Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 61

9K to 12K   out of 180.1K words

hankalina aka yi bikin Sakina, domin na shekara sha uku a duniya, saboda sai da ta yi karatun Nursing ta gama, a lokacin tana da shekaru ashirin da uku.

Tunda aka yi bikin Sakina na kasa jin da'din zaman, saboda ka'daici da rashin samun fuskar yin walwala, na fara a-sha-ruwan-tsuntsaye, idan ba Abba ne a gari ba, ba na kaunar kwanan wurin Umma.

A hakan dai rayuwar ta ci gaba da gudana ina kallon irin yadda mahaifiyata take rayuwa cikin zullumi da kaffa-kaffa, saboda takurar da Umma ta yi mata. Musamman da Abban ya sayi wani katon kango da yake jikin gidanmu, ya fasa kofa ta cikin gidan aka yi shuke-shuken su alaiyahu, shuwaka, lemon tsami, zogale da sauran tsirrai. To fa Mama ba ta isa zuwa ta tsinka ko ta aika a ciro mata ba.

Na kammala aji uku na sakandire ba dadewa da bikin Sakina, kwatsam sai ga Abba da takardar makarantar kwana ta Sojin Sama ta garin Kaduna, (Air force Staff School Kaduna). Ko ka'dan ban yi murna ba, domin ban ta'ba sha'awar boarding ba, Aunty Ramla ce kawai ta yi boarding a gidanmu, sai su Ya Sadik.

'Karin 'bacin raina Kaduna ta yi mini nisa, da ma a cikin Kano ne da sauki. Hankalina ya tashi, na dinga kuka. Baba ko ya ce ba zai yiwu Abba ya yanke hukunci ya yi masa musu ba. Ya Sadik da ke tsakaninmu da tsakuwa sai murna yake yi yana fa'din, "Na gode wa Abba da ya samo miki boarding wata'kila idan aka yi sa'a kya zazzage wannan tebar da kika ajiye tamkar wata uwar mata, ke kam da wuri za ki tsufa."

Wadannan kalaman su ne kullum a bakin Ya Sadik har ya sa na zama very guilty. Ina tunanin laifi ne don na kasance mai jiki.

A tsaye nake cak ma'ana ina da tsayi, sannan ina da jiki sai na zama irin giant din nan da suke tafe da tsayinsu da jikinsu, ni din fara ce tas, sannan na yi sa'a ina da manyan idanu dara-dara, hanci ba wani dogo ba ne, amma kuma dai ba laifi akwai, sai dimples a dukkan kumatuna, ko abinci nake ci, suna lotsawa bare na yi murmushi ko dariya.

Ina da gashi sosai, sai dai yawa ne da shi ba tsayi, har gaban goshina yake, har wani kamar saje ya yi mini, 'kirjina a cike suke kwarai da gaske, hakan ya janyo ana mini kallon na zarce shekaruna, haka 'kasana a bude yake, kusan ma kibar ta fi shahara daga kuguna.

Bangaren halayya kuwa na kasance mai nacin kan abin da na saka a raina, sannan ina da kafiya, sai dai kuma ina da hakuri, da wahalar gaske aji ana fa'da da ni. Ni ko irin fitinar yarinta ban yi ba, ba ni da abokin fa'da sai Yaya Sadik shi ma shi ne mai tsokanar ta hanyar ce mini Yar sukuta, ko Sady bon bon, ko Guduyo, duk cikin sunayen na fi tsanar Guduyo, ban san manufar sunan ba, amma dai na fi zaton saboda ina da jiki ne.

Ba yadda ban yi ya daina ba amma ya 'ki, sai na tsiri ce masa Gudale. A farkon abin ba kurarin da bai mini a kan na kiyayi ce masa wannan sunan domin ba sa'ana ba ne.
Ban ji ba, don kuwa ban daina ba, tun yana kawo mini duka, har ya hakura.

Ni dai tun tashina ban ga fitanannen a gidanmu irinsa ba, domin Umma ta riga ta sangarta shi, komai yake so sai ta yi masa koda kuwa ba daidai ba ne, yanzun nan zai gama yin iyashege amma da zarar ya bukaci abu to ba ta tuna laifukansa za ta yi masa son ransa jikinta na rawa.

Kowa nan nan yake da shi, ba ga su Mama da Baba da yafi zaman wurinmu ba, ba ga Ummansa ba, ba ga su Ya Abdallah ba, barin ma Ya Al'amin da komai zai yi a duniya sai da Gudale, wata irin soyayya da shakuwa ce a tsakaninsu tamkar tagwaye, kammaninsu daya sai bannacin shi Al'amin baki ne, sannan mai sanyin hali ne, yayin da Sadik ya zama siriri fari tas, yanayinsa 'daya da Ramadan Both hatta gashin kansu kusan iri 'daya ne saboda ya dauko jinin fulanin Yola.

Abba ne kawai ba ya ta Sadik saboda bai son giggiwar da yake yi, ba ya banbanta shi da yayyuna, kusan ma ya fi fifita Ya Abdallah domin ni dai ban taso na same shi a gidan ba, Abba ya kai shi 'kasar Oman yana karantar Law.

Haka Yaya Babangida a Sudan ya yi digirinsa akan Arabiya, Ya Ammar kuwa a Jami'ar Nigeria (Nsukka) ya yi karatunsa na (Mass Communication).

Dukkansu kuma Abba ne ya yi dawainiyarsu, hakan ba 'karamin damun Umma yake yi ba, sai dai kuma ba yadda za ta yi, tunda duk wani shigi da ficinta bai yi tasirin da ya hana Abba yi wa 'ya'yan 'dan uwansa hidima da zumunci ba.

Babban abin da ya sake dagula lamarin Umma a kan mu, a lokacin da su Yaya Sadik suka kammala sakandire, sun riga sun sakankance America ko England za a kai shi karatu, tunda suna ganin ya kai wasu bare kuma tilon 'dansa.

Sai dai fir Abba ya tire a kan ba inda zai tura Ya Sadik, a yanzu ma yake yin fitina kala-kala bare kuma ya sake tura shi kasashen da suke da 'yanci, don haka Ya Al'amin da Ya Sadik a Jami'ar Ahamad Bello suka samu gurbin karatu, inda Al'amin ya karanci Halayyar 'Dan Adam (Sociology). Shi kuma Sadik yake karantar Urban And Rural Development. (Tsara Cigaban Birane da Karkara). Yaya Abbas kuma ya samu (Geography).

Ba irin rikicin da bai yi ba a kan ba zai yi karatun ba ga'badaya. Ya samu daurin gindin Umma, Abba kuwa ya ja ya kafe ba zai sauya ra'ayinsa ba, tunda ba ya so sai ya yi ta zama, haka ya dauki su Yaya Al'amin ya kai su Zariya, ya damka su a hannun mijin Anty Hafsatu, wacce muke 'kiran ta da Antin Zariya, shi ne Vice Chancellor na makarantar a lokacin.
Kan dole Yaya Sadik ya tattara ya tafi Zariya shi ka'dai, ya fara karatunsa,da su Yaya Al'amin a gidan Anti suke da yake cikin kwatsas din makarantar.

Yayin da Antin Zaria babbar Ma'aikaciya ce a ma'aikatar E.F.C.C.

A lokacin da nake shirin shiga aji hudu na sakandire inda zan tafi makaranta a Kaduna, a wannan shekarar su Ya Sadik suka kammala digirinsu na farko, suka fito da sakamako mai kyau.

Ganin a lokacin shekarunsu ba wani yawa suka yi ba, bayan sun kammala bautar kasa, Abba ya tura su digiri na biyu (Masters) a wannan karon ne suka rabu domin Yaya Al'amin a Jami'ar Bayero ya samu, yayin da Sadik da Abbas za su sake komawa Zariya.
Yayin da Yaya Ashiru yake karantar pharmacy a B U K.

Ba'kin ciki a zuciyar Umma tamkar ta halaka, sai neman tsari da zama tare da dangin miji gida 'daya take yi, domin gani take yi ai don Gudale ya taso a sa'anninsa da yawa yasa Abba bai kai shi karatu waje ba. Tunda Ashir ma a shekara 'daya suka kammala.
A haka rayuwar ta ci gaba da gurgurawa, tunda na fara boarding ban sake ganin Ya Sadik ba, domin lokacin zan zo hutu, shi kuma ya tafi, ba mu hadu ba sai da ya kammala, a lokacin ni kuma ina shirin kammala sakandire.





# One Love
# Ana tare
# Surayya Dee ✍️.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*


```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?

*Gaisuwa da fatan alheri ga masu bibiyar labarin mussaman masu turo da ku'dinsu tun tafiyar bata yi nisa ba*
*Iyah Basiru da Mutarin Baffa suna gaisheku da godiyar soayyar da kuke yi musu*
*Jazakumullahu khaira*🤝






*Page* 3&4.


Na dawo sanye cikin uniform dinmu tamkar na sojoji, a lokacin na zama budurwa musamman da nake da jiki, komai nawa ya bun'kasa, na dan rage 'kibar, amma 'kirjina da 'kuguna sun cika tam, fuskata ta zama ta 'yammata, haka nan hankali ya fara shiga ta.
A harabar gidan muka yi kicibus da Ya Sadiq, ya bude baki yana mamamkin irin girman da na yi, saboda tsayinmu 'daya, shi bai samu irin tsayinmu ba, Allah ne ya so shi bai yi gajartar Umma ba.
Yadda yake mini kallon na girma, ni kuma kallon mamakin yadda ya zama 'dan 'kyamo nake yi, sai dai fuskarsa ta zama matured, ya ajiye gemu da saje, wani irin siririn saurayi fari tas, ma'abocin gashi ba'ki, ga shi kuma ya zamo wani irin hadadden guy dan kwalisa, tun yana yaronsa komai sai mai tsada bare yanzu da ya girma. Idan har lissafina daidai ne, shekarunsa ashirin da biyar, yayin da nake goma sha shida, ina shirin shiga sha bakwai.
Na bu'de baki da nufin yi masa magana sai na tuna bai ta'ba kai mini ziyara ba, don haka na dauke kaina, na yi tamkar ban gan shi ba, na shige shashinmu a guje.
Ya biyo ni da sauri, ko ya tsaya ya karbi Baba da ya janyo mini jakar kayana.
A falo na tarar da Mama na rungeme ta tana fadin "Kar ki kayar da ni, sai yaushe za ki daina mini irin wannan cakumar ne?"
Kafin na ba ta amsa na jiyo muryar Ya Al'amin a kicin ai kuwa na sake bazama na yi kicin din, sai dai ina isa na ci burki ban san me yasa a wannan karon na kasa rungume shi ba, shi ma ya tsaya yana kallona, da murmushi a fuskarsa ya ce "Autar gidanmu ta girma, ta 'kara hankali".
Na bu'de baki ke nan Ya Sadik ya shigo da saurinsa, sanin na yi masa abin da baya so, na gan shi na dauke kai, shi dai ya fi son na risina na gaishe shi tsabar son girma, alhalin shi ko antin Zariya sai ya ga dama zai gaishe ta a mutunce.
A guje na 'buya a bayan Ya Al'amin ina cewa "Wayyo Mamana zo ki boye ni".
Ai kuwa ya nufo ni gadan-gadan yana cewa "Ko bayan Abba kika je sai na hukunta ki wallahi".
Haka kuwa sai da ya ba ni rankwashi masu zafi har uku, Mama kuwa fa'di take "Haba Ya Sadik daga dawowarta?
Bar ta ta ci abinci ta huta sai ku 'dora daga inda kuka tsaya tunda dai dole sai kun tsokani juna."
Ransa a 'bace ya ce "Ai daina shiga shirginta zan yi, wai ni ta kalla ta daukewa kai?"
A tunzure na ce "A kan me ba zan dauke kai ba? Yau shekarata nawa a Kaduna, har ina shirin kammalawa kowa ya je mini ban da kai, na sani ko mantawa ka yi da ni, shi yasa ni ma na mantaka, gane ka ne ban yi ba, ba wai share ka na yi ba".
Ya girgiza ya ce, "Ban zo din ba, ba kuma zan zo ba, kin zama wata gandardar da ke, ba hankali sai girma tamkar go'diya"
Cikin takaici na ce, "Tubarkallah! Kuma in sha Allah sai matarka ta fi ni gandarewa, haka za ka yi ta zu'kewa kana zama 'dan tsurut, sai ka zo kana neman ka yi 'kibar ko don ka yi kwarjini amma ba za ka samu ba".
Takaicina ya kama shi ya juya ya fice bai ce komai ba. Amma na san bai bar maganar ba.
Kai tsaye shashinsu ya nufa ya tarar da Umma da Anti Maimuna, ya wuce ba tare da ya kalli Ramla ba, bare ta ci arzikin gaisuwa. Kaf yaran Umma ba mai halayyarta irin Maimuna don haka ita ma takun sa'ka take yi da mu, duk da tana gaisawa da mu, amma dai sama-sama.
Ya fito zai shige bayan ya ce da uwarsu Baba ya aike su shi da Al'amin.
A lalace Anty Maimuna ta ce, "Ka dai ji 'butur kana rawar 'kafa da 'yan uwan wasu amma naka ko kallo ba su ishe ka ba, da ma ka daina cusa kanka wurinsu domin da abu zai taso yanzun nan za su nuna maka kai ne bare ba ka da 'dan uwa namiji abokin ha'di, mu kuma da Ubangiji Ya ba ka ka raina mu, ba don iyashegenka ba da wa zai kai ka gata? Domin duk mai 'yan uwa mata ai ya wuce kaico."
Da'di ya kama Umma tana cewa fa'da masa dai, "A ce wai ba dama na sarrafa Gudale, indai ina son zaman lafiya da shi, sai dai na bi ra'ayinsa, ya 'ki ba ni hadin kai ta yadda zai jagoranci dukiyar ubanku, ba abin da ya sani sai dai ya saka sutura mai tsada, ya kuma fesa turare, sa'a 'daya ya yarda ya yi karatun. Ki dubi yadda Abdallah ya yi kane-kane jikin Abbanku! Ki ga irin dukiyar da aka narkar a lokacin aurensa?"
Maimuna ta tabe baki tana cewa "Addu'a za mu ci gaba da yi kawai, domin ba haka suka bar shi ba."
Ya galla mata harara tare da cewa, "Ke kam kin sha haushi a ce ba ki da aiki sai 'batawa, ko kadan ba ki san gyara ba?".
Sanin halinsa na rashin kunya da tijara yasa ta yi masa tsit.
Ya fice yana ayyana shi bai ga laifi don su Al'amin sun mori Abbansu ba, asalima laifin Abban 'daya ne a wajensa ta yadda sam ba ya sakar masa mara, ya takura shi, ban don haka ba, ba ruwansa da duk wadda yake so ya yi wa alheri.
A yanzu ma takaddama suke yi, a kan ya biya masa ya wuce Europe ya yi Ph.D 'dinsa amma Abban ya kafe ba zai kai shi waje da sunan karatu ba, a yanzu ma baya ganin kowa da gashi, bare kuma ya kai shi 'kasashen da suka riki 'yanci sama da addini da kuma zumunci.
A Daren ranar dai ya shigo ya iske ni a falo na bude jakar kayana, da wadda na zubo tarkacen ragowar kayan shopping 'dina.
Ya zauna bayan ya dauki remote ya canja zuwa channel O, na kalli allon talabijin 'din wata ce take rawa tamkar ba 'kashi a jikinta, wani abin mamaki kuma ba 'yar siririya ba ce, kusan yanayinmu 'daya ga tsayi, ga kuma jiki.

Yaya Sadik ya ce, "Idan kika yi irin wannan rawar dubu ashirin zan baki."
Na murgu'da baki na ce "Me aka yi dubu ashirin kuma?
Ai na wuce ta, nan kuma ba club ba ne, sannan ba studio ka ha'da don ka yi mini 'kidan ba."

Ya kafe ni da ido, ya kasa hadiye abin da ya zo masa wuya, ya ce, "Duk duniya ba mahalu'kin da ya mini rainin da kika mini, ina fatan na samu damar da zan biyar da ke."
Na gurmu'da baki na ce "Har abada ba za ka samu wannan damar ba, idan kuwa ka samu to zan roki Ubangiji ya hana ka sakat idan ka tashi biyar da ni din. Ina kuma fatan na samu damar da zan juyaka tamkar waina a tanda".
Gabansa ya fa'di, muka kalli juna a tare, ya kasa gane mene ne dalilin jin fa'duwar gaban da ya tsinci kansa a ciki, ya sake kallona. Wani irin abu ya dirar masa, rigar da take jikina ta yi matu'kar fito da surar 'kirjina. Ya tsinci kansa cikin wani irin yanayin da yake tsintar kansa idan ya kalli 'kirjina.
Kafin mu sake magana Mama ta shigo ta ce, "Halan dai al'kawari na neman cika, yaushe rabon da na ganka a gidan nan a daidai irin wannan lokacin, ko dai Sady bon bon ta ci galaba a kanka zance ka zo?"
Ya mi'ke a zabure ya ce, "Amma Mama kin gama da ni, ni kuwa me zan yi da wannan shirgin, 'kankanuwar yarinya amma ta zama gari guda, nan gaba kuma ai ba a san me za ta zama ba".
Wani irin abu ya shige ni, na fara kokwanton ko yadda nake ganin kaina, ba haka saura mutane suke kallona ba, ko dai da gaske shirgi guda ce?
Na hadiye wannan damuwar na ce, "Allah Ya sauwake mini me zan yi da kai, d'an tsurut da kai sai fitinar tsiya, da 'din ma da nake cewa sai kai yarinta ce".
Ai kuwa ya tunkaro ni, na yun'kura na arce ko nauyin jikina ban ji ba.
Na zauna bakin gado ina haki, ina ayyana kullum na ce zan daina kula Ya Sadik ba na iyawa ana jimawa idan na gan shi zan yi masa magana.
Tun ina 'yar 'karama ta nake son Ya Sadik, domin kowa ya san shi ne saurayina, tun yana gwale ni har ya koma dukana, amma ban fasa cewar shi ne mijina ba, hatta su Abba sun sani, har tsokanar sa ake yi idan aka ji yana kushe ni, ana fa'din kada fa nan gaba wannan 'yar lukutar ta wahalar da kai, ya kuwa sha mur ya ce baya son irin wannan wasan.
Hatta Ummansa ba ta k'aunar wannan maganar, a fili take fa'da tuni ta yi masa mata, 'yar aminiyarta za ta ba shi. 'Yar masu arziki irinsu, ba irina da muke rawa da bazarsu ba, tana neman tsari da hada iri da Safiyya.
Ire ire wadannan maganganun ne yasa da na fara wayo na daina cewa shi ne mijin domin kuwa idan har Umma ta ji, to ba abin jin nauyi ba ne ta zagi Mamana a kan idona, haka Ya Al'amin bai son wannan wasan, ko da wasa bai ta'ba zolayar Sadik ba, haka nan bai ta'ba shiga sahun masu tsokana ta a kan son da nake yi wa Gudale ba, duk kuwa da matsanancin amincin da yake tsakaninsu.
Ko 'dakinsu shi ya hana ni zuwa, ban san me ya cewa Mama ba, ta hana ni duk da bai fito ya fa'di dalilinsa ba, amma na da'de da fahimtar ko ka'dan ba ya son doguwar mua'amala tana ha'da mu.
Ba na mantawa a lokacin da nake shekaru sha uku, zuwa sha hudu, a lokacin da kirjina ya fara bun'kasa ba abin da nake so irin na yi kwalliya na saka dinkin da zai nuna nima fa na zama mace, idan na yi kwalliyar kuma ba abin da nake matu'kar marari irin mu hadu da Ya Sadik, ba abin da yake sani farinciki irin

4 / 61