Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
akan al'amarinta ba. Kana sonta menene dalilin da ba zaka nutsu ka mutunta zamanku ba?"..
Ya bata rai ya ce "Ai shikenan tunda kin gama bada ni a gabanta. Sakina kin sani ni mutum ne mai son sirri, mai son a girmama shi, akan me zaki mini hakan a gabanta. Yanzu kin bata lasisin da zata yi ta yin iyashege tunda ta sani an tsaya mata."
Ya kalle ni ya ce "Ki je ki biya Malaminki. Kin kwace mini Abba da sakinata. Kina kuma shirin raba ni da Al'amin. Babu komai Allah ya bani ladan hakuri kawai."
Ya juya ya fara tafiya da nufin barin dakin sai kuma ya dawo.
Ya kalli Sakina ya ce "kun dame ni akan kada na muzanta ta a gaban Amaryarta, saboda kuna kishinta. Amma ni ta wula'kanta ni, ta nuna wa amarya am nothing to her.".
Na zare ido na ce "Me na yi maka dan Allah?"
Ya harare ni ya fita yana cewa "Ki je kin samu. Ki kuma jira abin da zai biyo baya domin tare zamu dandana wannan ba'kin cikin da kika kunsa mini".
Sakina ta mini signal da Ido akan na rabu da shi.
Sai da ya fita ta ce "Idan yana wannan dagewar, ai yi zaki yi, bakisan kin yi laifi ba, bare har ki damu."
A hankali na ce "Tom". Domin gaba'daya jikina ya yi sanyi a dalilin yadda ya rikice cikin dakika ka'dan tamkar mai rauhanai.
Da sauri Sakina ta fita falo a tunanina bayansa ta bi. Ashe wayarta ta dauko. Ta kishingi'da ta kunnata sai ga maganganun da muka tattauna bayan ta shigo daki suna fita tar tar.
Ta dinga murmushi tabbacin Gudale ya yi abin da ya yi mata dadi.
Ta kalle ni ta ce "Na Moriki yau ya yi bin a yaba masa."
A sanyaye na ce "Me kika ji na fa'da da yake nufin na yi masa cin fuska?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba ki yi komai ba. Kawai tuntsirewa yake son yi. Kin yi jarumtar kara masa kwanakin amarci, sai dai na so jarumtar tafi haka, ina ma wata kika bashi, ta yadda zai gama doki da rawar kai kafin ya dawo miki".
Na yi kasa da kaina tabbacin ba zan iya ba, satin biyun ma ba karamin karfin hali na gwada ba".
Tare muka hau saman amarya da Sakina. Ta karbe mu da sakakkiyar fuska, ta kuma shiga da mu ko ina. Tabbas an shirya mata kayayyaki na alfarma, sai dai kuma basu kere nawa kayan ba. Muka zauna a falo ta bamu ruwa da lemo. Yayin da Gudale yake kishingi'de a kujera, a yanayinsa na fahimci baya cikin sukuni sosai. Yayin da duk motsin da zan yi said na ga Munubiya ni take kallo, wani irin kallon kurillah take yi mini da ya sanya na tsargu sosai. Bamu jima sosai ba muka dawo.
Kwanakin amarcin nan ba k'aramin juriya na yi ba. Domin Umma ta zo ta ga dakin amarya, karon farko da ta shigo gidan Gudale, amma ta kasa yi mini kara ta shigo wajena. Ko da ace ta shigo din tabbas zan ji a raina ba dan ni ta zo ba, amma dai na ci albarkaci.
Amma da suka hau saman amarya suka gama zamansu ba kunya ya ba kara suka yi tafiyarsu. Idan na ce ban ji haushi ba, na yi karya. Na dinga share hawaye ina ganin idan Umma tana ganin ni ba jininta ba ce, ba zata yiwa mijinta kara ba, to Anti Maimuna fa? Ace har zata ita zuwa ta shiga dakin Munubiya da basu hada komai ba illah matar kaninta. Amma Ni da jini ya ha'damu ta iya yi mini irin wannan wula'kancin?
Yini na yi ina share kwalla.
Komai ya nemi kwace mini a wannan kwanakin a dalilin shi kansa Gudalen wani irin fishi yake yi mini da bansan dalilin yinsa ba.
A daddafe aka cinye wannan satin uku da na lamince su yi tare. A lissafin kwanaki tabbas sati uku ne, amma a wajena sun zarta watanni uku nisa da tsanani. Kusan kullum sai na yi kuka wala da rana, ko da safe, idan nasa kaina a filo da daddare kuwa wannan ya zama wajibin.
Na yi zuru-zuru. Fuskata ta zama yar kuyas, ido ya sake fito wa.
Bana samun sauki sai na fita wajen aiki, idan na dawo kuwa tamkar a kofar gidan nake ha'duwa da bacin rai.
Kowa ya ganni yasan na fa'da amma ba wanda yake tambayar ba'asin ramar tunda ana ganin ina cikin yanayin da bai kamata a tambaye ni ba.
Abba ne kawai duk sanda na shiga gaishe shi, sai ya ce "Kara hakuri, nasan ke din mai hakuri ce, amma a wannan lokacin da ake son sai kin gaza, Sai nake son kin ninka juriyarki, ki kuma tsananta addu'a. Madallah da ke Halimatu".
Ire iren wadannan kalmomin na Abba su suke sanyaya mini zuciya, na samu k'warin guiwar ha'diye dukkan kalubalen da ake jifana da su. Domin na riga na fahimci ba abin da Abba yake so irin aurena ya tsira.
Ranar da zan karbi girki, yini na yi cikin doki da farin-cikin zan samu yau na yi cikakken barcin da na jima ban yi ba. Na tanadi wannan ranar, mussaman Aisha lame ta shirya ni da products din oriflame da sai manyan mata ne suka san Martabarsa. Bare kuma kayayyakin *Faseelat* da kullu yaumin nake hadiyarsu.
Cikin Sa'a ranar week end ce dan haka ina gida. Cikin karsashi nake yi masa snacks din duk da nasan yana sonsu.
Ni da kaina mamakin yadda na zaku mu kebe nake yi, ban sani ba, ko dan tsawon lokaci mai yawa bamu hadu bane, domin dai haduwar da muka yi a falo ta tsiya tsyia ce ban gane komai ba sai wahala. Tun lokacin kuma ba'a sake ba. Itama kuma kafin ayi an dauki lokaci mai yawa tun kafin na haihu.
Ko kuma supplement din da nake sha ne yake tasiri.
Tun karfe biyar na yi wanka, na yi kwalliya tamkar me shirin zuwa gasar miss Nigeria. Da kaina na dinga gode wa Ubangijin da ya kyautata mini halitta.
Sai dai me? Tunda ya dawo daga aiki na yi zaton zai shigo mini, amma sai jin takunsa na yi yana hawa sama.
Nan da nan zuciyata ta fara baci, amma dai na sake na yi masa uzzirin ko zai dauko wani abu ne ko dai wani al'amari.
Amma ga mamakina ya fito ya wuce sallar maghrib da ya dawo ma ko lekena bai yi ba, ya sake hawa sama abinsa.
Daga lokacin na karaya komai ya kwance mini, a falo na zube ina wani irin kuka, tamkar kirjina zai fado.
Wanne irin muzanci Gudale ya yi mini tanadi haka?
Rana ta biyu da na yi kwanan zaune ba tare da barci ya sure ni ba.
Na yi kuka fiye da kukan da na yi da na ji labarin karin aurensa.
Tun a ranar kuma wani irin abu ya tsaya mini a cikin zuciyata.
Washagari sassafe ya dawo daga motsa jiki ya shigo mini yana sanye da kayan motsa jikin, kafarsa sanye da boot an rubuta sport.
Ina zaune a falo ido ya yi luhu luhu, tamkar matar mamaci. Karon farko da na gan shi na ji har cikin zuciyata bana son ganinsa.
Ya zauna ya na mini tambayar da ta nemi sumar da ni.
"Menene ya same ki haka Gudidina?"
Na kalle shi hawaye na goce mini.
Na kasa cewa komai. Na tuna a safiyar jiya asabar sai da muka yi maganar da yamma zan kar'bi girki, amma ya murtsike ya kaiwa wata hakkin da yake nawa ne. Har da yamma ma da na kammala snacks sai da na yi masa waya akan ya taho mini da youghrt sannan kuma kar ya tsaya a ko'ina na tanadar masa snacks kala-kala.
Ashe kuwa babban wula'kanci ne ya tambayi ba'asin kukana ko ba'asin halin da nake ciki.
Ya mike ya ce "Na dai tambaye ki, na fita hakkinki.
Ya kalle ni, ina kuka! Ya ce "Dama zan fa'da miki ba sati biyu ya kamata ki bani ba, hudu zaki bani, kin ga ya zama sati biyar, a lissafin kwanaki kuma talatin da biyar.
Jarumta ta shige ni ta ban mamaki, na zuba masa ido sosai na ce "Na baka shekaru hudu Yaya Sadik".
Na mike na bar shi a wajen.
Ya tunzura ya ce "Kika sake yi mini wula'kanci, ni zaki tashi ki bari?
Waton kin wula'kanta ni, kin ci mutuncina a gaban wata ta hanyar neman kai da ni na sati biyu. shine yanzu kika yi na shekaru hudu?"
Na ja tsaki na ce "Na gama magana kuma Sadik! Na baka shekaru hudu, dan Allah ka yi tozarcin da yafi na jiya tsanani".
Yadda na kwana ban runtsa ba, haka na yini ban tsinana komai ba. Kuka da sallah kawai nake yi. Har dare ban saka ko ruwa a bakina ba, tashi guda na yi wata irin rama tamkar na shekara ina ciwo.
Kwana biyu ina cikin wani irin tashin hankali, da bana fatan ko makiyata ta shiga irin wannan yanayin. Amma da na tsananta addu'a, na fara azumi, a dalilin abincin ba iya cinsa nake yi ba. Dan haka sai kawai nake yin azumi, nake nacin tsayuwar dare. Alhamdulillah kuma na samu sassauci.
A kwana na uku na dawo daga asibiti ba jima wa. Munubiya ta shigo wajena ta ci kwalliya, kuma ta yi k'yau matuka da gaske. Hannunta dauke da babbar leda mai kyau da alamu suka nuna daga waje aka taho da ita. Duk da kishinta da yake cina, da hannu biyu na marabce ta. Ina ta yi mata yake bayan na baibaiye ta da ruwa da lemu, da snacks din da na bata lokaci na yiwa Gudale amma ya mini tofin Allah tsine.
Da muryarta da gayu da ilimi suka ratsa ta ce "Maman Amnah bayan sati biyu da kika bani, sai kuma kika sake kara mini da wasu 2weeks?"
Na sandare a zaun, na kasa cewa komai illah murmushi kawai na yi. Ta zarce da cewa "Na fa'da masa ban karba ba, wanccan dai da na karba, na yi godiya, na jinjina miki. Domin ni dai ba zan iya abin da kika yi ba. Dan haka nan da kwana hudu ki shirya karbar mijinki, Na gode sosai".
Na yi jarumtar ha'diye komai na ce "Babu damuwa ai ni na baki, sannan mijina na yiwa alheri dan yasan na gode da adalcin da ya yi mini a zamanmu."
Ta kai samosa bakinta ta ce "To dai ni ban karbi wannan k'arin ba."
Muka yi shiru, muna kallon talabijin.
Muna hakan iyalan gidansu suka zo mata. Ta ce su iso wajena. Na karbe su kuwa da girmama wa. Basu jima ba suka tafi wajenta yayin da na juyo musu cake din da na yi, ya zame mini na ba'kin ciki.
Ta karba tana godiya, ta turo mini ledar gabanta ta ce "Gashi ".
Na yi godiya, na rakata har kafar bene sannan na dawo wajena.
Na zauna ina mamakin lamarin Gudale wato ce mata ya yi ni na kara masa kwanakin ba wai kwace mini ya yi ba.
Na dan samu sau'ki amma ka'dan.
Na duba ledar, kayan da na gani na alfarma sun bani mamaki domin hatta super wax guda biyu ce, da kuma dankararen leshi da mayafinsa. Ga kuma turaruka da sabulai masu tsada.
Na kai cikin drower na adana, da nufin zan nuna wa Sakina.
Haka ranar da ya cika sati bayan wancan kwanakin da aka yi cikin yardata, ya tattaro ya dawo dakinsa na wajena. Amma ko ta kaina bai bi ba. Asalima yana dawowa yake rufe dakinsa. Abin dana fahimta, ya k'udire sai ya rub'anya kwanakin da ya ce na yi neman kai da shi.
Idan kwanakinta ya zo, yana rawar jiki, zai haye sama, idan ba dace na yi ba, ko gilmawarsa bana ga ni".
Haka nake rayuwa, ba wanda na bu'de baki na ce ga halin da nake ciki
Hatta mahaifina da bai cika saka baki akan al'amarina ba, sai da ya zaunar da ni a gaban mahaifiyata ya dinga yi mini nasiha da rarrashi akan na saukaka wa kaina kishin dana sanya a raina nake neman illata kaina.
Yayin da Mama ta ce "Idan kika kashe kan ki, ko kika hadu da jinya, shi bashi da asara.
Akan me zaki k'warzabi kan ki irin haka?".
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wanannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
*SDK*
*81&82.*
Na kasa bu'de baki na ce ga halin da nake ciki. A shekaruna na k'asa da talatin miji ya dauke mini kwana. Haka siddan, tsabar ya so wula'kanta ni.
Na dinga kukan da ya ta'basu. Mama da yake mace ce sai ta taya ni, muka saka Baba a gaba muna yi masa kukan da ya ki'dima shi.
Cikin karfin hali ya ce "Halimatu so kike yi na kasa yin jarumta a cikin zumuncina da dan-uwana?
Abbanku duk maganarsa da tunaninsa akan ki ne, ki yi hakuri, kada ki kunyata shi."
Na goge ido na ce "Na yi Baba".
Na tashi na tafi, babu ko waiwaye.
Haka Abba duk sadda zai gan ni, sai ya ce "Kin kasa yin jarumta ko Halimatu?"
Na kan ce "A a Abba ai bani ma da matsala. Sai da na ga ya tsananta da tambayar sannan ce masa "Fama nake yi da zazzabin dare, ga ba cin abinci, sannan ga kasala, wata'kila dai sai na ga likita an yi mini test."
Nan da nan, na ga ya samu k'warin guiwa har yana addu'ar Allah ya rabamu lafiya.
Muka shafe kwanaki muna haka, bai waiwaye ni ba, nima kuma na hakura da shi, idan girkina ne, yana dakinsa a garkame, sassafe zai fice, idan ya dawo kuma ya shige ya rufe. Na tattra na zuba masa ido, amma abin yana cina, na kuma yi al'kawarin ba wanda zan fa'da wa wananan matsalar domin ina ganin ba karamar fallasa zan yiwa kaina ba.
Ba irin rarrashi da hilar da Sakina ba ta yi mini ba, akan mecece matsalata nake wannan ramar da ta sanya na yi muni tunda asali ni mai garin jiki ce. Amma na yi juriya na ce bani da ita, kawai zazzabi nake yi da daddare.
Umma kuwa ta dinga farin cikin yadda take ganina domin haka take so ta sanya ni, cikin tashin hankali ta yadda hankalin uwata zai tashi. Tabbas a wannan karon ta yi nasarar ganinmu cikin tasku domin Mamana ma ramar ta dinga yi a dalilin halin da take ganina a ciki duk da ban ta'ba bude baki na ce mata ga matsalata ba. Amma tana ganin yadda Umma take gayyato k'awayenta ganin Amaryar Gudale. Abin da ta'ba yi mini ba, ni asalima bata taba zuwa gidana ba.
Haka nake rayuwa, ba wanda na cewa ga halin da nake ciki.
Amma ramar da nake yi, ta yi matu'kar damun dukkan ahalina.
Bai kula ni ba, sai da ya yi adadin kwanakin da ya kudire. Yayin da ni kuma na ki kula shi. Idan ya shigo dakina zan gaishe shi, amma bana ajiye masa abinci hakan nan ban yi gigin shigar masa daki ba, nima kuma bana bari ya zo nawa.
Zaman ya yi tsauri a tsakaninmu kowa a hassale yake da dan-uwansa.
A haka har amryarsa ta yi wata biyu, amma ni da shi abu kullum sake rikecewa yake domin na riga na taurare masa irin yadda bai yi zaton zan iya ba.
Dai-dai lokacin kuma ya fara gazawa, ya fara gasgata ni shekaru hudu na bashi.
Tun yana ganin bai kyautu ya neme ni ba, har ya ha'kura ya sauko ya fara neman shiri.
Ni kuma Ubangiji ya sanya mini ha'kurin da ban yi zaton zan iya yinsa akan Gudale ba.
Gaba'daya na tsike zuciyata, na kudire ba zan saurare shi ba, sai an yi shekaru hudu cif cif, idan muna da rai kuwa ranar da shekaru hudu suka cika a ranar zan bar aurensa, zan nuna masa zan rayu ko ba wanann mua'amalar, zan kuma tabbatar masa, na wuce irin wannan tozarcin da ya yi mini, mun riga mun yi zaman da ya fahimci alamurana ciki da bai, yasan abin da zanyi na gaskiya, da wanda zan yi da nufin tozarci. Dan haka rainin wayo ne kawai zai sa ya ce wai wula'kanta shi na yi da na k'ara masa kwanaki.
Tun yana ganin abin wasa ne har ya sare. Ya dinga rarrashi da neman sulhu, amma ko a jikina.
Rannan sai gashi ya dauko mini Sakina har cikin dakina.
Ta kada ta raya na fa'di menene ya ha'damu na tubure akan babu komai.
Shi kuma ya kafe akan fishi nake yi masa, akan laifin da bai sani ba ta bincike ni.
Da Sakina ta tsananta sai na fa'di da dalilin rashin yi masa abubuwan da ya lissafa.
Sai kawai na fashe mata da kuka.
Ba'kin cikin ya turnike ni mai tsananin gaske.
A dalilin yadda ya takarkare yana cewa Sakina."Ai sam sam na canja hali, tunda ya yi auren nan shikenan na dauki masifa na dora a raina".
Na dinga mamakinsa na yadda ya lauya zance haka tamkar mace.
Dan haka nima sai na ha'diye kukana na kalli Sakina na ce "tunda ya dauko ki ai kinsan bashi da gaskiya, amma na rufe wannan maganar tunda ya ce masifa na dora wa raina, ki yi tafiyarki, ki ta yi mini addu'a Àllah ya yaye mini masifar da ta dame ni."
Ina rufe baki ya ce "Sakina ba haka za'a yi ba Wallahi! Kashe wannan dambarwar kawai zaki yi tunda ke tana ganin mutuncinki".
Ta kalle shi, kallo mai tsananin gaske ta ce "Me ka yi mata Na Moriki?"
Ya bata fuska ya ce "Idan ina kaunar irin hakan da kike yi mini shege nake, ta yaya zan dauko ki akan ki kashe mini fitinar da ta sako ni gaba kuma ki zo kina neman yi mini bita da kulli? Kawai ki zartar mata da hukuncin ta zauna lafiya da mijinta tunda ta gamsu ke din yayarta ce, amma sai ki bararraje kina neman jin ba'asin da bai shafe ki ba".
Ta girgiza kai ta ce "Halima ki yi hakuri kin ji. Kara ha'kuri".
Na kalleta na ce "Ko da idan na yi ha'kurin akwai cutar wa a ciki?"
Ta zuba mini ido har sai da na ji a jikina ta ce "Ban ce ki yi hakuri na cutuwa ba, amma idan da yiyuwar zaki iya daurewa to ha'kurin shi ya fi."
Na yi yak'e na ce "To shikenan Maman Nana, na yi ha'kuri".
Sakina ta ce Na gode miki".
Ta tafi ba tare da ta sake cewa komai ba. Yayin da ya bita ina jin