Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   33 / 61

96K to 99K   out of 180.1K words

'karama ki ri'ke a hannunki. Bana son na kira ki, na kasa samun ki sai na ji tamkar zan rusa ihu ne.
A hankali na ce "Da ka barta kada Abba ya ce "Ina na samu waya?"

Ya yi tsaki ya ce wai ke dal'kiyar ina ce? Ace babu sirri tsakaninki da mijinki?
Guduyo ki kiyayi bata mini rai a cikin wannan halin da nake ciki".
Na sassauta na ce "Allah ya baka ha'kuri".
Dai dai nan Abba ya turo kofar dakin ya shigo.
Ya yi turus ganin Gudale a zaune dirshan sannan yanayinsa ka'dai ya isa ya fahimtar da shi halin da yake ciki.
Na shiga gaishe shi a Kunya ce. Ya amsa mini babu walwala kamar yadda ya saba yi mini a tsukun nan a dalilin na ki sakewa kamar yadda ya ke so.
Ya kalli Gudale da ya ha'de girar sama da ta 'kasa.
Shima ya sake daure fuska sosai ya ce "Sadik zo ka fice mini, na haramta maka shigo mini cikin gidan nan, har sai ka shirya.
Ya mi'ke yana ha'da hanya na sani zuciyarsa tamkar ta yi bindiga. Yayin da ni kuma hawaye ya fara zubo mini.
Yana ficewa Abba ya rufa masa baya ba tare da ya rufo mini kofar ba.
Ina Jin Yaya Gudale yana cewa "Dan Allah Abba! Kar ka bari dukkan raunina ya bayyana, idan maganganun da na fa'da a gaban Yaya ne suka sake tunzura ka, dan Allah na yi tuba, na janye su, 'karya nake yi, a mini aikin gafara yadda aka saba. Ka hanata koma wa, yanzu kuma ka ce kar na shigo maka gida alhalin iyalina suna cikin gidan. Ni yanzu idan ban ji motsin yadda *Wakili* yake ba, tashin hankalin yawa zai yi mini".
"Waye wakili kuma?"
Abba ya tambaya cikin mamaki.
"Wakilinka mana Abba! To abin cikin kwai dinka, ma'ana ajiyar dake cikin Guduyo".
Abba ya rasa me zai ce masa sai kawai ya yi tsaki ya ce "To kuma idan Magajiya ce fa?"
"Abba tabbas na sani uwa mai daraja ce amma a wannan sa'darar magajinka nake so ya fara iso wa. Ta yadda zan sanya masa sunanka. Domin so nake daga siffa har halayyarka ya yi wuf da su. Amma ba zan so idan an yi masa kuskure ya ce sai an dawo masa da abin da ya yi na alheri da neman yardar Mahallicci ba. Abba idan ba zan rufe ka ba. Wato Ubangiji ya maka baiwa da tarin falaloli. Kana da nagarta! Na yarda ban kyautata ba, amma ka wuce ka ce na biya ka hidimar da ka yi mini, Allah ya kewaye ka da ni'imomi daban daban. A duba Halin da nake ciki a yi mini sassauci, zan yiwa bakina linzami wa Billahillazi subutul kalam na yi".
"Sai fa ka dawo mini da kuda'dena duk siyasarka, dai-dai da ku'din sadaki sai ka dawo mini da shi."
Takaici ya ciyo Gudale ya ce "To shikenan Abba! Amma ka bani lambar wayar wanda ka bawa ya mini waliccin auren."
Akan wanne dalilin? Me yasa baka tambayar lambar dan ka gaishe shi ba sai yanzu?"
Ni kawia fa'da masa zan yi ya turo ku'din waliccin da ya yi mini, tunda zan biya9 sadakin aurena to kamata ya yi na na waklici kaina da kaina, dan haka sai ya turo mini ku'din da zan rage maka bashi.
Abba ya zuba masa ido sosai ya kasa yin magana.
Ya ce "kome zaka yi dai ka je ka yi, riba kuma ba zaka ci ta ba. Na kuma fa'da maka kada ka sake shigo mini gida wallahi! Matu'kar ba kudin nan ka samo ba, bana bu'katarka a cikinsa, idan kuma ka kafe zan dau mataki akan ka da wadda zata barka ka shigo mini gida".
Ya fice cikin sauri yana cewa "Na dai roki arzikin a mini gafara. Amma dole sai an zubar mini da 'kimata ta namiji a idon matata".
"Allah ya shirye ka Sadik"
Abba ya furta cikin wani irin yanayi.
Kwanaki biyar suka shude ba tare da mun ji ko da murya juna ni da Gudale ba.
Idan na ce ba a cikin damuwa nake ba na yi 'karya, mussaman da ya kasance ko gaisuwata da kyar Umma take amsawa.
Bani da matsalar komai amma babu sukunin zuciya, babu kuma walwala, tunda Abba ne kawai yake kula ni.
Rannan sai ga Sakina kamar jifa. Ina ganinta na fara kuka, ita kuma ta dinga dariya tana cewa "Halimatu tattbara". Dariya ta kama ni, ina dariyar hawaye na zubar mini, ina kuma cewa "Ni wlh na gaji tafiya dakina zan yi"
Ta make kafa'da alamun ko oho ta ce "Ai na gane ki kuma. Duk wani iyashegen mijinki kin kwashe su tsaf, ba wanda kike yiwa iskanci sai ni. Yanzu ma tashi ki tafi".
Na zum'bura baki ina kunkunin ina cewa "Abar ni kawai".
Kafin ta yi magana wayarta ta dauki kuwwa. Har ta katse bata dauka ba, sai da aka da aka 'kira sau uku sannan ta dauka a yangance ta kunna hands free ta ce "Na rantse maka Na Moriki ka uzzira mini haba".
Ina Jin yadda ya marairaice ya ce haba Anti Sakina! Ina ce dai dazu ma sai da na yi ta ro'kon ki, dan Allah ki daina yi mini hakan bana jin da'di, kin san dai bani da kamar ki ko?".
Ta yi murmushi ta ce "Haka fa! To fa'da mini ni da Guduyo wacece a gaba?"
Sai kuma ya bu'de murya ya ce "wacce irin tambaya ce ne wannan? Kinsan dai kowa da matsayinsa. Ina ce yanzu d'a zata haifa miki Sakina?
Kawai kowa da matsayinsa, dukkan ku jinina ne".
Sosai dariya ta kwace wa Sakina ta ce "Na Moriki manyan duniya".
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Sakina zaki mini taimakon nan, ko ba zaki yi mini ba?"
Ta ce "Sakina ko?"
"Anti Sakina na ce fa" ya fa'da a gajiye.
"Zan bata mana yanzun haka ina gidan ma".
Ya sake kaurara murya ya ce "Amma ba a dakinta kike ba yanzun?"
"A a ina kicin ne"
Yauwa Anti! Yadda na fa'da miki hakan zaki yi kin ji my dear sister. Kawai ki kira ni ki ce ga Guduyo ku gaisa, sai ki 'dan bamu space please and please Yayar auta".
"Amma ka yi al'kawarin ka daina mini rashin kunya ko?"
Da sauri ya ce "Dama kinsan ai ke ta daban ce a wajena kawai dai Allah ya sanya yadda muka makwabci juna a wajen haihuwa, Allah yasa a aljannah ma hakan ne".
A sanyaye ta ce "Ameen Namorikina".
Sai ta kashe wayar ina kallon yadda take wani irin farin ciki mai fitowa daga kasan zuciya.
Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, ta kira shi din, ta bani wayar. Ta fice zuwa wajen Ummah.
Na sanya wayar a kunnena, na yi masa sallama.
Ya amsa da wata irin murya da ni zan fahimci manufarta kawai. Ya lankwashe harshe ya ce "Guduyo tausayinki nake ji, bana son na yi miki sharing 'dina da wata, amma duk an rufe ido an ki gane halin da nake ciki. Kuma abin takaicin ma wai har da ke za'a ha'da kai, yanzun sai ki bada gudunmawar jefa ni a cikin tasku?"
Murya na rawa na ce kasan dai abin ne yafi karfina. Nima ba yadda zan yi ne. Ba dan Abba bane a cikin maganar ai da sai dai a ga lefina a banza."
Ya sake kashe murya ya dinga fado gunduma gunduman kalmomi masu nauyin bayyana wa, yayin da suke shiga jikina suna tasiri, soyayyarsa tana sake tunbatsa a zuciyata. Kewarsa ta kewaye mini gangar jikina. Na dinga murmushi ina shure shure akan gadon saboda yadda muryarsa da manyan kalamansa suka kidima ni, suka sanya ni cikin bege mai yawa.
A kasalance ya ce "*Hala*"
Tsigar jikin ta tashi, harshena ya yi mini nauyi na kasa amsa wa.
Bai jira amsar tawa ba ya ce "Kar ki bada kofar da za'a sanya miki shubuha a kaina. Kin dai san da bana son na rayu da ke ba zan baki ajiyar Babina ba ko?"
Da kyar na ce "Eh"
Ya ce "To ki cigaba da kallona a matsayin da kika bani, kar ki yadda a shigo tsakaninmu. Ke din matata ce da Ubangiji ya saka aka bani ke da karfin tuwo ba dan ana so a bani ba. Sannan ke din Allah ya za'ba ki zamewa 'yayana uwa. Kinsan kuma na gode Allah ko?"
Na yi shiru! Domin ban fahimce shi ba. Gane hakan da ya yi sai ya ce "Da ban gode wa Allah ba ai ba zan damu da ke ba, yanzu menene bana miki Guduyo? Har a cinya nake dora ki ko?"
Na ce "Eh!
"Yauwa to ko goyon ma da kike son na dinga yi miki idan kin haihu zan fara gwadawa kin ji. Sannan kuma ba ni, ba kallon yan mata. Ai na san ba kya so ko?"
Da sauri na daga kai, sai kuma na ce "Eh" .
Ya numfasa ya ce "To duk wanda zai ce miki bana son ki, ko kin fi sona, ba gaskiya ya fa'da ba, domin dai kinsan yadda nake lashe ki in and out, ai idan bana son ki ba zan iya yin hakan ba, tunda kinsan ina da 'kyan-kyami"
Ai kuwa na saki baki na ce "Ai nasan kana sona sosai, na sani, shiyasa nake kallon Maman Nana a kife da ta dame ni da mitar son da nake maka yayi yawa kuma bani da aji akan ka, nan gaba zaka nuna mini halin maza. Yaya Al'amin ma jiya da ya shigo duba ni har da cewa idan ban yiwa Abba biyayya akan hukuncinsa ba, sadda zaka zo ka juya mini baya na kuka da kaina. Dan kuwa baza su sake barin Abba ya shiga shirgina ba".
Ya fesar da ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "Al'amin da Sakina sune barazana a rayuwata! Wai ace wadanda ka bawa so da yarda, sune suke cin dunduniyarka. Allahu ya yi musu irin abin da suke nufi da ni. Duk kuma kutunguilarsu sai dai su buga su barmu tare, azzalaumai masu yiwa soyayya illah".
A sanyaye na ce "Amma dai ai suna son ka fa".
Ya kuwa dako mini tsawa ya ce "A a 'kaunata suke yi, ba so ba. Ina so ga wanda yake son ya shiga gidanka ya kafa maka fandishon fitina da tashin hankali?"
Na yi shiru na kasa bashi amsa.
Ya nisa ya ce "Idan kina ri'ke maganganunsu watarana zaki wayi gari ne ki ga mun yiwa juna tazara mai yawa, domin idan suka cigaba da hure miki kunne zan koma gefe ne na bar ki da su, ni kuma na yi aurena, na samo wacce yan'uwanta baza su saka ta bijire mini ba, ina ce shikenan?"
Nan da nan idona ya ciko da hawaye ina cewa "To na yarda da su ne? Ai ni kallon su kawai nake yi."
"To shikenan ya isa" ya fa'da da sigar rarrashi.
Ya cigaba da ratattabo maganganun da suke tasiri a zuciyar mace mussaman ace mijine yake wannan maganganun masu gigitar wa. Na dinga mamakin yadda ya iya fa'din irin wadannan kalmomin tamkar wanda ya yi ilimi a fannin.
Bai bar ni ba, sai da ya tabbatar ya mini sabis din da zan iya yin fito na fito da duk wanda ya nemi shiga tsakaninmu.

******
*Asibitin Malam*
Ashir na kewaye kawai sai ganin Sadik ya yi cikin sahun wadanda ake yiwa gwaji idan za'a ciri k'odarsu a ki'dime ya 'karasa wajensa yana tambayar ba'asi.
Amma Sadik ya 'ki kula shi bare ya bashi amsa.
Ashir na tsaye aka gama duk wani cike cike wani zabgegen Alhaji sai kaffa kaffa yake yi da Sadik din, alamun ririta shi yake yi.
Sai da suka fito daga wajen sannan Ashir ya tari gabansu, ya tambayi Alhaji menene hadinsa da 'dan-uwansa.
Sai lokacin Sadik ya bu'de baki ya ce " Ashiru bana shiga harkarka! Ka fita a tawa, ban sanka ba, bani da hadi da kai, akan me zaka nemi shiga al'amarina?"
Alhaji ya kalli Ashir ya ce "ka san shi ne?"
Da sauri ya ce "Wallahi kanina ne first cousins muke".
Alhaji ya kalli Sadik ya ce "Garbati ka ce mini baka da kowa anan kai mutumin 'Kasar Kamaru ne?"
Nan da nan ya diririce ya ce "eh hakane kuma gaskiyar kenan".
Zufa ta dinga karyowa Ashir ya dinga hasashen wanne irin abu Sadik yake 'kullawa haka?"
Nan da nan ya fito da waya ya kira Sakina, ya kwatanta mata inda suke tsaye, ya rufe maganar da cewa "ki gaggauta dan Allah".
Aikuwa ba'a jima sosai ba ta iso cikin fargabar me zata ga ni.
Ganinsa da Sadik sai ta samu nutsuwa ta sani dai fa'dansu ne da baya 'karewa.
Ganinta kawai ya tabbatar wa Alhaji ita din jinin Garbati ce kamar yadda Gudale ya fa'da masa sunansa kenan.
Nan da nan Gudale ya fara sababi kome za'a yi basu isa hana shi abin da yayi niyya ba, tunda an ri'ke masa mata duk sun zuba ido an ki a taimake shi. Ina zai samo uban milyoyin da aka ce sai ya kawo?
Ya kalli Sakina cikin ido ya ce "Ni ina da imani, Ni mutumin kirki ne, Ni kuma mai tsoron kwanciyar kabari ne, kin san da wannan. Dan haka ba zan dauki makami na fara tare hanya, ko na fara sace Bani adam ba, dan haka na zabi na sayarwa mabu'kata kodata d'aya na karbo Guduyo.
Wata'kila idan na yi hakan a daina nuna mini iko akan ikon da shari'a ta bani akan aurena"


*Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?*
*kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*.
*Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi m lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.*
*Sister Zainab 08039315577.*






# Team Gudale
# Team Guduyo
# Surayya Dee✍️
# Ana tare. 🤝
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Ummu Muhammad collections*
*Tana sayar da dukkan nau'in sutura masu kyau zababbu kuma masu sau'kin farashi*
*Tana sayar da takalma da jaka masu kyau*
*Tana ha'da lefe*
*Tana ha'da kayan haihuwa*
*Tana sayar da Data*
*Tana yin adashe, Kuma fasihiyar Tela ce*
*Tuntube ta a wannan lambar 08063358662*
*Siyan na gari aka ce maida ku'di gida*.


*SDK*
*61-62*


Jikin Sakina ya fara rawa, a ki'dime ta ce "Na shiga uku ni Sakinatu! Na Moriki wanne irin bahago ne kai? Abin da zaka yiwa Umma kenan?
Ka zo ka sayar da 'kodarka? Sadik 'koda fa?
Jikinsa ya yi sanyi ganin yadda Sakina ta rikice to Ummansa fa?
Kunyar duniya ta rufar masa, bai yi tunanin ba shi ka'dai yake da hakkin kansa da kansa ba.
Ya sani kuma matu'kar Umma ta sani ba zata bar shi ya sai da 'kodarsa ba. Ya tabbatar ko ita ce take bu'katar ayi mata dashen 'kodar ba zata so a ta'ba tasa ba, saboda tsananin yadda take sonsa, take kuma fatan ya rayu cikin farin-ciki da 'koshin lafiya.
Yau ina zaisa kansa idan ta ji akan Guduyo zai sayar da kodarsa?
Wai wanne irin abin ne ya same shi ne akan Guduyo?
Shin sone ko kuwa da gaske gigita shi ake yi dan a nesanta shi da uwarsa? Kamar yadda take fa'da masa a kullum.
Ya yi tsam a ransa tabbas ba yanzu ya fara jin abu akan Guduyo ba. Amma na yanzu ya fi karfi. Sai dai kuma bai ta'ba jin akwai wanda yafi Umma a duniyarsa ba, har Abba kuwa.
Da ana yi masa wani abin ai da ya ji wannan son da matsayinta ya yi rauni.
Ya fesar da ajiyar zuciya. Guiwarsa ta yi sanyi ganin Sakina tana share 'kwallah, yayin da idon Ashir ya ka'da sosai, ya hango soyayyarsa a cikin idon Ashir, amma yana tuna ai ya so Guduyo, da irin wula'kanta shi da yake sai ya dauke fuskarsa a kansa yana jin kishinsa na taso masa kwarai da gaske.
Alhaji ya ce "su sami wuri su zauna ayi maganar a tsanake".

Sakina ta ce "Ai gida zasu je ayi maganar a gaban mahaifinsu."
Haka Ashir ya yi insisting sai an je gaban Abba.
Yayin da Gudale ya nemi bijirewa shiga mota, ba zato ya ji Sakina ta dauke shi da mari. Ya zuba mata ido sosai yana dafe da fuskarsa, ransa in sun kai dubu sun baci.
Kafin ya yi magana Ashir ya ce "ko ka shiga ka mutunta kanka, ko kuma Wallahi na shigar da kai a wula'kance, zabi na gareka".
Kan dole ya shiga motar Alhaji suka dunguma. Basu zame ko ina ba sai falon Abba! Cikin ikon Allah duk suna falon daga Abban, har Yayar 'Kwalli da kuma Baba.
Ba kuma komai ya ha'da su ba illah bikon Halimatu da suka je yiwa Gudale.
Ganinsu a hargitse ga kuma bakuwar fuska a tare da su ya sanya suka shiga wasi-wasi.
Amma cikin juriya Abba ya shiga marabtar Alhajin da ba bai gane shi ba.
Cikin rawar murya Sakina ta ce "Ga Sadik nan Ashir ya gano aika-aikar da ya yi nufin yi. 'kodarsa ya sanya a kasuwa, shine wannan Alhajin zai siya ayi wa 'dansa dashe".
Gaba'daya dakin ya dauki salati da hailala.
Tsananin ki'dimar da Abba ya yi ya kasa cewa uffan.
Cikin karfin hali Baba ya mayar da hankalinsa akan bakon. Ya ce "Alhaji ya aka yi ka yarda da wannan cinikin alhalin baka ga kowa nasa ba?"
Ya numfasa ya ce "na bincike shi, tunda akwai inda sai magabatan mutum sun sanya hannu kafin ayi aikin mussaman iyaye ko matarsa. Sai ya ce mini shi din maraya ne, bashi da kowa kuma sunansa *Garbati Habu Shaho * zai bani dan Allah, dan kuma ya samu ku'din da zai dinga juyawa yana samun abin rufin asiri.
Duk da hakan ban yarda ba, sai da muka je kotu, ya yi wannan maganar, sannan muka je wajen yan sanda aka yi statement dinsa, duk ba dan komai ba sai dan tsoron abin da zai je ya zo".
Dakin ya yi tsit banda kukan Yaya da Umma ba abin da yake tashi a dalilin Sakina ta 'kira Umma dan ta ji ka sassabar da autanta ya yi akan matar da take fatan ya sake ta.
Yayin da Gudale ya yi 'kasa da kansa yana jin kunyar mahaifiyarsa tana katantawa da shi.
Da matu'kar rauni sosai Abba ya cewa Alhajin "nawa ka bashi?"
Ya girgiza kai ya ce "Milyan arba'in muka yi zan bashi, ban kuma kai ga bashin ba. Dama gobe ne zan yi masa transfer, kawai dubu dari biyar na bashi dan ya dinga cin abinci

33 / 61