Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
sauke maka wannan tsagerancin na ka Sadik".
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?*
*kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*.
*Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.*
*Sister Zainab 08039315577.*
*Ina tallata muku Data mai rahusa.*
*Ku tuntubi Marubuciya Aisha Dan Sabo lemu a wannan lambar*
*08167768704*
*SDK*
*93&934*
Kici kici suka fara kokawa tamkar suna cikin kuruciya.
Duk kokarin Yaya Abdallah akan ya raba su abin ya ci tura.
Domin dai Gudale ya zage dukkan k'arfinsa yana kai wa Al'amin naushi tabbacin jikakken tsumin bacin rai ya taso masa.
Yayin da Al'amin din shima ya dage suna gwabzawa "Tare da cewa "akan idon iyayenmu zaka zage su?"
Gudale kuma yana fa'din "sharrinka ya bika Aminu. A ina na zage su? Kuma da baku San inda take ba dukkanku da ban ganku a hakan ba, damuwarku ka'dan ce".
Fa'da sosai kowa ya ji jiki.
Sai da Abba ya daka tsawa Sannan Al'amin ya sake shi kowa na mayar da numfarfashi.
Baba ya ce "Na gode maka Al'amin! Ina tsaye a waje zaka yi fada da dan-uwanka?".
Kafin Al'amin ya magantu Gudale ya ce "Bai dauke ni dan-uwansa ba. Yar'uwarsa ya za'ba ya fifita a kaina.
Duk kuma shiga sharo ba shanunka Wallahi sai ka kallemu ka barmu ni da Guduyo. In sha Allah ba zaku mutu ba, kai da Sakina sai kun kunyata, sai kun ga karshen shiga sha'anin aure."
Yaya ta ce "Ba zaka yi shiru ba Sadik?"
"Bar ni kawai Yaya na fa'di abin da yake zuciyata daga nan har gaban abada ba zan sassauta wa duk wanda ya nemi kassara mini zaman lafiyata ba. Ai ke ce babba amma kin kasa fa'da musu gaskiya, kin ki bada umarnin a fito mini da matata.
Ubana mahaifi da ya rike mini Guduyo sai da na motsa kwanjina bare kuma wadannan azzaluman makirai.
Ke da Baba kuma ko a lahira sai Abba ya ji irin juya mini bayan da kuka yi bayan ya shiga kushe wa."
Ya zaro tissue a aljihunsa yana goge hawayen idonsa yana cewa "Allah ya jikan maza! Allahu ka karbi hidimar da Abba ya yiwa zumunci".
Take Baban Yara shima ya fara hawaye, haka Yayar ma. Duk wajen sai kuka domin Abba ne kawai ya fado wa kowa. Yayin da Sadik yake cewa "Abba ka tafi ka bar ni na zama maraya. Ank'i yi mini kara, ank'i yi mini uzziri, ana shirin yanke mini zumunta da iyalina gaba'daya, an kwashe mini yarana, an dauke mini matata".
Take Baban Yara ya cewa Abdallah ya ha'da masa dukkan ahalin gidan, har Antin Zaria bai dauke mata ba.
Dake alhamis ne sai aka bar taron ranar asabar.
Hatta Baban Gusau sai da ya zo a dalilin Gudale ana idar da sallar juma'a ya tafi ya durkushe gabansa yana hawayen Baban Yara ya zuba ido su Sakina suna wula'kanta masa aure.
Baban Gusau ya bu'de masa wuta yana fa'din ai yasan komai shi ya cakalkala al'amuran aurensa da kansa. Tunda har yarinyar nan ta iya yin jarumtar barinka ka kure mata ne. Abin da kuma ba'a so namiji ya yi kenan.
Da zarar aka kure ha'kurin mace to kuwa ba kasafai take sarrafuwa ta da'din rai ba.
Gudale fa'di yake "Na yarda na yi kuskure Baba amma ka taimake ni kada ka zame mini baya, nan duniya bani da wanda ya fika, ka taya ni wannan fa'dan kowa ya juya mini baya."
Fa'da Baban Gusau ta inda ya shiga bata nan yake shiga ba.
Mussaman da ya fahimci idan ba'a tashi tsaye akan Gudale ba sai ya ha'da yakin basasa a family gaba'daya.
Domin ya lura so yake ya jagoranci yan'uwansa su bijirewa Baban Yara, da Yayar Kwalli.
Sanin da Gudale ya yi Baban Gusau mai zafi ne, mai kuma fed'e gaskiya ne ya sanya ya dinga hawaye yana cewa "Ka yi ha'kuri zan gyara komai. Na rantse da girman Ubangiji. Amma ka taimake ni ka bi bayana sun fi karfina. Abba ya yi ta fa'din kada a bar ni da kaina, kada a yanke mini zumunta. Ka saka baki a dawo mini da iyalina, yau fiye da wata biyu ana mini garkuwa da ita. Hatta y'ay'ana ma an kwashe mini su Baba. Ba kuma sharrin kowa bane illah Sakina da Al'amin. Baban Yara kuma ya basu dama, Yayar Kwalli kuma bata tsawatar ba. Duk an ha'de mini kai, kai ne kawai ka rage mini, dan Annabi Muhammadu Baba ka tsaya mini".
Nan da nan zuciyar Baban ta karye ya ce "share hawayenka. Gobe da asuba zamu dauki hanya da ni za'a yi zaman da Ibrahim ya shirya. Amma ka mini al'kawarin ba zaka sake yi mata abin da ya tunzura ta ba, ka mini al'kawarin ba zaka kunya ta ni ba."
Da sauri ya ce "Wallahi zaman lafiya zamu yi sosai, ai na ga aya na kuma fahimci ita ce duniyata".
Kusan kowa ya halarci wannan zaman, in aka dauke Halimatu.
Nasiha da jan hankalin Baban Yara ba karamin sanyaya jikinsu ta yi ba.
Yayin da Yayar Kwalli da Baban Gusau suka yi shiru basu ce komai ba.
Cikin muryar gargadi Baban Yara ya ce "Al'amin da Sakina".
Suka amsa a hankali.
Kai-tsaye ya ce "idan har kunsan inda Halimatu take to ku fito mini da y'ata domin duk cikinku babu wanda ya haifar mini ita.
Idan kuma kuna da alaka da guduwarta kuka boye mini Ubangiji zan kai wa k'ararku ya bi mini kadin kukan da kuka sanya ni".
Kan dole Sakina ta ce tana wajenta.
Nan da nan Gudale ya ce "A to ai yanzu a yarda da maganata. Tsakanina da ku kuma sai a lahira".
Baban Gusau ya daka masa tsawar da kowa sai da ya shiga taitatayinsa.
Ya ce "Sakaran wofi idan ka kuma bu'de baki sai ranka ya baci.
Ya kalli Maimuna ya ce "Ummu na fahimci ke ce kan gaba wajen wargaza mana zumunci, ki kiyayi kanki Wallahi! Ki rabu da son zuciya. Ace har ki zabi wata akan kanwarki diyaey Ibrahim?
To Zan sassaba miki, zan wula'kanta ki Wallahi. Ta dinga kuka tana bada ha'kuri.
Ya kalli Ramla ya ce "je ki kira mini iyayenku mata."
Ba jima wa Mama ta iso, sai can kuma Umma ta iso cikin isar ita din matar wansa ce fa.
Sosai Baban Gusau ya dinga yi musu nasiha, sannan ya ce "zaman lafiyar yaranku yana danfare ne da yadda kuka ha'da kanku kuke yi musu sassauci.
Matu'kar babu soyayyarku da albarkarku a cikin lamarinsu to akwai mishkila."
"Sakina
Tashi yanzu ki dauko mini Halimatu".
Baban Gusau ya fa'da cikin muryar umarni.
Ba musu ta mi'ke yayin da Gudale ya yi k'wafa ya ce "oh wai ace kai da dan-uwanka babu jituwa? Bashi da burin da ya wuce ya samu damar da zai shatale ka?"
Baban Gusau ya ce "Idan ka sake bu'de baki da nufin yiwa Sakina ko Al'amin rashin kunya sai na basu damar su cigaba da ajiyeta tunda baka ganin mutuncinsu".
Nan da nan ya ce "Na yi shiru Baba".
Takaicin duniya ya rufar wa Umma wai Gudalenta ne ya susuce ya hargitse akan Halimatu.
Ta sani tun lokacin da Abbansa ya ri'ke masa ita, ta fahimci irin yadda yarinyar ta yi matu'kar yin tasiri a rayuwar danta. Mussaman da ya tafi siyar da k'odarsa.
A yanzu kuma da wannan lamarin ya faru ta sake fahimtar idan babu Halima a tare da shi ba zai ta'ba zama mutum mai nutsuwa ba. Dan hakan ta ha'kura da kokarin kashe masa aure, amma dai ita bata sonta, zai yi wahalar gaske kuma ta so ta.
Amma zata yi iyakacin kokarinta ta daina yin dalilin samun rikici a tsakaninsu. Sannan zata so ya k'ara aure nan ma ta kudire ba zata sake nemo masa da kanta ba.
Kawai bata son ace Halima da y'ay'anta ne suke da alaka da dinbin dukiyarsa kawai.
Domin dai ya tabbata Safiyya ce dai ta ci galaba akanta.
Jikokinta ne magadan Gudale.
**
Ina kwnace akan katifata sai ganin Sakina na yi, a hargitse tana cewa "Taso Halimatu! Baban Gusau ne ya bani umarnin na kai ki yanzu yanzu."
"Ina jin haka na fashe da kuka sosai ina cewa "Ai kin ce sai na yi watanni shida kafin asan I da nake. Sannan sai ina so zan koma, idan bana so ba, zaki tsaya mini. Dama tun jiya da kike ta cewa Namoriki ya gigice, ya fita a hayyacinsa nasan akwai abin da zai biyo baya".
Ta ce "Kin ga tashi mu tafi, ai damar a hannunki take. Sannan ki bu'de baki ki fa'di komai kike ciki da shi a gaban Baban Gusau. Kuma zan fa'da miki wata magana guda daya tak. Kada ki yarda har sai ya shawo kan mahaifiyarsa ta amince da ke a matsayin surukarta, domin ita din k'ashin baya ce a zamanku".
Na sake fashe wa da kuka domin dai na riga na gane rashin Gudale a kusa da ni shine kwanciyar hankalina.
Wadannan satittikan dana kwashe babu shi, babu jidalinsa sune kwanaki mafi da'di a gare ni tunda na kammala sakandire.
Ba wanda yasan inda nake, ko mahaifiyarmu sai da Yaya Al'amin ya ga irin damuwar da take ciki ne, ya fa'da mata ina karkashin kulawarsa.
Amma ta cigaba da nuna wa bata sani ba.
Kan dole Sakina ta tisa ni a gaba ina rusa mata kuka tamkar wanda ta bubbuge ni.
Ta tunzoro ta ce "Ki mini shiru Halimatu."
Kuka nake bilhakki Ina cewa "Ba dan kin so na koma ba, ai da ba zaki fa'di inda nake ba Maman Nana".
A kufule ta ce "Fiye da wata biyun nan da kika yi ashe baki gode mini ba? Kinsan hardship din dana tsallake saboda ke kuwa?
To Umma saura kiris ta yi mini baki a dalilin Autanta ya fa'da mata nice barazana a rayuwarsa, yanzu haka bata karbar gaisuwata, Baban Gusau ne ya matsa mini sai na kawo ki, bayan Baban Yara ya ce ko mu fito da ke ko shima ya kai kararmu wajen mahaliccinmu.
Shin ya ya kike son na yi ne?"
Kuka ya sake goce mini domin ba karamin tashin hankali na tsinci kaina a ciki ba. Har cikin zuciyata na tsani Gudale, na na tsani ko zaman mota mu sake yi.
Haka muka shiga gidan ina rusa kuka tamkar wanda aka sanar da ni mutuwar Mama.
Muna isa falon da ake zaman. Gudale ya wani zabura ya yo wajena yana fa'din "Bana son kukan nan kin sani. Share idonki mu yi tafiyarmu gidanmu ki fa'da mini duk abubuwan da ba kya so daga gareni In sha Allah zan kiyaye".
Ina kallon yadda Umma ta yi kicin kicin.
Yayin da Baban Gusau ya ce "Sadik idan na sake magana Zanci mutuncinka. Wanne irin yaro ne kai haka da baka san kunya da kawaici ba?"
Nan da nan ya kame bakinsa ya dinga cewa "Yi ha'kuri Baba! Kada ka yi fishi dan Annabi Musa".
Baban Gusau ya ce "Dan wa ka ce Sadik?"
Da sauri Gudale ya ce "Ina son na tuno maka irin girma da karamar Wanda ka ci sunansa ne. Abba ya ta'ba bani labarin Mahaifinku ya saka maka sunan ne saboda Girmama Annabi Musa (A.S).
Allah ya k'ara maka lafiya da karama Baban Gusau.
Gaba'daya Baban Gusau ya kasa cewa komai domin duk zafinsa sai da Gudale ya nemi birkita shi.
Nasiha irin wacce Abba ya wanzu yana yi mana ita Baban Gusau ya dinga yi har kowa jikinsa ya yi sanyi wasun ma har da k'walla.
Yayar Kwalli cikin kuka ta fa'di wula'kanta Baban Yara da Maimuna ta jagoranci kanneta da suka yi.
Baban Gusau ya dauki salati ya dinga zaginta irin wanda bata taba zaton zai yi mata irinsa ba.
Ya ce "Maimuna saurara na fahimci ce kece kike neman fita zakka, ke ce kike son ruguza dukkan ginin da Ubanku ya shafe lokacinsa yana ginawa. Wallahi hakkin Ibrahim zai iya damalmala miki lamarinki, ba irin biyayyar da bai yiwa Ubanku ba. Kun sani kuma ba haihuwarsa ya yi ba.
Zamu saka kafar wando da ke, domin har yau din nan baki wuce hukuncina ba, shasha marar tunani.
Haka ma Juwairiya ma ya wanketa, ya sanya suka tsuguunna har kasa suka bawa mahaifinmu ha'kuri. Ramla ce da ita a kullum take tsakiya, bata bayanmu, bata kuma bayam uwarta, a tsakiya take.
Gudale har da ri'ke kafar Babanmu yana fa'din "Abba ya ce "Biyayya biyu zan yi maka. Ka dubi Àllah da manzonsa ka yafe mini. Har Gusau na je na dauko maka dan-uwanka dan ya baka ha'kuri. Ka daina zuba wa rikicina da su Al'amin ido. Sun riga sun ha'de mini kai Baba. Kamata ya yi kai ka ha'da kai da ni."
Baban Gusau ya ce "Sadik rufe bakinka ko yanzun na saka Ashir ya lallasa mini kai. Soko kawai. Kullum kalaminka daya babu sauyi?"
Ba'kin ciki ya turnike Gudale a gaban Ashiru za'a yi masa irin wannan yankar kaunar?
Ya kalle ni ya ce "Yi hakuri Sadiya kin ji. Goge Idonki ki fa'da mini matsalarki, me yasa kika manta nine ubanki?"
Ina kuka sosai na ce "Ba manta wa na yi ba, na ji tsoron kada ya zo gabanka ya lauya zance, ya kuma sanyaya maka jiki ta hanyar cewa shi maraya ne".
Baban Gusau ya ce "Ai ni bai isa ya mini irin wannan iyashegen ba."
Nan da nan Gudale ya ce "Ina neman alfarma Baba! Ka sallami kowa a bar mu da kai. Ina jin tsoron magauta su ji sirrin gidana, a mini wannan alfarmar darajar Manzon Allah (S.A.W).
Baba ya mike ya ce "Mu biyo shi zuwa bukkar waje, su kuma su jiramu bai kammala ba.
Ban ji nauyi ba, kaina na kasa na fayyace komai har wula'kancin da yake yi mini a falo, da kuma zagi da duka a gaban y'ay'ana. Baya ga haka tarbiyar da yake son yiwa Aman da ware shi da yake yana fifita shi.
Da kuma matsalar Umma, da su Anti Maimuna ta yadda suka fifita bare a kaina, kuma duk yana kallo bai ta'ba taka burki ba.
Baban Gusau ya dinga jinjina girman iskancin Gudale.
Fa'da da yarfe ba irin wanda bai masa ba.
Karshen karshe sai ya buge da bani ha'kuri, da falalar mai yafiya mussaman idan yana da ikon ramako, amma ya ha'kura ya mance komai.
Ya kausasa murya ya ce "Sadik! Wallahi ka ji na rantse ko?
Duk ranar da sake yi mata tozarcin nan a falo da kaina zan jagoranci raba aurenku. Balle kuma duka ko zagi, ka tabbatar ka daki aurenka".
Baki na rawa ya ce "Na ji Baba! Zan kiyaye, ba zan sake ba".
"To kin ji Ssdiya, nine alkalinki komai ya taso kar ki sake ki yin shiru, idan kuma ya cigaba da yin wannan dabi'ar ki bugo waya ki sanar da ni, amma yanzu na kashe wannan maganar, kibi mijinki ku koma gida a cigaba da ha'kurin zaman, amma ban da na cuta.
Ba kunya na ce "Baba yi mini afuwa! Amma shawara kake bani na koma dakina ko kuwa umarni ne?"
Ya kuwa ce "Shawara ce Sadiya!".
Ba jin nauyi na ce "A sake yi mini afuwa, a gafarce ni Baba.
Idan shawara ce ka yi ha'kuri ban karba ba Baba. Domin wacce duk kuka kuna bani ina bi da dukkan zuciyata amma bata yi tasiri a wajen wannan Dan halikin ba. Amma idan umarnine to zan yi maka biyayya da dukkan iyawata".
Baba ya ce "Kalu Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun".
Wajen ya dauki shiru tsawon lokaci.
Gudale ne ya fara gazawa da shirun ya ce "Dan Allah Baba ka yi wani abin. Kar ka bar ni da kaina. Na gamsu duk abin da ta fa'da ina yi, sai dai wani lokacin ita take tsokanata. Amma na yi al'kawarin ba zan sake ba, idan kuma na sake duk matakin da zaku dauka ba zan yi kuka da kowa ba sai da kaina. A mini ha'kuri ba dan halina ba".
A sanyaye Baba ya ce "kin ji Sadiya".
Na fara kuka mai tsananin gaske, na kasa bu'de baki na ce komai.
Kukan da ya gigita su mussaman Gudale.
Domin ya sani kuka ne na ba'kin ciki da kaico, ya kuma hango tawayar da soyayyarsa ta yi a zuciyata.
Murya na rawa ya ke cewa "Allah ya baki hakuri. Dan son ki da Annabi ki sake yi mini uzziri ko da shine uzzirin karshe."
Baba ya numfasa ya ce "Ki yi ha'kuri kin ji."
Gudale a gigice ya ce "kin ji ya sake baki ha'kuri, komai kike so zan yi miki, na daina yi miki duk abin da zai sa ki yi ba'kin ciki da gangan".
Tsawon lokaci ana ta turzawa amma na kafe ni dai na gaji da zaman.
A karshen dai Baban Gusau ya yi ta maza ya ce "Ya bani umarnin na koma dakina.
Na fashe da kuka na ce "Baba duk abin da yake so hakan za'a yi masa kenan?
Na rantse maka ina koma wa zai cigaba da cin zarafina".
Baki na rawa ya ce "Guduyo na ga aya ai. Wallahi Tallahi ba zan yi ba. Ai dai ga Babanmu nan shine alkalinki, shine shaidarki, kuma duk abin da ya shimfi'da mana akansa zamu zauna, ki yi ha'kuri kin ji Guddin Abba".
Ya zarce da cewa "Tunda aka dauke ki har yau din nan na rantse miki da girman Ubangiji ban sake samun nutsuwa ba, an dauke mini su Amnah, kema bakya kusa ban fahimci kune duniyata ba sai yanzu.
Baba ka zama shaida kome take so matu'kar bai karya ka'ida ba, zan yi mata, hakanan zan yi iyakacin kokarina na kiyaye cin mutuncinta ta kowacce fuska. Amma kuma ban yi al'kawarin ba zan bata mata rai ba, ban yi al'kawarin ba zamu samu sabani ba, amma na yi al'kawarin zan yi kokarin kiyaye hukunci cikin fishi. Zan kuma yi kokarin yi mata sassauci a sadda ta kuskure mini."
Baba ya saki nannauyar ajiyar zuciya ya sake cewa kin ji ko Sadiya. Da ni ya kafawa kansa hujja".
Hawaye ya goce mini na ce "Tunda ka bani umarnin komawa shikenan amma ba yanzu ba Baba. Ka tafi da ni Gusau nan da wata biyu ya turo Umma ta yi masa bikona a hannunka da sharadin tana son zamana da shi.
Sannan yadda yake tisa ni a gaba na bata ha'kuri ko da ban yi mata laifi ba. To wajibi nima sai ya bada ha'kurin zagin da yake yiwa tawa uwar".
Da sauri Gudale ya tsugunna guiwa bibbyu ya ce "Na janye, bacin rai ne, da sharrin zuciya. Mama uwa ce a wajena, aurena da ke kuma ya sake girmama lamarinta