ni ya rungume yana cewa "komai Ashiru da Sakina zasu fa'da kada ki yarda da su.
Domin idan kika ce zaki bijire mini, ko yin wasa da lamarina to komai yana iya faruwa a tsakaninmu".
Murya na rawa na ce "Allah ya tsare ni, komai kake so hakan zan yi maka, koda zai bata rayukan jama'a da dama".
Ya sake rungume ni sosai yana shfa cikina da ya fara tasawa yana cewa "Hey Magajin Abba barka da hutawa".
Na dan yi murmushi na ce "Idan kuma magajiyar Umma ce fa?"
Ya gimtse ka'dan ya ce "Na sani ai Mama zaki gado dan hakan Magajiyar Umma zata zo later".
Lafiya lau muke zaune, mussaman da yanzu ba matsalar komai, ba ciwon ciki ko mara, hakan nan babu kasala da amai.
A wannan tsukun Asuu ta janye strike din da take yi, na koma makaranta.
Kaffa kaffa nake yi da abin da zai motsa ransa.
A haka muke gungurawa har cikina ya shiga watan haihuwa.
Siyayyar kayan da suka zama dole kawai muka yi, irin su riguna unisex da shawul da kuma towel sai su Pampers, amma duk ragowan ya ce sai an yi haihuwa.
A satin da na kammala rubuta jarrabawar karshen zangon aji hudu aka kai ni asibiti, tunda tuni an gano ba zan iya haihuwar da kaina ba.
Ranar *14 ga watan Janairu* aka ciro mini kyakkawan jaririyata mai cike da koshin lafiya.
Na farfado na yi tozali da kyautar da Ubangiji ya yi mana wanda yawan dangi ko yawan ku'di basa sawa a samu.
Kallon farko da na yiwa yarinyar ta shiga raina, soyayya irin ta uwa ta dinga kekketa dukkan jikina.
Tun tana jaririya na tabbatar tafi kama da Gudale ba abin da ta dauko nawa. Amma koluluwar kama da Sakina ta ke yi.
Na dinga kallon yarinyar ina jin dokin samuwarta, na sani Babanta ba ita yake harin samu ba. Amma ina da yakinin idan ya ga yadda ta dauko Sakinansa zai manta da waccan fatan nasa.
Umman Danladi Nasidin ne a wajena.
Amma kusan dukkan ahalin gidanmu a Asibitin suke yini.
Hatta shi kansa Gudalen sau uku yake zuwa, dan haka ban fahimci halin da yake ciki ba, kawai dai baya daukar jaririyar sai dai ya kalle ta a cikin gadonta ko a hannuna ko hannun Umma wai bai iya daukar jarirai ba.


*Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?*
*kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*.
*Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.*
*Sister Zainab 08039315577.*






# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee ✍️.
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.


*63-64*.


Ana gobe za'a sallame ni Mama da kanta ta nuna wa Yaya Gudale sha'awar idan an sallame ni na koma gabanta, ta kula da ni ko da na sati hudu ne.
Kai tsaye ya ce "A a Mama kawai ki dawo gidana ki zauna amma ba zai yiwu ba, ni bana 'kaunar wannan al'adar bare ni da kiris ake jira ace ba zata dawo ba".
Shiru kawai ta yi masa, amma a yadda na fahimta ba ta gamsu ba, mussaman yadda Umma ta sake tsananta gaba a tsakaninmu, ba zai yiwu ace kullum sai ta zo gidanmu ba.
Haka nan ta sani duk wacce zata kawo ta zauna da ni, sai ya zama fitina tunda zuri'ar su Mama ne gaba'daya Umma bata 'kauna.
Ashe da ta koma gida da kanta ta je gaban Abba ta ro'ki arzikin na dawo gabanta tunda bani da lafiya ga kuma jego.
Take ya tabbatar mata idan an sallamo ni zai sa a kawo ni.
Tana tafiya kuwa ya kira Yaya Gudale a lokacin muna tare.
Umarni ya bashi na kai-tsaye akan cewa zan koma gida a kula da ni. Dan haka idan an yi sallama a wuce da ni kofar Baban Yara.
Ya kara da cewa "Ban da Umman naku bata girma ina ce ita zan damka wa ragamar kulawa da Halimatu tunda ko ba matar ka bace 'ya ce a gunta ta sosai".
Wani irin bacin rai ya taso wa Yaya Gudale.
Ya kasa cewa Abban komai.
Har sai da ya tambaye shi ya ji me ya ce? Ya amsa da ya ji.
Yana katse wayar ya watsa mini wani irin kallon da ya tsorata ni.
Na gigice, ya nuna ni da yatsansa ya ce "Wai ke wacce irin kafaffiyar mace ce ne?
A gaban ki Mama ta tambaye ni akan ki koma gida na ce mata a a. Dake ita tasan girma da 'kimar aure sai ta hakura da hukuncina. Saboda ta san yadda Ubangiji ya karrama miji akan matarsa.
Amma ke baki san komai ba sai kafirin taurin kai shine kika taurare kika kai maganar gaban Abba ko?".
Na fara rawar baki ina fa'din "Wallahi ban san komai ba, ka yarda ni, ko Mama bansan zata yi maka magana ba".
Ya sake yi mini wani lalataccen kallo ya mi'ke ya ce "Na rantse miki idan har kika tafi gida da sunan wanka, to ki tabbatar kin tafi kenan. Na ha'kura da ke, ba zan iya wannan auren da ban isa na zartar da hukuncina ba sai wanda kika tsara".
Nan da nan na fara kuka ina cewa "Ka dinga fahimta ta mana, na rantse maka da girman Ubangiji ban san komai ba."
Ya sassauta ka'dan ya ce "To na yarda baki san komai ba, to ina son yanzu ki fa'da wa Abba kin fi son a kawo miki wacce zata kula da ke, ki sami dai dabarar da zaki kubuce kawai. Idan kuma kin kafe ki sani ban yaudare ki ba. Dan kuwa sallama ki zan yi, na ha'kura Wallahii."
Na sake fashewa da kuka na ce "komin kankantar abu sai ka ce "Zaka sallama ni, me yasa kake mini hakan?
Kana son na gane, na kuma fahimci cewa kai baka sona, kuma bani da wani amfani a wajen ka matu'kar zan yi kuskure ko da kuwa a cikin rashin sani ne?"
Ya mi'ke ya make kafa'da ya ce "komai kika gamsu da shi duk daya a waje na.
Amma ina nan akan bakana matu'kar zaki tafi, to ki sani kin tafi kenan.
Kuma da kaina zan shigo har cikin gidan na dauki wannan 'Yar taki da ba kya gajiya da kallon ta kina murmushi, tamkar wanda wakili ne ya fara iso wa.
Duk tunanina Mama zaki biyo tunda ance galibin iyaye mata ake gado."
Na kalle shi idona fal da hawaye ina ma zan iya ce masa tabbas gado ne, amma shine ya yi gadon tasa uwar.
Sai dai na sani fa'din hakan zai zame mini sanadin bacin rai ne mai tsananin gaske. Banda bala'i daga haihuwa daya tak har ya yi raddi?
Na kalle shi na ce "Allah ya sani ban sani ba, amma 'kira Abban na fa'da masa".
Ya daure fuska ya ce "Ki 'kira shi a layin ki, ai na riga na gane so ake a sake wula'kanta ni, a ri'ke mini iyali, dan kawai ayi ta ganin raunina".
A hankali na ce "kasan wayata tana gida".
Ai kuwa ya 'kira Abban ya danna handsfree ya miko mini, ya koma gefe yana cin magani.
Abba ya dauka na gaishe shi a raunane.
Ya shiga tambayar ko lafiya nake?
Na amsa da "lafiya 'kalau a matu'kar sanyaye".
Ya ce "Ina sauraron ki".
Cikin rawar murya irin ta jin tsoro da kuma rashin mafita na ce "Abba bana son tafiya gida! Na fi son a kawo mini mai zama".
Karon farko da Abba ya bu'de mini wuta tamkar ba shi ba, tunda a kullum harshensa mai taushi ne sosai a kanmu.
Amma a wannan ranar cikin fishi ya ce "kin ci ubanki Halimatu! Ni kika kira kina inkarin umarnin da na bayar?
Na da'de da fahimtar baki da kunya ko ka'dan.
Idan kin koma din me zaki iya yiwa kan ki?
An yanka miki jiki, ba zaki bari a taimake ki, ki dan ji dama ba?
Da ciwon zaki ji ko da raino ko kuwa da fitinar mijinki?
Ba abin da zamu dora masa na dawainiya a dalilin kin dawo gida. Komai da aljihunmu zamu yi miki. Dan haka dole ki dawo ko na wata daya ne shasha da bata san ciwon kanta ba. Da kaina na zan zo na dauke ki, na ga wadda zai sake tunkara ta da maganar raini tsakanin ke da wanda yake saka ki wannan rashin mutuncin.".
Daga haka ya kashe wayarsa ya bar ni cikin zullumi.
Na kalli Yaya Gudale ya na'de hannu a kirjinsa ya cika ya batse tamkar zai fashe tsabar fishi.
Zuciyata ta sake tsinkewa shin me zai biyo bayan aurena?
A rarrabe na ce "Ya ya ka ji me ya ce ko?"
Ya galla mini harara ya ce "Na ji da kyau! Sai dai ki sani ina nan kan bakana idan har aka tafi da ke to ba zaki dawo mini ba, na ha'kura kawai".
Na fashe da wani irin kuka na tashin hankali, har wani shidewa nake yi.
Ya yi tsaki ya ce "Baki fara kuka ba Wallahi".
Take ya karbi wayarsa, ya kira Antin Zaria ya sake danna hands free suka gaisa cikin nutsuwa tamkar ba Gudale ba. Domin baya shiga shirginta ko ka'dan, baya ta'ba neman ta da kansa. Sai dai ita ta neme shi, duk yawan shekaru da mu'kaminta kuwa.
Cike da farin-ciki ta ce "Gudalen Umma ya zama Dady! Gashi har girma na sosai ya fara kama shi.
Ya bu'de murya ya ce sai yanzu ne na zama Dadi?
Shin tun ina da shekaru nawa kika haifa mini 'ya'ya?
Abba ya sha fa'da mini 'ya'yan da 'yan-uwanka suka haifa maka sune naka, domin sune zaka ga ni ranar tashin alkiyama. Ko kina nufin ni kawai yake yiwa wannan karatun kawai?"
Nan da nan ta ce "Gaskiya ne Gudale ba kai kawai yake jaddada wa ba. Ka dade da manyan 'ya'ya tabbas, har kana Shirin daukar jikoki. Wannan 'ya tawa ce halak malak. Ban taba yaye ba saboda bani da lokaci, amma akan ta zan fara, Allah ya albarkaci rayuwarta gaba'daya".
Ya sake kame wa ya ce "Sunanki ne da ita! Sannan na baki ita halak malak. Dan ki gane kina cikin mutanan da suke da 'kima a duniyata amma baki fahimta da wuri ba".
Ai kuwa nan da nan muryarta ta fara rawa tabbacin kuka take yi na farin ciki.
Cikin kuka ta ce "lallai kuwa ban fahimce ka ba Gudale! Ka bani kyautar 'ya macen da Ubangiji bai kaddara mini haihuwar ta ba?
Tabbas Ubangiji baya juyar da addu'a! Ni ka'dai nasan yadda nake tashi cikin dare ina addu'ar Ubangiji ya bani 'ya mace ko guda daya ce.
Har na ha'kura na fitar da rai. Ashe Kai ne zaka haifa mini, zan kuma tashi da ita a filin barka."
Sai kawai ta fashe da kuka sosai, domin ba ta yi zaton Gudale yana tunawa da ita ba.
Domin ko abu yake so ta yi masa, ba ta kai ya fa'da mata da kansa ba, sai dai Umma ta fa'da mata, ta kuma sanya dole ta yi masa.
Godiyar da Antin Zaria ta ke yi cikin kuka shi ya tabbatar mini ba ta dauki al'amarin kyautar da sau'ki ba.
Ni shaida ce yadda take tsananin son haihuwar ya'ya mata amma Ubangiji bai bata ba.
Kwata kwata 'Ya'yanta ma uku ne da rak kuma dukkansu maza ne.
Ya kaurara murya ya ce "Ki fara hidimar ta daga yau, dan kuwa ni ba zan taya ki ba".
Da hanzari ta ce "yanzu kuwa! Bari na turo Maimuna yanzu, da sai jibi zan taho ganin baby da mamanta, amma yanzu gobe in sha Allah ina tafe bari na tura a siyo mini ticket 'din jirgin karfe bakwai na safe."
Daga haka ya kashe wayar ya kalle ni, na yi sukuri, ido cike da hawaye.
Ya ce "sunan yarinyata Hafsatu ba Saudatu ba.
Abba ya saka mata sunan Ummah! To ni sunan Antin Zaria zan saka mata, ai shima 'Yar shi ta farko sunan Yayar 'Kwalli ta ci.
To ko yi zan yi da shi, Umman ta zo daga baya".
Na kasa cewa komai a dalilin fargabar da nake ciki sosai.
Ya sake cewa "Na bada kyautar yarinyar kin ji da kunnenki. Dan haka kina tafiya gida shikenan, zan zo na karbi abata, na bawa sisterna.
Ke kuma ki 'karata ke ka'dai sarkin masu gatan iyaye.
Ai wlh mata irin ku idan mutum ya aureku bai more ba.
Ace komai sai an nuna wa miji gazawar sa?
Ba dama abar mutum ya yi yadda yake so da iyalinsa".
Ya ja 'kwafa mai nuna bacin ran da yake ciki.
Ilahirin jikina 'bari yake yi. Cikin 'karfin hali na ce "ka yi ha'kuri ba laifina bane, Dan Allah! Dan darajar Annabi ka janye wannan kudirin, zuciyata zata iya buga wa, ko ban ci arzikin komai ba, na ci albarkacin jinin da ya ha'da mu".
Na fa'da cikin kuka sosai.
Ban san ya aka yi ba tausayina ya kama shi ya ce "ke me ya hana na ci arzikin jinin a wajen ki?
Me yasa kike yarda ake mini iko akan aurena?
Ai kinsan wula'kanta ni za'a yi, shi yasa aka shirya wannan mana'kisar."
"Wallahi ban sani ba Yaya Gudale ka yarda da ni".
Ya shiru ya ce "alright na fahimce ki, na kuma yarda amma bisa sharadi daya tak.
Billahillazi ba zaki yi ko sati uku ba. Yanzu ki fa'da mini da bakinki adadin kwanakin da zaki yi, idan kika saba to shikenan wanccan kudirin ya tabbata."
Na sauke ajiyar zuciya ina goge hawaye na ce "Na gode sosai! Idan an sallame ni gobe, nasan su Anti zasu shirya walimar suna nan da sati guda to ka yi ha'kuri mu bar shi nan da 2weeks".
Ya kuwa girgiza kai da sauri ya ce "A a ban gamsu ba, ba zan iya ba".
Na ce "To kawai mu barshi nan da kwanaki goma sha biyu dan Allah".
Ya numfasa ya ce "Idan fa ranar ta zo ba maganar wani uzziri ko ba zaki iya ba, zaki dawo ne salin alin ba wanda ya sani".
Na daga kai.
Ya ce "baki zaki bu'de ki yi magana Malama".
A sanyaye na ce "Na amince".
Hakan da muka yi ya saka ya sauko ya zauna a gefen gadon yana cewa "Na nuno masa fuskar yarinya mai karambani ta je ta kwaso Sakina sarkin kazallaha.
Ina murna na gyara masa ita yadda zai ganta sosai. Ya dinga yi mata pics a wayarsa. Na ce me za'a dinga ce mata ne?"
Ya ri'ke baki ya ce "ke Guduyo ki bari iyayenta su zaba mata mana, tunda dai ke kika haife ta ai magana ta kare. Yi kara ga iyayenta su zabi kowanne inkiya su fa'da mata."
Na ce "To".
Ina mamakin al'amarin Gudale.
Yanzu ya gama fa'din ba zai bi ra'ayin Abba akan sunan yarinyar ba, amma kuma ya ce a bar su Sakina su zabi Nick name din da ya yi musu. Gudale sai Allah.
Amma na fahimci yadda Abba yake yi akan lamarina ne yake matu'kar sosa masa rai.
Muna hakan Umman Danladi Nasidi da likita suka shigo, dama ganinsa ya sanya ta fice, ganin shiru ya yi yawa ta shigo da taga likita zai shigo.
Cikin ikon Ubangiji sai kawai ya bani sallamah.
Bai fa'dawa kowa ba! Ya kammala komai ya debo mu da kansa ya kai ni har dakin Mama.
Farin-cikin Mama ya kasa boyuwa ta dinga yi masa godiya, yayin da shi kuna ya maze babu yabo babu fallasa.
Da daddare Abba da kansa har falon Baban Yara ya dinga mini nasiha cikin rarrashi da nuna kulawa.
Ya dubi Baba ya ce "D'an ka dai ya same ni gar da gar ya ce sunan yarinya Hafsatu, yadda na yiwa Yayar Kwalli takwara da Antinsu ta Zaria shima haaka zai yi sunan Yayar tasu zai saka."
Dariya saosai Baba ya yi ya ce "Sadik manya! Àllah dai ya kara shirya mana su".
Washagari Antin Zaria ta iso. Da yamma kuwa ta fita ta jibgo siyayyar tamkar wanda a bishiya ta tsinko ku'din.
Kaya masu koluluwar daraja ta narkowa yarinya, har da drower. Komai na siyayyar nan mother care ne, hatta setin robobin wanka. Abin koyon zama, na koyon tafiya, keken Yara, har da su lilo.
Ga sarkar gold.
Ni kuwa super da asalin leshi mai tsada bibbyu.
Banda Wanda ta bayar a mini dinkin fitar suna.
Dake Ina da kwararriyar tela a hannu sai ban damu da mishkilar da tela zai iya bayar wa ba.
*Umm Muhd collections* kenan hazikar tela kuma shahararriyar yar kasuwa.kuma mai hada kayan haihuwa da na lefe. *08063358662*.

Kwanaki uku masu zuwa za'a yi taron suna kamar yadda Antin Zaria ta shirya.
An kara kwana biyu kenan. Hidima saosai Anti Zaria ta yi, domin taron sunan mai sunanta yafi kama da bikin Yar gata, domin kaza gida hudu ake raba ta.
Harabar gate din gidan aka shirya aka kawata dake a lokacin ba'a fara kama hall dan yin taron suna ba.
Alherin da na samu sanadin wannan yarinyar sai da na sayi fili a hannun kwararrun masu hadahadar gidaje da filaye *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS.*
*08083909947*.
Sai da Yaya Al'amin ya ga filin ya yadda, ya kuma gamsu da siye da siyarwar *AMYAS* din domin idan ka siyi gida ko fili a hannunsu ba ruwanki da zullumi ko fargaba sabanin wasu da zasu samu filin wani su siyarwa wani, kai Allah ya shirya mana dabi'u kawai.
An ci, an sha an gyatse. Hatta Umma da tun case din 'kodar nan bata sake budi baki ta mini magana ba. Ko gaisheta na Yi matu'kar ba akan idon Abba ne ba, ba zata amsa ba.
Amma sai da ta yi kwalliyar kece raini a taron sunan Hafsat.
Antin Zaria da kanta ta saka mata *Amnah*
Yayin da Sakina ta ce *Ablah* zau kira ta.
Dan haka kowa yana fa'da mata wanda ya so.
Kullum safiya ana yiwa yarinyar wanka Umma zata aiko mai aikinta ta dauke ta ba za'a dawo da ita ba sai azahar, domin goya ta take yi, abin da ba'a taba ganin ta yi ba goyon jiko ki.

*Ummma*
Tana goye da Amna ta lullube ta da shawul din ta.
Zaune take a falon ta ita ka'dai tana cin dumamen tuwo.
Gudale ya shigo da sallamah. Kusa da ita sosai ya zauna, ya kalle ta ya ce "Umma ba kya gajiya da goyon wannan yarinyar ne? Kada tasa miki ciwon baya fa".
Ta

35 / 61