Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
ne Abba sai dai a haifesu a rainesu, sai kuma a bada aurensu suma suje su yi ta haihuwa da raino. Idan suka yi rashin sa'a suna haifar ya'ya mata shikenan sun zama marasa daraja, tunda basu haifi wadanda zasu zama garkuwa a gida ba".
Na karasa cikin kuka na tashin hankali.
Ya yi shiru ya kasa magana, tsawon lokaci ina gunjin kuka bai ce kala ba.
Sai da na nisa dan kaina ya ce "Yi salati Halimatu zuciyarki ta nutsu."
Na dinga salatin kuwa, har na dan sami nutsuwar.
Ya sassauta sosai ya ce "Ki bude zuciyarki da kunanki ki ji ni da kyau, wata'kila wannan ce maganar da zan fa'da miki ta karshe da zata jagoranci halin duk da zaki samu kanki a rayuwarki".
"Haihuwar ya'ya mata daraja ce da ba kowa ke rabauta da samunta ba. Duk wanda kika an jera masa yara mata Ubangiji ya so shi da alheri mai yawa. Hadisin nan na Annabi(S.A.W.) ka'dai ya isa ya nutsar da zuciyar iyayen y'a'ya mata. Annabi ya ce Aljannah ta tabbata ga wanda ya haifi mata uku ya kula da tarbiyarsu har zuwa aurensu.
Shin wacce daraja ce tafi wannan?"
Bai jira ni ba, sai ya zarce da cewa "Bayan haka Halima halittar mace ta wuce ace bata da daraja domin duk namijin duniya an wajaba masa neman aljanna a kafar uwarsa. Shi kuma matarsa ta yi masa biyayya, bayan an dora masa nauyin cinta da suturarta, da maganinta, da kuma kare mutuncinta. Amma shi kuwa cikin kowanne bigire aka ce yabi uwa, yabi uwa. Duk kuma tumbatsa da kasaitar namiji da za'a ce wancan mutuimn bashi da aure sai kin ga darajarsa ta fa'di saboda babu mace a tare da shi."
Ya nisa ya cigaba da cewa
"Kada ki yarda a cusa wa zuciyarki dabi'u irin na jahiliya da har yanzu jama'ar da suka samu ilimummuka suke jahiltar lamarin.
Duk wanda yake da ya'ya mata yana da arziki mai yawa.
Na farko zuri'arsa zata yadu da wuri.
Sannan ku a halittarku Ubangiji ya sanya muku jin kai da tausayi.
Duk sadda kika kalli ya'yan da Allah ya baki sai ki hango ni."
"Ai nima su ya bani, na kuma gode masa da dukkan zuciyata, shi kuma sai ya shirya mini su, ya daukaka su. Na yi imani ko ban tara arzikin da Ubangiji ya sanyawa albarka ba. Antinku ta Zaria ka'dai ta ishe ni jari.
Sakina kadai idan na kalleta sai na tsinci kaina da cewa Ubangiji ka bani, ka sake k'ara mini na gode. Domin Sakina ita ka'dai tana daidai da wasu mazan ashirin.
Har yau din nan Halimatu ba wanda ya san cewa tun shekaru goma da suka wuce duk abin da ake saukewa a gidan nan da kofar Baban Yara har ma da kofar mijinki da yake fankamar namiji ne cewar Antinku ce.
Komai na bangaren kayan abinci da ake sauke wa babbar mota guda duk bayan wata uku, ita ce.
Har yau din nan tunda Sakina take aiki ban kara siyan ruwan da nake sha ba, duk yawan ruwan robar da kike ga ni a gidan nan ko a wajen Baban Yara bamu muke siya da ku'dinmu ba."
Mijin Ummu kuwa ba abin da baya yi. Duk da yasan mu din ba mabu'kata bane, sannan kwai da kajin da take sana'a kina ganin yadda ake shigo wa da su Kamar banza.
Ga Juwairiya itama tana iya nata kokarin, sannan ko yara nawa zan bata takardunsu da nufin ta nemo musu gurbin karatu zata nemo koda kuwa ba a makarantar da take aiki ba.
Ramla kuwa anan ta zo ta tsugunna ta ce "Ta dauke mini yiwa uwarsu sutura, tana yin kuma na alfarma, sannan tunda take aiki a NEPA ban sake biyan ku'din wuta ba.
Gaki kema fara aikinki kullum naki abin arzikin a tafe yake.
Dan haka duk abin da zaki yi, ki saka Allah! Ki yawaita istigifari, ki kuma tsananta yin godiya ga Allah.
Idan kin tashi addu'a ki tsananta fa'din Ubangiji ka sanya albarka a cikin duk abin da ka bani, na dukiya ko na zuri'a.
Baban Yara da Ubangiji ya bashi mazan a jere ai tare ya bamu, muka yi sa'a kuma ya shirya mana su, kowa yana ri'ke da kansa da iyalinsa, suna kuma iya kokarinsu na tallafin abin da zasu iya, sun kuma zame mana garkuwa, kuma abin ado, domin kuwa tabbas da namiji yakan zama garkuwa a gidansu amma idan ya zama a cikin nutsuwarsa.
Dan haka ki yi ta haihuwar ya'ya mata cikin farin-ciki da godiya! Ga Sakinanki nan ta haifa miki mazan da na tabbatar zata saka su yi miki abin da zasu yi mata na alheri. Idan kuma ya kaddara kin samu namijin to kada ki yarda ki bashi wani matsayin da ya wuce na yan'uwansa domin dai d'a gaibu ne, kowa da irin baiwarsa. Muhimmi kawai ka yi wa kowa adalci ta hanyar yi musu tarbiya mai kyau, a basu dukkan nau'in ilimi, a kuma bisu da addu'ar shiriya. Amma nuna fifikon nan da galibin iyaye suke yi idan sun samu namij bayan an haifi mata da yawa yana matu'kar taka muhimmiyar rawa wajen damalmala tunanin yaron wanda galibi sai ki ga sun zama rudeness ta yadda su kansu basu amfani kansu ba, bare su amfani waninsu"
Ya nuna kansa bayan ya numfasa ya ce "Nima victim ne Halimatu! Ba wani boye boye, amma Ubangiji ya sani na iyakacin kokarina akan Sadik! Amma uwarsa bata fahimta ba, tarbiya kuma ko ana so ko ana ki mafi yawa ta uwa ce.
Tasirin uwa mai yawa ne akan danta. Sa'a daya da na yi, da Ubangiji ya tsare shi daga lalacewar zuciya, tunda yana sallah akan lokaci, sai nake da yakinin duk abin da yayi masa rauni da sannu Ubangiji zai daidaita masa. Sannan an yi sa'a yayi karatun da zai iya ri'ke kansa. Amma ai baya ciki bangon gidan nan. Sai dai kuma bis adalci shi yake saka mana katin waya tunda ya fara aiki. Sannan yakan siyo mini ice cream da yogurt tsabar shiririta".
Ya murmusa ka'dan ya ce
Wadannan misalan ya isa ya kwantar miki da hankali, ki fahimci gatan da Ubangiji zai yi miki a gaba. Domin idan kika yi musu tarbiya, suka sami ilimi ina tabbatar miki nan gaba kin huce takaici mussaman da yake Ubangiji ya cika galibin zuciyar y'ay'a mata da alheri da jin k'ai".
Na samu nutsuwa sosai da kalamin Abba. Nauyin da kirjina ya yi a dalilin tsoro da firgici ya yi sauki. Amma kishi sai babbako mini yake ta inda duk ban yi zato ba.
Na sauke ajiyar zuciya, amma hawaye na tsere na ce "Allah ya baka lafiya Abba! In sha Allah da sauran nasihohi da zaka mini a gaba masu yawa."
Ya murmusa ya ce "Shekaru fa sun tafi Halima! Ko babu cuta ai ni kaina na sani nesa ta zo kusa.
Duk wani ni'imomin duniya Ubangiji ya cika mini su."
Ya nisa ya ce "babban burina shine na cika da imani. Ina muku fatan ku yi rayuwa cikin salama da tsantseni".
Ya fito da waya ya kira Yaya Gudale da bai jima da fita ba.
Ya ce "ka dawo yanzu nan".
Ya kashe ya kira Baban Yara shima ya ce ya zo yanzu.
Ba a dauki lokaci mai yawa ba suka shigo a tare, tunda dama tare suke.
Suka zauna Abba ya dinga fa'da akan me yasa ba'a sanar da ni auren ba har zuwa yanzu alahalin ina da hakkin na sani.
Dukkansu suka yi shiru. Domin sun tabbatar ba wanda ya sanar mini a cikinsu.
Na dinga kallon su tamkar zautacciya Ubana da mijina sun boye mini za'a mini kishiya.
Na sunkuyar da kai ina sake fashe wa da kuka.
Sosai jikin Baban Yara ya yi laushi tubus, kukan nawa ya dinga taba shi, ya rasa karsashin da ya shigo da shi.
Sosai kukan ya shige su Abba ne ya ce "Ashe kuma daga kai har d'an naka baku sanar mata maganar auren ba har zuwa yau da ya rage mako biyu".
Baban Yara ya kasa magana. Yayin da Gudale ya ce "Na zabi na boye mata ne dan kada ta tashi hankalinta, ina son sai saura sati daya haka. Yanzun da ta ji baka gashi nan duk ta birkice ta ki'dima ba".
Abba ya girgiza kai ya ce "hakane sai dai kuma za'a daga auren har sai nan da wata biyu idan ka fa'da wa matarka ka kuma kwantar mata da hankalinta sai a saka rana."
Yaya Gudale ya yi shiru cikin bacin rai.
Yayin da Baban Yara ya ce "Ha'kuri zaka yi! Ai bai kyautu a daga aure babu wani gamshasshen dalili ba. Ba girmanmu bane".
Abba ya yi shiru yayin da Baba ya dinga bashi ha'kuri.
Ya kalle ni ya ce ",Ki kwantar da hankalinki Halimatu! Karin aure halak ne matu'kar mutum yana da dama, kuma zai yi adalci. Sadik dan-uwanki ne na sani ba zai cutar da ke ba".
Na kalli Baba kamar na ce cutar wa kuma na nawa?
Sai kawai na daga kai na ce "Hakane Baba! Na gode Allah ya sanya alkhairi."
Na juya na kalli Abba na ce "Na gode sosai Abba Ubangiji ya baka lafiya, na gode kwarai da gaske. Amma ka yi ha'kuri abar Baba da Yaya Sadik da ra'ayinsu"
Na fa'da kuka na sake kwace mini.
Tsawon lokaci kowa ya kasa cewa komai hatta Yaya Gudale kansa ya yi laushi sosai.
Na nisa na ce "Abba zan tafi mu yini lafiya."
Na tashi na tafi yana ta sanya mini albarka, yana kuma neman mini tsari daga dukkan abin ki.
Na fito na dan labe ta bayan windo na ji yana ta fa'da akan abin da Gudale ya yi.
Ya daga murya ya ce "Sadik idan ka cuci yarinyar nan alamuranka baza su daidaita ba. Anan kusa ban san yarinya mai yin soyayya dan Allah irin ta ba. Ban san mai ha'diyar ba'kin ciki irin nata ba. Sanin kowa ne zama da kai sai wanda ya shirya, sai mai ha'kuri kwarai da gaske."
Tari ya sarke shi. Ya ce "Bana son auren amma Babanku ya mini fin karfi ya nemo maka, dan ya nuna mini ikon da yake da shi akan ka. Bude kunne ka jini Sadik, shine fa ya haifi Halimatu. Shine ubanta, ko na mutu idan ka ruguza mini zumunci ka tabbatar hakan na nufin rugujewar al'amarinka gaba'daya. Har yau ban haifi d'an da ya mini biyayyar da Babanku ya mini ba. Ina jan kunnenka Sadik ko bana raye biyayya biyu zaka yi masa, da wacce zaka yi mini da kuma tasa ta karan kansa."
Baba ya ce "Ba zaka ma ka mutu ba Abba! Muna tare sai mun sake turawa."
Abba ya nisa ya ce "bar ni dai na dinga fa'din abin da yake raina saboda yanzu mutuwa ko babu jinya yinta ake yi. Bare ni da take ta nuna mini alamu."
Ya sake numfasa wa ya cewa Baba ka hado minl zamu tattauna in sha Allah"
Baba ya amsa da "In sha Allah".
Na wuce daga haka na barsu.
Tafe nake ina jin wani irin zugi a zuciyata.
Na doro alwallah na dinga sallar da ban san me nake fa'da ba.
Wani irin azabben kishi mai saka ciwon kirji.
Na dinga kuka a sujjuda na kasa cewa komai. Tsawon lokaci kafin na iya cewa Allah ka taimake ni, Allah ka sassauta mini, Allah kada ka saka ta sha gabana.".
Na dago na tarar da shi a bakin gado ko shigowarsa ban ji ba.
Dana sallame nake tashi na sake tayar da wata, karon farko a rayuwata da na fara jin ban son ga ni ko jin kalamin bakinsa.
Yana zaune bai gaza ba, har ni na gaza na zauna.
Ya saussata ya ce "Kin kai karata akan ban sanar miki zan yi aure ba. Ni kuma cikin adalcina da tausayina ne ya sanya ban fa'da din ba. Domin na sani zaki tayar da hankalinki ki zube a banza".
Na zuba masa ido ina kallonsa cikin fitar hayyaci. Na rasa gane me nake ji gaba'daya.
Ya sake cewa "Yarinyar bata da fitina haka take innocent kamar ke. Sannan ko kin girmeta ba zai wuce da one year ba. Kin san ni adali ne ba zai yiwu na bari sai kin tsufa sannan na dauko miki yarinyar da dole sai ta kere ki a shimfida saboda kuruciya ba. Amma yanzu competition zaku yi, idan kin fita hikima ma shikenan.
Dan haka share hawayen ki. Kinsan kuma tunda aka miki aikin nan kusan wata biyu na barki ki dan gyagije. Amarci nake son na fara tun daga yau.
Hawaye ya sauko mini. Na kasa cewa uffan. Ya sassauta ya ce "Ban son irin wannan kukan Guduyo! Kin sani bana so".
Murya ba amo na ce "Nima bana so din, bani nake yi ba. Zuciyata ce take yi."
Ya ce "To wanne irin abu take yi hakan? Akan me zata dinga wannan kukan bayan ta sani, na damu da ita, na kan shiga tasku idan tana cikin bacin rai?."
Na zuba masa ido sosai har ya tsargu.
Na dauke idona ba tare da na ce komai ba".
Ya yi matu'kar tsargu wa ya sauko daga kan gadon ya ri'ke hannuna ya ce "Guduyo".
Na kalle shi ba tare da na amsa ba. Ya ce "kar ki bari ki shiga wasi wasi a kaina kin sani dai ina son ki, kina da muhimmanci a rayuwata.
Na dauke kai na ce "Hakane! Tunda kan Antin Zaria har Sakina. Babu mai kishiya sai ni. Tunda kan Yaya Abdallah har zuwa Yaya Al'amin babu mai mace biyu sai kai. Na sani su dukkansu sun sami son ransu, ni kuma ba type dinka ba ce . Dan haka dole ka samo taste d'inka kuma baka yi laifi ba."
Ya sake tsananta ri'kon da yayi mini ya ce "kada ki fassara da hakan".
Na cije na ce "Am sure haka ne! Ina yi maka fatan alheri, ina fatan ta kasance uwar mazaje dan ta da'de tana jan zarenta".
Ya ce "Ameen Guduyo, kinsan addu'arki ana karba. Amma kema kina jan zarenki, kinsan dai I really love you. Karon farko da ya fa'da mini wannan kalmar babu zagaye zagaye. Sai dai bata mini da'di ko ka'dan ba, domin bata zo a sadda ta dace ba. Bata zo a mini a sad'arar da ta kamata ba, domin ya fa'da a dalilin na yi masa addu'ar da ta yi masa da'di ne. Ya kuma riga da ya yi imanin ina da zafin yawu.
Na sake kallonsa na tabbatar wannan rarrashin da yake mini har da bu'katar kansa da yake son saukewa.
Yayin da ni kuma kishi ya turnike ni. Na ji ko kadan bana sha'awar wannan al'amarin ya je na bar wa Munubiya.
Na mi'ke, shima ya mike ya ce "Abba dai ya ce "Kada na musguna miki, na roke ki kema kada ki bari kishi ya saka ki zalunce ni."
Murya na rawa na ce "Har abada ba zan iya zaluntakar ba Yaya Gudale. Amma na rokeka ka barni na samu nutsuwa, ka bar ni na yi fama da bakin cikin da yake nukurkusa ta".
Na karisa kuka na goce mini.
Ya yi shiru jikinsa ya mutu sosai.
Ya ce "so kike kawai sai raunina ya bayyana Guduyo. Menene na wannan kukan saboda Allah? Gutsurata za'a yi ne, ko me? Saboda sanin ina da muhimmanci a wajenki shiyasa nima na yi miki adalci ban dauko miki yar karamar yarinya ba. Na fa'da miki fa warinki ce. Kin ga ai gogawa zaku yi. Sannan na rantse miki ita ba Guduyo ba ce, ba kuma jinina ba ce".
Hawaye na zuba na ce "Amma ita zata haifa maka boys ko?"
Ya ce "kema kafirin taurin kai ne da ke, ban da haka tunda kinsan kina cikin kebantattun halittun da ake amsa addu'arku me ya hana ki yi addu'a ki haifo mini boys din? Amma na lura kwata kwata baki damu ba".
Na rausayar da kai na ce "Ban damu ba ko ka'dan! Idan na tuna Abbah da ahalinsa sai na ji ina alfaharin sawunsa dana tako."
Ya hassalo ya ce "Bar ganin ina rarrashinki! Wallahi this wil be the last time da zaki sake tsayawa a gabana ki fa'da mini iyayena kika gado. Billahillazi sai na miki abin da zaki yi kuka na gaskiya. Domin wannan kukan duk na jin da'di kike yi fitannaniya tabattacciya kawai. Dama na fa'da miki gorin da kika yiwa Umma ba zai tafi a banza ba, to ta zabo mini wacce ba zata ta'ba yi mata gori ba, kuma na karba da dukkan zuciyata, domin ta dace da ra'ayina."
Ya fice ya barni ina zubar da k'wallah.
Wannan ranar tana cikin mafi tsaurin ranaku dana fuskanta a duniyata. Na ga tsayinta kwarai da gaske. Ana idar da sallar isha ya dawo, falo ya tarar da ni, domin zaman dakin ya gagare ni. Rabon da na ganshi a gida a irin wananan lokacin na manta.
Kallo daya na yi masa na gane yana cikin matsuwa ne.
Na ki yarda na kalle shi a dalilin ina cikin ba'kin ciki mai yawa.
Dake yana neman hadin kai sai ya lankwashe harshe ya ce "Tunda na fita nake ta tunanin ki, takaicin kaina ya kama ni. Na ji ina ma ban daga miki harshe ba. Domin na hakikan ce kina cikin yanayin da kike bu'katar rarrashi da tarairaya daga gare ni, very sorry Gudidina".
Maimakon na ji da'din kalamansa ko na sami sau'kin *HALIN YAU* din da nake ciki sai kawai na ji tamkar yana watsa mini garwashi ne.
Kishi da kuma ganewar da na yi akwai abin da zai biyo bayan wannan kwantar da kan da ya yi, ba wai dan ya damu da halin da nake ciki bane.
Ya turo mini ledar hannunsa gabana ya ce "gasashhiyar k'odar da kike so ce."
Ban dago ba, bare na kalle shi ko na bude na ga ni.
Ya mike ya na cewa bari na dauko miki fork da plate Maman Amnah".
Bai jima ba, ya dawo da ya zauna daf da ni.
Ya juyo mini ita gaba'daya.
Bayan ya fito da fresh milk daga leda.
Ya sani a jikinsa sosai.
A da idan ya mini irin haka sai na jini tamkar sarauniya, zuciyata ta cika da shauki da bege.
Amma a yau ban da suya babu abin da take yi mini.
A baki ya yi nufin bani, amma na ki na karbi fork din, na fara ci da kaina.
Sai dai sau biyu kawai na kai bakina na ajiye a dalilin bakin babu da'di tunda zuciya a cunkushe take.
Ya zuba mini ido sosai ya ce "Duk wahalar da na sha dan na dada miki, ba zai sa ki ci dan na ji da'di ba?
Haba Guduyona".
A hankali na ce