Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 61

12K to 15K   out of 180.1K words

na dinga zirga-zirga a gabansa, da zarar na ga Ya Al'amin ya fita to kuwa zan zari jiki na je dakin da zummar kai abinci ko yi musu shara.
Tun a lokacin na fahimci irin yadda Yaya Sadik yake shagala da kallon kirjina, cikin dabara kuma zai dan shafe ni, ko ya zaunar da ni kusa da shi, ta yadda jikinmu zai dinga gogayya, ya biye mini ina ba shi labarai marasa kan gado.
Wani lokacin tafin hannunmu yake hadewa ya dinga murzawa cikin wani irin yanayin da ban fahimta ba, ko kuma sai ya kunna mini waka wai na yi rawa ya gani ko na iya, shi yana son wacce ta iya rawa, haka zan dage na yi ta karairaya don kawai na burge shi.
Kafin na gama zan ga yana ta faman matse cinyoyinsa, idonsa kuma ya canja, a haka har Al'amin ya fahimci barnar da take neman samun muhalli a cikin gidanmu. Sai ya fara hana ni zuwan, ni kuma sai na kwashe na fa'dawa Ya Sadik, sai da Mama ta sani a daki ta mini duka, ta hana ni kuka, sannan ta hana ni zuwan.
Na nisa na ce, "Watau Yaya Sadik ya dauka har yau din nan kallon rashin hankali yake mini, anya kuwa ba ya afa 'kwaya? Ban da haka mene ne zai sa ya ce na yi rawa a gabansa a cikin falon gidanmu a gaban iyayenmu?"
Na muskuta na sani har yanzu da nake shirin kammala sakandire ina jin son sa a raina, matu'kar kuma zan hararo mijina to babu shakka Gudale ne yake zuwa mini, sai dai ina cike da fargabar yadda ya ke kushe ni, yake ganin tamkar ban kai na shiga cikin zaratan mata na kece raini ba.
Na mike na isa gaban madubi, na kalli kaina, kallo irin na tsanaki, duk da dai ban isa na jefa kaina cikin jerin matan da kyaunsu ya kai ya kawo ba, to amma kuma ba ni da makusa, musaman da na yi sa'a ina da tsayi, sannan fara ce ni tas, ga gashi sannan ga idanuwa, bayan haka ga dimples, tabbas ina da jiki, ta yadda k'irjina a cike suke dam, sannan daga kwankwasona ina da fa'di, wato dai a wannan lokacin da nake cikin shekarun budurci jikina yana da matu'kar daukar hankali duk kuwa da 'kibata.
Na yi jim ina tunanin dalilin da yasa har yau 'din nan Gudale bai daina 'kure ni da kallo ba, musamman dai 'kirjina, shin shi ma ya fara son nawa ne ko kuwa sha'awa ce kawai tunda a yanzu na fara fahimtar so da kuma sha'awa.
Ban fito daga dakin nan ba sai da na tabbatar ya fita, sannan na je na ci gaba da harha'da kayana.

Washegari na shirya tafiya gidan uwar dakina Anti Sakina da har yau 'din wani iri zumunci muke yi ni da ita, sanin kowa ne, Sakina ta daukake ni fiye da su Ramla, balle kuma Sadik da ba wani shiri suke yi ba, ko da yake shi kam da wa yake shiri ne? Gara ma da Ya Al'amin shi ma a hakan don Al'amin 'din ba mai son hayaniya ba ne, da kullum sai an raba su, saboda wuyar zamansa.
Na isa na tarar da ita a hadadden falonta tana yiwa yarta Nana kitso, tana manna mata sabulu a karshen jelar a dalilin tsantsin gashin Sakina ta 'debo.
"Oyoyo Autarmu, zancenki nake yi yanzu ina cewa bari na zo na yi miki wainar fulawa na kai miki gida, ko kin dawo da gajiya."
Na yi murmushi na zauna ina cewa, "Kullum cikin canja kaya kike, yanzu har kin sake gyara falon nan?"
Ta murmusa ta ce, "To mene ne jin da'din duniyar, idan kana da hali ka more rayuwarka, ta hanyar cin abin da kake so, da kuma mallakar abin da ya ba ka sha'awa, ka yi kyauta, ka kyautata zumunci, ka yi sadaka, shike nan fa, da ka mutu taka ta 'kare".
Na ce, "Haka ne!" ne da iyakacin gaskiyata.
Domin na shaida hakan Sakina take mai kyale-kyale ce, musamman da mijinta ya kasance mai wadata, bayan hakan kuma ma'aikaciyar lafiya ce. Tana da yawan alheri tamkar mahaifinta Abba! Sannan ma'abociyar sadaka da kyautata zumunci ce, duk kayan kwalliya da dogayen riguna na mafi yawa ita ke saya mini, ita take saya mini mayukan da suke gyara mini fata, haka nan inner wears dina asalin designers take saya mini a cewarta su ne suka fi dacewa da ni ta yadda za su kama mini jiki sosai.
Ta kalle ni da sakakkiyar fuska ta ce "Allah dai ya sa ki samu gatan da na samu, ki fara karatu kafin Abba ya bijiro da maganar aure, sai a yi ta miki kallon girma saboda yanayin jikinki".
Na mike na yi kicin ina fadin "Ai ni sai na kammala degree kafin na yi aure duka-duka fa ko sha bakwai ban yi ba".
Ta ce, "Allah ya sa dattijon namu ya yarda, ki ga ni ma fa da yadda aka yi na karatun, Abba ya daukaki aure, Baba ne ba ruwansa duk yadda ta fàdi sha ne, sai dai, shi ba ya cikin kwamitin zartarwa".
Na isa kicin ina dariyar Sakina wai baya cikin kwamitin zartarwa, tamkar da wasu mahukuntar wata ma'aikatar take. Na dawo d'auke da ruwa da lemo na zauna ina cewa, "Su waye yan kwamitin zartarwar?"
"Yaya da Abba mana!"
Ta amsa mini a ta'kaice.
Kafin na yi sallama sai ga Yaya Sadik ya shigo, ya yi sallama a 'kasan ma'koshi.
Ya zauna yana karkada 'kafa 'daya kan 'daya
"Na Moriki yau kuma abin ba ko sallama?"
Sakina ta fa'da cikin kwantar da murya.
Ya bu'de idonsa tamkar wadda ya tashi a barci ya ce, "Na yi fa, ba ki ji ba ne, ke kin ji?"
Ya mini tambayar yana dawo da idonsa gare ni.
Na girgiza kai ina cewa "Gaskiya Yaya Gudale ba ka yi ba."
"To ban yi 'din ba 'katuwar banza marar tsoron Ubangiji."






# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*


```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?


*Fatan alheri ga marubuciya*
*JAMILA JANAFTY*
*BA WACCE TA KAI KI SON LABARIN SABO DA KAZA BALLE TA FIKI*
*DAN HAKA GUDUYO NA MIKI SON SO FISABIDILLAHI*.






Page 5&6.


Sakina ta zuba masa ido tana hasashen 'kanin nata, tana son tuno yaushe rabon da ta gan shi a gidanta, ta kasa tuna when last da ya zo mata. Kaso mafi yawa ta fi zaton so na yake yi, sai dai rashin alkiblarsa ya sa ba za ta yi saurin gaskatawa ba. Amma a ranta addu'a ta shiga yi, Allah ya sa hakan ta kasance domin ta riga da ta fahimci ina son shi, da zarar ya furta da gudu zan amince, duk kuwa da rashin mutuncinsa.
Ya katse tunanin Sakina da cewa, "Yanzu saboda Allah ruwa sai na ro'ka?"
Na tashi ina cewa, "Bari a kawo maka Yaya Sadik!"
Na dawo dauke da robar ruwa ta sona mai sanyi na ajiye masa ha'di da tumbler.
A lalace ya kalle ni ya ce, "Ke kam ina tausayin mijinki wallahi wanda zai kwashe ki abin a yi masa jaje ne, kin wani taho sankamkam tamkar ra'kuma".
Ba'kin cikin kalmar rakumar da ya jingina mini yasa na zauna a sanyaye, hawaye kuma ya kwace mini, abin mamaki sai ya jikinsa ya yi laushi, ina kallon yadda Sakina ta tsananta kallon mu musamman Yaya Sadik.
Tsawon lokaci ina shar'be Sakina ta 'ki yin magana, ya ja tsaki ya ce, "Ki dubi Allah Sakina! Me na yi mata da za ta dinga yin irin wannan kukan?"
Ta nisa ta ce, "Ta yi maka abin arziki, kai kuma ka zage ta?"
"Sakina ban son 'karya! Gidan uwar wa na zage ta?"
Kai tsaye ta ce, "Gidan uwarka".
Ya yi kanta tamkar zai dake ta, ko gezau ba ta yi ba. Ya tsaya yana nuna mata yatsa cikin fishi ya ce, "Kar ki yi zaton don na zo gidanki shi ne za ki zage ni, ki kwashe 'kalau".
Uffan ba ta ce masa ba, ta ci gaba da yi wa 'yarta kitso da take ta barci.
Share shi da ta yi, yasa ya koma ya zauna.
Cikin kara'di ya ce, "Guduyo kin sani ban son irin wannan iskancin, ta ya ya ke da kike yar lukuta da ya kamata ki nisanci za'ki, kin 'dauko lemo kina sha, ni kuma sai ki ba ni tsurar ruwa. Ban da rowa mene ne hakan? Na yi magana kin saka mini kuka, har wannan tana neman 'kulla munafuncin na zage ki, me na ce da yake nufin na zage ki?"
A tunzure Sakina ta ce na fuskanci a tsiyace ka zo , sai dai kar ka shiga ru'du ba gidanku na je ba, bare ka tisa ni a gaba da cin mutunci, nan gidana ne don haka ka iya harshenka".
Ya mi'ke yana cewa, "Idan ni 'dan halak ne a cikin Habu da Saude, ba za ki kuma gani na a gidanki ba, da'din abin namu gidan ba kango ko kufai ba ne".
Ya kalle ni ya ce, "Zo mu wuce na rage miki hanya".
Na galla masa harara na ce "Ina ce ba kai ka kawo ni ba?"
Ya wuce yana cewa, "Me za a yi da shiga lamarin mata, daga wacce za ta yi maka sharri, sai wacce idan ka fa'di ainihin yadda take za ta ce ka ci fuskarta, yo mene ne don na ce miki ra'kuma? Alhalin dangantakar danjuma da 'danjummai ne a tsakaninki da ita."
Muka bi shi da ido domin lamarin nasa tamkar a buge yake musamman yadda idaonsa suke tamkar mai jin barci ko wanda ya tashi a barcin.
Sakina ta kalle ni ta ce, "Iyashegensa kullum 'kara tsananta yake yi, amma ba komai ba za mu gaza da yi masa addu'a ba har Ubangiji ya amsa mana".
Na yi shiru ina jin tausayin Sakina saboda yadda take cikin bacin rai, a dalilin ba 'karamin so take yi wa 'dan uwan nata ba, amma shi ko ka'dan ba ya mata ragayya har gara ita ma a hakan a kan manyan yayun nasu.
Bai zame masa abin kaico ya ci mutunci duk wacce ta nemi yi masa fa'da irin na gyara kayanka ba. Yana isa gida kai tsaye shashinsu ya nufa, ya samu Abba a falonsa. Ya shiga ya zauna, ya gaishe da mahaifin nasa ba sukuni a tare da shi.
Ya amsa cikin kulawa.
Ya numfasa ya ce, "Abba so nake na ji me ake ciki a kan tafiyar tawa".
Abba ya ce, "Ba za ka je waje ba, idan karatun kake so ka nema a nan k'asar."
Ransa ya kai 'kololuwar baci ya ce, "Abba wai ni kam ba ni da hakki a dukiyarka ne?"
Abba ya harzuka ya ce, "Ilimin da na yi bai yi zurfin da zan gane kana da hakkin ko ba ka da shi ba, sai dai ka fahimtar da ni yanzu. Daga haihuwarka zuwa yau adadin dukiyata nawa ka lashe mini? Amma ban tsira daga ba'kin cikinka ba, shin ba ni da hakkin ka mini biyayya ne?"
Sosai ya sake daure fuska ya ce, "Tsakanina da Allah Abba na fahimci ba ka ta tawa, a kullum adawa kake da duk wani 'kudirin da zan zo gabanka da shi da zummar ka lamince mini."
"Akan me zan yi ta taka Sadik? Har yau din nan fa ban huta da yi maka hidima ba, amma ba ka gane irin kyautatawar da nake yi maka ba, yau kwana nawa ina cewa ka je ka rage wannan sumar da ka tara?
Dubi wani irin gemun rashin mutunci da ka ajiye! Tamkar wani 'dan akuya".

"Abba Sunnah ne fa!"
Ya fa'da cike da iyashege.
Ya masa da'kuwa ya ce, "Ungo naka! Wannan kam gemun raini ne ba na Sunna ba, ba za ka ji da'dina ba har sai ka yarda da ra'ayina ko da ba a ra'ayin ka ba ne, in ko ka ci gaba da yin fito na fito da ni, ni kuwa ba zan fasa nuna maka cewar ka zo duniyar nan ka same ni ne a cikin shekarun girmana, ma'ana ko da ban same ka ba, ba abin da zai shafi ni'imomin da Ubangiji ya yi mini. Uwarka ta cusa maka ra'ayin iska wai Gudale, to ina tabbatar maka a wajenta kake Gudale domin ba a kanka na samu haihuwar namiji ba, tuni da ma Ubangiji ya ba ni su da yawa, Ga su Abdallah, ga Ashir ban ta'ba kallon ka fisu ba, don haka ka ri'ke wannan".
Takaici ya kama Umma da take gefe tana kallon su, haka ma Sadik din, don haka ya mike yana cewa, "A wannan era din dai babu na biyunka. Madalla da kai Abba! Mai fifita 'ya'yan dangi akan biological son d'insa, na hakura da karatun, digiri biyun da na yi ka daure ka saka mini albarka, sannan ka mini alfarmar samo mini aikin yi, domin a yau na fahimci ya kamata na fara tsayawa on my leg, domin dukiyarka ba tawa ba ce, bal ma 'ya'yan 'yan uwanka sun fi ni dama a cikinta".
Tsoro ya kama Abba! Yana kallon Sadik yana nazartar sa, anya kuwa a she'dantarsa bai fara afa 'kwaya ba? Ya sani ba 'karamin tsoron sa yake ji ba, amma a watannin nan wani zubin yana iya zama a gabansa ya fa'di duk maganar da ta zo bakinsa babu fargaba, da za a jima kuma ko washegari sai ya ga wannan shakkar sa da yake yi ta dawo, tabbas ba zai yaudari kansa ba, tilon 'dan nasa yana shan wani abu da idan yana cikin wannan yanayin zai iya keta kowa.
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!" Abba yake ta fadi yayin da Sadik ya fice da sauri.
A fili Abba ya nisa ya ce, "Allah ka kawo mini 'dauki, Allah ka shirya mini Sadik, ka sani ban ta'ba jin rashin da'di akan 'ya'ya matan da ka ba ni ba, ban taba zakuwar sai ka ba ni namiji ba, Allah ina tawasili da adalcin da na yi wa 'ya'yana mata ka shirya mini wannan yaron da kullum yake sake kangarewa".
Umma ta yi wuki-wuki da ido domin ta ji a jikinta tamkar da ita mijin nata yake.
Ta nisa ta ce, "Abban yara tsakani da Allah ya kamata ka ba shi damar tafiya karatun nan, irin haka yara suke shiga wani hali, kana da damar kai shi ko'ina a duniya, amma ka 'ki. Saboda Allah ka kai wasu ma bare shi, ai kamata ya yi mu gode masa da ya yarda ya yi karatun yake kuma son ya ci gaba".
Takaicin ta mai tsananin gaske ya kama shi, ya nuna ta da yatsa ya ce, "Ina gargadin ki ki kiyayye ni, ki bar ni na ji da ba'kin cikin sangarta yaron nan da kika yi, an 'ki gode masan, da bai yarda ya yi karatun ba, wa ya yiwa asara?
Kansa ya yiwa wallahi, domin ko ke uwarsa da arzikina kika same ni, kuma Ubangijina ya suturta ni ta yadda ba zan jira wani ya taimake ni ba. Ke dai da zuciyarki ta zarme akan sai 'da ya zo ya tallafa miki sai ki yi ta yi, da ikon Allah ni kam sai dai yaro ya mini abu don neman ya yi albarka, amma ba don ya tallafe ni ba".
Sanin da ta yi ba ya kashedi sau biyu yasa ta mike sum-sum ta bar falon.

Washegari da safe na fito daga shashen Umma inda nan nake kwana bisa umarnin Abba, domin tunda aka yi auren Sakina na gudu, a dalilin rashin samun fuska a wurin Umma, sai idan Abba yana gari.
Amma a yanzu da girma ya cim masa bai cika ma yawace-yawace ba, sai Yaya Abdallah ne ya fi yin harkokin Abban shi yasa ma ba ya aikin gwamnati, amma Babban lauya ne mai zaman kansa.
A hanyar da ta raba shashin Umma da na Mama muka yi kicibus da Yaya Sadik, na yi kamar ban gan shi ba, na wuce shi, ina ganin yadda ya tsaya ya bi ni da kallo, ba tare da ya ce mini uffan ba, na dai san ya 'kulu da dauke kan da na yi masa.
A tunzure ya isa gurin Umma, tana kicin tana saka wa masu aikinta ido kan abincin da suke yi. Ganin da ta yi masa a tunzure yasa ta fice ta ri'ke hannunsa, sai da suka shiga 'dakinta ta zaunar da shi a bakin gado sannan ta dafa kafadarsa ta sassauta murya ta ce, "Mene ne kuma na bacin rai yanzu da sassafe nan?"
A zafafe ya ce, "Wula'kanta ni da waccan 'katuwar yarinyar take yi a gidan nan ne yake mini ciwo".
Gaban Umma ya buga, ta 'kare masa kallo ta ce, "Gudale mene ne abin damuwa akan Halimatu? Na fara jin tsoro fa". Sai ta fashe da kuka sosai!
Ya ce, "Saboda Allah Umma kin so ki sake bata mini rai ne, mene ne abin kukan kuma?"
Da hawaye face-face ta ce, "Ina jin tsoron kada Safiyya ta kwace mini kai, tamkar yadda 'ya'yanta suka kwace mini Abbanku, ina jin tsoron yawan damuwa da ka yi da lamarin yarinyar nan, mene ne da har za ka dinga 'bacin rai saboda ita? Anya Gudale ba son ta kake yi ba?"
Ya mike da sauri zuciyarsa tana tsananin bugawa, bakinsa na rawa ya ce, "Wanne irin ba'kin hasashe ne wannan? Ni kike ganin zan so wannan yarinyar, to na yi yaya da ita? A yanzu haka ta fi ni girma, ta fi ni tudu to nan gaba kuma ai ban san me za ta zama ba, wallahi kin b'ata mini rai Umma! Shike nan sai ba zan yi zumunci da ita ba, ai tunda jini ya ha'da mu dole zan ji zafi idan ta gan ni ta bagarar".
Cikin kara'di ta ce, "Ban son wannan damuwar da ka yi da ita, tunda har take bagarar da kai, mene ne kai ba za ka yi watsi da dukkan lamarinta ba?"
Ya nisa ya ce, "Haka ne zan yi yadda kika ce".
Ta goge fuskarta ta ce, "Na dade da gane duk kinibibin uwarta ta kwashe su tsaf, duk namijin da tsautsayi yasa ya kwashe ta ya shige su! Domin an

5 / 61