Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
yi wanka ba? Duk yadda nake fama da ciwon cinyoyi na yun'kura na tashi ban langwabe ba.
To kinsan dai ni ba mijin novel bane bare na yi 'karfin halin sunkutar ki ko da ina nishi ne, na kai ki toilet na wanke ki sannan na na'do ki a tawul tamkar jinjira".
Dariya ya bani sosai na ce "zaka iya mana Gudale! Ina ce dai ban zan zarta nauyin dinner-set din nan da ka kinkima cak rannan?"
Ya bu'de ido ya ce "Kina nufin dan kin ga girmana har kin jingine Yayan daga yau? Gudale gatsal? Haka dazu ma kika ce wai Gudalen Umma babu sakaye".
Na gimtse dariyar ina tuna dazu da rana ya dinga gatsa sunan yayarsa, amma shi yanzu yana tuhumar an gatsa sunan sa.
Na lallaba na tashi na yo wanka, bayan na kama ruwa da ruwan zafi sosai har sai da na ji dai dai sannan na fito na ganshi akan gado yana goge inda muka bata da tissue. Kunya ta sake kama ni, na dauke kai tamkar ban gani ba. Mansa na shafa, na fesa body spray na mayar da rigata.
Na kalle shi ya yi 'dai'dai a gado, fuskarsa sai annuri take yi, da alamun gajiya a jikinsa.
Na ce "a kashe fitilar?"
A hankali ya ce "zo ki kwanta".
Ban musa ba, illah iyaka na sani ba zan iya barci ba yau, tunda bana iya barci da haske a kaina.
Da na kwanta, da kansa ya lulluba mini dubet sannan ya kashe fitilar ashe akwai makunna a kusa da jikin gadon.
Ya kwanta ina jinsa yana karanto addu'ar barci. Hakan yasa nima na ankara na fara yi, muka gama, muka shafe jikinmu.
Ya matso ya rungume ni sosai a hankali ya ce "Kin ri'ke tarbiyarki! Allah ya sanya albarka a dukkan rayuwar ki my *Halah*".
Mamaki ya kama ni ashe dai Gudale ya iya abin arziki haka? Ya jiyar da ni da'di domin irin yadda ya biyar da ni ne ya hana na ji tsananin zafin da ake cewa ana ji. Sannan yanzu yana sanya mini albarka.
Ya nisa ya ce "Zan fa'dawa Abba baki watsar da tarbiyarsu ba. Sannan nima ban lalata musu ke ba, sai da suka bani aurenki da kansu".
A hankali na ce "Yama za'a yi ka ce haka?"
Ya yi dariya ya ce "Ai na sani gani yake yi zan iya 'bata miki rayuwarki, alhalin ni ba zan iya cutar da ke ba".
Daga haka muka bar maganar barci mai nauyi ya dauke mu.
Duk da mun kwanta very late, amma Gudale ana kiran sallah ya tashi. Sai da ya yi alwallah ya tashe ni. Ya fice zuwa masallaci! Madallah da mutanan da suke katse barci ko wani aiki da zarar an kira sallah.
Na ji shigworsa, amma shiru bai hawo saman ba.
Kusan minitin ashirin sannan ya hawo.
Ga mamakina sai ganinsa na yi da tray,
Ya ajiye a gabana, na ga flask din tea da cups guda biyu da kuma sugar, sai kazar da na saka a fridge ya yi warming dinta. Ya shiga bayi ya wanke baki.
Ya ce "akwai sabon brush a toilet din je ki yi, ki zo mu karya muna bukatar cin abu mai dumi kinsan dukkan mu virgins ne, dole sai mun kula da kan mu".
Kunyar maganar ta kama ni, na kasa tashi.
Ya ce "Ni dai na yi iya abin da zan iya yi. Ba zan ce sai na sabe ki na kai ki na miki brush ba, sannan na zo na dora ki a cinya ina baki a bakinki, ni na manta da kaina ba.
Kai wasu marubutan ma da tsiya suke, haka siddan sun zo sun sakawa mata shubuha suna raina 'ko'karin mazansu na zahiri. To ki ji da wai marubuciya Ubangijin rubutun ta ne, ita zata ta shirya komai ta tsara, ta kashe wanda bata so, ta kuma raya wanda take so. Dan haka wasu suna yi rubutunsu tamkar gaske saboda yadda suke za'kulo matsaloli suna rubutun ta hanyar yin hannunka mai sanda dan ya zama iznah da gargadi. Yayin da wasu suke rubutun karya da batsa ta yadda tarbiya take kara shiga cikin garari. Yara suke ganinsu dai-dai da manya. A kuma cusa wa mata raina kokarin mazajensu a shimfida, ko a mua'amalar zaman yau da kullum."
Na kifa kaina a jikin gadon ina dariya sosai! Kaina a kasa na ce "Wai kam ya aka yi ka san haka suke fa'da a littafin?".
Ya ce "abokina Faruk budurwarsa tana yawan bashi labarin littafi, har tana tura masa wasu pages din. Sai yake tura mana. Wani shafi da na ga abin da mijin yake yi na ce "Amma wannan zasu cusa wa yanmata shubuha a ransu domin dai namijin bil-adam indai a cikin hankalinsa yake ai ba zai yi irin hakan ba. Sai dai a aljannah. Kuma fa ita bilhakki take ganin haka zai dinga yi mata."
Dariya sosai ya bani na tashi na wanko bakin, na dawo ya ce "Bari na ha'da miki tea din da kaina Guduyo. Yau kin tabbata amarya mai aji".
Na murmusa na ce "Da sannu kunkuru ya je inda zomo ya je any way na gode".
Ya wani harare ni ya ce "Yau komin zungure zunguren maganar ki ba zan yi fa'da da ke ba *Hala*. Nasan alheri fa! Wato Sa'adu Bori da hikima yake da ya ce ashe mata wayo suke yi mana abin da'di na can..... Ashe dai reality yake fa'da?".
Na yi dariya ban tanka ba. Illah iyaka na sani da dukkan zuciyarsa yake wannan shaukin.
Sosai muka ci naman, yana ta fa'din dirty talks masu saukar da nauyi da kunya.
Muna kammalawa na tattra na kai kwanukan kicin din dake saman na ajiye.
Na dinga kewaya falon da ya sha�? kujerun alfarma tamkar falon kasa.
Jina shiru ya le'ko ganin ina ta zagaye ya sanya shi murmushi ya ce "Kin kyauta! I thought guduwa kika yi ai".
Da kansa ya ri'ke hannuna muka koma daki, barci sosai muka yi dan kuwa bamu farka ba sai shabiyu da rabi na Rana.
A gurguje ya shiga wanka dan tafiya sallar juma'a, ni kuma na sauko 'kasa.
Duk yadda na so na yi shara kasawa na yi a dalilin nauyin da jikina ya yi mini. Sa'ar da nayi babu datti, amma da na yi din da zai fi.
Wanka na yi da ruwa mai zafi sosai, na shirya cikin wata coffee din abaya mai kyau da na sameta a *Amyas newly* na goga sabo janbakin oriflame.
Na shiga kicin na fito da miya a fridge.
Ganin zata isa har zuwa dare sai kawai na 'dora ruwa dan dafa farar shinkafa.
Na hau aikin ha'da coslow.
Kafin ya dawo na shirya komai na gyara kicin din sama sama.
Na dauko robar yagourt din ta yi saura na sha, na ha'diyi Panadol, na kwanta.
Ba jima wa ya dawo, na kalle shi, na ga yadda kayan suka yi masa kyau.
Ya zauna yana ta'ba jikin nawa yana cewa "Wai jikin ne da gaske ko kuwa shagwaba ne?"
Na ce "kawai nauyi ya yi mini, sai kuma kasala amma lafiyata kalau.
Na shirya abinci a dining"
Ya dago ni yana cewa "to taso mu ci, ai da akwai yunwa ma".
Shi ya zuba mana a plate 'daya yana cewa "daga fita ta har kika yi wannan abincin?"
Na ce "ai dama ina da miya".
Ya cigaba da cin abincinsa bai ce komai ba. Ni Kuma so nake ya ce kin yi kokari, kuma abincin ya yi da'di.
Tun ranar bai fita ko ina ba, sai dai zuwa masallaci, yana gida muna barzar amarci ba kakkautawa. Na gamsu hadin amare da *Faseelat* ta yi mini ya taka muhimmiyar rawa a rawar kan da Yaya Gudale yake yi a kaina.
A raina na sake yarda Sakina babbar mace ce, duk wanda zata yi harkar saye da saryawa da su za ki samu kayansu zababbu kuma amintattu ne. Tunda na ga tana ha'diyarsu na tabbatar ta gamsu da nagartar kayan kamfanin *G.H.T* da jakadancin *Faseelart* ne tunda jamiar kiwon lafiya ce.
Tuntu'be *Faseelart* a wannan lambar *07039269802.* dan ki samu naki supplement din da zai dace da ke. Cikin sassaukan farashi fiye da na sauran.
Abu mai daraja shi ke sayar da kansa.
Guduyo dai ta tabbatar tasted and trusted ne, domin ta sake samun sabon suna mai da'di sanadin yadda aka sameta zanzan *Hala*. Ga barin jiki da sanyayyar soyayya. Tamkar ba Gudalen Ummah sarkin son girma ba.
Ranar Monday tun asuba na shiga kicin na kammala komai na abin karyawa, na gyara gidan ya yi fes.
Karfe bakwai saura na fito a wanka, a gurguje na kurbi shayi.
Na na'de meatpia a foil papper na dauki lemo na saka su a leda.
Na hau sama na sanar masa zan fita.
Ya zabura ya zauna ya ce "Yanzu ni ka'dai zaki bari a gidan? Kewar ki illah zata mini Halah".
Wani Dadi ya ratsa ni. Na makale murya na ce "akan dole zan fita Yaya Gudale rabona da zuwa tun Tuesday kada na samu matsala"
Ya ja numfashi ya ce "juya bayan ki na gani".
Na juya din ya ce "gaskiya wannan kayan ba su mini ba. Ni kawai ya kamata na ga ni a jikin ki".
Na kalli kayan ba wani illah a tare da su.
Amma saboda masalaha na canjo wasu, kamar yadda ya ce din. Amma Ina dawowa a tunzure ya ce "Kin ga idan ba zaki saka hijabi har kasa ba sai ki fasa fitar".
Jikina ya yi sanyi saboda yadda na ga ya yi kicin kicin, bana kaunar abin da zai ruguza tarairayar da yake yi mini.
A hankali na ce "Tom bari na sako."
Na sako dogon hijab har kasa na yadin toyobo da ya sha guga, kalar kunun kanwa.
Ya kalle ni sosai ya ce "Ba wani Hijabin da bai kai wannan goguwa ba?"
A Hankali na ce "akwai sai dai iya guiwa ne shi"
Ya girgiza kai ya yi shiru. Na lura gaba'daya fitar ce baya so. Dan hakan nake ta lallabawa mu rabu kalau.
Har cikin makarantar ya kai ni yana saka mini dokoki iri iri. Hatta glass din da ya tabbatar medicated ne sai da ya ce na cire shi, sai idan zan yin karatun zan saka.
To kawai na ke cewa cikin ladabi da yardar zan kiyaye ka'idojin da ya sanya mini.
Da zan sauka ya tambayi yaushe zan kammala.
A hankali na ce "4".
Ya nisa ya ce "alright" ya ciro gudar dubu ya bani tare da cewa "ga pocket money".
Na kar'ba ina godiya sosai, domin nasan shi da son a gode masa.
Na sauka cikin murna mai yawa.
A wannan lokacin ba abin da nake so, yake kuma sanya ni farin ciki irin na ga walwala a fuskarsa.
Ga mamakina 4 din a harabar makarantar ta yi masa. Kaina ya fasu, muna tafe ina ta yi masa barin jiki wajen jan doguwar hira a tsakaninmu.
Ya kalle ni ya ce "yini na yi, ina zullumin lallen hannunki. Bana son sa Guduyo, dole abokan karatun ki maza su ga hannun ki. Wannan tunanin ya sababa mini kyamar lallen ki duk da yadda ya yi miki kyau".
Na sassauta na ce "Ka yi hakuri zan kiyaye sosai, dan kuma ka samu nutsuwa ba zan sake yi ba, har sai ina cikin hutu mai dogon zango".
Ya ce "Ko sai kin kammala karatun ma gaba'daya ba."
"Na ce To".
A wannan lokacin na sake sakankacewa akan tabbas fahimtar Yaya Gudale a baibai ake yi kawai. Domin yadda ya saukar da kai muke shan soyayyarmu abin tamkar almara.
Wani lokacin idan ya yi abu na dinga kallon sa kenan domin ban zaci zai ajiye girman kansa a kaina irin hakan ba. Yayin da ni kuma na sake zama deep a cikin soyayyar sa.
Har zuwa Friday lafiya lau, shi yake kai ni ya kuma dauko ni. Amma duk ranar Monday sai ya rikice mini. Ba karamin juriya nake yi ba, domin ya dinga sani canja kaya kenan. Na kasa gane wannan al'amarin. Bana samun kansa sosai sai a kwanakin week end.
Satinsa uku da dawowa ya fara aiki da F I.R.S. Dan haka tare muke fita, kowa a motarsa, tunda ina iya zuwa makaranta da kaina yanzu.
Har lokacin kuma
Wata biyu da gyaruwar al'amura a tsakaninmu na kasa gane kaina, wani irin zazzabi nake yi cikin dare. Ga amai sai dai idan ban 'dora girki ba, sannan ina matu'kar kuntata idan ya nemi ya kusance ni. Kai tsaye na tabbatar da ina da shigar ciki da ya wuce kwanakin wata a dalilin karatuna na Anatomy tamkar na likitan ci ne.
# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee ✍️
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *53-54*.
*SDK*
Sosai nake shan wahala a dalilin komai na ci sai ya dawo, ga karatu da ya dauki zafi, saboda ina daf da fara jarrabawar zangon karatu na farko a aji hudu.
Ba abin da nake ci ya zauna mini sai garin rogo.
Duk na fyade jikina yayi laushi tubus. A hakan kuma nake kokarin rufe hancina na yi masa abinci. Sa'ar da na yi idan na yi snacks da yawa na saka fridge sai na dauki lokaci ban sake yin wani ba.
Miya kuma Mama na kaiwa ta yi mini mai yawa itama na saka a fridge.
Amma duk da hakan indai zan dafa shinkafa ko na 'dora miyar da nufi 'dumamawa ba zaman lafiya na dinga amai kenan.
Ranar wata litinin da bana mantawa, da safe ina zaune a kicin domin kammala abinci yayin da Gudale yake falo, saboda zaman namu sama sama ne a dalilin daren jiya ya matsa na yarda da shi sai dai tafiyar bata yi nisa ba, na dinga kwarara masa amai shikenan ya tunzura ya ingiza ni yana fa'din ya fara gajiya da wannan iskancin da na tsira ba dama ya ta'ba ni zan gabatar da uzzirin bani da lafiya tamkar ni kawai aka tattara wa jinya.
Haka na tashi na gyara masa wajen na zo zan kwanta ya ce Ata fau bai san wannan maganar ba, sai na fita na bar masa dakinsa tunda dai bani da wani amfanin da zan yi masa.
Shine yake ta fishi, ya kuma rantse ba zan je makaranta ba sai na yi masa abin da zai ci. Tunda jinyar bata hana ni fita da sunan makaranta ba, to lah shakka sai na yi masa abin karyawa.
Ina aikin ina nishi, ina toshe hancina, amma dankalin yana dauko soyuwa na fara kakarin amai, ba komai a cikin nawa ban da ruwaan Lipton. Na amayar da shi tas.
Ina shirin wanke baki wani aman ya sake subuce mini dai dai lokacin ya shigo kicin din, ya ja ya tsaya a bakin kofar yana kallona cikin takaici.
Ya bu'de murya ya ce "Wato hidima ta ce kawai take saka ki amai Guduyo?
Bayan wula'kanta ni da kika yi jiya bai ishe ki ba, shine yanzu kike ta mini amaye amaye akan abin da zan ci?
Sannan anjima ki ce zaki fita makaranta?"
A hankali na ce "Da gaske ba ni da lafiya, ka kalle ni mana, ai kasan dai ba hakan nake yi maka ba. Ka kai ni asibiti ka tabbatar. Makarantar ma ba dan exam ne da ni ba, da ha'kura zan yi".
Ya juya ya fice ban samu arzikin sannu ba.
A daddafe na kammala na kai masa, ganin bakwai da mitina biyar ya sanya na sassauta murya na ce "Zaka daure ka ajiye ni ne? Ba zan iya tu'ki ba".
Ya kafe ni da ido ya na kallon irin yadda na yi laushi.
Ya ce "Tom".
"Na gode" na furta da sauri.
A gurguje na wanke jikina. Na zura doguwar riga, na dora hijab na fito, man zaitun kawai na shafa a dalilin kamshi ma ya gagare ni.
Ya kalle ni ya ga ba abin da zai ce na canja domin a hargitse na ke.
Har muka isa zaman kurame muke yi. Na dinga nazarin akan wannan shariyar da yake yi mini. Wato indai ba zai mori jikina ba, ba sauran walwala a tsakaninmu. Nan da nan na kore wannan zargin na yi masa uzziri. Domin ai bai san sababin ciwon nawa ba, wata'kila da ya fahimci yana shirin zama Dady ne da na samu kulawa da kuma ya ninka mini soyayya, hakanan zai mini uzziri ya gane ba da gangan nake gudunsa a shimfida ba.
Ya mi'ka mini gudar dari biyar tare da cewa kin ce "11 zaki kammala?"
Na ce "eh".
"Gashi kina kammalawa ki hau adaidaita ki koma gida, ba zan samu zuwa ba".
Na kar'ba ina godiya.
Da muka kammala har 'kofar gida Aisha Sani abokiyar karatuna ta kawo ni.
Na zauna a falo ina numfarfashi, ba abin da nake so irin na ci garin kwaki, da lemo mai sanyi. Daga nan na yi barci.
Na 'kwada garin na ci, na kuma sha lemona.
Na shige daki na kwanta a kasa kan kafet barci ya sure ni.
Ban farka ba, sai azahar. Ina idarwa na fa'da kicin, na hau hidimar abincin Yaya Gudale.
Yana dawowa cin abinci, ina kammala wa. Ya ci abinsa, ya koshi, ya tsare ni da ido ya ce "kin warke ne ko kuwa kin yi amaye amayen yayin da kike girki?".
Na yi 'kasa da kaina ina jin hawaye yana shirin goce mini. Ba sannu, ba nuna kulawa sai tuhuma?
Ya tunzura ya ce "Ban gane ba?"
Sanin da na yi ba ya son ya yi mini magana na yi masa shiru, ya sanya cikin rawar murya na ce "Ban yi ba".
"Guduyo me na yi miki?"
Na girgiza kai na ce "Babu komai" amma hawaye sai tsere suke akan fuskata.
Ya zuba mini ido ya ce "To kukan na mene ne?"
Cikin kukan sosai na ce "Bani da lafiya Yaya Gudale! Jikina ciwo, komai ciwo yake mini, bana iya cin abinci, gashi ina jin yunwa saosai".
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Allah ya baki lafiya. Gobe sai mu je ki ga likita".
"Na gode" na furta ina goge hawayen idona.
Da zai dawo ya siyo mini apple cikin ikon Allah da na ci ban yi aman ba.
Washagari bani da exam. Dan haka ya je office ya gabatar da uzziri sannan ya dawo muka nufi asibitin Malam. Da taimakon Sakina na ga likta. Bayan gwaje gwaje aka tabbatar inda da ciki na watattani biyu ba sati daya.
Har mota Sakina ta rakomu, tana ta farin-ciki da addu'ar Allah ya ingan ta. Ita ta siyi magungunan da aka rubuta mini, na karin jini da tsayawar amai.
Tun a wajen na lura Sakina ta zarce uban gayyar murna da mararin samuwar cikin. Shi dai gashinan kadaran kadahar.
Sai da muka isa gida na dauko apple a fridge na zauna a falon ina ci.
Ya zuba mini ido sosai ya ce "Shikenan har