Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
zarce shashinmu! Ya shiga ya gaisa da Mama a dakinta, ya wuce falon Baba. Sai da ya je gaban Baba sosai sannan ya durkusa, ya fara gaishe shi.
Ya amsa ba yabo, ba fallasa.
Tsawon lokaci yana gurfane, ya kasa magana domin sai da ya zo gaban Baban ya gane girman rashin mutuncin da ya yi masa.
A sanyaye ya ce, "Baba ka dubi Allah ka yi mini ha'kuri. Ni kaina na san na yi maka ba daidai ba, wallahi tsananin tashin hankali da fargabar kar na rasa aurena ne ya sanya na yi abin da na yi din. Amma na yi nadama, don Allah ka yi hakuri ka yafe mini".
Tsawon lokaci bai ji amsa ba, ya sani laifukansa sun tsananta, masu wahalar a yi afuwa cikin sau'ki ne. Ya sake sunkuyar da kai kasa yana cewa, "Baba daurewa zaka yi, ka karbi tubana indai ba so kake hakkinka ya sake damalmala mini lamaruna ba".
Sai a lokacin Baban ya saki ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "Idan ban yi ha'kuri ba na yi ya ya da kai? Ai duk abin da ka fa'da ko ka yi mini ai gaskiyar lamarin ke nan".
Cikin nauyi sosai Gudale ya ce, "Ni dai Baba ka yi mini afuwa. Na yi tuba, a mini sassauci don Àllah".
Ya nisa ya ce "Sadik ba abin da za ka yi mini a duniya da zai saka na fita daga al'amarinka! Kawai abu daya ne matu'kar ba ka yi ba, ni kuma ba ka isa na yi maka ba. Ba komai ba ne illa gaisuwa, indai har za ka gan ni ka dauke kai to ni kuwa ba ka isa na gaishe ka ba. Inka dauke wannan komai iyashegenka ai dole na yi hakuri tunda Ubangiji ne ya ba ni kai, kuma kamar yadda ka fa'da mini cewa mahaifinka ba abin da bai yi mini ba, tabbas haka ne ba na inkarin hakan, ban kuma ji zafin furucinka ba, domin ko mahaifinmu kawai ya haife ni ne, amma Alhaji shi ne komai nawa".
Kunyar duniya ta kama Sadik yana tuno lokacin da ya tsaya a gaban 'kanin mahaifin nasa yana zazzaga masa dibar albarka. Ya dinga jin tamkar 'kasa ta tsage ya shige, tunda ba zai yiwu ya dawo da baya ya goge waccan ta'asar ba.
"Ni dai ka yi ha'kuri Baba! Na sani ni mai laifi ne". Ya fa'di hakan cikin matsananciyar kunya.
Ya zuba wa Sadik din da yake gurfane ido, yana jin tarin 'kaunarsa, yana sake jin alhinin rashin 'dan uwansa, ya tuna maganganun Abba da ya yi ta yi masa mafi yawa akan Sadik ne. Tabbas da a ce kowanne 'da halin mahaifinsa yake yi da ya bugi kirji ya ce Sadik sai ya fi kowa more kyawawan dabi'u. Sai dai kash, muna cikin wani irin zamanin da yara suke zama masu dabi'u irin na albasa.
Ya nisa ya ce, "Tun tuni na yafe maka Sadik! Idan na ce ban ji zafin abin da ka yi ba na yi 'karya, idan na ce hankalina bai tashi ba, nan na yi munafunci. Sai dai na koma na auna maganganunka sai nake tuhumar kaina ko dai da gaske na yi son kai din? Na gaskata ka, tabbas da Alhaji ne ba zai daga ido ya yi magana akan ka ba, bare ya nuna an zalunce ka saboda tsananin kara da inganta zumunci."
Daidai lokacin hawaye ya 'balle masa ya janyo tissue ya hau gogewa. Da rawar murya ya ce, "Har cikin zuciyata na yafe maka, ina fatan Ubangiji ya bude maka zuciya ka fahimci gaskiya, babbar damuwata da fargabar da nake ciki akan lamarinka guda 'daya ne. Yanzu Ubangiji ma ba zavka kiyayi ta'ba shi ba ? Ya maka baiwa kala-kala, ya ba ka rai, ya yi ka a Musulmi, ya ba ka lafiyar ji da gani. Sannan ya ba ka lafiyar cin duk nau'in abincin da kake so, ya ba ka damar zuwa bandaki da kanka ka yi lalurarka salin alin. Bugu da 'kari ya ba ka mace ta gari da take yi maka wani irin so da ko a wasan kwaikwaiyo yana wahalar samuwa. Ya azurta ka da lafiyayyen abin hawa, ya backa yalwataccen gida. Haka nan ya ba ka iyaye da dangi da kowa hankalinsa a kanka yake.
Sannan ya ba ka haihuwa da wasu kullum a cikin kukan rashinta suke, wasu suna can, suna kashe ma'kudan kudade don neman maganin da zasu samu haihuwar".
Ya yi shiru saboda yadda kuka ya sake zuwa masa.
Tsawon lokaci Baban yana share hawaye, yayin da Uban gayyar idonsa ya cika taf da 'kwalla, jikinsa ya mutu murus, nadama ta sake kama shi.
Da rawar murya Baba ya ce, "Sadik fa'da mini da bakinka me ya kamata ka yi wa Ubangijinka bisa wannan tarin falalar da ya yi maka? Don ya san kai bawa ne mai godiya".
Cikin rauni sosai ya ce, "Kamata ya yi na kasance mai yawan godiya da tuba izuwa gare shi, sannan na kiyaye ka'idojin shari'a na girmama dokokin da aka gindaya, bayan haka na karbi duk abin da ya yi mini da hannu biyu ko da kuwa ba hakan nake so na ga ni ba".
Baba ya ji dadi ya ce, "To mene ne ya hau kanka da kake yi wa Ubangijinka izgilin ba 'ya'ya mata kake so ba? Mene ne ya yi maka da'di wajen musgunawa matarka don kawai ta haifi mata, tunda na san kana son ta".
Da sauri Sadik ya ce, "Alhamdulillah! Ubangijina yana mutunta ni Baba! Na gode masa da ya fahimtar da kai ina son Gudidina tamkar rai. Amma Sakina da Al'amin sun shigo mini cikin gida sun yi mini kane-kane sun hana ni damata ta mai gida. Da.ma bayan tuban da zan yi a gabanka, har da 'kararsu na kawo, ka fa'da musu su fita a harkar gidana idan kuwa ba haka ba Billahillazi kotu ce za ta raba ni da duk wanda ya sake shigar mini gida a cikinsu, munafukai azzalaumai yan ta'adda masu zuwa lahi..."
Tsawar da Baba ya buga masa ce ta saka ya katse maganar ba don ya kammala ba.
"Kai! Saurare ni mashiriricin banza marar kunyar wofi! A gabana kake wannan kalaman bayan ka ce tuba ka zo yi.
Wanne irin tuba ne? Amma dai tuban muzuru ko?"
Ya yi shiru ya kasa ba shi amsa.
"Yanzu ashe ba duka ka ajiye makaman naka ba Sadik? Ina cikin fa'da maka irin rashin da'ar da ka yi wa Mahallicinka, sai ka katse ni ta hanyar kawo wata magana da babu komai a cikinta sai shiririta da rashin fahimta. Kasan irin son da Al'amin da Sakina suke maka kuwa?"
Da sauri ya ce, "Na rantse Baba duk duniya su ne makiyana, ba su da buri irin su gan ni ina cikin ragaita da tagayyara. Na riga na shata jan layi da su. Ni kuwa mai za su mini a duniya? Wai su ne za su dauke mini mata, su boye ta, su koya mata yi mini tijara sannan a ce su masoyana ne? Ai kuwa Allah wadaran wannan son da suke yi mini da babu komai a cikinsa sai zalunci".
"To yanzu dai na daina yi maka nasihar tunda ba shiga take yi ba ko?"
Baba ya tambaye shi a raunane.
"Ci gaba Baba ina jin ka! Ai tuni na yi wa Allah kuka a cikin sujjadda, na ro'ki shi gafara. Sannan ai na daina, da ma namijin nake kulafacin samu to an same shi, me ya rage ban da a yi godiya? Kuma Wallahi Baba nake fa'da maka, ba 'karamin son su Amna nake yi ba ashe? Ban fahimci hakan ba sai da waccan ta Zarian ta kwashe su, yanzu kuma don mulkin mallaka wai ba za ta dawo da su ba. Shin an ta'ba yin haka ne Baba? Ni ba yarda zan yi ba, kawai jira nake mu gama shiryota da Gudidina. Wallahi sai an ba ni 'ya'yana tunda ta ce ba za ta bayar ba sai ta ji a bakin uwarsu".
Mamaki ya cika zuciyar Baba ya ce, "Waton da zarar ta huce za ka saka ta yi rashin mutunci kamar yadda ka saba ko?
To na rantse maka da Allah umarni na ba ka kar ka kuskura ka yi wannan maganar idan kuwa ka yi babu shakka ban isa ba, ba ni kuma da mutunci ko ka'dan a idonka".
"To shike nan na ha'kura saboda kai, ba zan yi magana ba Baba! Yanzu yaushe zan zo ka kai ni wajen Yayar Kwalli na ba ta ha'kuri?"
Baba ya dan yi tari kadan ya ce, ,"To mu bar shi zuwa Juma'a daga Masallaci sai mu wuce. Sannan ina jan hankalinka ka sasanta da 'yan uwanka Al'amin da Sakina".
Ya dinga godiya sosai, har ya mi'ke ya sake komawa ya gurfana. Ya kalli irin yadda ya sake gurfana tamkar zai kwanta masa. A ransa ya san wani al'amarin zai sake barowa. Ilai kuwa sai jin sa ya yi yana cewa, "Ka daure Baba ka je ka yi wa Guduyo nasiha yanzu fa gaba'daya ta bijire mini, yau dai kwanaki hudu ke nan da dawowarta amma har yanzu ba maganar arziki a tsakanin mu balle a je ga maganar gyara mini 'dakina".
"Kunya ta kama Baban cike da nauyi ya ce, "Je ka zan kira ta a waya".
Yana jin haka ya mike da azama yana cewa, "Na tafi to, ka kira fa kafin na isa, so nake ina shiga na gane ka yi magana".
Da ido kawai ya bi bayansa yana ta faman yi masa addu'a a zuciyarsa. Domin ya gane akwai abubuwan da ba zai ta'ba dainawa ba.
Bai zame ko ina ba sai bangarensu ya tarar da dukkan sisters dinsa suna nan, sun saka Umma a tsakiya a nata dabdala. Ya tsallake ya ratsa tsakiyarsu ya zauna jikin uwarsa.
Cike da shagwa'ba ya ce, "Umma shi ne ake wannan dinner din babu ni?"
Ba walwala ta ce, "To na sani ko za ta bar ka ka zo, tunda dai na gane ta yi galaba a kanka ta fi karfinka, sun kwace mini kai".
Ta fa'da cike da rauni sosai.
Cikin tarin soyayya ya ce, "Mai kwace Gudale a hannu Umma ai sai mutuwa, ba dai biladama ba. So nake yanzu ki yafe mini, ki kuma sanya Guduyo cikin jerin 'ya'yanki, matata ce kuma ita ce uwar su Amnah da Aman, ta ci albarkacinmu".
Ta nisa ta ce, "To amma da sharadin za ka sake yin aure, har yau Fauziyya tana son ka".
Gabansa ya yanke ya fa'di, ya zabura ya tashi a jikinta ya zauna sosai ya ce, "Gaskiya Umma ki yi ha'kuri ba zan sake jawo wa kaina masifa ba, waccan ma da na yi yaya na kwashe ne? Ki yi ha'kuri, a bar wannan maganar kawai don Allah".
Sakina da take gefe ta kyalkyale da dariyar iyashege, yayin da su Antin Zaria suke fa'din yaro ya gane Jahar Borno a Arewacin 'kasarmu take".
Ya hassalo musamman dariyar da Sakina take faman tintsirawa. Ya ce, "Umma ki ja wa Sakinatu kunne ta fita a harkata! Ba don ina gudun bacin ranki ba da tuni na saka an sakaye mini ita".
Ai ko Umma ta hauta da fa'da tana cewa, "Yo Sakina za ta girma ne, tana gudun bacin rai na ne? Kai dai da ka damu da damuwata 'kara ha'kuri da ita kawai, idan ka hadu da dan-uwa mai wuyar zama ai sai dai ka yi ta ha'kuri kawai".
Ya mi'ke ya saka hannuwa biyu ya dagata ya ce muje daki akwai abin da zan fa'da miki Umma!
Ai kuwa ta bi shi suka bar su a falo. Sai da ya zaunar da ita a bakin gado, sannan ya tsugunna jikin kafafuwanta ya ce, "Na ro'ke ki Umma ki yi ha'kuri, ki sassautawa 'kaddarata! Ki yi hakuri ki karbi Guduyo a matsayin surakarki, ki yi mini alfarmar hakan Umma".
Ta fara goge idanuwanta cikin kuka ta ce, "Na yarda zan sassauta mata, amma ka sani idan ka fifita ta a kaina zan janye sassaucin wallahi"
Ya ru'ko hannunta ya ce, "Har abada ba ni da kamar ki, ba wata halitta da zan fifita sama da ke, ina ro'kon Ubangiji ya mini tsari da yin hakan".
Cikin rarrashi ya ce zan kawo ta gabanki ta baki ha'kuri Umma! Na kuma jaddada mata cewar za ta iya bata mini rai na ha'kura, amma ta'ba ki na nufin fishina mai gigitarwa. Ke kuma sai ki saka mana albarka ki fa'da mata kin amince da zamanmu tare kina farinciki da hakan".
Ta ce, "Sharadin haka ta sanya maka?"
Da sauri zuciyarsa ta buga, ya aka yi ta harbo jirginsa da sauri?
"A a Umma so nake dai kawai a yi afuwa a sassauta ko zuciyoyinmu sa nutsu, nan duniya ke ce cikon farincikina. Idan babu kyakkawar alaka tsakaninki da ita wallahi zan dauwama cikin kaico da nadama."
Ya fa'di hakan cikin matsananciyar damuwa saosi.
Karon farko da ta yarda za ta yi ha'kuri da Halimatu a matsayin surakarta ba don tana so ba, sai don hakan Gudalenta yake so.
Ta nisa ta ce, "To shike nan na amince, amma ka sani yayarku ta ce ta ri'ke su Saudatu! Idan har na ji kun yi magana akan hakan, na san ita ce tunda kowa ya san yadda ta ma'kala su a ranta. Wallahi idan hakan ta faru har kai ma ba za ka ji da'dina ba, bare kuma ita".
Da sauri ya ce, "Haba Umma ta isa ma ta fara wannan katobarar? Ke dai Allah ya kara miki lafiya na gode sosai Ubangiji ya shaida na yi godiya sosai Umman Saddi'ku".
Suka dawo falo ya kalle su ya ce, "Kowacce ta tashi ta tafi gidanta kun zauna har takwas ta yi." Ya juya ya fice yana jiyo irin carin da suke yi masa.
Ya dawo ya tarar da ni a falo ina kallon M.B.C 3 saboda yadda na saba da kallon Cartoons a dalilin su Amnah.
Na amsa sallamar da ya yi na ci gaba da kallo na.
Ya zauna kusa da ni ya ce, "Baba bai miki waya ba ke nan?"
Ban kalle shi ba na ce, "Ya yi mini mana".
Ya shige yana cewa, "Ki zo ki same ni, ina son mu tattauna wata muhimimiyar magana".
Na tabe baki ina jin a raina kuma na san ba dai na taka dakinsa ba kam".
Ina ganin ya shige na tashi na kashe komai na shige nawa dakin na rufe da mukulli.
Ina jin sa ba irin sintirin da bai yi ba, ba kalar bugun kofar da bai yi ba, amma fir na ki.
Waya kuwa kashe ta na yi.
Washegari ya tarar da ni a Study Room! Fuskar nan a daure tam ya ce, "Kin kyauta da kike wulakanta mijin aurenki, ina bin ki ne saboda na san na yi miki laifi amma ke sam kin kafe, kin ci laya.
To ki sani wallahi ba zan yarda ba, dole sai kin zo dakina wallahi".
Na dago na watsa masa harara na ce, "Sai na ga dolen ai".
Ya ce, "Kin gama abin karyawar ko kuwa?"
Kai tsaye na ce, "Ba zan yi ba".
Ya jijjiga kai ya koma." Ba a jima ba ya dawo cikin Shirin fita, Aman na hannunsa shi ma ya yi masa wanka, sun yi fes da su, kammaninsu guda har rashin jikin. Sai da suka fita sannan na gyra gidan na yi wanka. Ina zauane sai kawai na tsinci kaina da son ci gaba da hararo ba'dakalar da na shiga a baya.
*LAIFIN DADI KAREWA*
*Karshen Free pages ke nan na wannan kayataccen littafi mai suna _SABO DA KAZA..._ Zan dakatar da yin posting na dan lokaci ka'dan, da zarar kun karbi labarin ta hanyar sayan littafin zan ci gaba da sakar muku shi a Paid Group dina. Ku karanta cikin lumana da salama. Wanda ya yi noma dai ya huta da awo.*
*Labarin Guduyo labari ne mai ta'ba zuciya, labarine da dole sai kin ci karo da irin kalar taki matsalar ko kaddarar. Ubangiji ya kara mana ha'kuri da juriya*
*Duk wannan bayanin sharar fage ne. Ina tabbatar muku ba za ku yi nadamar saya ba, lallai kwalliya za ta biya kudin sabulu.*
*Na san da yawa cikin masoyaba su ya kamata su fadi ba ni ba, to amma kasancewar an ce 'waka a bakin mai ita ta fi dadi.' Sannan kuma akwai sabbin masoya da ba su san littafina mai suna _HALIN YAU_ ba. Don haka ku hanzarta sayen wannan littafi don jin yadda aka haihu a ragaya!*
*Bissalam! Sai na ji ku*.
# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee.
# One Love Ana Tare!🤝
2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
*SDK23&24*
*Umma*
Wata irin salama ta shige ta. Da murna sosai ta ce, "Ashe ya same ka da maganar yarinyar nan? Ni kuma har ina jan kunnensa kar ya zo da maganar gabanka, tunda ba lallai ka amince da ita ba".
Ya numfasa ya ce, "Bai fa'da mini ba, amma na ji labarin 'yar wajen Alhaji Namakole yake so. Sai dai kuma kin sani ba zai yiwu ba, duk wanda yake unguwar nan ya sani, uban yarinyar ba shi da wanda yake 'ki iri na.
Shi ne yake ya'dawa wai safarar miyagun kwayoyi nake yi, sannan ina kar'bar ku'din ruwa. Idan kuwa za a auna wannan maganganun a mizanin hankali ai kin ga ba zai so mu ha'da jini ba".
Dake ita ma Umma ba son lamarin Nusaiba take yi ba, tafi son sa da Fauziya 'yar aminiyarta wanda hamsha'kan attajirai ne na garari, tun shekarun baya Allah ya yi wa mai gidan rasuwa, ke nan matar ce take sarrafa komai da tallafin manyan yaranta maza. Kawai don tana girmama ra'ayin Gudalenta sama da nata ra'ayin, shi yasa ba ta matsa masa sai ya auro Fauziya ba.
A hankali ta ce "Haka ne, amma wace ce yarinyar? Domin akwai yar wajen marigayi Anbasada Jalo Jimeta. Da take son sa, na ga kuma za ta dace da ra'ayinsa da ya lissafa".
A gajarce ya ce, "Madalla! Sai dai ni kuma ba ta dace da ra'ayina da tsarina ba. Sai ya ya ke nan?"
Da sauri ta ce, "sai a bar shi, domin ta kula 'kankancinsa a kusa yake yanzun nan zai yarfata.
*Shin kina bibiyar Faseelat kuwa?*.
*Shin kina gyara kanki kuwa?*
*Faseelat ta kware wajen zaba miki supplement din da zai dace da jikin ki*
*Hakan ya sanya ta samu lambar yabo daga G.H.T*.
*Tuntu'beta 0703929802*
*Gudale dai ya ce zaki