Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   45 / 61

132K to 135K   out of 180.1K words

zata k'i saboda kin tsani uwarta".
Ana idar da sallar la'asar ya shigo da leda a hannunsa. Bai ko kalle ni ba, ya fa'da dakinsa tunda yanzu ya tattaro ya dawo dakinsa na kasa tunda saman sun yi jere sun rufe abinsu.
A kokarina na son dawo da mua'amala mai kyau a tsakaninmu na mike na bishi.
Ina shiga na tarar wanka ya shiga.
Na zauna na jira ya fito.
Ya hau shirya wa cikin hanzari.
Na isa gabansa na fara balle masa links, bai hana ba, bai kuma ce uffan ba.
Muka kammala. Na kalle shi ya yi matu'kar yin kyau na dan murmusa na ce "Wannan amarya ta tsinci dami a kala. Autan Umma yafi tsada, tsada."
Ya dauke kai. Na ce "Bai kamata ka bar ko wanne irin kunci a zuciyarka ba, kana shirin zama angon Yar shawalwala".
Ya kafe ni da ido ya ce "Kin biyo ni nan din ma ki sake zagina ne?"
Da sauri na ce "Haba dai rannan din ma subul da baka na yi. Ka yi hakuri".
Ya ta'be baki ya ce "Ai ni ban iya hakuri ba, ke ni ban ma san shi ba".
Ya dauki turare yana fesawa.
Ni kuma na saka hannu na sake gyra masa zaman hularsa.
Har bakin falo na yi masa rakiya.
Na dawo na zauna ina ta hailala. Umma ce ta shirya kasaitacciyar mother's day a wani katafaren Hall.
Na so zuwa amma Sakina ta hana ni ta hanyar cewa an baki gatin gayya ne?"
Na ce "A a ".
Ta ce "to yi zamanki kawai, ki yi ta salatin Annabi".
Na ce "Tom".
Duk yadda Umma ta ware Sakina a cikin hidimar sai da ta halarci wannan yinin wanda hakan ma bai fitar da ita a wajen Umma domin cewa ta yi tsurku ta je yi.
Washagari asabar 7/01 aka daura auren Yaya Gudale da Munubiya.
Auren da Umma ta so ta kuma girmama shi da dukkan zuciyarta.
Yayin da Abba ya debi ido ya zuba a cikin sha'anin illah iyaka yana gefe yana addu'a kada Allah ya sa a kai ni k'asa.
Sakina ta tabbatar mini zuciyarsa cike take da ba'kin cikin yadda aka raba masa gidan Sadik zuwa jami'iya biyu.
Dan haka ta sake rokona na yi hakuri da duk abin da zan ga ni, domin hankalinsa ya kwnata, Lafiyarsa kuma ta inganta.
Ita ma a daren ta kawo mini akwati biyu shake da kaya tamkar na lefe.
Na yi murmushi da naga irin iner wears din a ciki ta bani wanda na saka dana kwana a gidanta.
Dukkan yaran Umma na saman amarya inka dauke Antin Zaria da ta yi mirsisi ta k'i halarta bikin, duk kuwa da kusan rabin ku'din da Umma take wadaka da su daga aljihunta ne, sai kuma Anti Maimuna.
Sakina ce kawai a wajena sai ka'dan daga cikin dangi, amma rabi da kwata suna sama domin kowa so yake ya samu shiga a wajen Umma.
Amma nima dangin uwata da matan yayyena sun cika mini daki kowa yana kokarin sanyaya mini zuciya.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *SDK*.
*79&80*.

Zuwa goman dare kowa ya kama gabansa, gidan ya watse hatta kawayen su Yaya Al'amin sun mayar da su, sosai shi da Yaya Abbas suka shiga hidimar dan su huta gorin da Gudale yake yi musu na basu yi masa kara a lokacin aurenmu ba. Tunda shi a nasu bikin shine kirjin biki.
A wannan karon sai suka wanke wancan laifin da yake ta kirarin sun yi masa duk da basu yi laifin ba. Tunda sun ce shine ya yiwa bikin rukon sakainar kashi.
Sakina ce kawai ta rage a wajena, ta kasa, ta tsare kwana zata yi, duk kuwa da ta yiwa Umma sallama akan ta wuce gidanta.
Muna zaune akan gado sai hawaye nake yi a dalilin gaba'daya kishi sai ya nemi dawo mini sabo fil. Yayin da Sakina take fa'din "Duk kokarin da kika yi, kuma sai ki dawo da hannun agogo baya?".
Ban ce komai ba aka turo kofa, da sallamah ya shigo.
Ganin Sakina ya yi turus.
Da karfi ya ce "Oh oh waton Sakina na rantse kazallahar ki ta wuce min sherri. Kowa ya tafi ke kin zo kin tasa ta a gaba, kina sake koya mata dabarun kangarewa miji."
Ta dauke kai bata tanka ba.
Ya matso kusa da ni ya ce "Zo mu je ina son yin magana da ku".
Na kalli Sakina na ga ta d'aure fuska.
Dan haka na k'i tashi.
Ya kalleta ya ce "Wai ke Sakina me kike ji da shi ne?
Me kike nufi ne?
Ni da gidana, da kuma matata amma maganarki tafi tawa muhimmanci?"
Ita dai kawai kallonsa take yi, bata bu'de baki ta ce kanzil ba. Yasan kuma indai har ta zama irin haka to ta kai koluluwar fusata ne.
Ganin hakan sai ya sassauta ya ce "Ni bana son irin haka gaskiya, to me na yi, kike mini irin wannan fishin?"
Still kallonsa kawai take yi.
Ya kalle ni ya ce "Ta so tana jiranmu".
Sai lokacin ta ce "Tunda dangin amaryar basu kawo mata ita gabanta ba.
To ita ma kuwa bata isa Halimatu ta je dakinta da kowacce irin manufa ba. Duk abin da aka dora ta akai zamu tabbatar mata, mun riga ta tashi".
Nan da nan ya karaya ya ce "Sakina ke din cikinmu daya meyasa zaki bada gudunmawar ruguza gidana?"
Da sauri ta ce "Cikinmu daya tabbas. Sai dai ni din yar'uwar Halimatu ce dan haka zan yi komai dan bata kaskanta a idon Amaryarka ba, ko da hakan na nufin tarwatsewar gidan ba wai ruguzarsa ba".
Ya girgiza kai ya ce "kin zabi Halimatu kenan?"
Ba ja ina ja ta ce "Eh".
Ya yi kwafa ya ce "To yanzu fa'da mini yadda za'a yi?"
Da sauri ta ce "Ka yi tafiyarka, gobe idan Allah ya kaimu sai ka daukota ku zo gabanta sai ka yi kowacce magana, na yi maka al'kawarin kuma zata saurareka".
Ya juya yana cewa"yau ina ganin lukutar masifa, wai ni Sadik ake yiwa irin wannan tijara da ba'kin iko a gidana amma na kasa katabus.
Tabdi jam! Annabi ya yi gaskiya da ya ce kaid'inku mai girma ne. Na tabbatar kin fi masifa tijara Sakina. Allah ya jikan mijnki ba dan ya mutu ba."
Yana fita ta ce "tashi ki yi sallah har sadda zaki gaji, a maimakon ki zauna zuciya tai ta hakaito miki al'amuran da ba zaki iya hana faruwarsa ba, amma idan shaidan ya ga zaki ci riba sai ki ga ya bijiro miki da barci mai gushe dukkan damuwa. Dan haka ribaci daren, a maimakon ki zauna wasiwasi ya sake kidima ki".
Hakan kuwa aka yi. Na yi sallah sosai na, har sai da gabbaina suka gaji.
Akan sallayar na bingire.
Sai da asuba ta tashe ni.
Ina sallah ina kuka, ba dan komai ba, Sai dan kirkin Sakina ya shahara.
Bamu koma barci ba, ita ta jagoranci aikin abin karyawa.
Ni nawa ido ne, da nuna inda wani abu yake.
Kafin taran safe ta shirya lafiyayyen abin karin kumallo.
Muka yi wanka, muka kintsa.
Wata irin kwalliya marar hayaniya ta tsantsara mini. Na sanya tsadaddiyar kamfala da ta samu shahararrren dinki. Ga kamshi tamkar ni ce amryar. Ta yi murmushi ta ce "Hakan nake son ganin ki. Uwargida sarautar mata, muka yi falo.
Ta zubo mana abincin ni da ita a waje daya.
Na zauna ina share hawaye.
Ta ce "To kukan na menene?"
Na girgiza kai na ce babu komai.
"Ina so na ce miki na gode ne. Amma sai na ga kalmar ta yi kadan a ma'auni".
Ta girgiza kai ta ce "To menene abin godiyar, idan za'a mini kishiya ba zaki zo mini dannar kirji ba kenan?"
Na murmusa na ce "Ai ke Baban Nana ya same ki fiye da yadda yake hari".
Sai kuma kukan ya subuce mini gaba'daya.
Ta ce "da kuwa sai yamma zan tafi, amma na fasa ina kammala karya wa zan yi gaba tunda zaman nawa bashi da amfani".
Na ru'ko hannunta na ce "ki yi hakuri dan Allah".
Goma saura ya fito, ya yi wankansa ya shirya. Ya zauna kusa da Sakina yana cewa "Ran ki ya da'de kasaitacciyar mace".
Ta yi kamar ba da ita yake ba.
Ya kalle ni ya ce "babu gaisuwa ne?"
Na yi yake na ce "Ina kwana, ya kwanan bakuwa?".
Ya amsa da cewa "A safiyar nan kuka shirya wannan abin karin?"
Na dan yi yake domin ganinsa da na yi har ya yi wanka ba karamin haushi na ji ba.
Cikin karfin hali na mike na dauko masa na su da Sakina ta shirya musu cikin basket.
Na ajiye a gabansa na ce "Ga naku".
Ya kalli Sakina da ta yi kamar bata wajen, ya ce "kirkinki yawa ne da shi Sakina. Sannu na gode sosai.
Kawai kallonsa ta yi.
Sakina ce kawai take share Gudale ya damu, haka nan ita ce zai yiwa magana ta bagarar da shi, ya dinga bibiyar ta kula shi.
Kusan ma daga ita sai Abba ne kawai Gudale ya damu da fishinsu, domin ko Umma ce, ita take fara saukowa ta neme shi, duk da ba kasafai ma take dogon fishi da shi ba, sai a dalilina ko a dalilin yana shigewa mahaifiyata ko yan-uwana.
Ya dauki basket din yana "Madallah da kokarinku. Amma da Sakina zata bar ki, kamata ya yi ki kawo mana da kanki, dan ta ga girmanki, kin katse barci kin yi mata irin wannan alherin".
Na kalli Sakina na ga ta d'aure fuska tamkar an fa'da mata mugun abu.
Ganin hakan sai nima na kame, ya tafi yana cewa "Rakumi da akala".
Ta girgiza kai ta ce "zai yi wahalar gaske ta yaba alherinki, kawai yi kokarin yin komai dan Allah domin kuwa dan Adam yana da dabi'ar manta alheri, da ri'ke kuskure. Sannan mafi yawanmu bamu cika yin uzziri a cikin mua'amalar yau da gobe ba. Dan haka duk da abin da zaki yi, kawai yi dan Allah, domin idan kika yi saboda shi to ko mutane basu yaba miki ba, baki da kaico. Domin wanda kika yi saboda shi zai yaba miki'.
Na ce "To" da dukkan zuciyata.
Sakina na gidan suka sauko tare. A falo muka zauna, na karbi amarya cikin karfin hali da juriya. Na dinga yake ina gabatar mata, da lemo, ruwa da cincin.
A hankali ta gaida sakina. Yayin da Sakina ta amsa bayan ta mi'ke yi latse latse a wayarta ta ajiye ta a inda ta tashi.
Na zauna a kujerar da take fuskantar mai uku wacce suke zaune.
Cikin hikima nake kallonta. Tabbas kyakkawa ce, farace ta sosai, sannan mai gashi domin yadda ta nannade shi cikin ribon ta yadda daurin kallabinta ya zauna sosai.
Baya ga haka kuma doguwa ce siririya daidai da ra'ayin Gudale.
Sai dai tun a lokacin na fahimci ta girme mini. Domin a lokacin shekaruna asirin da biyar, yayin da ita ba zata yi kasa da ashirin takwas ba.
Yadda nake satar kallonta, haka itama take satar kallona tana kare mini kallo.
Tsawon lokaci yana cin cincin dinsa tare da kallo a allon talabijin.
Kafin ya yi gyran murya ya fara yin addu'a.
Ya zarce da cewa"Ina fatan ku zauna lafiya. Dukkanku ina sonku, ba kuma wacce zata saka na wula'kanta wata."
Ya kalleta ya ce "Na san halin matata, nasan abin da zata yi, nasan wanda ba zata yi ba. Idan har kika ga baku zauna lafiya ba, to matsalar a gunki ce. Domin mai hakuri ce, matu'kar ta bude baki da nufin yin korafi to ta da'de tana yin hakuri da alkunya ne. Na auro ki ne, dan ina sonki, ina kuma da muradin yin hakan, amma ba dan ta gaza ko dan bana sonta ba".
Dukkanmu kowa ya yi shiru yana kallo da saurarensa, gaba'daya mamakinsa ya rufe ni, ban yi zaton zai yi fatali da hudubar Umma na ya nuna mini iyakata idan ya yi aure a gaban matarsa ta yadda zan gajiya na bar gidan kowa ya huta.
Ya juyo ya mayar da hankalinsa kaina.
Ya ce "Guduyo! Kada ki aro halayyar da ban sanki da ita ba, domin ba zan yarda ba. Kin sani ko a wani gidan kike aure, ni din zan iya zuwa na ladabtar da ke matu'kar kika hana a zauna lafiya, bare kuma a hannuna kike, matsayinki yawa ne dashi a wajena, domin tun kafin aure ya hadamu, jini ya ha'damu, bayan haka ke ce uwarsu Amnah. Dan haka yadda kike da alfarmomi masu yawa a wajena, haka hukuncin da zan yi miki idan na same ki da laifi zai fi yawa. Domin kin fita sani na, yadda kika fahimce ni, ita bata fahimta ba. Komin kankantarki ke ce babba, dan haka ki ri'ke girman da Ubangiji ya baki, ki mini uzziri a inda na kuskure. Abin da nake son ki ri'ke shine ban yi aure dan na musguna miki ba, idan kuma ajizanci ya saka na musguna miki din kar ki ji cewar an sha gabanki ne a wajena, domin itama wataran zata ga abin da zan yi a kanki har ta yi zaton ban san komai ba sai soyayyarki."
Na dinga kallonsa ina sake mamakinsa, ban yi zaton Yaya Gudale zai iya wannan jarumtar ba. Ban yi zaton a halin da muke ciki zai daura mini zani a kasuwa ba. Gaba'daya na fi zaton yadda yake kushe ni, yake gasa mini bakaken maganganun da suke gigita zaman lafiyata, hakan zai nuna wa amaryarsa dan ta raina ni, na sake shiga kunci. Sannan ashe yasan ta girme mini, amma ya dinga cewa sa'ata ce.
Sai dai abin da yayi yanzu ya fahimtar da ni Gudale murdadden mutum ne, na bugawa a jarida.
Fahimtar abin da yake zuciyarsa sai Ubangijinsa. Na sani yana sona, amma soyayyar bata hana ya mini iyashege. Kaso mai yawa na kishin da yake cina ya sake yin sauki a dalilin maganganunsa.
Ya sake tsananta kallona ya ce "fa'di tsarin da zan yi muku wajen rabon kwana".
Na sake yin yak'e a dalilin yadda zuciyata ta fara rawa, ba dan komai ba sai dan a yanzu zan dinga raba shi ne da wata. Kai ban da Ubangiji ne ya kaddara wannan al'amarin namiji ya mua'amalanci mace sama daya abin a kyamace shi ne kwarai da gaske.
Cikin karfin hali mai yawa na ce "Na bar muku zabi duk abin da ya yi muku zan bi ra'ayinku da dukkan zuciyata."
Ya kalli Munubiya ya ce "To ke fa'di tsarinki".
Girgiza kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Ya juyo gareni ya ce "To ku dinga yin kwana biyu".
Na ce "To".
"Sai maganar girki kowacce ta yi nata, hakan ya yi muku?".
Nan ma ni na amsa da cewa "Ya yi".
"Shikenan mai magana ta yi a Cikinku".
Tsawon lokaci Munubiya bata ce komai ba.
Ganin hakan ya sanya na ce "Kuna da sati guda da shariaa ta lamince ku yi kafin a raba kwana. Ni kuma na k'ara muku sati biyu. Kenan sai nan da sati uku za'a fara bin tsarin kwana bibbyun da ka ce".
Munubiya ta 'dan murmusa ta ce "Na gode".
Yayin da ya kafe ni da wani irin kallon bacin rai. Kallon da yake mini ya tabbatar mini ban yi masa gwaninta ba . Asalima tamkar na kunduma masa ashariya hakan ya yi. Sai dai da yake ido mashi ne sai idanuwan munubiya suka sanya ya ha'diye dukkan fishin da nake ganin yana kutsowa tun daga kasan zuciyarsa. Murya ba amo ya ce "Allah ya zaunar da mu lafiya". Ta mi'ke ta ce mini "mu yini lafiya. Yabi bayanta. Yayin da na bisu da kallon mamakin yau ni nake ganin Yaya Gudale da wata macen da muka yi kunnen doki a wajensa.
Sai da ya rakata corridor din da kafar benen take ya ce "Ina zuwa bari, na ga Sakina".
Ya dawo ya kalle ni ya ce "Su Guduyo iyayen gida, sarakan kankanba har da fece kwalliya haka, ke a dole sai an ga kema fa ba dama".
Na murmusa tunda na sani zolaya ya yi mini.
Ya shige daki wajen Sakina.
Na bi bayansa. Ina shiga ya juyo ya ce "Koma inda kika fito domin sirri zamu yi".
Sakina ta fit ta ce "Babu sirri a tsakanina da ita, komai ka fa'da mini zan fa'da mata, idan kuwa baka son ta ji to kawai ka rike maganarka."
Ya girgiza kai ya ce "Sakina mu ture wasa kinsan dai ina da hakkin zumunci da ke. Tsakani da Allah ya kamata ki yiwa daya matar tawa ma adalci. Ba zan so tun yanzu ta fahimci bani da kima ko ka'dan a wajenki ba. Tana da hakkin ki yi mata a adalci a matsayin matar kaninki"
Ta ce "Zan yi mata amma idan ka toshe kofofin da zata raina ni, ko ta raina Halimatu. Sannan ka fahimtar da ita cewa da akwai banbanci a tsakaninta da Halimatu a wajena, tunda uta wannan k'anwata ce kuma gidanmu guda. So karku yaudari kanku cewa zan mua'amalence ta yadda zan mua'amalanci Halimatu".
Ya sake girgiza kai ya ce "Hakane! Amma dai ki kamanta Sakina. Kinsan dai yadda nake kambaba ki".
Na yi sukuri ina mamakinsa yanzun nan ya gama daura mini zanin arziki a gaban matarsa, ya zo daki zai kunce mini ita kuma ya d'aura mata. Na yi murmushi domin dai ya wanke mini zuciyata, sannan gara ya mini hakan akan ya muzanta ni a waje ya ce zai kyautata mini a d'aki.
Ta mike ta ce "Anjima ka'dan zan tafi, zamu leka muga dakin amarya. Amma ka saurare ni Namoriki! Ka zama adali a gidanka, kar ka sake ka muzanta Halima a gaban amaryarka da sunan zolaya.
Koda wasa idan ka bada ita a gaban matarka, ka tabbatar zan jagoranci ta bayar da kai a idon duniya".
Ya cukune ya ce "Sakina! Gaskiyar magana kankanbarki yawa ne da ita. Gaba'daya kin nuna mini mi bani da wani alfarma da zaki yi mini, komai Halimatu, duk alherinki ba kya nufar kowa da shi sai ita. To bari ki ji. Tafi son Al'amin akan ki, shima ya fi sonta a kaina, amma ke fir kin bantse mini, na kasa sarrafa ki cikin dadin rai, alhalin kinsan yadda kike a wajena".
Nan da nan sai rauni ya shigeta. Ta sassauta ta ce "Ba haka bane, ai kaima ka sani bana ha'da al'amarinka da kowa. Sai dai kuma idan gaskiya zan fa'da ana fa'da maka abubuwan da yake gurbata mini tunanin dan-uwana. So nake Namorikina ya zama tsayayyen mutum mai ra'ayin kansa. Ya mutunta abin da zuciyarsa take so, ya kalli dunbin soyayyar da matarsa take yi masa, ya daina bari ana haska masa ita nagative. Sannan ya tsaya akan kafafunsa, kada ya yarda ayi masa ingiza mai kantu, domin lah shakka anzo kadamin da bazan yi maka uzziri

45 / 61