Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   17 / 61

48K to 51K   out of 180.1K words

rufe shi da duka har sai ya karyata kansa.
"Dallah rufe mini bakinki, makaryaciya kawai". Ya fa'da da kara'di.
Na yi shuru! Na kame bakina a dalilin na ji haushin yadda ya daka mini tsawa.

Bansan dalilin da ya sanya ya yi zagaye da mu ba, ina Hausawa ina asibitin Malam?
Sai kawai ya bi ta gate din da yake Kan titin Zaria road, muka dinga tafiya, har muka isa round din tafiya Kaduna, sannan ya juyo.
Na dinga mamakin hakan.
Mun zo dai-dai gadar lado na ce "Yaya Gudale siya mini plantain chips ina son ci".
Ya share! na sake maimatawa.
A hassale ya ce "Ba zan siya ba, tun wuri ma ki daina wannan hamburin hayam din nan. Dan kuwa ba zan laminta ba, shiyasa kike ta hawa tamkar kina shan yist alhalin ciye ciye kawai kike yi ba control".
Bansan ya aka yi ba sai kawai na tsinci kaina da cewa "ka fasa barwa Yaya Ashir din ne?".
Ya dugunzuma ba ka'dan ba.
Takaici ya shake masa makaoshi ya kasa cewa komai.
Muna isa gidan ya karbi file ni kuma zan wuce wajenmu.

Ya gallah mini harara tare da cewa "Tare zamu kai masa".
Na bishi a baya. Muka tarar da Abba yana zaune a falo.
Murnar ganin sakamakon gwajin ya dinga yi ta hanyar fa'din Alhamdulillah!
Ya dinga sanya mana albarka.
Ya rufe maganar da cewa motar Gudale tana hanya.
Na fito na barsu.
Ina shiga wajenmu na tarar da Mamah tana kuka irin hawayen nan na shar'be.
Hankalina ya tashi matu'ka da gaske.
Na dinga tambayar dalilin kukan, amma bata bude baki ta ce mini ta tafasa ba.
Sai da aka jima bayan ta ga nima na fara kuka sosai.
Murya ba amo ta ce "Umma ce ta fa'dawa Babanku wai ina yi mata shaguben na riga na sha gabanta a gidannan, sannan kuma Ina yi mata gadarar aurenki da Sadik har ina alfahari zai zama shugaban kasa. Da sauran maganganu na sharri".
Na yi shiru! Raina ya baci, ita dai Umma kullum a cikin kirkirar matsala take. Yayin da Mama ta kasance mai damuwa da lamarinta.
Yo Ni Allah na tuba idan ma na zama surukurta, komai zata yi ina ruwana da ita, ai kulawa ma yabace.
A ganina Mama tana damuwa ne, shiyasa Umma take sake yi mata yadda ta ga dama.

Na nisa na ce "ki yi hakuri Mama! Kayan lefe nan ne yake cinta, tunda aka kawo ta gansu ta sake birkicewa, hatta Sakina ma baki ga cin mutuncin da ta yi mata ba.
Ta sani Ina dakina na sashinta amma ta daga murya tana yiwa Sakina tijarar yadda ta narka dukiya mai yawa a lefen.
Amma sai na yi kamar ban ji ba. Dan Allah kema ki daina damuwa Mama! Ba yadda zata yi da ke sai kanadi".

Ta zuba mini ido ta ce "Na lura ke ba Kya fargabar da nake jiye miki".
Na saki ajiyar zuciya na ce "To ya zan yi tunda haka kaddara ta zaba mini".

Ta mike tana cewa "Allah ya sani bana son auren nan, amma tunda kun dage ba zan yi jayayya da ikon Ubangiji ba. Ina fatan ko menene zai biyo baya ya kasance alheri ne, amma ki sani sai kin Kulla abota da hakuri da kuma juriya."

****
Bayan kwanaki biyu. Ina zanue a falon Mama sanye nake cikin wata kyakkawan atamfa Yar Togo wacce na siya a wajen *Amyasa newly & Used* 08083909947. Koriya shar mai zanen yakuwa, da ro'di ro'din jah kadan
Sosai ta karbi lallausar farar fatata. Mussaman yadda dinkin ya zauna a jikina, doguwar riga ce mai kwala.
Ba zato na ji wayata ta hau kuwwa. Ina dubawa na ga sunan Yaya Gudale yana yawo akan allon wayar. Na dauka cike da matsanancin mamaki.
"Ki fito ina wajen bukkar nan ina jiranki yanzun nan"
Ya kashe wayarsa, ya barni ri'ke da tawa cikin matsanancin mamaki.
Na dinga ayyana me ya faru da safiyar nan Gudale zai nemi ganina.
Na mi'ke a sanyaye na shiga dakina, na dauko Jan mayafi, na tsinci kaina da sake goge fuskata da hodar da ta dace da nau'in fatata ta shararren kamfanin nan na oriflame, na tsinci kaina da shafa Jan baki ja. Na kalli kaina, na tsorata da yadda fatata ta zama. Wani irin sheki luwai luwai tamkar irin manyan mata yan kwalisa suke, haka na dawo. A zuciyata sai yabawa kawar Sakina nake yi, duk da kasuwanci take yi, na tabbatar zata samu ladan yadda take tsayawa kai da fata take gyarawa mata fatarsu cikin gaskiya da aminci.
Na shafa turaren mai na Haramain Madina a hannuwanwana da wuyana ka'dan.
Na fito, na isa zuwa kicin na cewa Mama "Na fita waje Yaya Sadik yana kira na".
Ta kalle ni sosai ta kasa ha'diyewa ta ce "Da sassafe nan? Ashe shiyasa kika tashi kika shirya, tamkar zaki je wani gurin?"
Ina dariya na ce "Wallahi ban san ma zai zo ba Mama".
Na fita ina kallon lokaci a wayata da ya nuna 10:52 am.
A fili na ce "Rana ta fara yi ai"
Na murmusa na ce "idan mutum na zaune a gida ba ya gane lokaci ya tafi."
Na ma'kala jan takalmina flat a dalilin tsayina ya ishe ni.
A hankali nake tafiya, ina hango shi yana zaune a bukkar shi ka'dai yana ta faman latsa waya.

*Sadik*

Ba zato ya 'daga kansa ya hango ta a dalilin 'kamshin turaren da ta shafa ya kaiwa hancinsa caffa.
Zuciyarsa ta buga saboda yadda yaga ta yi kyau na ban mamaki, dinkin ya fito da ainihin surar 'kirjinta daga kasa kuma ya bude.
Take ya ji zumudin kwanakin da suka yi masa saura su zo da gaggawa. Domin yaga abin da ya jima yana harin ganinsu a zahiri.
Bai san me yake ji akanta ba.
Amma babu 'kiyayya, kawai dai shi yafi son yar siririya ne wacce zai ta cafewa babu nishi ko haki.
Baya ga hakan, Yadda Ummansa take adawa da lamarinta yana rage masa tasirin yadda yake jin 'kaunarta wacce yake ganin dan jini ya ha'dasu ne da kuma yadda yake hango soyyayyarsa a idanuwanta.
Na isa inda yake zaunen sai da na yi sallamah sau biyu sannan ya yi firgit alamun ya yi zurfi cikin tunanin.
Na zauna na gaishe shi
Ya amsa yana bina da kallon 'kurillah.
Sanye yake cikin 'kananun kaya, jikin rigar an rubuta Gudale. Kusan duj rigunansa da handkerchief dinsa an rubuta hakan.
Ya numfasa ya ce "Guduyo yaushe kika fara sanya janbaki saboda Allah?"
Cike da iyashege na ce "baka lura bane dama ina saka wa from time to time".
Ya 'daure fuska ya ce "Bana son karya kin ji! Fa'di dalilin da ya sanya kika saka kawai Malama".
Na yi murmushi ina jin da'din yadda yake magana cike da rikici da wani irin abu da ban san yadda zan fasalta shi ba.
Amma dai ya fara saukowa daga dogon fishin da ya yi.
Na ce "To kawai a barshi na saka ne irin yadda yanmata suke yin kwalliya idan zasu fita, ko sun idan yi nisha'di".
Ya bata fuska tare da zuba mini ido sosai ya ce "gyara kalaman ki. Basu yi mini ba, dan haka ban karbe su ba'.
Na shagwabe fuska tare da cewa "Kai Yaya Gudale".
Ya gallah mini harara tare da cewa"Ashe ban hana fa'dar wannan sunan ba?"
Na sunkuyar da kaina kasa ina gunagunin ni ina son sunan, yana sanya ni nisha'di domin kuwa har cikin zuciyata nake jin shi din Gudale ne tamkar da dubu.
Dan Haka ba ina nufin Gudalen da Umma take nufi ba.
Ina nufin The only one I love.
Ya girgiza "Wai shagwaba kike yi ne ko Ta'bara?"
Kafin na yi magana ya ce "Ina jin ki, fa'da mini dalilin sanya wannan jan bakin?"
Na yi kasa da kaina na ce "Ho Yaya Sadik! To mu barshi kai na sanyawa tunda zance ka zo".
Ya wani zabura ya ce "Ka ji masharranciya! Wanne zance zan zo kuma?" Allah ya yafe miki hakkina da kika dauka kawai Guduyo".
Ya fa'da yana gintse dariyar da take son bayar da shi.
Ni kuma ganin sassauci a tare da shi na sanya na ce "Ya mini kyau kenan? Tunda ka tanka".
Ya ci magani ya ce "Abba ne ya ce mu yi shawarar kalololin furniture's din da za'a zuba a gidan".
Cikin son na kureshi na ce "wanne gidan kenan?"
A raina kuma ina cewa ba zuwan kansa bane ke nan.
Ya ce "Kin ga ki bini a hankali. Na riga da na za'bi wanda nake so a zuba mini a wajena, ba dan Abba ba, da ina zan bi ta kanki tunda na gane makiyana sune abokan huldar ki. Akan Ashir zan yi matu'kar baki mamaki Wallahi".
Ganin zai birkice mini, ya sanya na yi gaggawar cewa "Na wajen nawa ma ka za'ba, ni ina da wani ra'ayin ne bayan naka?"
Bai iya boye yadda maganar ta sanya shi farin-ciki ba a dalilin son girma irin nasa.
Nan da nan ya sauko daga fishin ya ce "Na zabi Royal blue! Na wajen ki kuma kina son Coffey?"
Da sauri na ce idan ya yi maka, nasan zai yi mini".
Shikenan muka shiga hira cikin nutsuwa. Ya shaida mini Abba ya bashi ku'din siyayyar da zai yi, yaushe zan raka shi na taya shi zabe?
Murna tamkar na zuba ruwa a 'kasa. Na ce "koda yaushe ma in ka cire Monday da Tuesday"
Ya ce "shikenan".
Na ce "kwanakin nan nafi zaman gidan Anti Sakina! Idan Ina can sai ka dauke ni a can din ko?"
Na tambaya cikin sigar ro'ko.
Ya ce "sai na mu je da ita ta taya mu zabe kinsan bayan 'kwarewarta a wajen kazallaha, tana da taste mai kyau. Ta iya zabe".
Na yi dariya sosai, yayin da shi kuma ya 'kurawa saitin kirjina ido ya ce "kin fi dacewa da Guduyo" cikin wani irin yanayi.
Sai kuma ya mi'ke yana fa'din daga yau din nan duk inda zaki je sai kin fa'da mini"
Da'di ya kama ni a tunanina ya riga ya fa'da sona ne irin deep din nan.
Cikin sigar tsokana na ce "An gama sir".
Ya yi tafiyarsa babu waiwaye illah ni da na bishi da ido, ina addu'ar na samu damar shiga zuciyar sa fiye da yadda ya shiga tawa.








# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee.
# Ana tare đŸ€.
2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.



*SDK*
*33-34.*

Kwanaki ka'dan Mama da Umman Danladi Nasidi.
Suka yi mini siyayyar kayan kicin za'bab'bu kuma na alfarma, na dinga mamakin yadda aka yi suka za'bo unique kaya suka dawo cikin kankanin lokaci, ba shan wahala, ko rana. Da na tsananta bincike sai na gano da Aziza suka fita inda ta kaisu wajen matasan Yan kasuwar da suke kasuwwancin da babu algus, suke bin 'karamar riba. Kayan su kuma mai aminci da tsananin kyau.
*Amyas newly & fairly items* 08083909947.
*Umm Muhd collections*
08063358662.
Na dinga mamakin yadda Aziza ta sansu, amma dana tuna itama tana dan ta'ba business din tana shiga da kayan cikin makarantar da take zuwa North West,
sai na janye mamakin. Sannan sau'kin kayansu da kyaunsu ya sanya manyan mata da yanmata 'yan kwalisa suke rubibin saya.
Duk wacce take bu'katar kayan kicin ta tuntu'be su. Haka nan suturu na alfarma ba a barsu a baya ba.
Kina so
Sister kina bu'katar sai da kayan katako na 'dakin ki, ko layan daki na hannu ki kike bukata ko tuntu'bi *Amyas newly& fairly items* a wannan lambar 08083909947. Zaki samu dukkan nau'in kayan da kike bu'kata.

Tare muka fita tunda asabar ce, Yaya Al'amin ne yake tu'ka su. Inda suka ajiye ni a gidan Yayar Kwalli. Daga nan kuma gidan Sakina zan wuce, zamu fita tare da ita da kuma Yaya Sadik duk da dai sai yamma ne fitae ta mu, ina son na je da wuri ne dan ta huce gaba'daya.

Muka gaisa da Yaya! Ban jima ba ta bani kayayyaki a cikin babbar leda.
Tana cewa da takardar yadda zaki yi amfani da su na ciki.
Na yi godiya duk da yadda kunya ta kama ni dan na gane kayayyakin mata ne a ciki kala kala. Maman Kebbi ce ta aiko mini.
Jim ka'dan na ce zan tafi.
Ta tashi tana fadin bari idan Yayanki Ashir na nan sai ya kai ki, ki huta yawo da wannan kaya.
Ta isa bakin 'kofar falon ke nan ya shigo. Ta ce "dama kiranka zan yi, ka zo ka Mayar da Halimatu gida daga nan ka karbo mini sakon a wajen Saude".
Ya kalle ni muka gaisa ya ce "ba ni mintina goma na watsa ruwa, ba zan yarda na fita haka dukun dukun da ni ba, alhalin ke kin cakare tamkar mai zuwa gasar kyau".
Na murmusa na ce "Yaya Ashir na baka minti ashirin ma".
Yaya ta yi dariya ta ce idan ya so ya canja launin fatarsa ya kamo ki haske ba".
Ya fita yana cewa "sai na fita Yaya! Wannan duk wata hikima ce da ake yiwa Amaren zamani, amma ai kowa yasan ba ta kai hakan ba."
Ya fito sanye da yadin filtex ruwan toka, ya yi kyau sosai. Ni da kaina na dinga yaba haduwar Yaya Ashir. Ya fi Gudale cika ido.
Amma bai kai shi kyau da fari ba. Amma batun haiba ya kere shi.
Uwa uba ya fi shi nutsuwa da sassau'kan hali.
Amma ni kuma zuciyata ba shi take so ba, ba shi yake burgeta ba, hakanan ba shi take sha'awa ba.
Muka fito Yaya ta bimu da fatan alheri da kuma addu'ar mu gama lafiya.
A hankali yake tu'kinsa tamkar ba ya so mu isa inda muka nufa.
Na kosa ya kai ni unguwar Sallari inda Sakina take zaune.
Amma sai tafiya yake tamkar irin tafiyar hawainiya.
Ya sassauta murya ya ce "me kike so na siya miki dan ki gane dan kin za'bi Sadik kin bar ni ba zai zama dalilin gaba a tsakaninmu ba. Sai da maganar aurenku ta bayyana, na gane ashe 'Dan Bala ne ya yi miki kamun kazar kuku.
Shiyasa kika dinga nuna mini baki fahimci halin da nake ciki akan ki ba".
Na fashe da dariya a fili na ce "Anya akwai wanda ya kai Yaya Sadik yawan suna?"
Domin kusan kowa da sunan da yake jingina masa.
Yaya Ashir ya kirne fuska ya ce "Ato ai Sadik dan bala'in gaske ne, shiyasa nake ce masa 'Dan bala. Sai dai duk bala'insa na dama shi na shanye, Ni da shi kar tasan kar ne".
Na sake yin dariyar domin na san gaskiya ya fa'da.
Ban ta'ba ganin wanda ya tsarewa Gudalen Umma gaba irin Yaya Ashir ba.
Ina tuno wani fa'dan da suka yi a gida daga cacar baki, Yaya Ashir ya ware iya karfinsa ba fargabar komai ya warware Gudale da wani irin gigitattcen mari. Dan kawai Gudalen ya ce masa ma'katulu shegen dangi".
Ai kuwa kafin ya rufe baki ya ji saukar Marin da sai da jini y kwanta a gefen idonsa na hagu.
Ya masa haka ya fi sau a 'kirga, shiyasa Yaya Ashir bai cika son zaman gidan mu ba. Saboda sun dinga tayarwa ahalin gidan hankali kenan, Sadik mai raini da wulakanci ne, yayin da Ashir yake da rashin daukan raini gashi kuma da saurin hasala fiye ma da Gudale.
Sosai suke 'yar tsama, basa shiri ko ka'dan.
Al'amin da Abbas ne maraina wayonsa, amma Ashir kam baya ta'ba shi ya kwashe kalau. Bansan dalili ba idan akwai abin da yake yiwa Gudale ciwo to bai wuce ko da wasa ace Ashir saurayina ne ba. Ya dinga kumfar baki ban dace da wanda zuciyarsa bata da alheri ba. Shi fa ko gani yayi mun yi magana da shi ya dinga fishi da ni yana fa'din bashi ba ni. Sai da Abba ya yi shari'ar cewa "Ashir Yayana ne kamar yadda yake jin shima Wa ne a gareni.
Kai tsaye ya cewa Abba "Ni gidanmu 'daya da ita, shikuma nan ba gidansu bane , tunda ba Babansa bane 'Dan gidan, dan haka a fa'da masa ya daina tsallake iyaka".
Abba ya rasa gane nufin Yaya Sadik! Ya dai lura 'yar tsamar da suke yi ne yasa yake yawan yi masa gorin ai shi 'dan mace ne dan hakan ba 'dan familinmu ba ne.
"Ina zamu je ki za'bi abin da kike so?"
Ya katse mini tunanin da nake faman yi.
Na ce "ko ina ma Yaya Ashir".
Kai tsaye wani hamsha'kin store ya kai ni.
Ya ce na zabi komai nake so!
Na gama ruwan idona, na zabi wani ba'kin dinner set mai kyau da tsada tun a lokacin ma kudinsa ya zarce dubu talatin bare yanzu.
Ya ce ya yi ka'dan na kara da wani abin.
Ina tunanin me zan dauka saboda komai an saya mini, idona ya kai kan dispenser sabuwar zuwa, dan da alama new moden ce.
Bata da 'kan'kanta, kuma bata cika girma ba. Ya biya kudin aka saka mana a boot muka wuce.
Har muka iso gidan Sakina hira muke yi, Kuma mafi yawa ta Gudale ce, a ranar na gane Yaya Ashir bai 'kullaci Gudale Kamar yadda shi ya kullace shi ba. Asalima kamar yana masa kallon hankali ne bai gama yi ba, amma nan gaba ai ba zai yi wani abin ba.
Ya rufe maganarsa da cewa "Tunda ya yi sa'a ya same ki, ai Ubangiji ya cika masa niimomin duniya, duk wani abin da ya rasa na kyawawan dabi'u zamansa da ke zasu canja shi.
Amma sai kin yi hakuri, kin yi juriya, kin yi addu'a mai yawa. Tunda kina sonsa na sani komai zai zo da sauki".
Maganganun sun shige ni mussaman da ya ce Ina son Gudale.
Na tausasa harshe na ce "Ina sonsa fa ka ce?"
Ya gyada kai ya ce "kwarai kuwa! Domin na tĂ bbatar sonsa ne ya katange ni daga samun ki, sannan shi ya kasance dan gata ne mai kuma sa'a.
Na sani Abba zai so ki kasance matar Sadik tunda kowa ya miki shaidar hakuri, duk yadda na shaidi Abba mutumin kirki ne, masoyin zumunci ne. Na sani zai fi son Sadik a kaina, sai dai kawai ya nuna 'duk daya muke a zahiri Saboda yadda Ubangiji ya cika kirjinsa da alheri. Dan hakan banga laifinsa da ya bashi auren ki ba".
A sanyaye na kalle shi na ga yadda idanuwansa suka ka'da tabbacin yana cikin alhini mai yawa. Na ce "Yaya Ashir"!
Ya amsa da "Na'am" murya a dakushe.
Na ce "Ina son ka gane, Wallahi ina sonka, ba wai Yaya Sadik kawai nake so ba".
Ya murmusa ya ce "Na gode! Ina tabbatar miki wannan maganar zata mini fitila a dukkan ragowan rayuwar da ta mini saura a cikin wannan duniyar. Ina miki fatan alheri. Ki dauke

17 / 61