Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
ina karami nake addu'a na zama namijin duniya a cikin gidana."
A makance Baba ya ce "Hakane".
Ba dan ya fahimce shi ba.
" To a gaskiya ni dama fa bana son wannan zaman da take yi a gidan nan da sunan jego, shiyasa..".
Kafin ya karasa Mama ta shigo tana cewa "Har kun dawo daga asibitin ne, ina suke?"
Nan da nan kwanyar Gudale ta hakaito masa ai rufin asini da Mama ta saba yi masa idan ya yi laifi ne yauma ta yi masa. A cikin mutanen da ya yarda karimai ne a rayuwarsa har da Mama halittar da Umman sa ta tsana tamkar ta shafe ta a doron 'kasa.
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "mun dawo Mama amma na yanke hukuncin ba zata dawo ba, na mayar da su gida, shi Abba bai fahimce ni ba ko ka'dan shiyasa na zo inda za'a fahimce ni. Na tsani na bu'de ido na ganni ni ka'dai a cikin gidan."
Mama ta yi sukuri tana kallonsa cikin rashin abin cewa.
Domin ta sani shine ya zo ya tafi da Halimatu, ita kuma soyayya ta saka ta bishi babu shawara ba komai. Ashe kayan da ya yi ta fita da su da manufarsu, dama sun shirya sai dai a wayi gari a ga sun yi tafiyar su? Lallai sai kyale dan yau da rashin kunya da mutuncinsa, amma sanin da ta yi Sadik zai yi fiye da hakan yayin da Halimatu zata biye shi ta yi abin kunyar da ya zarce hakan saboda tsoron fishinsa sai ta hada su ta yi musu uzziri, amma ta kudire a ranta duk ranar da aka ce Halimatu ta zo gidan da nufin kwana a ranar zata gane bata wayo.
Ya rarrafa ya je gaban Mama ya ru'ko hannunta ya ce "Allah dai ya kara miki lafiya Mamanmu! A duniya ina son mutum mai sirri bai rufa asirin wani, Allah ya rufa miki naki asirin.
Ina matu'kar godiya sosai, sannan kar aga laifin Guduyo, laifina ne, ko kallon baki kyauta ba kada ayi mata, domin na baro ta tana ta kuka da bacin ran ya zata kalle ku.
Na ce "Ta daina kuka zan zo na wanke ta".
Baba ya ce "Ka wanke ta! Zo ka fice mini tunda dai kai kullum ba zaka bar ni na huta ba".
Har ya je bakin kofar sai dawo ya ce "Saboda Allah me na yi Baba?
Yaushe rabon da na kawo kara, ko a kawo maka tawa?
Indai baka son na rame kawai ka samu Abba ka ce "Kai ka bani umarnin na tafi da matata, idan kuwa har ka bari ya yi mini fa'da. Àllah Baba a satin nan na dinga tsokanar fa'dan da sai ka gaji da sharia dan kuwa har mijin Juwairiya sai na tsokano, ta yadda zai koro muku ita".
Baba ya daga hannu ya ce "Allah ga Sadik ka yafe masa , ka shirya mini shi".
"Ameen ya adalin Uba! Ina godiya fa, na gode sosai. Ayi barci lafiya."
Ya tafi babu waiwaye.
Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Oh Sadik duniya! Shifa bilhakki yake al'amarinsa, Allah dai ya daidaita."
Baba ya amsa da cewa"Amin".
**
Ina falon ya dawo yana cewa "sai ki saki ranki na je na binne kunyar".
Ya dauko ledar kazar ya kawo gabana. Ya shige ya debo ruwan wanke a hannu a faffadar roba, da kuma plate.
Ya kalle ni ya ce "kwantar da ita ki sauko ki ci".
Na kuwa shinfide ta akan kujerar na lullube ta da shawul dinta, ya murmusa ya ce "oh ni Garbati! Guduyo ta zama Mummy".
Kunya ta kama ni na zum'bura masa baki.
Yana mini wani irin kallo ya ce "Ba dan ciwon jiki ba, da bubbuge zan yi, ki yi ta zum'bura baki, sai an wayi gari an ga bakin ya zama tamkar na shantu".
Kirki sosai ya yi mini a wannan daren domin hatta gashin da mama take yi mini na kwankwaso da cinyoyi zuwa kafafuwana shi ya mini, duk hannuwansa suka yi jawur.
Muka zo kwanciya ya ce mu koma dakinsa na can gefe wanda yake kasa, shima sanyine ya koro shi daga sama.
Mamakin da ya shayar da ni bai nemi komai ba. Kawai dai bai yarda yarinyar ta shiga tsakaninmu bane, a gadonta da ya kara siya mata ya saka a dakin ya ce na kwantar da ita. Na lullubeta sosai dama kuma Mama bata yarda ta kwanta a jikina sai ta sanya mana zani a tsakanina da ita.
Kafin mu yi barci ya dan yi kissing dina sai dai bai yarda yaja wasannin da yawa ba.
Kawai mamakin da ya bani da ya mayar da abincin Amna nasu su biyu.
Na dinga mamakin baya jin karnin nono?
Ashe da gaske ne matan da suke neman fatawar da mazansu suke zama tamkar jarirai idan suna shayarwa?
Gudale na cikinsu. Don hakan ya 'kara mini yawan madarar da nake sha. Kullum kuma sai ya shigo mini da fresh milk yakance mutum biyu kike shayar wa dole a kula da cimar ki da kyau. Banda kaji da su kwai da yake lodosu kamar me, bayan wadda Abba yake aiko mana da su.
Sati biyu ba wanda ya leko ni, nima kuma tattali da kulawar da nake samu irin wacce bai ta'ba gwada mini ba ya sanya na yi lakwas na manta da kowa kamar yadda yake so.
Har kuma lokacin bai neme ni ba, duk kuwa da yaga na fara sallah tun kwanaki biyar.
Lafiya lau muke zaune, kullum safiya na yiwa Amnah wanka idan zai fita office da kansa yake damke ta ya kai ta wajen Umma, ba za'a dawo da ita ba sai azahar.
Suna fita kuwa Atika yarinyar da yake samo mini mai Taya ni aiki zata fito ta gyara ko ina, da alamu suka ta taba yin aiki a wani gidan ta iya aiki sosai, sannan tana iya fere dankali ta soya, ta kuma iya dafa indomi. Banda gyara kayan miya da sauran aikin girki masu sauki.
Bai fara nuna zalamar sa ba sai da muka yi arba'in na dinga gode masa, domin ban yi zaton zai yi kawaici har haka ba.
Ranar da komai ya faru ya kankame ni yana ta sakin maganganun masu nauyi yadda ya saba, ni kuma na lafe a jikinsa ina jin shau'kinsa na sake kekketa mini mussaman yadda ya yi komai very soft yana ririta lafiyata.
Kwanaki biyar da yin arba'in din mu Amna ta fara wani irin kukan dare, idan shabiyun dare ta yi ta fara kuka ba zata yi shiru ba sai ukun dare tamkar mai lissafin lokaci.
Tun yana dan yin kawaici yana taya ni, har ya fara kosa wa, domin kukan nata mai gigitarwa ne.
Ni da kaina sai na koma dakina da barci, Sai dai yana dan lekowa ya mana sannu wanda a raina na kan dan ji babu da'di, nafi son ya bar barcinsa ya taya ni kamar yadda nake jin labarin wasu mazan na yi, ko irin mazan da nake karantawa a littafi suna karban yaran suce uwar taje ta kwanta ta huta.
Na tuna haka mama take yi mini, komai Amna zata yi bata bani ita, sai ta ce na kwanta na huta matu'kar na bata nono ta sha.
Kuma wai bayan ukun nan idan na samu ta yi barci sai ya lallabo ya jani dakinsa ya yi abin da zai yi, asuba kuma tana yi zan tashi na sallame shi, na kuma shirya ta, bana samun kaina sai wajen tara idan na yi wanka na shirya sannan nake dan samun barci kafin a dawo mini da ita.
Kwanaki suka yi ta shudewa bata daina kukanta ba, sai dai yana dan raguwa, yanzu idan ta fara sha biyu to biyu saura take ha'kura.
Shima kuma ba kasafai yake ma lekowar ba mussaman da a yanzu ba kukan gigita take yi ba.
Ranar da ba na mantawa kwanaki biyu Amna bata yi kukan dare ba, ina ta murna, komai zai dai-dai mini domin rashin kwana a wajen Gudale ya sanya sama sama muke da shi yana ta yi mini shaguben na dauki son duniya na dorawa yarinya, akan me idan ta yi barci ba zan waiwaye shi ba, sai kawai na yi kwanciyata dan na nuna masa yanzu ina da wacce ta fi shi.
Cikin kwantar da murya na ke cewa "Haba Yaya Gudale yaushe zata fika? Ha'kuri zaka kara sadda take yin shirun ni kuma barci ya ci idona, kuma a hakan fa ina zuwa maka ai".
Ya ta'be baki ya ce "idan na zo na jaki da kaina ba".
Wataran na yi shiru, watarana na yi karfin hali na ce "kamata yayi fa ka dinga tashi muna rainon tare".
Ya ce "ai ke raina kulawar da nake baku kike yi mussaman ma na yarinyar nan, saboda kawai kin kwallafa ta a ran ki".
Ana hakan rannan tun kafin shabiyu yarinyar take wani irin kuka na tashin hankali domin ba kakkautwa yi take yi da iyakacin iyawar ta.
Har wani shidewa take yi. Har karfe biyu babu sauki. Atika kanta kasa barci ta yi ta dinga safa da marwa tana cewa "kawo ta Anti, bani na goye ta ki dan huta".
Ni kuma ba zan iya bata ba , a dalilin kukan ya zarce na koyaushe gigitarwa. Na tabbatar mutanan cikin gida zasu iya jiyo ta. Amma Gudale ko leke.
Wajen karfe biyu da abin ya tsananta nima kawai sai na fashe da kukan tana yi, ina yi, Atika ta rasa inda zata saka ranta.
Murya na rawa ta ce "Ki yi ha'kuri Anti zata daina kuka, ko na je na kira miki Mama ko Umma halan bata da lafiya ne?"
Wani irin kuka ya sake goce mini.
Yarinya karama da bamu hada komai ba ta ji kuka ta fito ta damu, amma uban yarinya yana gidan yana shan barcinsa babu wata damuwa.
Na goye ta ina cewa "Bari asuba ta yi Atika kada a tayar musu da hankali, zama uwa ai ba karamin al'amarine
mai sau'ki ba."
Ina ta jijjiga ta tare da kewaya falo zuwa daki, Atika na ta yi mini sannu a ranar son yarinyar ya shige ni, domin na ga tausayi karara a tare da ita duk kuwa da ba zata wuce shekaru sha hudu ba.
Sai da kukan ya dan lafa na doshi dakin Gudale har lokacin tana yi duk da dai ya yi sauki da alamu barci ne zai dauke ta.
Ina tura kofar na tarar da shi a tsakiyar gadon da waya a hannunsa, na yi turus raina ya yi koluluwar baci, murya na rawa tunda har lokacin da hawaye a idona na ce"
"Idonka biyu Gudale? Yanzu duk wannan kwakwazon da ya cika gidan ashe kana ji?
Wacce irin 'kiyayya kake gwada mini ne, har ta yi naso ta shafi abin da ka haifa a cikinka?"
Ya dago a tunzure ya ce, "Allah Ya nuna mini ranar da za ki gode wa kokarina. Shin ha'kkina ne na fahimci matsalar jaririya ko kuwa hakkin uwa?"
"Ba dama ki ga na runtsa sai kin addabe ni akan yarinyarki, wai a kanki aka fara haihuwa ne da kullum sai kin yi mini sanadin bacin rai akan ta? Baki da lokacin komai sai nata, ba ruwan ki da hakkina matu'kar yarinyar nan tana hannunki. To yanzu me kike so na yi miki? Nono zan bata ko goyon ta zan yi ne?
Haba na gaji da wannan fallin naki na sabuwar uwa, shin jiya ta fara kuka ko yau? Ko kuwa jinya take yi, kin fa'da mini ban kawo magani ba?"
Na juya na bar dakin zuciyata kamar ta fashe.
Shikenan washagari ya dauki gaba da ni, ko tsayawa ya karya bai yi ba, bare ya kai ta wajen Umma.
Mama da kanta ta shigo ta ce taji kukanta tana dubawa Ashe ciwon kunne take yi ruwa a kunnen sosai, abin tausayi.
Mama ta dinga fa'dan ai da ban biye wa miji na gudo ba ai da duk na fahimci irin wa'dannan matsalolin.
A take na buga wa Anti Sakina waya ta ce "Na kawo ta asibiti tana jiranmu.
Muka fita tare da Mama ta yi kofarta yayin da ni da Atika muka shiga kofar Umma na gaisheta ta amsa Kamar akan dole, na sanar mata zan kai Amnah asibiti wajen Anti Sakina.
A lalace ta ce "Wa zai kai ku?"
Na ce "Adaidaita zamu hau".
Ta kyabe baki ta ce "Allah ya bata lafiya".
Na mike muka fito. Cikin Sa'a muka samu adaidaita na dauke shi drop har asibitin Malam.
Dake Sakina a bangaren yara take nan da nan ta mana jagora har gaban babbar likitar yara ta asibitin gaba'daya *Dr Fatima Hanga*. Aka gama bincike ciwon kunne ne kawai. Aka goge ruwan aka hado ni da magunguna muka dawo gida.
Ko abinci na ki yi, indomie kawai na dafa mana ni da Atika muka karya tunda bamu cu komai ba muka fice.
Ganin barci sosai Amna take yi ya sanya nima na kwanta kusa da ita barci mai nauyi ya yi awon gaba da ni.
Da rana bai dawo ba, nima na ji da'din hakan ina tashi na tarar da Atika ta yi karambanin dafa farar shinkafa ta yanka salad ta wanke ta barshi a colonder ta rufe da murfi.
A falo na sameta tana kallo.
Ta mini sannu, na shiga kicin ta biyo ni, na bu'de kula na ga shinkafa, har da karas a ciki ta yi kyaun dahuwa. Na kalle ta na ga alamun tsoro tsoro a tare da ita.
Na murmusa na ce 'Madallah da Atika! ashe har haka kike da aiki?" mussaman yadda ta gyara kicin.
Dadi ya kamata na yadda na yabe ta na kuma gode.
A raina na ce wato dan adam yana da son a yabe shi, a kuma gode masa idan ya yi abin kirki. Atika yarinya da ita ta ji dadin yabawar da na yi mata duk da aikin ku'di take yi. Amma Yana matu'kar wahalar gaske Yaya Gudale ya yaba mini ko ya gode mini.
Na saki hucin takaici na ce "To ya baki fito da miyar kin dumama kin ci ba?"
Ta yi kasa da kanta ta ce "Ai ban fa'da miki ba, sannan ba zan iya zuba wa da kaina ba ina jin tsoro".
Ban tambayi dalilin tsoron ba na ce mata "Daga yau idan kin girka abinci na miki laminin ki zuba wanda kika san zaki cinye, idan baki koshi ba ki 'kara, 'karya da gulma ne bana so kina ji, amma ki dinga zuba abincinki kina koshi.
Na dumama miyar na dauko plate din da na ware mata na zuba mata sosai dan nasan ta da ci. Ni kuma cinta baya damuna tunda morarta nake yi ba ka'dan ba, kuma alhakin ciyarwarta yana kanmu, ta yini tana mana bauta an rabo ta daga gaban iyayen ta ba batun karatun arabi bare na boko, shin idan ba'a basu abinci sun koshi ba ina ake so su je su ci? Bayan suna mana hidimar da baza mu iya yiwa kan mu ba.
Take tunanin saka ta a islamiyya ya zo mini, bai kamata na barta cikin jahilci kashi kashi ba. Tunda ta rasa na neman duniya wato boko, to gara ta je ta ji abin da zai taimake ta ta san Ubangiji ta yadda zata kyautata ibadarta, ta tsira da lahirarta.
Tunda na fara disa mata maganin bata sake kuka ba, dama kuma likitan ta tabbatar mini tunda kurjin ya fashe to zata samu lafiya.
Kwanaki biyu muna yar shariya a dalilin naje asibiti ban sanar da shi, ban kuma je na yi masa bayani ba.
Kwana na uku na dinga jin kamar na yi masa magana, amma ina tuna yadda ya banzatar da mu shikenan sai na ji raina ya sake baci.
A cikon kwana na hudu ya ha'kura ya sauko daga nasa fishin zai fita da sassafe ya shigo yana cewa "kin shirya ta ne na kai ta?"
Na girgiza kai na ce "Je ka, kar a bata maka lokaci, ko riga ban sa mata ba, Atika zata kai ta".
Ya zauna a bakin gadon yana son sai mun hada ido ya sakar mini kallon da yake susuta ni, ni kuma na share na ki yarda na kalle shi.
Ya sassauta ya ce "Guduyo wai ki dinga wula'kanta ni akan yarinyar nan, yau da ba nine ubanta ba, tabbas sai dai a wayi gari aga na ha'diyi zuciya na mutu.
Duk wani hakkina kin yi fatali da su, dan kawai kin haihu. Da haka duk mata suke yiwa mazajensu na rantse ba wanda zai yarda ayi masa haihuwa.
Ba ruwan ki da zuwa wajena, yanzu ko tsafta ce mini shi kin daina. Ba ruwan ki da cikina, na ci abinci ko ban ci ba duk ba matsalar ki bane saboda na fa'di abin da bai miki da'di ba akan 'yar gold".
Na numfasa na ce "plz mu bar maganar nan, tunda ka bu'kaci na gyara, zan gyara shikenan?".
Da sauri ya ce "To yi gaggawa ki shirya ta na kaiwa Umma ita da kaina. Ta ji dumina, ba naki kawai ba
Zan je office na dauko excuse ki shirya tarba ta, sosai na yi kewar ki Guduyo".
Ya fa'da yana kanne mini ido.
Na tsuke fuska na ce "Gaskiya ba sai ka dawo ba, dan barci zan yi".
Ya sassauta ya ce "To Gudidina! Yadda kike so hakan za'a yi, ba zan dawo yanzu ba, ki kwanta ki yi barcinki ki huta. Amma zan dawo cin abinci da rana daga nan ba zan koma ba. Plz kar ki ce mini a a kinsan dai bana son ki zame mini tamkar doll a shimfida shiyasa nake son ayi cikin so da walwalarki.
Me zan taho miki dashi, me kike sha'awa?"
Na daure fuska na ce "Bana bu'katar komai".
"Kash! Sadiyayye ana baki kina tankwabar wa. To ki shirya zamu fita idan na dawo".
Na yi shiru na cigaba da shirya ta. Duk share shin da na yi sai da ya jira kuwa ya karbe ta suka tafi.
Na yi zaune ina mamakinsa, dake yana da bu'kata ya ajiye fishin! Na sani kuma ba karamin aikinsa bane yana samun abin da yake so ya sake yi mini wani sabon iskancin, koma ya dora gabar a cigaba da yin ta.
Ai kuwa da rana sai gashi sabe da Amnah tabbacin sai da ya fara shiga wajen Umma.
*Ban ta'ba tunanin xan samu matsala a wannan tafiyar ba. Amma kasancewar Ubangiji ne yake sarrafa al'amura, abin ya juya ta inda ban ta'ba zati ba. Zan dan dakata zuwa lokacin da al'amura zasu dai-daita mini, bana fatan na dauki lokaci mai yawa.*
*Allah ya