Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
da ya zo daidai da fahimtata na kuma gaskata shi".
Na juya na ci gaba da abin da nake yi, ba tare da na sake tankawa ba. Tsawon mintuna ya katse shirun da ya ratsa kicin 'din ta hanyar cewa, "Kin bar ni a tsaye Guduyo".
"Cike da rashin damuwa na ce "Na ba ka abin zama fa".
Cikin rikici ya ce, "Ba na so! Ba zan zauna a kai ba, na kuma gaji da tsayuwar".
"To ka koma falo ka zauna mana".
Na fa'da don kaucewa rikicin gangan 'dinsa.
"Ba ni da ala'ka da mai falon, ke nake nema, a inda na gan ki a nan zan tsaya".
Na ajiye wu'kar hannuna na bude fanfon sink na wanke hannun na fita cikin fishi-fishi, murna-murna.
Na dawo masa da stool din jikin mirror.
Ya karba ya zauna, na bude fridged na zuba masa lemo da ruwa.
Na zubo masa meat pie din da ban jima da kammala shi ba.
Na kai gabansa, ban yi zaton zai ci ba.
Amma ga mamakina sai gani na yi ya mi'ke ya wanke hannu.
Ya dinga cin meat pie din nan tare da korawa da lemu.
Da'di ya debi shi ya fara santi da cewa, "Har ga Allah na so kin amince da Comrade Anas, saboda a kusa kike ba zan dinga kewar kayan kwadayin da ba kya gandar yin su ba".
Na bata rai na ce, "Kai kuma sai ka yi ta zaryar zuwa gidan kanwarka cin abinci?"
Sai da ya hadiye na bakinsa ya ce, "Ai na san ni na daban ne a wajenki aiko mini za ki dinga yi".
Na tabe baki na ce, "Idan mijin nawa ya amince ke nan?"
Ya dago a razane ya ce, "Ashe nan gaba wani zai iya shiga tsakaninmu Guduyo?"
"A to ai gaskiya ne, Yaya Gudale na san ko kai ba za ka amince kullum matarka ta dinga girki tana aika wa cousin ba".
A sanyaye ya ce, "Ashe kawai cousin nake a wajen ki ko?"
Ina jikin gas ban juyo ba na ce, "Idan ka so ai za ka iya 'kara wa kanka matsayin da ya zarta komai ma"
Ya nisa ya ce "Ta ya ya?" Ni wallahii kaina daurewa yake yi".
Na juyo da nufin canja akalar hirar tamu na tarar da ya cinye meat pie din nan tas.
Na san da ma ma'abocin son snacks ne, domin kuwa ya fi son su fiye da abinci.
Na kaikaice baki na ce "Yaya Gudale mai abin mamaki".
Ya watso mini harara.
Na waske na ce, "Ba ka magana da matar gidan amma ka zo kana cinye mata abinci, na taya ka jin kunya".
Ya tashi da sauri yana ka'da 'yan yatsu alamun yin kashedi.
Da bacin rai ya ce, "Kina shiga hancina Guduyo! Ina jiye miki ranar da zan fato ki".
Na yi sukuri, sai kuma na ce, "Yi hakuri Yaya Sadik! Ni ai wasa nake yi maka, ba na son wannan harzukar da kake yi.
Anty Sakina ta damu da kai, kai ma ka sani, daga maganar fatar baki, sai ka gindaya dutse a tsakaninku irin haka?"
Ya zuba mini ido yana mini kallon takaici, amma hakan bai sa na karaya ba, na nisa a tsorace na ce, "Sakina mai son ka ce, mai 'kaunarka ce ba ta cancanci haka daga gare ka ba, saboda kawai ta yi maka fa'da irin na gyara kayanka".
Kafin ya ce wani abu ta shigo kicin din. Mamakinsa ya kama ta, ta hadiye fishinta a kansa ta ce, "Na Moriki barka da lokaci."
Ya dauke kai tamkar bai ji ba, bayan ni da na fi shi nesa da ita na ji ta.
Ta sake 'daga murya ta ce, "Na ji da'din ganin ka, da ma fita zan yi amma motata ta yi faci taimake ni ka kai ni mana".
Ido cikin ido ya ce, "Kar ki fara, don kuwa ba inda za ni, abin da yasa kika gan ni a gidan nan saboda maigidan 'dan abokin Abba ne na sani, ke ma kuma kin sani, ashe kuwa ina da dalilin shigowa, don haka kar ki yi zaton na kasa cika alwashin da na yi ne, kawai na gano ai ba gidanki ba ne."
"Yanzu ba ka ji kunya ba? A gaban budurwarka kake fa'din irin wannan maganar ta sokwaye?"
Ya tunzura ainun ya dinga nuna ta cikin rawar jiki ya ce, "Wallahi ke da Umma! Za ki san kin ce mini soko, za ki san kin mini 'kazafin ina da budurwa."
Yana kallon ta ya nuna ni da yatsa ya ce, "Ni kika jinginawa waccan abar ko?"
Ya girgiza kai cikin 'kunan rai mai tsanani. Ya fita fuu yana jaddada cewa ranar lahira sai Mai samaniya ya yi musu hukunci shi da Sakina. Sannan ta jira hukuncin duniya fishin Umma ke nan! Ya fice cikin shagwaba tamkar yaro 'dan 'karami.
Haushi ya turnike ni, wai ni ce waccan abar tamkar wata abin 'kyama. Takaicinsa mai tsananin gaske ya sha'ke ni.
Sakina ta juya tana azanci da fa'din, "*Sabo Da Kaza*".
Ta sake dawowa kicin 'din tana 'kir'kirar wata guntuwar wa'karta da take cewa "Ruwa cikin cokali ya ishe mai hankali ya yi wanka, ka rungumi wadda yake son ka, ba wanda ka san 'koshin wahala kake yi ba, ko wanda bai san darajarka ko ta makusantanka ba".
Na san da ni take, musamman da ita din ba ma'abociyar yin wake ba ce, hawaye ya 'balle mini. Na kashe gas, na bar kicin din ba tare da na kammala aikin ba. Na shige daki ina hawayen ba'kinciki. Tabbas da gaske son Yaya Sadik nake yi, irin son nan mai tsananin gaske. Na kuma san Sakina ba wai son ha'din ne ba ta yi ba. illa halin 'dan-uwanta take jiye mini, musamman da ba shi yake son ba. Ni kuma a yadda nake jin sa zan jure komai, ko da iyashegensa ya fi haka shahara.
Gayunsa, kyaunsa, ginshirarsa, da komai nasa suke yi ruda ni, hatta rashin kunyarsa kuwa.
Ba ni da wani lokacin da nake jin 'da'dinsa, na ji ni cikin shau'ki da farinciki irin idan ina tare da Gudale, ko da kuwa ba fararen lafazi zai mini ba.
Na nisa ina jin takaicin waccan abar da ya 'kira ni da shi, na sani ba yau ya fara kira na da sunayen cin fuska ba, don kuwa hatta Guduyo din da ya kama bakinsa na sani don na yi ba'kin ciki ne ya sanya ya za'kulo wannan sunan da ban taba jinsa akan wata bil'adama ba. Sai dai abin mamaki ni kuma son sunan nake yi musamman da shi ne ya lan'kaya mini yake kuma fa'da mini. Na dinga jin ba zan sake kula shi ba, har sai ya gane ni ba waccan abar ba ce.
Sai dai da kaina na dinga tambayar kaina ko zan iya wannan jarumtar? Domin duk abin da zai mini ana jimawa idan na gan shi zan hau masa magana, don 'karfin hali yana sha mini 'kamshi tamkar ba shi ya yi laifin ba.
Haka na kammala kwanakin hutuna a gidan Sakina, na fara shirin komawa makaranta.
Tirjiya na samu daga wurin Abba akan ba komawa makaranta har sai na tsayar da miji, da kyar ya bar ni bayan na yi al'kawari a cikin kwanakin zan tsayar.
Na shiga ru'du sosai, to ni wa zan tsayar?
Tabbas ba zan auri Alhaji Anas ba. Ina isa makaranta muka hadu da Munir, wani saurayi ne da yake nacin so na, ma'aikaci ne a kotun shari'ar musulunci. Ya 'dan manyata auren ne bai yi da wuri ba, masters yake a fannin Arabiya.
Sam bai yi mini ba, saboda ustazu ne na 'karshe. Sai dai kuma ba shi da makusa, sannan so na yake tamkar ransa, kullum sai ya zo Old Side saboda ni, duk da ba wani kula shi nake yi ba.
Muka gaisa a gajarce, ya dinga surutun na ba shi dama ya bayyana a gidanmu, a san da shi, idan Allah ya 'kaddara shi ne mijina zai yi farinciki, idan kuma bai 'kaddara ba zai ha'kura".
Na yi murmushi na ce, "In sha Allah za ka ji ni".
Muka rabu ina jin wani iri, a raina kam ba na jin son sa, amma kuma ba shi da wani kashin da za a 'ki son sa.
Sai dai da na tsananta nazari sai na gane son Gudale ne yake hana ni kallon duk wani namiji balle har ya burge ni.
A daddafe na yi sati ban nemi Yaya Sadik ba, shi ma kuma ya yi 'diban karan mahaukaciya da ni. Kan dole na gaji da fishinsa na dinga bibiyar sa har na samu ya huce yake kula ni. Bayan ya mini jidali iri-iri, wai don yana shiga shirgina ne yasa na raina shi, har nake ganin zan yi gaba da shi haka siddan.
Na dinga mamakin yadda ya fusata, ashe ya san raini ne ka dauki gaba da mutum daga maganar fatar baki? Amma shi yake yi da duk wadda ya shiga gonarsa, ko da kuwa kuskure aka hango yana yi aka yi gyara masa.
Da a ce Antin Zaria ba ta kammala sakandire aka yi mata aure ba, da ta haifi wanda ya fi shi, amma ba ya jin nauyin yi mata cin mutunci ko ya gan ta ido cikin ido ya dauke kansa.
Haka anti Maimuna, ko 'dar ba ya ji wurin keta ta. Bare kuma Juwairiya da yake ganin tamkar ba 'yar gidansu ba ce a dalilin tun kafin a haife shi aka bawa Yayar Kwalli ita. Shi har ya fi mutuntata 'kananun yayyensa Ramla da Sakina.
Duk da dai ba yadda za a yi su hadu da Sakina ba su yi fa'da ba, har yau fa'dan sa'ko da sa'ko ba su bar shi ba.
A cikin fa'dan nasu za ka fahimci wani irin so suke yi wa juna mai wahalar samuwa a yau. Ni shaida ce ba 'karamar 'kauna Sakina take yi wa Gudale ba, kai dukkan sisters 'dinsa ma kawai wulakancinsa ne yasa suke kaffa-kaffa da shi.
Kwana biyu a tsakani ya huce gaba'daya, ya yarda na shiga motarsa, muna dawowa a hanya ya ce, "Na samo lambar Nusy da kika 'ki samo mini".
Zuciyata ta buga da tsananin gaske. Na ce "Na taya ka murna".
"Ke ba kya murna na samo miki sister in-law?"
Na yi ya'ke na ce "Na yi mana".
Ya murmusa ya ce, "Muryarta me za'ki tamkar ta ki, kin san Ubangiji ya hore miki amo mai da'di, idan aka ji muryarki ta waya ba za a yi tunanin tu'ke'kiyar halitta aka bawa wannan muryar ba."
Idona ya ciko da hawaye, wai har haka 'kibata ta munanta ne ko kuwa a idon Yaya Sadik ne ta 'kazanta?
Na hakaito Nusaiba, siririya ce ta sosai tamkar Rahma Sadau a farkon shigowarta wasan kwaikwaiyo.
Na dinga tunanin ni kuma da wacce jarumar zan kwatanta kaina? A lokacin na dan fi jarumar Izzar so da ka'dan musamman daga 'kasa, amma yanayin farinmu 'daya hatta idanuwanmu, haka tsayinmu zai zo 'daya, kawai dai jiki zan 'dan nuna mata, a dalilin na zarta ta cikar 'kirji, da fadin 'kugu. Sai dai ita ma daga baya ta zo tana kibar sosai.
A fili na ce, "Hala dai kana mini kallon giwa saboda girma?"
Ya ja gemunsa ya ce mini, "Nan kusa kafin a samu me jikinki ai za a jima, shekarunki ashirin fa kike da wannan jikin, idan kika kai shekaru talatin kuma ai sai addu'a".
Wata irin karaya ta dinga shiga ta, hawaye ya goce mini, ina dauke su cikin dabara.
Har muka isa gida ban sake magana ba. Na shiga ban'daki na ci kuka na koshi, kishin Nusaiba ya fi maganganunsa ciwo a zuciyata. Kwana biyu ban yarda mun tafi tare ba, na yi sa a ma tafiya ta same shi zuwa Enugu akan wani darasi.
*Kina bu'katar canja kayan dakinki?*
*Kina bu'katar abaya ta zamani?*
*Kina bu'katar kayan kicin na alfarma?*
*Kina bu'katar siyan ginannen gida?*
*Kina bukatar samu gidan haya mai cike da tsaro?*
*Kina bu'katar siyan filin da ba zaki shiga matsala ba?*
*Tuntu'bi AMYAS NEW & FAIRLY USED*
*CIKIN AMINCI DA SAUKAKKAN FARASHI* 08083909947.
Bai dawo ba sai da ya shafe sati guda. Sosai na yi kewarsa, na dinga murnar dawowarsa na manta da komai. Ranar wata litinin tana cikin jerin ranakun da ba na mantawa da su saboda irin tozarci da na sha a wajen Gudale. Sanyin safiya muna tafiya zuwa B. U.K. mun zo daidai 'Danagundi danja ta tsayar da mu.
Na zuba masa ido ina masa kallon tsaf! Wani irin al'amari ya dinga keta dukkan sassan jikina, kwalliyar da ya yi cikin tsadaddun kananun kaya sun matu'kar yi masa kyau, 'kuruciya sosai a tare da shi.
A lokacin bai jima da yin birthday dinsa na shekaru 28 ba.
Ya juyo muka hada ido, na waske na dauke kai.
Bai yi magana ba, ganin ya daina kallona yasa na ci gaba da 'kare masa kallo ina tasbihi ga Ubangijin da ya kyautata halittar Yaya Sadik. Ban sani ba ko matsanancin son da nake yi masa yana da ala'ka da kyansa da nake gani sosai.
Dan tsurut da shi sai 'daukar hankalin 'yammata musamman ma ni. Yanayinsa a wancan lokacin ya fi kama da Ramadan Both din shekarun baya. Kafin ya yi 'kiba.
Mun zo daidai 'Kofar Famfo danja ta sake tsayar da mu. Na ci gaba da kallonsa, ba zato ya ce "Oh ni Guduyo saboda Allah wane irin kallo kike bi na da shi haka? Ba na so, ni gaskiya ki daina tsorata ni haka".
Na nisa cikin borin kunya na ce, "Wane irin kallon ka kuma? Shin kai din tauraro ne ko me?"
A kufule ya ce, "Ban son rainin wayo! Ina ce sau uku ina kama ki kin kafe ni da ido?"
Cikin shau'ki da subutar baki na ce, "Kai mai kyau ne fiye da farin wata, bakinka ya dace da gemun nan da ka tsayar, ka iya zaben turare mai nutsar da zuciyar mai bege, komai naka cif tamkar kai ka za'ba".
Ina rufe baki na ji ya dauki salati, idonsa ya canja sosai, saboda bacin rai ya ce, "Ashe ke 'din lalatacciya ce Guduyo? A gabana kike yabon kyaun halittar namiji? Kaicon ki! Zan fa'da miki da babbar murya, ni Saddi'ku 'kwalelenki, ba kya cikin jerin matan da zan nuna wa duniya su, asalima kunya zan ji a ce ke 'din matata ce.
Amma zan fa'da wa su Abba gaskiya su yi gaggawar mi'ka ki 'dakin aure kafin a wayi gari a ga kinfi haka fitsara, Dan l ji tsoro ma Kika bani, Dan kuwa zaki iya shammatata ki danne ni".
# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee
# Ana tare🤝
2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺
*NA*
*SURAYYA DAHIRU*
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(�?)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?
*Masu son karanta cikakken labarin babu yankewa ku biya 500 kudin karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 08032773332*.
*Tunasarwa*
*Ina Jin koarafin cewar typing yana yin ka'dan.*
*Ina bin umarnin kungiya ne na kada shafi ya wuce yawan allon comfuter biyu. A hakan kuma ina yi muku yawan allon comfuter uku ne.*
*Amma in sha Allah za'a duba korafinku. Zuwa gaba*
*Na gode sosai da yabawarku, da soyayyarku*🤝
*Page 13&14*
Hawaye ya 'balle mini, wani irin takaicinsa ya mamaye mini 'kalbi. Cikin murya marar amo na ce, "Ni ka jefa da wannan 'kazaman kalmomi irin haka?"
"A to 'kazafi na yi miki? Ban da lalata har kin san siffofin maza? Amma na gane ba ki da laifi, sakacina ne da nake bibiyarki nake zama sakarai a gabanki".
Na kasa bu'de baki na ce masa uffan a dalilin bacin ran da yake raina mai girma ne.
Har muka isa makaranta ya tsaya a inda ya saba ajiye motar ban ankara ba.
Shirun da na ji ya yi yawa ne, ya sanya na 'dago fuskata jage-jage da hawaye amma na kasa furta kalma ko guda.
Na yun'kura na 'dauki jakata na bu'de kofar amma na ji ta a rufe, na juya na kalle shi ya ha'de girar sama da ta 'kasa.
Na san nufinsa, tunda ya sanya mini dokar da ta zame mini ka'ida kullum muka zo sai na yi masa godiya da fatan alheri don na gane shi ba direbana ba ne.
Tun ina yi cikin iyashege da mamakin son girma irin nasa, har na dawo ina yi cikin farin-mciki da shagwa'ba.
Amma a wannan ranar sai na ji sai dai komai zai faru ya faru din, amma ba zan gode masa ba, bayan ya gama tozarta ni.
Fiye da shudewar awa guda muna zaune cikin motar, dukkanmu mun rasa darasin wannan lokacin.
Ya hassalo sosai ya dube ni ya ce, "Ke ba na son iskanci kin ji! Za ki yi abin da ya kamace ki ko kuwa?"
Yana rufe baki na ce "Ba zan yi ba".
Ya sake harzuka ya ce, "Guduyo ki shiga hankalinki, bar ganin ki haka zan yi miki duka, zan karairaya ki na watsar da 'kasusuwanki a ruwan 'Bagwai".
Na share shi ina jin yau dai kam bai isa na bi shi ba.
Ya bu'de murya ya ce, "Idan na 'kirga uku ba ki yi dalilin da kika fitar mini daga mota na daina kallon ki ba, za ki yi mamakin abin da zai same ki".
Ban san lokacin da tsaki ya subuce mini ba. Na ce "Allah yasa gadar Zurmi za ka kai 'kasusuwan nawa ka zubar. Ba na tsoron mutuwa, Ubangijin da ya 'kagi mutuwa ka'dai nake jin tsoro".
Ya yi matu'kar ka'duwa ya kalle ni ya ce, "Ni Abubakar Sadik kika yi wa hakan?"
Na dauke kaina ba tare da na tanka masa ba.
Ya nisa ya ce, "Wallahi matu'kar ba ki yi godiya ba, za ki 'dan'dana kudarki a hannuna, sai hakan ya zame miki sanadin kuka mai yawa, don kuwa zai zama dalilin da ba zan sake yi miki sassauci ba. Kaf gidanmu ke ka'dai kike shiga hancina na dauke miki kai, amma tunda na gane ke din tabbatacciya ce zan gwada miki 'karshen tsageranci! Kumbusar banza kawai. Na fa'da miki da babbar murya duk jarabarki wallahi ni dai kam 'kwalelenki".
Na daure na hadiye kukan da ya zo mini na ce, "Ko ina danne maza ai ka san dai kai sai dai na matse ka, domin ka yi mini ka'dan, yo ni maza irinku ma marasa zati mene ne abin burgewa a tare da ku ne?"
Ya kuwa zabura ya dam'ke gashin kaina da ya sha dauri da ribbons da 'karfin gaske.
Sosai na ji zafi amma na 'ki nunawa bare