Author : SURAYYA DAHIRU Category : African Stories & Novels
na hadu da jakadiyar su da ta lakanci mayukan da suka dace da kowacce irin fata walau dry ko oily. Tun lokacin yanmattancina na gasgata mayukan oriflame da *Aisha lame* ta za'ba mini su, har yau kuma ban canja ba, domin kuwa duk tsiyar Gudale da kansa yake bani ku'din siyan mayukan Yana fa'din yana ganin amfanin su.
Tuntu'be ta Dan samun naki nau'in man da zai dace da fatarki mussaman a wannan season 'din na hammattan.
07036662633. Na gasgata ta.
Sai da na kammala komai, dakin ya kaure da kamshin kayan da na yi amfani da su. na fita kamar wacce zata je kicin sai kawai na shige dakin su Afrah na rufe na yi kwanciyata.
Har barci ya fara 'dauka ta na dinga jin bugun kofar tare da 'kiran sunana.
Na yi tsaki sosai na yi bakam.
Da safe kuwa, da wuri na fito na shirya masa abin karin kummalo.
Ya fito cikin shadda getzna fara 'kal.
Kyau iya kyau ya yi, duk da fuskarsa a 'daure take, idonsa na gefen dama jini ya kwanta a ciki tabbacin yana cikin bacin rai mai tsananin gaske.
Na yi kamar ban gane ba na ce "Ina kwana? an kammala abinci".
Bai ko kalleni ba, bare ya amsa, ya fice da Aman.
Na yi murmushi na ce "wanzami bai son jarfa.
Kai tsaye wajen Umma ya nufa, ya same ta ta idar da walaha. Yayin da Amnah take kan gado tana barci, Afrah kuwa tana tare da Antin Zaria a 'daya dakin.
Ta karbi Aman tana yi masa wasa.
Ta shafa cikinsa ta ce "Da alamun cikin nan bai cika ba maigidana".
Nan da nan ta 'kira Abida ta dauke shi tare da cewa "ki ha'da masa tea ya sha".
Ta zuba masa ido sosai ta numfasa ta ce "Ya jikinka?"
A hankali ya ce "Da sau'ki Umma! Dama zan fa'da miki ne zan je Gusau".
Da azama ta ce "Yanzun?"
Kai kawai ya daga mata. Ta zuba masa ido sosai tana nazartar sa. Cike da kulawa ta ce "A cikin halin da kake ciki na jinya zaka dauki mota ka tafi har Gusau? Idan baka damu da rayuwar ka ba ni na damu dan haka ba inda zaka je".
Ya yi kasa da kansa ya ce "Ki yi hakuri ya zama dole ne, idan ba zuwa na yi ba, ba zan ta'ba samun nutsuwa ba."
"Fa'da mini me zaka je yi"
Ya yi shiru domin a yanzu ba zai ta'ba iya fa'din laifin Guduyo a gabanta ba.
Dan haka sai ya ce "Zuwa zan yi na gaida Baban kawai".
Ta ce "To sai ka samu lafiya sannan zaka je din".
Ya yi shiru amma yana jin tamkar ya yi ta ihu, ba abin da yake so a yanzu irin ya samu kwanciyar hankali. Ya tabbatar kuma ba zai samu ba, sai ya samu aminci da Guduyonsa.
Cikin rauni ya ce "Zan iya zuwa Umma".
"Ba fa zaka je yau ba wallahi".
Jin ta rantse ya sanya shi ha'kurin dole.
Ya tashi yana cewa "To shikenan bari na koma na dan kwanta".
Ta amsa da ambaton "Hakan ya fi".
Ya shigo da sallamh ya tarar da na yi wanka na gyaran gidan tsab, ina zaune a falon ina karyawa cikin nutsuwa. Sanye nake cikin dankararen leshin da Kawata ta zana shi da kanta, ta yi oder, Ni kaina leshi ba karamin shiga raina ya yi ba, sannan ban ta'ba ganin wata da shi ba, saboda selected oder ne na manyan Mata. *Amyas newly & faily items* kenan.
Murmushi na yi na yadda na samu hayar gida cikin sau'ki da rahusa a kuma area mai kyau da tsaro a hannusu. Na sake tuna sadda suka zo har guday suka sayi kujeruna cikin aminci da mutuntawa.
Na tuna injin wanki na hannu mai kyau da na siyawa Aziza a hannusu tamkar sabo Kuma cikin farashi mai rahusa.
Idan kuna neman komai da ruwanki to samu *Amyas newly & fairly used items*
Komai na su cijin tsari da sauki da kuma.mutuntanta abokan huldarsu.
O8083909947.
Ya wuce wajen cin abinci ya zubo ya dawo falon ya zauna kusa da ni.
Har ya kammala zaman kurame ne a tsakaninmu.
Kallona kawai yake yi na sani kwalliyar da na yi ta ki'dima shi, sau tari
yana yawan tambayar inda ake zabga mini dinkuna na garari. Da kansa ya nemi shagon telar Dan ya gasgata maganar da na fa'da masa cewa mace ce. Domin a farko ya dauka namiji ne yake auna ni saboda tsananin yadda idan aka mini dinki suke zama a cikina na yi cass, duk da ina da jiki.
*Umm Muhd collection* kenan kwararriyar tela kuma shahararriyar yar kasuwar da bata saba al'kawari duk abin da kike so zata kawo miki har gida, dangin sutura, hatta kayan kicin, zababbu rantsattsu kuma a saukaka miki. Tabbas ni shaida ce. Wanda duk yake group dinta zai shada hakan 08063358662.
Ya kasa ha'kuri ya dube ni ya ce *"Halah* fa'da mini matsayina a gidan nan".
Ba ja in ja na ce "Mai gida mana".
Yana kallon nawa dai ya ce "Amma saboda kin samu daurin gindi shine na zama banza, na zama abin wula'kantawa a wajen ki?
Sau nawa zan baki ha'kuri? Me zan yi ki gane ina son ki? Me zan yi dan na samu zaman lafiya da ke? Kin hana ni nutsuwa, kin gigita mini zaman lafiya ta, ya ya kike so na yi ne?".
Na yi shiru na 'ki tankawa.
Ya sake cewa "Tunda kika dawo a cikin rarrashin ki nake amma kin kafe kamar Dutse.
To gaskiya zan fa'da miki na gaji, *Haka ya isa(Fatima Aminu Baba).*"
Nan ma na yi shiru bance komai ba.
Da ya gaji da jiran amsa ta. Cikin bada umarni ya ce "ki tashi ki je ki gyara mini dakina".
A gajarce na ce "Na gyara tuntuni! Shiga ka gani."
Bai musa ba! Ya tashi ya nufi dakin.
Ya ganshi a tsabtace. Komai a kintse, haka ban'dakin ga kuma kamshin turaren mutanan gabas na tashi.
Ya kwada mini kira "Hal Mohammadah".
Na zum'bura baki na amsa sannan na mi'ke na tsaya daga bakin kofar dakin.
Na ce "Ga ni".
Yana mini wani irin kallon da yake rikita ni, ya kashe murya ya ce "Gyara ya yi kyau! Na gode miki, Allah ya yi miki albarka".
Na amsa da "amin" a kasan ma'koshina.
Ya matso kusa da ni ya kamo hannuna ya ce "Shigo mana Guduyo ki ji abin da zan fa'da miki".
Ya jani har tsakiyar dakin ya yi 'kasa da murya ya ce "Taya ni mana mu yamutsa shimfi'dar nan. Ba dan ni zaki yi ba, ki duba Ubangijin da ya wajaba miki yi mini biyayya."
Na tsuke fuska sosai ba tare da na ce uffan ba, idona ya cika da 'kwalla na kasa magana.
Ganin hakan ya saka ya fara kokarin rage tufafin jikina.
Bakina na rawa na ce "Ba zan iya ba".
Da sauri ya dinga fa'din "Zaki iya baby nah! Bari a fara 'din"
Na fisge jikina na shammace shi na fito kusan a guje.
Ya biyo ni muka fara kokawa, ganin da gaske zai kai ni 'kasa ya sa na fara kuka ina cewa "Na rantse sai na fa'dawa Baban Gusau baka daina wula'kanta ni a falo ba".
Tamkar na watsa masa ruwan zafi haka ya sake ni a zabure.
Murya a dashe ya ce "Ba anan nake nufin yi ba Wallahi! zo muje ki taimake ni dan girman Allah".
Ya zura hannu a aljihunsa ya fito da key din motarsa ya dam'ka a hannuna.
Ya ce "Na baki motata! Duk 'kasar da kike so zan kai ki, zan saya miki bangle din gold."
Da karfi na ce "Bana so! Duk ka had'awa amaryarka, Ni kuma ka bar mini abina tunda kofar 'Dan-agundi ne".
Ya tunzura ainun ya ce "Haka kike da kafiya? Ba kisan rarrashi da ban ha'kuri ba?"
Na ce "A wajen ka na koya".
Ya zauna ya dafe kansa, yana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.
A kausashe ya ce "fa'da mini me kike nufi da nine Halima?
"Ina nufin ka sahale mini, na je na samu wanda zai so ni da dukkan na'kasuna. Tunda a wangale kake jina, 'yar slim kake so, ba Abuskutu irina ba. Na sani zaka sake samo wacce ta yi daidai da taste dinka. Uwar maza ba uwar 'ya'ya mata Irina ba. Don haka nima ka bani damar da zan samu wanda ya dace da ni".
Ina rufe baki ya dinga fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" da 'karfin gaske.
Shudewar mintina goma muna haka. Ya dago muka ha'da ido, duk jijiyoyin kansa ta fito ta yi ru'du ru'du.
Na dauke idona daga kallonsa.
"Ba zan iya rabuwa da ke ba, na baki ha'kuri, manyanmu sun baki.
Me yasa zaki tsananta irin haka, me yasa ba zaki ha'kura ba?"
Kai tsaye na ce "saboda ban san ha'kuri ba, ban kuma iya shi ba."
A hankali ya ce "Ban san wata halitta a doron 'kasa da ta zarta ki ha'kuri da *Yakana(Takori)* ba."
"Cikin ido na kalleshi na ce "A da ne! a lokacin da nake tsananin son ka, nake tsananin son na rayu da kai.
Amma a yanzu babu sauran ha'kuri a tsakaninmu tunda na gane baka so na, bani da mutunci a idon ka.
Na riga na fa'da maka, na ha'kura da komai.
Na fa'da hawaye yana silalowa daga idona"
Cikin rauni sosai ya ce "Don't do this to me Halimatu! Ina son ki, ina son na rayu da ke, ki taimake ni ki yi ha'kuri.
Zan miki wani al'kawari da zan dauwama ina ro'kon Ubangiji ya bani ikon cika miki shi matu'kar kika yafe mini".
Na gallah masa harara na ce "Ri'ke al'kawarinka idan ka auro Fauziya sai ka yi mata. Ni kam ba abin da nake so daga gareka irin ka sahale mini, ko na sha'ki iskar da babu takura a ciki.
Sanin kanka ne akwai wadanda suka fika dacewa da ni, kamar yadda na fahimci ban dace da kai ba a yanzu".
Ya zuba mini ido sosai yana jin wani irin tashin hankali na kekketa shi.
Bakinsa na rawa ya ce "Ni kika fa'dawa hakan? Ni ko Guduyo?"
Ba kunya na ce "Eh".
Ya mi'ke ya sake fita. Ni kuwa ko ka'dan ban ji tsoron abin da zai biyo baya ba.
Ban tashi a wajen ba, ya sake shigowa! Ya shige dakinsa.
Yayin da tunanin da nake yi ya dinga kutso mini.
Ba abin da nake bu'kata irin na samu lokaci irin haka na cigaba da hakaito al'amuran da na fuskanta.
# Team Gudale#
# Team Guduyo#
# Surayya Dee✍️.
# Ana tare 🤝.
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
*Na fa'da muku kuwa mai sirrin kayan *G.H.T. mai sau'kin farashi fiye da na sauran jakadun su?*
*Faseelat ta kware wajen gyaran amare da nagartattun supplement marasa illah.*
*Tana da supplement din dagargaza infection .*
*Tana da maganin ulcer da na basir*
*Haka nan tana da mayukan da suke gyaran fata.*
*Tana da supplement masu narkar da kitse, masu daidaita shape din mace *.
*Tuntu'be ta a wnanan lambar dan Karin bayani 07039269802*.
*SDK*
*45-46.*
*Gudale*
Kai tsaye gida ya koma, ya karya, sannan ya yi wanka ya rufe gidan ya doshi cikin gidansu.
A falo ya tarar da Umma, tana karyawa.
Ba wani walwala ta amsa gaisuwarsa.
Cike da kulawa ya ce "Umma menene? Tun shekaranjiya nake ganin ki a haka".
Kai ta girgiza alamun babu komai.
Ya matsa kusa da ita sosai, ya ce "Dan Allah Umma bana son wannan yanayin da nake gani a tare ke"
Ya fa'da cikin rauni sosai.
A hankali ta ce "Gudale tun ba'a je ko ina ba ka fara canja mini? Sai ka kwana ka yini baka leko ka ganni na ganka ba! Idan na ce za'a karbe mini kai, ka ce mini ba hakan ba, amma a 'kasa da kwanaki ashirin ka fara mance uwarka.
Wannan ne alwashin da ka yi mini?
Na ce maka kar ka yi kuskuren ta'ba yarinyar nan, amma alamu sun nuna ba ka ji maganata ba".
A hankali ya ce "Ina nan akan ra'ayina Umma! Ina tabbatar miki ba abin da ya faru, ina sake jaddada miki ba wanda zai sha gaban ki a wajena, balle har a sa na manta ki.
Zan kuma tabbatar miki da gaskiyar maganganuna nan gaba ka'dan. Ki daina damuwa Ummah".
A hakan Abba ya shigo ya same su. Ya zauna yana jin da'din yadda yake ganin nutsuwa tana ratsa Gudale.
Ya dinga farin-ciki! A ransa yake raya da ya san aure zai sa ya nutsu haka da wuri ai da tuntuni ya yi masa.
Ya mi'ka masa file, hannu biyu Gudale ya sanya ya karba.
Abba ya ce "Jarrabawar daukan ma'aikata zaka je F.I.R.S. ranar laraba mai zuwa.
Ya yi godiya, sannan ya ce "Akwai wata jarabawar ma da zan yi a Lagos satin sama, a sani cikin addu'a ba'a san inda za'a dace ba".
Addu'ar kuwa duka iyayen nasa suka dinga jero masa.
Tsawon lokaci suna tare kafin Abba ya fice ya barsu.
Sai da Abba ya Jima da fitar, Gudale ya numfasa ya ce "ki kwantar da hankalinki Umma! kwanan nan zan tabbatar miki bana son Guduyo, ba kuma zan zauna da ita ba".
Murmushin jin da'di ta yi! Sannan ta ce "Ni kuwa zan tsaya maka dan ka samu cikar burinka. Bana fatan ha'da iri da zuri'ar gidan mai Ashafa".
Suka rabu cikin farin ciki.
Ganin lokaci ya tafi ya sanya ya zarce massalaci dan gabatar da sallar azahar.
Ana idarwa ya koma gidansa.
Sai da ya kunna talabijin sannan ya kwanta a doguwar kujerar falon.
Ya kalli agogo da ya nuna 1:33pm ya ja tsaki sosai ya furta "Ko sai yaushe zata dawo?"
A ransa yake ayyana da ace tana gida da yanzu an kammala masa abincin da yake son ci.
Amma yanzu, yana gida matarsa tana waje da sunan karatu.
Wani irin abu ya tokare shi da ya tuna hijabin Guduyo bai hana aga tudun kirjinta ba.
Abin da yake ki'dima shi a tare da ita.
Yana son ya gansu a zahiri. Sannan ba abin da ya tsana tun fil'azal irin ace bata gida.
Ko ba maganar arziki za su yi ba, yafi son ya ganta a gida. Balle kuma yanzu da take amsa sunan matarsa.
Ya sake jan tsaki mai tsananin gaske tamkar yana tare da ita dan ta fahimci halin takaicin da yake ciki.
Kamar daga sama ya ji an turo 'kofa ha'de da sallama.
Ya yi bakam tamkar mai barci.
Ganin hakan ya sanya na wuce dakina a hankali dan kar na tashe shi.
Sallah kawai na yi, na fito zuwa kicin.
Hidimar abinci na hau yi, ba jimawa gidan ya karade da 'kamshi.
A nutse nake yin komai. Bansan ya tashi ya haye sama ba.
Ina cikin shirya abincin akan dining na ga ya sauko da alwalarsa.
Na bu'de murya na ce "Sannu da gida! Na dawo ai kana barci".
A lalace ya ce "sannu da asibiti"
Ya yi wucewar sa.
Na yi sallah, na koma na hau aikin snacks tunda na fridge ya kare, shi kuma yafi son su akan abinci mussaman da daddare.
Ban samu kaina ba sai wajen biyar.
A gurguje na yi wanka, na shirya, sannan na zuba abinci na dawo falo.
Ina ci ya shigo hannunsa da leda baka.
Na karba tare da cewa "Sannu da dawowa".
Ya zauna yana ta kumburin da ban san dalilinsa ba.
Na cigaba da cin abincin.
Ya gaji ya ce "tashi ki wanko mini! Banda dai ke yar wula'kanci ce na kawo abu, amma ki kasa budewa ki ga menene a ciki?"
Na ajiye plate 'din hannuna na mi'ke, da ledar ina cewa "Yi ha'kuri".
Na bu'de na ga yalo da 'data ne.
Na wanko na zubo a bowl na ha'do da ruwa na kawo masa.
Sai da na kammala cin abincin.
Ya kalleni ya ce "Banga kin dauko yalon ba?"
Na girgiza kai na ce "Basu dame ni ba".
Ya kuwa tunzura ya ce "Dole su dame ki, domin suna rage kitse! Kin san kuwa ke cinsu ya kama".
Na ce "Hakane" a gajarce.
Na mi'ke da nufin barin falon.
Ya ce "kar ki sake ki barni a zaune".
Na koma na zauna, na kasa cewa komai.
Ya 'kan'kace ido ya ce "fado mini hakkokin miji akan matarsa".
Na yi shiru!
Ya ja tsaki ya ce "sai ki fa'da mini me da me kika yi a Asibitin?"
A hankali na ce "karatun da na je koya shi na yi kawai".
Ya girgiza kai ya ce "kuma yanzu dan kawai Nasara asarar duniya sun yi galaba akan musulmai. Kika iya tsayawa gaban maza a haka, suna kallon surar 'kirjin ki cikin munafukin hijabin da bai hana komai bayyana ba.
Alhalin ni da na biya sadaki bani da 'kimar da za'a nuna mini su. Ai wallahi 'karshen cuta an yi mini, sai dai fatan ta zame mini kaffara".
Kaina ya daure, na zuba masa ido sosai sai na ga tamkar mai jin barci.
Gaba'daya idonsa ya jirkice. Zuciyata ta dinga harbawa da sauri da sauri a dalilin zargin da ya tsananta a zuciyata.
Ba komai make zato ba illah a buge yake domin maganar tasa tafi dace wa da wanda yake cikin maye.
Ban da haka yaushe zai yi zaton ni ce zan nemi ya kalli wani abu a jikina mussaman 'kirjin da budurwa ta fi 'boyon sa a jikinta.
Maimakon da ya ji na yi shiru, shima ya bar maganar sai kawai ya sake cewa "Tashi tsaye ki cire mini rigarki na ga yadda suke.
Idan kuma zaki fa'da mini yadda suke da bakinki to".
Na rasa inda zansa kaina.
Na kasa tashi, haka na kasa ce masa uffan.
Ya kalle ni ya ce "kin san Àllah sai kin za'bi daya! ko dai ki cire riga na gani da kaina, ko kuwa ki fa'di yadda suke da baki".
Idona ya ciko da hawaye na ce "Bana son irin haka Yaya Sadik".
"Idan ma Yaya Abubakar zaki ce Wallahi sai kin yi 'daya a cikin biyu".
Na goge 'kwallar da take zuba.
Na ce " ai ni bansan yadda zan kwantanta su ba."
"Then sai ki cire mini rigar".
Na fara kuka sosai.
Ya tabe baki ya ce "ko bubburwa zaki yi sai kin bi umarnina Wallahi".
Jin rantsuwar da ya yi ya sanya na ha'diye kukan na ce "Bani hasken yadda zan kwantanta su din".
Ya numfasa ya ce "Ban da mugunta ki bu'de su to kawai mana".
A hankali na ce "Ba zan iya ba".
"Ooh to sai ki yi wanda zaki iya 'din".
Ya fa'da a banza ce.
Cikin daurewar fuska na ce "manya ne kamar kan jariri".
Ya zungudo ya ce "wanne irin description ne wannan?
Kinga Malama bayani sosai zaki yi mini, zubin mangwaro ne ko lemon za'ki, ko kuwa zubin kwakwa ne?".
Na zum'bura baki na 'ki yin magana.
Ya tunzura ya ce "To na ma fasa bayanin, ganinsu zan yi".
Na yi kamar ban ji ba.
"Kin ji"
Ya fa'da da karfi.
"Eh" na amsa masa a gajarce.
"To Bismillah! Mi'ke domin ba a zaune