Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   34 / 61

99K to 102K   out of 180.1K words

mai kyau, da fruits ta yadda aikin zai tafi cikin Nasara".
Kafin Abba ya yi magana Umma ta ce "Wallahi karya yake yi maka ba maraya bane, dan gata ne na bugawa a jarida. Ga ubansa nan, ga ni uwarsa, wadannan kuma duk iyayen sa ne, dan haka ciniki ba zai yiwu ba, bamu yarda ba, ba kuma zamu amince masa ba".
Ta karasa cikin rishin kuka.
Baba ya ce"Bani lambar asusun na dawo maka da 'kudinka, tunda aiki ba zai yiwu ba, ka karbi ku'din da ka bashi kawai".
Alhaji ya ce "Na lura yana cikin damuwa ne yaron! Na ji dazu yana fa'din a ina zai samo milyoyin da aka ce sai ya kawo kafin a bashi Gunduma ce ko menene oho. Na dai fahimci tamkar matarsa aka ri'ke masa aka gindaya masa shara'di mai tsauri.
Ina ro'konku tunda har tunaninsa ya bashi ya yi irin wannan akan yarinyar to ku saka hannu, ku tallafa masa a dawo masa da ita kawai. Idan kuma ku'din da zai biya bai wuce milyan biyar ba ni zan biya masa domin na gane ita ce nutsuwarsa, idan ba dawo wa hannunsa ta yi ba, wata'kila ya je ya jefa kansa a hanyar 'batan ci".
Aka dinga yi masa godiya saboda fahimtar da ya yi da kuma yadda ya yarda aka rabu cikin mutuntuntawa tunda dubu dari biyar din da ya bawa Gudale ya ce ya bar masa halak malak.
Baba ne ya raka Alhajin har wajen motarsa sannan suka yi musabaha suka rabu, Baba yana ta sake godiya, tare da yiwa 'dansa addu'ar samun lafiya.
Fa'da tamkar a rufe Gudale da duka haka aka rufar masa kowa ya fa'di son ransa. Abin kaicon kuma har da Ashir a cikin masu fa'dan.
A take Yaya ta zartar da hukuncin lallai Abba ya yi hakuri ya bashi matarsa kada a wayi gari kuma aji zai sa idonsa 'daya a kasuwa.
Umma kuwa zuciyarta tamkar ta yi bindiga haka take ji. A ranar ta sake gane zahirin 'kiyayyar da take yi wa Safiyya domin ace a sanadin 'yarta Gudalenta zai salwantar da 'kodarsa ta tabbatar son da yake yiwa Guduyonsa ya wuce misali. Ya wuce ya tankwa'bu cikin ruwan sanyi, tabdi jam.
Duk yadda yake jaddada mata aurensa da Halimatu ba rayayye bane. Ashe shaidanun mutanen nan sun shiga sun fita sun cusa masa soyayyar da tafi kama da sha-sha-shau! Tabbas nan gaba ka'dan zasu saka almakashin datse alaka su raba ta da shi, bata haufi akan hakan.
Bakin cikin ya yunkoro mata, ta kasa sarrafa fishinta kawai sai ta barke da kuka mai tsananin gaske.
Jikin kowa ya sake yin sanyi, domin su din shaidu ne na yadda bata ha'da al'amarin Gudale da komai a duniyarta. Sai gashi ya tafi zai yiwa kansa illah, ba tare da neman shawararta ba.
Yayin da oga Gudale yake gefe yana Jin guiltiness yana kama shi.
Kunyar Umma kawai ta hana shi motsa kwanjinsa, amma ba dan ita ba, da ba zai risina ba, zai tabbatar wa Abba zai iya yin komai ban da zubar da jinin mumini, dan ya samu kudin da zai fanshi Guduyo.
Idan kuma ya dawo masa da kudadensa shi kuma ya kudire ba za'a sake shigar masa harkar gidansa ba. Akan me za'a nemi a dinga mulkar aurensa? Shi ba Baban Yara bane, da komai zai yi a gidansa sai abin da Abba ya ce ko ya zartar.
So yake a barshi a mai cikakken iko a gidansa, tunda an gamsu ya isa aure, an yi masa, ga kuma matar da ciki ai kuwa an san ya girma, dan haka a barshi kawai da gidansa.
Ba'a kula da cewa yanzun ya saba da mace ba, ba'a lura da cewa ko ba zai iya ri'ke kansa idan babu ita ba, sai kawai aka rufe ido ake tozarta shi, dan haka zai yi komai dan ya samo kudaden da Abba ya wula'kanta shi saboda su.
Idan kuma ya dawo da su din to kuwa ba mahalukin da zai masa iko a gidansa tunda shi ya yi wa kansa komai.
Idan kuma bai samu ku'din ba to zai na'de kafar wando ne kawai ya yi fatali da dokar Abba na haramata masa shiga gidansa, dan kuwa a dakin da Guduyo take zai dawo da kwana ko me za'a yi kuwa ba abin da zai fasa yi.
Ko ya dinga kwana a dakin Abba a tsakiyarsu, tunda ana mua'amalantar sa tamkar yaro 'dan 'karami to kuwa zai koma tamkar mai shan nono, ba shikenan ba.
Gyaran murya Abba ya yi ya ce "Yaya tunda kin karaya da iyashegensa zan bashi ita, saboda ke dan idan ta nine sai dai ya sayar ba damuwa ta ba ce. Amma kune shaidu Billahillazi duk ranar da ya kuma cewa "Na cuce shi da na bashi aurenta to lah shakka babu maganar ya cigaba da zama da ita."
Yaya ta ce "Ba wannan maganar ai, domin yanzu ya gane komai, ya girma, gashi yana shirin zama uba."
Da murya marar amo Gudale ya ce "Ni nasan na girma Yaya! Amma shi Abba so yake sai ta raina ni. So yake ta ga dukkan raunina, ta gane abin da ke kirjina ta yadda ba zan iya sarrafata ba. Baban Gusau ya fahimce ni, kwarai da gaske a kullum yana nuna mini miji ne yake da cikakken iko akan aurensa.
Dan haka Baba ina baka wasiya idan mutuwa ta zo mini kafin zuwan *wakili* to na fa'da maka sunan Baban Gusau zai amsa. Karma a mayar masa da sunana a zaci sunan Abban Sakina ne".
Sai lokacin Abba ya ce "Wai kai kana son fa'da mini ka fasa mini takwara ko?
Yo masu sunana nawa ne?
They're uncountable. Abdallah ya yi mini, su Hafsatu da Ramla kusan kowa yana da ni.
Dama kuma Baban Gusau din shine Babanka ai, Madallah da wannan karamcin.
Kuma ba zaka bar nan ba sai ka fa'da mini dalilin jigina mini *Shaho* a sunana da ka yi. Ko hakan ya zama sanadin rasa aurenka dungurungum, idan ya so ka je ka sayar da kanka gaba'daya".
Nan da nan raunin Gudale ya bayyana domin tashin hankalinsa Abba ya ce zai raba masa aure.
"A sanyaye ya ce "Ni fa Abba ba da kai nake ba.
Nima sunan nawa Abubakar ai, sannan na jingina Shaho ne a matsayin sunan kauyen mu a Kamaru".
Da'kuwa Abba ya yi masa ya ce "Gidanku".
Ganin Abba zai sake murdewa Yaya ta katse Abba da cewa "Ya isa haka Alhaji. Salati goma ga Annnabi(S.A.W).
Sai da aka yi addu'a sannan ta ce "Na rufe wannan maganar haka nan. Ya gane, ya kuma 'karyata kansa, kuma kowa ya gane yana son matarsa magana ta kare."
Tamkar wanda aka zaburi Gudale ya ce "Yanzu Yaya har Guduyo an bari ta gane ina son ta har haka?"
Zan roki arzikinku kada a fallashe ni, bana son tonon silili, kada zancen 'kodar nan ya fita waje domin ba dan ita zan sayar ba, zan yi ne dan na sauke nauyin da aka ce sai na biya.
Ya kalli Sakina da Ashir ya ce "idan na ji maganar nan a waje a tsakaninku ne, kuma zan iya shata layi da mutum".
Ashir ya hassalo ya ce "gyara kalamanka, domin dai da Sister Sakina kake amma ba da ni ba, don kuwa ka tabbatar sai na fa'dawa kowa wannan shashacin naka, na fahimtar da mutane su fahimci 'Kifadi ne kawai da kai amma babu jarumta. Idan ka so ka sanya dutse a tsakaninmu ba wai shata layi kawai ba".
Ai kuwa ya hassalo ya kalli Yaya ya ce "Yaya kina jin Ashirunki ko?
Na rasa masifa irin tasa, na ce bana son ya shiga harkata, idan ina 'kaunar ko kallona Ashiru ya yi shege nake bare kuma ya yi mini magana. Yayin da takaici ya shake Ashir. Wato ya lura da isgili Sadik yake ce masa Ashiru, tunda kowa Ashir yake fa'di idan aka cire Abba.
"Yi ha'kuri ka rabu da shi ka ji". Cewar Yaya ta fa'da cikin rarrashi.
Kafin Sadik din ya ce wani abu Ashir ya yi fit ya ce "daina bashi baki Yaya! Dan Allah Garbati kada ka ha'kura! Do your worst. Wanda zai sayar da kodarsa akan wacce baya so dan tsabar asaranci".
Ba'kin ciki ya turnike Gudale.
Murya na rawa ya ce "Ya Allah! Ga Sakina, wa Ashir wa Al'amin, Allah sun fitine ni, sun ha'da kai sun uzzara mini, suna neman kai ni k'asa a cikin al'amarin da bai shafe su ba, Ubangiji a mini maganinsu, a yi kishina".
Umma da takaicinsa ya kai mata ma'kura sosai ta ce "Shasha kawai! Wanda bai san me ya kamace shi ba, idan ka kuma bu'de bakinka sai na ce maka kaico"
Da 'kyar aka gama zaman bayan Yaya ta tabbatar ba zata bar gidan ba sai ta mayar masa da Halimatu gidansa.
Baban Yara dai bai ce komai ba illah nasiha da yake ta faman yiwa Sadik dan ya gane ya zauna da yan'uwansa lafiya. Ya kuma zama mai biyayya da ha'kuri a akan sha'anin rayuwar duniya.

**********
Ina zaune kan gadon Yaya ta shigo tamkar jifa ta ce "sauko Halimatu! Tashi na mayar da ke dakinki, ki yi ta ha'kuri da Sadik, kowanne Dan Adam da yadda yake da kuma yadda tsarinsa yake. Sadik na cikin karkatattun mutane da ba straight suke ba, duk yadda kake da su kuma zasu rufe ido su yi maka cin Kashi.
Wato dai halayyarsu ta yi dai dai da dabi'armu ta yadda *Sabo da kaza* baya hana mu yanka mi cinye tas.
'kara hakuri da shi, kalar tasa soyayyar kenan".
Murya na 'dan rawa na ce "Ni fa Yaya bai mini komai ba, lafiya muke zaune, amma Abba ya jingine ni, ki zama shaida ban ce yana mini wani abin ba. Haka kawai an janyo mini rikici bayan ban ce ina da matsalar komai ba".
Ai kuwa jikin Yaya ya yi sanyi, nan da nan ta gyra bakinta ta ce "Ai shi Sadik fahimtar sa ne ba'a yi ba, amma rikicinsa sai an ta'ba shi".
Ai kuwa na ce "Ashe kin gano Yaya! Dan haka Ni dai idan ban ce ga laifinsa ba a daina kirkirar mini matsala da shi".
Ta zauna tana kallona ta ce "Wato aike na kika yi wajen Abbanku?
Wato duk abin da bawan Allah nan ya yi dan ya nema miki 'kima a idonsa, a wajen ki laifi ne ashe?
Na zum'bura baki na ce "Gaskiya laifi ne! Yanzu Allah ka'dai yasan halin da yake ciki. Ni nasan yana sona, dan haka ban damu da ake kallon ni nafi sonsa ba".
Ta mike ta ce "To fito na mayar da ke tunda na fahimci kema babu arziki a tare da ke. Oh ni Hafsatu yau ina ganin yadda Tinkiya ta haifi Akuya. Ko da wasa ban zaci Abbanku zai haifi tijararre irin Sadik ba. Haka ban zaci Baban Yara zai haifo kafaffiya marar kawaici irin ki ba.
Allah mun tuba! Àllah ya shiryeku".
Na bata rai na hau tattara kayana, kasan raina kuwa fal farin ciki zan koma gidana, gidan da nake rayuwa da mutumin da nake sonsa fiye da komai.

*****
Gudale yana durkuse a gaban mahaifiyarsa yayin da ita take zaune a bakin gado tana kuka har da shessheka.
A matu'kar gajiye ya ce "Na yi tuba Ummah! A gafarce ni, ba yadda kike zato bane ba fa".
Filo ta dauko tana maka masa tana yi kuma tana kuka.
Karon farko da ta daga hannunta da sunan duka cikin bacin rai sosai.
Dan haka sai ya sake ri'ke kafarta cikin rauni ya ke cewa "Ki mini komai matu'kar zaki huce Umma ke ce duniyata".
Sai lokacin ta bu'de baki ta ce "Ai yanzu bani ce duniyarka ba, tunda har zaka iya mantawa da halin da zan shiga a sanadin rashin lafiyarka, ko ma rasa rayuwarka gaba'daya".
Ta sake kecewa da kuka riris tana cewa"Safiyya ta ci galaba a kaina. Amma ka sani na tsani Halimatu! Tunda har al'amarinta ya yi tsananin da zaka sayar da 'kodarka dan ka rayu da ita. Ba zan yaudari kaina ba, kana tsananin sonta ta yadda idan na rabaku ma ni ce a ruwa. Dan haka ba zan sake cewa ka saketa ba, amma ka sani bana sonta, ba kuma zan so ta ba. Tsakanina da su sai a lahira, idan mun je sai mai rumfa ya yi alkalanci na gaskiya."
"Umma dan Allah ki daina irin wannan kukan! Tabewa ne a gare ni. Sharrin Sakina da Ashiru ne, ba su fa'di maganar dai dai ba fa".
Sosai ta hassalo ta ingiza shi ya Fa'di warwars ta ce "Na ha'kura da kai Sadik! Tunda na haife ka nake tattalaka, nake nuna maka gata da ya zarce na yan-uwanka. Amma kai kuma kai ne kake wahalar da ni, ka ke bijire mini, kake ha'da kai da abokan gaba ta. Ba komai ba zan yi maka baki ba, amma tabbas ban mori wahalar da na wanzu ina yi akan ka ba.
Ka je komai zaka yi babu ruwana, na riga na sallamawa Safiyya kai. Àllah barshi a filin kiyama Ubangiji ya mini sakayyar abin da kuka yi mini. Tunda na sani ko asiri ne ai yana tarar da hali".
Ta dinga goge hawayen idonta tana fa'din "Allah kar a kama shi da laifin kukan da nake yi, sharrin hatsabiban bayinka ya hadu da shi, Ubangiji idan akwai abin da yafi afuwa da yafiyar uwa na yi masa, Allah ka tsare shi daga fa'dawa makircin masu tofi a cikin kulle kulle".
Wani irin hawayen tausayin uwarsa ya dinga tsere akan fuskarsa, ya kasa magana, ya kuma kasa tashi daga faduwar da ya yi.
Cikin karfin hali ya rarrafa ya fa'da kan cinyarta murya na rawa ya ce "Na yi kuskure Ummah! Na kuma gamsu na na yi din. Amma ki yafe mini, ki yi hakuri".
Ta zaro tissue a Geffen gadon ta face majina ta ce "Na yafe maka! Na sani ba yin kanka bane, gayyah ake son yi mini da kai ta yadda zan kunyata, na yi ba'kin ciki. Fatana dai ka dinga fahimtar nafi kowa hakki akan ka. Zan fi kowa ba'kin ciki idan ka na'kasa ko ka mutu ka barni.
Safiyya tana da irinka reras hudu ne ko biyar, Ni kuwa fa? Kai ka'dai ne da ni. Duk yadda Yayarku ta haifi maza ai dai jikokine su."
Baki na rawa yake fa'din "Na gode sosai Umma! Ki cigaba da yi mini Addu'a. In sha Allah ba abin da zai same ni. Ba zan fasa fa'da miki ba, ke ce duniyata, ki cigaba da yi mini uzziri, Guduyo kaddara ce ta bani ita, ki cigaba da yi mini Addu'a da sannu komai zai dai-dai ta mini".
Dake shi din na mussaman ne a zuciyarta a lokacin ta yafe masa, ta dinga sanya masa albarka da neman kariya. Amma zuciyar ta yi mata nauyi ainun akan Halimatu. Tunda ga kasan zuciyarta take jin tsanar yarinyar, da kuma an cire wa Gudale 'koda ta sanadinta da sai dai Abba ya ha'diyi zuciya ya mutu amma tabbas sai ta yi shari'a da dukkan ahalin gidan su Halimatu, har mahaifinta kuwa.
Sakina da take tsaye bakin kofar dakin tana sake jinjina girman soyayyar da ta ke tsakanin Umma da Gudalenta.
Duk wannan laifin da ya yi, ta rufe ido ta ce ba yin kansa bane, asiri ne.
Sannan ta yafe masa har tana yi masa addu'a ta mussaman.
Ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya 'kara rufa asiri."
Ai kuwa Gudale ya dago fuskarsa da take kan cinyar Umma ya harareta ya ce "Duk abin da kike fatan ayi mini ba'a yi mini ba.
Wato Sakina na kusa sallama ki wallahi. A duniya na tsani kazallaha, na tsani mai shiga sharo ba shanu".
Ta'be baki ta yi ta ce "Ka da'de baka sallama ni ba. Wanda baisan komai ba, sai kansa".
Karon farko da Umma ta bi bayan Sakina ta ce "Yi ha'kuri Sakinan Abba. Ya za'a yi da shi, ai sai ha'kuri a sake tsananta yi masa addu'a dan ni tsoro lamarinsa ya fara bani, amma dai na yafe masa".
Ya jima kafin ya mi'ke ya tafi.
Sai da ya shiga falon Abba ya tsugunna ya ce "A yi ha'kuri da ni Abba! Kar a gaji, a kuma sake yi mini alfarma kada a bari yarinyar nan ta gane raunina. Na jima ina fatan na zama namiji a gidana, a taimake ni burina ya cika".
Nisa wa Abba ya yi tare da cewa "Ai matu'kar zaka dinga wula'kanta Sadiya tabbas ka kwana da sanin ni kake wula'kantawa. Fallasar da baka so, ai ka janyo wa kanka. Yanzu kowa ai ya gane cika baki ne, sonta kake yi fiye da yadda take son ka, tunda zaka iya salwantar da ranka akan ta."
"Nifa Abba ba dan haka bane, dan kawai na sauke nauyin da ka ce sai na biya ne."
Abba ya numfasa ya ce "To ai na ce idan baka biya ba, ka sallama mini ita, ai da sai ka sallama din kawai."
"Haba Abba! haba Abba yanzu dai baka gode mini ba, dan na nuna kulawa ta akan Shalelenka?.
Tunda ka ha'kura zata koma, ina maka albishir din wakili sunanka zai amsa, Baban Gusau ya biyo bayan ka tunda dama 'kaninka ne".
Ya mi'ke ya ce "Bari na je na marabce ta, na sani tuni Yaya ta tafi da ita.
Àllah dai ya kara maka lafiya *Ya Abati*".
Ido kawai ya bi shi da shi domin kuwa al'amarin ya girmame shi.

*****
Yaya tana fita shi kuma yana dawowa a gurguje ya tsaya ya yi mata godiya ya shigo ciki abinsa.
Masu aikin Umma sai share gidan da moping suke yi kamar yadda Abba ya ce su zo su yi, tunda ansan gidan ya yi kura, duk da mai gidan a ciki yake kwana.
Ina tsaye a tsakiyar dakina, sai kamshi turaren wuta yake tashi a dalilin an riga an kammalah gyransa.
Ba sallama ya shigo, kaitsaye ya rungume ni yana shinshinata tare da sauke ajiyar zuciya.
Murya ba amo ya ce "Really missed you my *Hala*.
Farin-ciki ya dinga rasta ni. Na dinga jin inama zamu tabbata a haka.
Tun kafin masu hidimar gyara gidan su tafi ya rufe dakin ya hau rawar jiki, bai samu nutsuwa ba sai da na biye shi, muka shayar da juna madarar kauna.
Sai da muka nutsa ya kalle ni ya ce "Kin je kin yi mini hadin

34 / 61