Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sabo da Kaza Complete Hausa Novel by Surayya Dahiru

Author :  SURAYYA DAHIRU Category :  African Stories & Novels

Chapter   55 / 61

162K to 165K   out of 180.1K words

a idona.
Ban ta'ba yi mata kallon raini ba, ko dan wannan mu bar maganar nan a tsakaninmu. Bata sani ba, ba a gabanta na zageta ba, da wanne idon kike son na je gabanta na tsugunna na ce ta yafe mini na zageta? Kada ki zubar da k'imar uban yayanki a idonta, ke zaki iya mantawa amma har abada ita ba zata manta ba. Ki yi ha'kuri."
Baba ya ce "Tunda ke da shi kuka yi, ya ajiye dukkan girman kai ya durkushe a gabanki, to ki karbi tubansa".
Na yi shiru tabbacin na yarda.
Yana durkushen ya ce "Baba a sake mini lamini, wata biyu ya mini yawa Billahillazi ba zan iya ba, kema kin sani. Ba dan Abba ya ja kunnena kada na ajiye aikina ba. Da sai na ajiye na biki Gusau din. A yanzu hakan adalcin shugabannin ne ya saka ba'a kore ni ba. Tun batan ki bana iya yin komai.
Ki ji tausayina Guduyo".
Ana kuma Baba yaki tankawa. Amma akan tilas sai da Gudale ya sanya ya ro'ke ni na rage masa
Tsananin nacin da ya sanya Baba a gaba ya sanya ya ce "Tunda na kafe, to ya barni na yi wata a wajensa na sake hucewa. Kuma tabbas ba zai bawa kowa ni ba sai mahaifiyarsa kamar yadda na bu'kata."
Wannan hukuncin ya yiwa Gudale tsauri matu'ka gaya.
Amma Baba ya ce "sai anyi hakan.".
Mu koma falo aka cigaba da nasiha da ban ha'kuri.
Gudale ya bawa Baba ha'kuri, tare da Yayar Kwalli.
Washagari kuwa Baban Gusau ya tafi da ni bisa rakiyar Yaya Abbas.
Ai sai Yaya Gudale ya mayar da Gusau tamkar unguwa.
Ko tunanin aikinsa ba ya yi.
Duk weekend acan zai yi duk kuwa da ba kulashi nake yi ba.
Umma ta shiga tashin hankalin ganin Gudalenta a cikin tashin hankali gaba'daya ya birkice bashi da lokacin zama da ita.
Iyakacinsa da ita ya leka a gurguje ya gaisheta. Kullum yana tafe a titi.
Hatta Aman idan ya shigo baya bi takansa, wani lokacin yana kuka amma zai wuce ya bar shi.
Kuka saosai Umma take yi tana gasgata an haukata mata Gudale ta yadda idan babu Halimatu a tare da shi ba zai amfani kansa ba, bare waninsa ya amfane shi.
Hatta a wajen aikinsa an bashi quairy.
Amma bai shiga taitatayinsa ba.
Satina uku Baban Gusau ya tausaya masa kwarai da gaske, ya nemi na yi masa afuwa idonsa cike da k'walla akan na yarda na koma dakina hakanan dan Allah.
Bashi Zan duba ba, na duba Allah na duba ubansa".
Jikina ya yi sanyi na ce "Na ha'kura zan koma, amma ba dan na huce ba".
Domin ni kaina mamakin kaina nake yi, na yadda aka cire mini ko da son ganin Gudale bare na zauna da shi.
A ranar Baba ya tabbatar masa ko gobe Umma ta zo zata taho masa da ni.
Jiki na rawa yake godiya.

*Umma*
"Dan Allah Umma, ki ji tausayina mana"
Gudale ya fa'da idonsa cike taf da k'walla.
Ta kufula ta ce "Duk wannan susucewar da ka yi ba zai sanya na tashi na tafi uwa duniya dan na dauko maka irin tsiya ba.
Ashe duk iskancin da nake ganin a tare da yarinyar nan ka'dan ne?
Ni zata yiwa hakan?
Waton sai na kada billena zata zauna da kai, to dan kan uwarta kar ta zauna da kai, ina ce "kanta ta yiwa asara"
Akan Guduyo! Gudale babu jarumta sai kawai ya fashe mata da kuka riris yana cewa "Allah a turo mini mala'ika Azara'ilu ya tafi da ni, dan darajar Annabinka. Uwata da matata sun ki yi mini uzziri. Zuciyata na ciwo, tunanina yana rikecewa, idona na zafi, yunwa tana neman kassara ni. Ubangiji a yanke mini wannan ukubar haka nan. Allah na tuba. Wayyo Mala'ika Azara'ilu ka zo ka kaini wajen Abbbana".
Tsoro ya yi matu'kar kama Umma ganin yadda yake birgima a dakinta.
Tausayi da rauni irin na uwa ya shigeta.
Ta fashe da kuka ta ce "Allah ka yi wannan shari'ar da kanka. Wula'kanta da ake yi, ake bina da alkaba'i Ubangiji ka tausaya mini, ka shiga cikin al'amarin.
Tashi ka daina wannan addu'ar, Gobe Direba ya kaimu tunda ka zabi wata a kaina, rashin Halimatu ne zai sanya ka nemi mutuwa ka bar ni. Na gode maka"
Ya sake kece mata da kuka.
Yana fa'din "Ba hakan bane Umma! Ki fahimce ni, bana ha'da ki da kowa Wallahi.
Amma Guduyo a kusa da ni shine kwanciyar hankalina. Ki ji tausayina"
Ta yi kwafa ta ce "Ai shikenan tana mika masa Aman tare da cewa "Karbe shi ya ji duminka kun taru kun mayar da shi maraya, me za'a yi da azzalumar yarinya irin Halimatu.
Safiyya mai fa'da da ke ya ci riba ba dai mutum ba, sai bakaken aljanu. In Sha Allah sai kin tsokano fadan da za'a kai ki kasa tunda ni kin gama da Ni".
Akan dole ta bi shi zuwa Gusau.
Tun a mota yake ta ro'konta Allah da maaiki, ta yi magana mai nuna biko zata yi masa a gaban Baban Gusau.
Ta taimaka ta samar masa kwanciyar hankali.
Ta numfasa ta ce "Ban da dai an ga bamu da Abba ta yaya iyayenka zasu kasa yi maka biko sai ni uwa?"
Ta goce da kuka tana fa'din "Baka share mini kukana ba Gudale. Duk gatan da nake yi maka,baka huce mini takaicin duniya ba tunda kake son jinin Safiyya har hakan.
Makiyana kake so, sune farin cikinka. Wannan na cikin babbar jarawabata.
Da ana mutuwa a dawo da Alhaji ya yi kallon yadda yan'uwansa suka bar ni da kai.
Kuma da a gaban mahaifinta take Wallahi da sai dai ka ha'diye zuciya ka mutu da ba zan je ba, tunda su din butulu ne masu manta alkhairai.".
Ha'kuri kan ha'kuri yake bata.

**
Da hantsi suka iso.
Sun jima ita da Baba a falo. Sannan aka kira ni.
Na gaisheta ta amsa ba yabo ba fallasa.
Baba ya sake bani ha'kuri, Yana ta fa'din na cigaba da ha'kuri, sannan wancan sharudan akansu zamu zauna, mu mutunta junanmu.
Umma ta numfasa ta ce "Allah ya kiyaye gaba".
Muka kamo hanya har muka iso Kano ba um ba um um a tsakaninmu.
Da la'asar muka iso, maimakon ta raka ni k'ofarmu sai kawai ta yi shigewarta wajenta.
Nima kuwa na bita, ina ayyana matu'kar bata raka ni da kanta ba, to kuwa bata shirya zamana da d'anta ba.
Haka har dare ina dakina na wajenta.
Gudale ya zo yafi sau a kirga ko kallonsa bana yi.
Zuwan da ya yi da daddare Wanda a kiyasi zai yi daidai da shigowarsa dakin sau goma.
A sanyaye matu'ka da gaske ya ce "Me kike nufi ne Guduyo?
Ki yiwa Allah ki zo mu tafi gidanmu.
Komai zaki yi mini, na fi son na ganki a dakinki, ki mini alfarmar hakan".
Rai a bace na ce "Tunda na biyoka ai na yi maka sassauci.
Amma na rantse ba zan bika ba.
Ba kai ne zaka mayar da ni ba".
Ya fita da sauri, sai gashi da Antin Zaria da ke tana hutun shekara.
Har da su Amna ta zo sai dai suna gidan Anti Maimuna.
Fadi yake bata ha'kuri Anti! Ki raka mini ita".
Ta ru'ko ni jikinta tana cewa "Ya aka yi ne autarmu?"
Ina hawaye na ce "Ni Umma ce zata raka ni".
Ta mike tana fa'din "Je ka fa'dawa Mamanka abu mai sau'ki kenan.
A gigice ya ce "Bata da lafiya fa Anti! Shin ba ke ce second Mum dina ba. Me yasa ba zaki dinga taimkona ba?"
Ya fice a har gitse.
Sassafe sai gashi da Yaya Abdallah.
Akan ya ro'ke ni ya mayar da ni.
Gaba'daya ya birkice ni sai nake ganin ya jima ko wanaka bai yi ba. Ya yi zuru zuru tabbacin baya cin abinci da gaske.
Duk wani gayu da kwalisar nan babu.
Gaba'daya babu jituwa tsakaninsa da Umma. Fishi take yi masa, ta hanyar yi masa zuru.
Sai a lokacin na gane hatta Aman din da ya makalashi a ransa bashi da lokacinsa.
Idan ya shigo dakin da nake, ya dinga cewa "So nake ki koma dakinki na dauko miki su Afrah ki ga yadda suka girma, suka koma tamakar y'ay'an larabawa."
Uffan bana ce masa.
Ya rasa yadda zai yi. Yayin da Umma ta ja ta kafe, tunda ta je har Gusau ta kada billenta to daga haka ba inda zata kuma zuwa.
Ya fara wani irin zazzabin tashin hankali.
Rannan sai ji na yi Umma tana waya da Sakina tana fa'din "sun zuba mini ido ita da yayarsu Antin Zaria kenan zan kassara mata zuciyar Gudale.
Indai ita din uwarta ce ta zo ta mayar da ni ta huta da wannan jarabar tunda ita ce uwar dakina, kuma kanwa uwar gami.
Ta k'are da fa'din "Wallahi Sakina ki yi kokari ki rabu da ni lafiya".
Ban ji me take cewa ba ita Anti Sakinan.
Ai kuwa tana dawowa daga aiki sai ganinta na yi.
Tana shigowa dakina ta d'aure fuska tamkar bata ta'ba dariya ba.
Ta ce "Tashi na mayar da ke, idan kin so ki cigaba da ri'ke mutuncin da aka taru aka nema miki, idan kuma kin ki kije ya kallalame ki, ki koma Yar gidan jiya.
Kiyi masa biyayya, ki kyautata masa, amma kada ki yarda da cin mutunci ko da na magana ne bare zagi ko duka".
Na fashe da kuka ina cewa "Kada ki mayar da ni."
Nan da nan ta rantse da cewa "Yau kam indai na isa a dakinki zaki kwana, abin da zai biya baya kuma, na kara nemar wa kanki Karin daraja yana hannunki, ai ke ba yarinya ba ce."
Haka ta tisa ni a gaba, ina kuka har cikin dakina. Tsabar yadda na tsani koma wa Gudale ya sanya na ji a zuciyata Sakina son kai ta nuna. Alhalin itama uwarsu ta matsa mata.
Inda muka tarar da shi a falon, yana ganinmu da Sakina.
Ya mike da kyar yana cewa "Na huce da Sakina. Na yafe miki."
Ta ja tsaki ta ce "Dan Allah kada ka yafe mini. Ban da Umma ta roke ni arzikin na rako maka ita, kai ka isa ma ka ga k'afata a gidanka?"
Ya kasa yin shiru ya ce "Tunda kin rakota ai magana ta kare. Yadda kike shiga al'amarin gidana ki hana ruwa gudu, na kai wannan k'arar gaban Mahaliccinmu.
Amma ki sani idan wannan jinyar da nake yi, ta zama ajalina ke ce silah Sakina. Allah ne shaidar yadda nake tsananin son ki. ke kuma fir kin bantse mini, kin k'i ni, kin tattara kin watsar da ni.
Ya karyar da murya ya ce "Ke da Abba wallahi! Ai ya ce kada a yanke mini zumunta".
Ga mamakina sai na ga jikinta ya mutu murus. Ta kasa ce masa komai.
Ta fita tana cewa "Allah ya sauwake ya tashi kafadunka."
Duk nacinsa ya kasa samun hadin kaina.
Ba irin da'din bakin da bai mini ba, amma ban saurareshi ba. Duk yadda ban kula shi ba,sia da ya samu sau'kin jikinsa tabbacin zulumi yafi yawa a jinyar.
Washagari ya tarar da ni a dakina, ina ganinsa na fito na bar masa dakin.
A sanyaye ya biyo ni harabar falon.


*Assalamu alaikum*. *makaranta littafin Sabo da kaza barkanmu da yini.*
*Ina Yaba muku, Ina kuma gode muku Ubangiji ya fini yabawa.*
*Ina son ku koma ku karanta shimfi'dar labarin shafin farko kenan, daga nan sai ku karanta 19&20.*
*Sai Kuma ku karanta 41&42 da Kuma 43&44.*
*Sannan Ina jiran Jin ra'ayin ku ta yadda zan gina karshen duk kuwa da ba zan mika alkalamin a hannunku gaba'daya ba. Domin ina rubutu ne akan abin da yake faruwa ba wai abin da muke son ya faru ba.*

*Zan dakata har zuwa sanda zan k'irga yawan ra'ayinku, dan nasan ta yadda zan bullo wa al'amarin*.

*Ina cikin hidima mai yawa kanina dan-uwana zai yi aure a Wannan satin, ina neman addu'arku*.
*Na gode sosai*
*Surayya Dee ✍️*
2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Shin kina bibiyar Faseelat kuwa?*.
*Shin kina gyara kanki kuwa?*
*Faseelat ta kware wajen zaba miki supplement din da zai dace da jikin ki*
*Hakan ya sanya ta samu lambar yabo daga G.H.T*.
*Tuntu'beta 0703929802*
*Gudale dai ya ce zaki rabauta a sanadinta*

*Fatana alheri ga*
*Aliyu Dahiru (Abba)*
*Da*
*Safiyya Ahamad Sani*
*(Malama)*
*Allah ya sanya albarka a rayuwar aurenku*.


*Ina godiya ga dukkan wadanda suka kira ni a waya/WhatsApp suka mini murnar auren kanina, da tambayar jikina.*
*Na gode sosai Ubangiji ya saka muku da alheri*


*SDK*
*95&96*
Ana kiran sallar azahar ina sauke doguwar ajiyar zuciya, saboda kammala hakaito badakalar da na shiga.
Kafin na yi yun'kurin tashi. Ya fito cikin shirin fita masallaci ko kallon inda nake bai yi ba. Na bishi da kallon yadda yake ha'da ha'da hanya.
Na idar da sallah Kenan na shiga kicin da nufin d'ora girki, ko su Afrah zasu shigo mini.
Ina kicin din ya dawo.
Murya kasa kasa na ji yana kirana.
Na wanke hannuna na fito bayan na amsa.
Ya kalle ni ya ce "Tunda kin kwashe kayanki a gaban ma'aikin Allah. Dauko mayafinki muje gaban Baban Yara.
Ai na ro'ke shi ya baki ha'kuri. Tunda bai ro'ke ki ba, muje ya ro'ke ki a gabana. Na gaji, ina nufin koluluwar gajiya na yi Guduyo. Ina jiye miki tsoron kada ha'kurin da nake ta yi dan ki huce ya kwace mini."
Na ja k'aramin tsaki na ce "Ya jima bai 'kwace ba".
Ya girgiza kai ya ce "zo ki shige mu je".
Yana rufe baki na ce "Wallahi ba inda zan je. Ai ni Baban Gusau ne babana".
Nan da nan fishinsa ya sauka ya ce "Ma sha Allah! Tunda sarkin adalci ne Babanki maganar ta kare. Domin kuwa a gabanki zan kira na fa'da masa tsiyar da kike shuka mini duk da irin ha'kurin da ya yi ta baki."
Na gallah masa harara na ce "Kai ko kunya baka ji, motsi ka'dan sai ka kai k'ara?"
Ina rufe baki ya ce "To ya zan yi ne Guduyo? Ai tunda kika ha'da kai da Sakina na sani sai an mayar da ni tamkar yaron tumari. Me za'a yi da wuyar zama irin na Sakina?
Gaba'daya babu tausayi bare imani a sha'aninta, na rantse bata siffantu da aikin jinya ba, tunda aiki ne na masu taushin zuciya da imani. Babu abin da ya kamace ta irin jami'ar tsaro, ta yadda halinta na ba sani ba sabo zai yi tasiri."
Na bata rai na ce "lallai baka canja ba, ba kuma zaka canja ba, tunda kake yiwa Maman Nana irin wannan wula'kancin akan idona. Idan da gaske kana sona, ka kuma shirya daina cin mutuncina ai dole kuwa ka girmama dukkan ahalina. Sakina ai surukarka ce tunda kake aurena".
Ya kame baki yana cewa "Subutul kalam ne. Ai kirkin Sakina yawa ne da shi. Ita ta dawo mini da ke, madallah da ita."
Ganin da ya yi na biye shi muna magana sai ya bijiro da maganar da ta dame shi.
Ya sassauta murya ya ce "Guduyo kina lissafin adadin watannin da na yi ni ka'dai kuwa?
Wai ke ba kya kewata ne?"
Na bata rai na ce "Bana yi! Har menene abu mai da'di a tare da kai da zan yi kewarsa?"
Maganar ta yi matu'kar dukan zuciyarsa.
Har hakan ya bayyana akan fuskarsa.
Ya yi karfin halin cewa "Bani da abin arziki ko ka'dan a wajen ki ko?"
Nan da nan na ce "Na tsiyar yafi yawa, ya kuma fi tsananta.
Ka riga ka yiwa kanka illah a zuciyata".
Ya juya ya tafi yana kunkunin shi ba zai yarda ya zama sauna a gidansa ba.
Domin shi da Yunus din Sakina ba d'aya bane.
Na bishi da ido ina tabbatar wa kaina akwai abubuwan da dole sai dai na yi ha'kuri amma ba zai ta'ba barinsu ba, barin zance da son girma na kan gaba.
Na shirya abinci. Na leka na ce "Na gama abinci, na ajiye maka maganinka, sannan akwai supplement na GHT da Anti Sakina ta aiko maka na ulcer ne.
Kamar ba zai amsa ba sai ya ce "Kin ji da'dinki Guddi. Ace wai har yau da kika shafe shekaru a dakin aure baki fahimci cewar a ko ina nake zan iya samun abinci ba?
Baki fahimci kuma cewar duk abin da zan ci matu'kar bani da nutsuwa a zuciyata ba zai yi tasiri ba?"
Na yi sakare ina kallonsa.
Na nisa na ce "Jiyan nan na ji kana fa'dawa Sakina akan ta sani na dinga yi maka girki. Na yi din amma ban yi gwaninta ba?"
Ya ta'be baki ya ce "Da hira kika zo mini dakin nan da nafi yaba miki, da na fi gode wa."
Na fito Ina fa'din "Maman Nana dai ta ce kada ayi wasa da supplement din nan idan aka sha akan ka'ida za'a rabu da ulcer in sha Allah.
Madallah da Faseelat 07039269802, da kayanta na GHT. Domin sau'kin kayanta da ingancinsu ne k'ashin bayan rubibinsu da ake yi.
Ni kaina har murmushi na yi a dalilin har da nawa supplement din Sakina ta hado mini a wajen Faseelat.
Ga kuma femwash na oriflame a wajen Aisha lame 07036662633. Da sauran kayan gyara na mussaman.
Na yi tsam ina nazarin irin soyayyar da Sakina take yi mana ni da Gudale.
Komai ta yi amfani da shi na gyaran jiki, sai ta siya mini ko sai ta saka na yi.
A zahiri ni take gyarawa. A bad'ini kuma k'aninta take yiwa tanadin hutu da nutsuwa.
Amma shi da yake kullum a karkace yake sai ya fi karkata a so take yi ta mayar da shi lusarin namiji a gidansa. Komai Zan yi masa matu'kar bai yi dai-dai da ra'ayinsa ba sai ya ce Sakina is behind everything am doing.
Ya fito da kyar yana tafiya ya zauna a wajen cin abincin, ya kalle ni ya ce "Zuba wa miji abinci bauta ne, ko rashin yanci ne shima?
Me zai hana kina ganin na fito ki zo ki yi serving dina?
Allah dai ya yafe miki Guduyo".
Ko kula shi ban yi ba, a dalilin na fahimci so yake ya shiriritar da fishin nawa.
Bayan bai bani mukullin motar ba, bare ya siya mini bangle din gold din da kuma fita wajen da ya yi kirarin zai yi Kai ni. So nake kawai ya dauke ni mu barwa Umma gidan na dan wanai lokaci.
"Ki shirya yanzu ki je gidan Sakina.
Anjima zan zo."
Na ce "To ba dan na fahimce shi ba, sai dan bana son doguwar magana a tsakaninmu sannan dama ina son zuwa gidanta.
Ina gidan Sakina ta dawo daga aiki.
Ba jima wa sai ga wayarsa yana cemin ya iso.
Na ce "Ba zaka shigo bane?"
Da sauri ya ce "Daga zuwan farko sai kawai na shigo gidan mutane?"
Kaina ya daure. Na kasa cewa komai, fahimtar da ya yi ban fahimci manufarsa ba.
Sai ya ce "Ki yi ha'kuri na zo ban sanar miki ba.
Na kagu na zo na ji muryarki mai

55 / 61