Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
ta fita da su Amnah gidan kawarta Anty Sa'adan Mk.
Suna ta shirin auren Junaid dinta.
Muka zube a gabanta muna gaisuwa.
Karon farko da ta amsa gaisuwa ta babu izgili, ko fishi a ciki.
Abida ta mike sabe da Aman a kafadarta ta yi cikin daki, a dalilin bata ganin fuska a wajensa.
Gudale ya numfasa ya ce "Ga mu a gabanki, muna neman afuwarki da albarkarki".
Na yi shiru ina mamakinsa, ai fa'da mini abin da zamu je yi ba kenan.
Ta numfasa ta ce "Na yafe muku! Sai dai zan ja kunnenku ko bayan raina kuka nuna wa Yayarku iko akan yaranku data ri'ke su Wallahi ba zaku ga da kyau ba. Y'ay'anku ne tabbas amma tunda ta ce zata ri'ke su to kuwa sun zama nata, zasu zauna a wajenta har zuwa sadda Ubangiji ya so. Idan kuwa ita ta dawo muku da su dan ra'din kanta shikenan, amma a bangarenku duk wanda ya yi magana tabbas ya nemi yin rikici da ni ne."
Ta yi shiru! Can kuma murya ba amo ta ce
"Allah ya muku albarka ya baku ha'kurin zama".
Na saci kallon Gudale na ga wani irin farin ciki ya mamaye shi.
Ya dinga fa'din "Mun gode sosai Ummah! Za'a kiyaye, Àllah ya k'ara miki lafiya da nisan kwana mai albarka".
Ta amsa da "Amin".
Nima dole na daure na hau godiya da yi mata addu'ar gama wa lafiyar.
Muka mike Umma ta bude murya tana kiran Abida ta kawo Aman mu tafi da shi ya ji dumina.
Nan da nan Gudale ya ce "Bar shi Ummah! Sai jibi ya zo, bata jin da'di".
Muna tafe na ce "Me yasa baka karbo shi ba?"
Kai-tsaye ya ce "Bana son a takura mini a wananan daren.
Gobe asabar zan yi barci sosai da safe. Sannan na sani barina zaki yi da shi".
Na yi shiru. A daddafe muka ci abinci, duk inda na saka kafata nan yake mayar wa.
Ya ajiye dukkan girman kansa, ya zama tamkar bafade.
Cewa yake yi "ki kwantar da hankalinki na miki al'kawarin Afrah zata dawo gabanki. Ai ban kyautar miki da ita ba. Amnah kawai na bata."
Na kame bakina na ce "Amma dai ban ce komai ba. Ka ji dai kuma abin da Umma ta fa'da".
Ya ce "na ji! Amma nan da wani lokaci ka'dan zan dawo da ita, yanzu dai na ha'kura saboda nasan akan ki laifin zai juye. Anti kuma mai fahimta ce. Baki da baki na fa'da mata Amnah kawai na bata, ita kuma ta ce Afrah ta raka ta kafin ta warware ta saba, dan haka duk zan tuna mata".
Na ce "Bar ta kawai Anti ta wuce komai ai, ina laifin wanda ya so jininka?"
Ya ce "kinsan Allah sai an dawo mini da ita, ai na sani k'arfin hali kike gwada wa na kuma gode miki. Ba kuma kowa ya ha'da wannan kitumurmurar ba sai Sakina.
Ita ce a karambana ta zakalkale sai an tafi da Afrah dan kawai ta raba ni da komai ita ala dole sai na ki'dime na gigice. Tabbas sakonta ya buge ni, rashinku a tare da ni ya fahimtar da ni al'amura masu girma, ya saka na gane kune farin-cikina.
Sai dai kuma bata san cewar Afrah ita ce mowar y'ay'a a wajen ki ba. Ta yadda rashinta a kusa da ke zai shafi farin cikinki".
Da sauri na ce "Ba haka bane Yaya Gudale! Dukkansu daya ne a wajena, dan Allah kada ka fa'di hakan a gaban wasu, bana son a fahimci ko a zaci hakane zata yi ba'kin jini a tsakanin yan'uwanta. Shaidan baya raina kofar da zai shiga ya haddasa fitina da kyashi a tsakanin yan'uwantaka."
Jikinsa ya yi sanyi ya ru'ko ni yana fa'din madallah da ke Guduyo! Kin fahimtar da ni abin da ban fahimta ba, a duk tsawon lokacin nan."
Ya yi shiru zuciyarsa na ayyana masa ba dan Ubangiji ya cika zuciyar y'ay'a mata da alheri da tausayi ba, da tuni sun jefi shi a dalilin matsanancin banbancin da gyatumarsu take nuna wa a fili muraran a tsakaninsa da su.
Ba dan addu'ar mahaifinsu ba da tuni ya zama tuburan tsabar gatan da ya taso a cikinsa na babu kyara ko kwaba. Komai yake so haka Umma take masa ko da kuwa ya ci karo da ra'ayinta. A kullum bata da ra'ayin kanta sai nasa.
Ya tuno duk shawarar da zata yi da su Antin Zaria da ya zo ta zayyana masa. Matu'kar ya ce ba hakan za'a yi ba. Ba nauyi ba kunya zata bisu daya bayan daya a waya tana fa'da musu ta rushe waccar maganar. Ga sabuwar matsayarta. Ba kuma yadda zasu yi, dole ayi hakan.
Ya tuna komai zasu bata matu'kar basu hado da wani abu nasa ba, baza su ga ta yi zumudi ko murna ba. A karshe ma sai dai ta bashi gaba'daya tana fa'din shi ya dauka. Ko Kuma ta ce "Mai son farin cikinta to ya faranta wa Gudale.
Ya nisa ya tuna matsayi da shekarun Anti Zaria. Amma matu'kar a gaban Umma ne to bata ganinsu. Cewa take yi duk girman mace ai namiji ne jagoranta, Ubangiji ma bai daidaita tunanin namiji dana mace ba, sannan kuma namiji ne jagora a ko'ina.
Karon farko da jikin Gudale ya yi sanyi, tausayin kansa, tausayin uwarsa da na sisters dinsa ya masa wani irin dirar ba zata.
Ya tuna yadda Abba ya wanzu yana fa'dan illar banbanci da take nuna wa a zahiri babu fargaba babu damuwa.
Ya sake tuno kalaman Abba a duk sadda ya ga tana wannan mummunar dabi'ar.
Cewa yake yi "Àllah kada wannan ta'adar ya lalata al'amuran Sadik gaba'daya. Allah kada ka barshi da dabararsa. Ina kuma rokar masa a cika zuciyar yan'uwansa da soyayyarsa, a tsare mini zumuncinsu daga rudanin shaidan da hassada".
Ya sauke ajiyar zuciya ya na gasgata addu'oin Abba ne kawai suka yi tasiri a kansa da yan'uwansa. Banda hakan da ya sani gaba ce mai tsananin gaske zata biyo baya. Domin har yau a fili Umma take sake nuna wa su Amnah sun fi y'ay'an su Sakina. Komai zata yi musu sai ta banbanta, bata kuma jin nauyin fa'din su din sune yan gida, su take da iko da su, sune zasu yi amfani da sunan Abba.
A fili ya ce "Allah na tuba! Allah ka yafe mini, ka yafe wa Ummana, ka jikan Abba".
Ya jima cikin sanyin jiki kafin ya kalle ni ya ce "Ina son ki Guddin Abba. Ina jin takaicin da har ya mutu ban tsugunna a gabansa na yi masa godiyar gatan da ya yi mini na bani aurenki ba. "
Ya ru'ko hannuna sosai ya ce "Ina sake yi mana ta'aaziya Guduyo. Àllah ya jikansa. Kada kuma mu manta ba abin da yake so irin aurenmu ya wanzu muddin rai. Ki yi ha'kuri. Na yi kuskure kan kuskure. Amma zan kiyaye a gaba da dukkan iyawata. Ina sake miki al'kawarin ko y'ay'a mata goma zaki haifa mini a jere ina so, zan karbesu da farin ciki da godiya, zan kuma yi adalci a tsakaninsu.
Zan dai-daita su da Aman! Allah ya shirya mana su gaba'daya".
Na kalle shi, shima ya zuba mini ido, tsawon lokaci muna kallon juna cikin shauki da begen da ban yi zaton zan ji shi a kusa kusan nan akansa ba.
Tsigar jikina har wani tashi take yi a dalilin kallon da yake mini girman al'amarin da ya kunsa ya kai kurewa.
Daga haka ya mikar da ni, ya juya yana cewa "Hau na goya ki, na huta gorin ban ta'ba goyon ki ba."
Na kuwa d'age rigata na d'ale shi.
Ga mamakina bai durkushe ba, sai ma zunkuda ni da ya yi ta yadda na hau sosai. Ya dinga zagaya falon da ni. Na dinga mamakin karfin da Ubangiji ya bawa namiji, duk zatona ba zai iya saba ni a baya ba shiyasa yak'i ko da gwada wa ashe ba hakan bane.
Na tabbatar ni kuma ban isa na goye shi na yi tafiya sak hakan ba, duk da bashi da wani girma.
Na sake girmama lamarin Ubangiji.
Mun jima a hakan na yi luf.
Ya fara nishi ya ce "To sauko haka, gobe ma zan sake goya ki."
Ai kuwa na ce "Ata fau ban san zance ba, sai ya hau sama da ni".
Ya shige dakinsa da ni, yana fa'din "Wannan ne kuma ba zan iya ba, ina laifin wannan din da na yi, wato na hau sama da ke cinyoyina su rike na kasa katabus ko?"
Kunya ta kama ni bayan ya wurgo ni kan gado ya biyo ni ya d'ora mini nauyinsa, sai numfarfashi yake yi.
Na cuna baki na ce "Kawai dai sona da yake k'irjinka ne bai yi k'arfin da zaka mini hakan ba. Ban da haka menene a hawa saman? Ai na dauka ko Sallari na ce ka kai ni gidan Maman Nana zaka saba ni ka tafi babu musu".
Ya galla mini harara bayan ya cire rigarsa ya ce "A a k'walli zan kai ki gidan Yaya. Ke ki raba kanki da soyayyar novel. da kallon Korean firms, to suma duk k'arya ne, zama ake a shirya yadda za'a yi. Amma ku sai ku ta yin hasashen hakan za'a dinga yi muku. Tun farko na fa'da miki hakan ba zai faru ba sai a aljannah.
Yanzu kuwa tunda duk mintinan da kika shafe a bayana baki gode ba, baki yaba ba, to goben ma ba zan goye ki ba. Haba ku tausaya ku dinga gode wa kokarinmu. Mazan novel din nan fa babu su. Kema da a novel ne ba za ki zo a mai jiki ba, ba zan zama ina da cikakken iko akan ki ba. Da kin yi fishi shikenan zan bar ra'ayina na gaskiya na dawo na ki ra'ayin na son rai, komai zai tsaya mini ne cak har sai na ga murmushinki. Kai Allah dai ya shiryi mazan novels ragwaye ne na karshe.
Gudalen Umma kuwa namiji ne da yake tsaye akan kafafunsa. Ina son ki amma ba zan yarda da iyashege ba. Kawai abin da yake damuna har nake ganin ina kama da mijin novel, idan na shigo gida ban ganki ba. To anan kam bani da jarumta, tun kafin na aure ki ma. Na bar hakan kuma a tasirin jini kawai."
Karon farko tunda na dawo gidan na kyal-kyale da dariya har cikin zuciyata.
Yayin da ya nufi bandaki yana fa'din "Ato ai gaskiya ne. Nima da a novel ne a wani ingarman namiji zan zo, mai k'irar zaki, miskili, yan mata na ta cuso kansu ina yarfa su. Ku'di kuwa ba zai zame mini matsala ba. Amma da ke a duniya mai cike da kalubale nake rayuwa ai kina ga ni dai kafin na karbi kudi mai auki sai karshen wata, idan kuwa ba hakan ba sai na sha tambayar ba'asin me zan yi da su a wajen Yaya Abdallah"
Ya shige ya bar ni ina sake fashewa da dariya.
Har Cikin zuciyata na ji ya wanke kaso mai yawa na bakinsa da nake ga ni.
Nima dakina na nufa na shiga wanka.
Wanka na yi sosai da kayan oriflame.
Ga famewash na mussaman, ba abin da yake burgeni da shi irin yadda ko pant na saka sai ya yi kamshin famewash din nan.
Bare kuma da Aisha ta sake nuna mini spray dinsa. Mussaman idan kika gama period kika yi amfani da shi a kasanki kin huce takaici, da kalubalen infections.
Shiri na mussaman na yi.
Na fito, na shirya bayan na dauko ledar kayan GHT na ha'diya. Kai nikam na dace da jakadun da suka san kayayyaki masu daraja. Gashi dai tunda Yaya Gudale ya fara shan maganin ulcer din GHT shikenan, haka supplement din GHT na basir ne ya warkar da mijin Sakina. Bare kuma ni da nake hadiyar na gyara mutuntakar mace, na tabbatar kayanta original ne.
Madallah da jakadun kwarai.
Kafin wani lokaci na dauki sheki duk da ko powder ban shafa ba.
Na saka rigar barcina.
Da kaina na tabbatar mun yi kewar juna, wannan ne karon farko da muka shafe watanni masu yawa ba'a hadu ba.
Wata uku har da kwanaki.
Sai kuma na kasa koma wa dakinsa.
Kunya ta rufar mini tamkar sabon aure.
Kwatsam sai jinsa na yi yana bude gate, ban gama mamakin inda zashi ba, na ji ya ja mota ya fice.
Na kalli agogo na ga goma saura.
A fili na furta "Ashe daren bai yi sosai ba."
Bai wani jima ba, ya dawo, a falo ya yi burki ya dinga k'wada mini kira.
Na fito bayan na sanya hijabi.
Ya kalle ni ya watsar ya ce "Dauko plate".
Na dauko na kawo masa.
"Juye mana Guduyo, ya zaki ajiye mini ba tare da kin duba ledar ba, ashe ban hana na shigo da leda amma ki bar ta inda na ajiye ba?"
Na ce "Allah ya baka ha'kuri". Tare da jan ledar ina bud'e wa.
Gashasshiyyar koda ce da yougurt.
Na juye a plate din.
Na zauna. Ya kalle ni ya ce "Na ro'ke ki kada ki b'ata mini rai. Ina fork din dan Allah?"
Na tashi na nufi kicin ina mamakin Yaya Gudale.
Na kwaso na dawo. Ya karbi nasa ya fara ci, ba tare da na saka hannu ba.
Ya kalle ni ya ce "Na fa roki kada ki b'ata mini rai?"
Na zum'bura baki na ce "To ka ce na zo na ci ne?"
Ya zuba mini ido, sai kuma murmushi ya kwace masa ya ce "To sauko na baki a baki ma. Duk jaye jayen fadanki, yau kam ba zan biye ki ba.
Addu'a kawai nake ta yiwa Abba da ya bani ke, babu zancen na biye wa kuruciyarki mu yi fada."
Na kafe shi da ido na ce "Hmm kai dai Yaya Gudale dila ma nan ta barka da wayo, shirya zance kuwa ko mace sai an tona wadda zata kai ka iya sarafa harshe da lauyewa.
Komai yanzu zaka ce na rarrashi, gari na wayewa kuma zaka fara muzarai kana fa'din kai namiji ba za'a raina ka ba".
Ya yi murmushi ka'dan ya ce "To ba namijin bane?"
Na sake zum'bura baki tare da cewa"Namiji ai baya ja da baya a fagen daga, mu yi fa'dan kawai".
Ya girgiza kai ya ce "Akan me zan yi fada da ke?
Haram ba'idan! Jarumta ta akan namiji ne, amma ban da ke mace halitta mai rauni, kuma halittar da nake tsananin so. Ni da kika gan ni ba abin da nake so daga gare ki irin total submission. Ki yarda da Allah da manzonsa ki yarda da ni.
Na canja, zan kuma tabbatar miki na canja din.
Matso kusa da ni na dinga ba ki a baki kamar yadda kike ga ni darakta na bawa sharukhn umarni ya bawa kajol abu a baki".
Akan dole sai da na yi dariya, a bakin kuma ya bani.
Yana gama wa ya ce "Ba ki ce mini Thank you my love ba".
Na fashe da dariya ya ce "A to kema gara na fara nuna miki yadda matan novel din suke yi."
Daga haka ya jani daki, rawar jiki, sumbatu, kusan koma wa ya yi yana yin abubuwa out of control.
Tausayinsa ya kama ni, domin Ni shaida ce shi din mabukaci ne na gaske, sannan kuma bai yarda da wayewar neman matan banza ba.
Wannan daren na cikin jerin dararen da ba zasu gogu a tarihin aurenmu ba.
Ba abin da bai fa'da mini na soyayya ba.
Ba irin rawar jikin da bai yi mini ba.
Ba kalar styles din da bai yi ba, kalmar ina son ki kuwa ya fa'da tamkar an goranta masa.
Ha'kuri ya bani ya fi cikin carbi, al'kawarin ba zai sake duka ko zagina ba, ya yi su uncountable.
Da kaina na gamsu son da yake mini yafi karfin kwatance. Ya sake jaddada mini Allah ya halatta masa mata uku bayan ni, amma shi ya haramtawa kansa. Na ishe shi rayuwa, zai dauwama yana rokon Ubangiji ya kaddara ya cika wannan al'kawarin.
Amma kada hakan ya saka na yi wasa da al'amarimsa, ko na nemi takure shi, domin yana da hanyoyin da zai bai ya ladabtar da ni, ai na riga da nasan baya barin ta kwana.
Na kiyaye bata masa rai da gangan ko bijiro da wani alamarin da zai kawo mana rud'ani.
Ya sake rokon na k'ara ha'kuri da shi, na kara girmama Umma idan na yi masa hakan shi kuma zai dauwama yana yi mini sassauci.
Har tsakiyar dare idonmu biyu.
Jikina ya yi ligi ligi tsabar gurzar da na sha.
A karse sai muka koma hawayen rashin Abba a dalilin maganganunsa da Gudale yake ta bitarsu.
Fad'i yake Abba ya ce "Idan na cuce ki, ba zan ga da kyau ba. Abba yana son mu rayu tare. Abba ya ce kaza, Abba ya ce kaza.
Karshe dai sai muka yi wanka muka hau nafila domin nema wa Abba gafarar Allah".
Sai da muka yi sallah asuba sannan muka kwanta.
Gudale na dawowa daga masallaci ya kankame ni muka yi kwanciyarmu.
Barci sosai muka yi domin sai shabiyu muka farka.
A daddafe muka karya.
Sannan ya wuce masallaci.
Yana dawowa ya shiga wanka.
Ni kam sai da na yi wanka na shirya sannan na tada Sallah.
Ban kai ga idarwa ba, ya shigo ya shyrya tsab da shi.
Ya zauna bakin gado ya jira na idar ya kalle ni ya ce "Zan fita, zamu je gidan Yaya da Baban Yara, jiya bamu samu zuwa ba."
Na kashe masa ido na ce "Adawo lafiya. Amma dai kada ka fitar mini da motata"
Ya mi'ke ya na cewa "Wallahi ki cire hankalinki akan motar nan dan kuwa ba zan baki ba, na fasa fas".
Na shagwabe fuska na ce "Amma..
Ya katseni da cewa "Maganin irinku da basa karbar rarrashi da wuri kenan. A lokacin da kin yarda Wallahi bar miki zan yi, idan ya so na tisa Yaya Abdallah a gaba sai an siyo mini wata.
Amma tunda baki yarda a lokacin ba. Na fasa, ki dai yi addu'ar na samu na siya miki bangles din suna ba ni sha'awa sosai."
Na sake kwakkabe fuska na ce "Kai Sweat heart".
Ya kwashe da dariya Yana cewa "An marairaice murya za'a yiwa Gudale wayo. Allah dai ya yafe miki Guduyo. Adana wannan shagwabar sai mun je oza room zan kar'ba".
Ya fice yana cewa "yau na zama sweating Guduyo! Allah ka jiqan Abba. Da yana nan ruga wa zan yi na fa'da masa sabon sunan da na samu."
Na murmusa na ce "Abba ai ya san ina son ka! Ya sani sosai".
Ya dawo ya rungume ni yana fa'din "Hakane! Na gode miki. Nima kuma na tabbatar masa Ina son ki tunda na nuna masa zan iya siyar da komai nawa dan na tsira da ke".
Na kyal-kyale da dariya na ce